Showing 21001 words to 24000 words out of 88612 words

Chapter 8 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

16 Aug 2025

8304

13

***


WASHE GARI

Cikin ikon Allah Aynu ta wayi gari lafiya k'alau kamar ba tayi ciwo ba.

"Umma gaskiya maganin nan yana da kyau kinga k'unar hannun sab'a takeyi har ta warke
kenan?".

"To masha Allah haka ake so ai, Allah ya k'ara lafiya".

"Amin Ummata".

Sallamar Babanta ce ta katse su daga hiran da suke ya shigo ya nemi waje ya zauna, Aynu tayi
masa sannu da zuwa tana mai mik'ewa domin kawo masa kunu da k'osansa na karyawa, taje
ta d'auko ta ajiye a gabansa ya bud'e kwanun ya kurb'i kunun kafin ya dubi Aynu yana fad'in.

"Ya k'arfin jikin naki?".

"Naji sauk'i sosai Baba".

"Allah k'ara lafiya, haka akeson ji dama".

"Amin Baba".

"Yau ba zaki je gidan Sarkin ba ne?".

Ummanta ta fad'a tana mai duban gefan da Aynu ke zaune, Aynu ta d'an yatsina fuska kafin
tace.

"Ban jin fita wallahi yau Umma ki bari har gobe naje".

Babanta yayi murmushi yana fad'in.

"Kiyi zamanki ki huta 'yar gidan Umma ki k'ara samun sauk'i sai kije".

"To Baba".

Baban nata ya sake dubanta karo na biyu fuskarsa fal murmushi yana yinsa da komai Aynu ta
d'auko kama ce kawai ta d'auko ta Ummanta kamar antsaga kara.

"Ina Umar Faruq kuwa Aynu?".

"Ohh Baba Ya Sayyadi Umar wai? yana nan".

"Yaron na da kirki sosai kullum ya ganni har k'asa yake gaishe ni yauma fitar nan da nayi kinga
naira d'ari biyar ya bani wai ayi cefane, nayi-nayi ya barta amma yak'i dole na karb'a".

Aynu tad'anyi murmushi tana wasa da yatsun hannunta take fad'in.

"Ai yana da kirki sosai akwai shi da kyauta ko a islamiyya".


"Bashi ne nake gaya maka yazo har gidan nan wancen satin ya gaishe ni ba".

Umma ta fad'a tana mai wasa da sandar hannunta.

"Ai inaji araina kamar akwai wani abu da yaron yake b'oyewa".

Cewar Baba kenan yana mai kallon fuskar Aynu cike da murmushi, itama murmushin take duk
da kuwa fad'uwar gaban da taji ya tsanan ta a cikin zuciyarta, haka kawai taji hiran ta fara
gundurarta tamik'e tsaye tana fad'in.

"Bari ingyara d'aki Umma".

Ta wuce ta barsunan suna ta tattaunawa, daga k'arshe sukabar hiran Ya Sayyadi Umar aka
koma ta Yarima, Aynu duk tana jinsu tayi luf a d'aki domin duk cikin su babu wanda take ji
hirarsa nayi mata dad'i, sun jima suna hirar kafin Baba yamik'e ya fita waje yabar Umma nan
zaune.

Sai sannan Aynu ta fito domin sama musu abin da zasuci da rana kuma.



°°°

Yarima kuwa ranar wuni yayi yana zuba idon ganin Aynu amma har dare shiru, haka ya wuni
kamar mara lafiya jama'a da dama suna d'auka alhinin rasuwa ne, amma anashi b'angaren
abun da yakeji aransa game da Aynu shiyafi komai d'aga masa hankali da kuma mamaki.


Har ya yanke shawaran zuwa k'ara dubota domin ya zaci ko ciwon ne har yanzu ya hanata

zuwa, amma sai dai ya share domin bayaso zak'ewarsa tayi yawa ta rai na shi.

Hakan na d'aya daga cikin abin da yasa Yarima k'in yin soyayya duk cikin shekarun da suka
wuce, domin shi mutum ne mai son girma mai son a girmama shi baya son raini ko kad'an, a
ganinsa da zaran ya furtawa budurwa yana sonta to raini zai iya shiga ciki shiyasa yake kau da
kansa akan duk wata 'ya mace.
Amma kuma abin mamaki sai gashi rana guda ya kamu da son 'yar aikinsa kuma 'yar miskinai
so mai tsanani kuwa, duk da yasan abune mawuyaci Aynu ta rainashi domin yarinyar nada
tsoro sosai duk da k'arancin shekarunta ya fahimci yarinyar nada hankali da nutsuwa da sanin
ya kamata, uwa uba kuma ya yaba da tarbiyarta, ba kamar sauran 'yan matan da suke son
saba.


Murmushi yayi yana mai dafe kansa da yaji yana masa ciwo kad'an-kad'an, ya san hakan na
faruwane sabida rashin ishash-shan bacci da kuma hayaniya domin shi baya son hayaniya ko
kad'an shine dalilin da ya sama yake wuni a d'aki abinsa.

Maganin da ke aje gefan katifarsa ya d'auka yana mai bud'e robar faron da ya aje gabansa
yasha maganin ya koma ya kwanta nan da nan kuwa bacci yayi awon gaba dashi. (ASUBA TA
GARI YARIMA).


***

Washe gari tun da wuri kaman yanda ta saba tayi dukkan abin da ya kamata ace tayi kafin ta
tafi, tayiwa iyayenta sallama ta kama hanya domin yau alhamis suna azumine bata tsaya bata
lokacin neman abincin safe ba.

Ko da ta biyawa Zainab harta tafi sai sannan taga lokaci ashe har takwas ta kusa setting
agogonta ya goce kenan? ta gaida Babah Tasallah ta fito a gurguje ta nufi gidan domin bata
son yin late ko kad'an.

Bata tsaya ko ina ba sai cikin falon Yarima Fudhal tayi mamakin ganin falon fes dashi kamar
jama'a basu zaunaba kai tsaye cikin d'akinsa ta nufa da sallamarta ta tura k'ofar d'akin tasa kai.


Yana kwance abinsa lullub'e da bargo ya takure waje guda kaman mai jin sanyi hakan yasa ta
kashe AC dake ta famanyi ita kad'ai a d'akin har lokacin baccinsa ya ke hankalinsa kwance bai
ma san ta shigo ba, ta wuce toilet tahau aikinta har ta gama bai farkaba ta fito tashare d'akin ta
goge amma bai ta shiba ta wuce falon ta sake sharewa ta goge, ta lek'a d'akin taga baccinsa
yake har lokacin ta dawo falo ta zauna, ganin baccin nashi bamai k'arewa bane yasa ta fito
daga part d'insu zuwa cikin gidan.

Taje tayiwa Jakadiyya gaisuwa tare da Uwar soro, sannan ta wuce wajen Fulani Sokoto tana
shiga cikin falon ta tadda Fulani zaune tare da Yarima Jalil da Jalila suna ta hiransu ta durk'usa
ta gaishe su tare da yi musu gaisuwa, shi kuwa Yarima Jalil tun da tashiga ya kafeta da idanuwa
ko k'iftawa ba yayi, ciki-ciki Fulani ta amsa ki dan taga ba 'yar aikin wajenta bace? Oho.

Aynu ta mik'e ta fito daga b'angaren ta nufi wajen Fulani Bingel itama falon cike ta taddashi
tayi musu gaisuwa suka amsa Fulani na fad'in.

"Kwana uku kenan ban ganki ba, ko k'unarce ta dameki?".

"A'a k'una ta warke ma banajin dad'i ne dai, sai yau naji dama-dama".

"Allah k'ara afuwa".

"Amin".

'Yan d'akin suka amsa banda Aunty Sa'ida da take ta faman banka mata harara ita dai Aynu
kanta na k'asa batama san tanayi ba.

Aunty Sadiya ta dubi Fulani da murmushi tana fad'in.

"Wannan ce Aynul-hayat d'in?".

"Ehh ".

Fulani ta bata amsa, murmushi ta ya fad'ad'a a fuskarta tace.

"Kai amma taci sunan nata wallahi Hajiya".

Ita ma Fulani murmushi tayi tana fad'in.
"Sosai kuwa".

Aynu ta mik'e tana fad'in.

"Zan koma aiki".

Ta fice daga d'akin suka bita da kallo, Aunty Sa'ida taja tsaki.

"Kai wallahi Aunty Sadiya da kayan haushi ki ke !, meye wani abin kyau anan yarinya bak'auya
yar talakawa".

"Ke ! banson jin wannan sha shancin anan kinji ko ina ruwanki to".

Aunty Sa'ida taja tsaki, tare da cizon leb'e.

Fulani tace "Allah ya shiryeki Sa'ida meye wani abu ajikin talaka da har zai zama abin k'i, ka
da insake jin wannan maganar abakin ki".


Tafiya take kanta ak'asa tana wasa da yatsun hannunta sai ji tayi anjata gefe guda ta d'ago kai
da sauri domin ganin waye?, ajiyar zuciya tayi tare fad'in.


"Zainab kin ban tsoro wallahi !".

Zainab tayi murmushi taja hannunta gefe guda suka zauna tana fad'in.

"Ke kinsan abin da yafaru kuwa?".

"A'a sai kin fad'a !".

Aynu ta bata amsa, Zainab ta cigaba da fad'in.

"Gaskiya Aynu Yarima na sonki sosai, bakiga yanda hankalinsa ya tashi ba kwana biyu da baki
zoba".

Tsaki Aynu taja kad'an tare da fad'in.

"Amma ke kam kin fiye zato wallahi !, daga kinga ya shiga damuwa sai ki ce akai nane,
mutuwafa akai musu kuma kinsan yanda suka shak'u da ita fa?".

Zainab abin ya bata dariya sosai ta kanne tana fad'in.

"Ba wani wallahi, shifa ya nemeni na bashi kwatancen gidanku, kuma wallahi bakiga yanda
hankalinsa ya tashi ba sanda nace masa baki da lafiya, sai da yaji ciwon kai kike sannan naga
hankalinsa ya d'an kwanta ko bai zo gidan naku ba ne?".

Aynu shiru tayi tana duban Zainab har sai da Zainab tad'an zungureta sannan ta dawo daga
tuanin da take.

"Dama a wajenki yasan ciwon kai nake?".

"Ehh mana, yazo gidan naku kenan?".

"Ehh yazo da dare har da magun guna da kayan snack ya kawomin".

Zainab ta fad'ad'a murmushinta cike da sonjin bayani .

"To mai yace da ke?, fad'amin dan Allah yace yana sonki ko?, ki ke wani b'oyemin !".

"Sai kiyi kuma !, ke kam kina da matsala wallahi, ke nifa ko yace yana sona banjin zanso mutum
irin sa".

"Sabida me?".

"Haka kawai".

"Aynu kenan ke kam baky fahimta wallahi".

"Ehh naji kinga mubar wannan maganar, kinsan kuwa Ya Sayyadi Umar sai faman zarya yake a
gidanmu nifa har ya fara bani tsoro".

"Meye na tsoro kuma?, ta tsuniyar gizo dai bata wuce k'ok'i, amma nidai nafi sonki da Yarima
!".

Zainab takai maganar tana dariya, Aynu ta mik'e tana turo baki wai ita adole fushi tayi ta wuce
tabar Zainab nan zaune, ganin da Zainab tayi da gaske tafiya za tayi shine yasa ta mik'e itama
ta bi bayanta da sauri tana kiran sunanta, amma Aynu ta toshe kunnuwanta tayi tafiyarta.


Ko da ta koma d'akin ya farka daga baccin yana zaune gefan katifarsa ya had'a kai da gwiwa,
da sallama ta shiga d'akin ya d'ago da sauri yana dubanta, sai kuma ya kau da kai gefe guda
kamar bayason ganinta a can k'asan zuciyarsa kuwa farin cikin ganinta ne fal ransa.


Har gabansa tazo ta durk'usa tana gaisha shi ya amsa can k'asan mak'oshi, Aynu ta d'an gyara
zamanta sosai tana fad'in.

"Ya k'arin hak'uri kuma?, nagode sosa da kulawa, nazo na tadda kana bacci ne shine nak'i
tashinka fatan banyi laifi ba?".

Bai ko kalle taba bare ya nuna mata ya san dashi take magana, bata damu ba ta cigaba da
fad'in.

"Ko kana buk'atar wani abu ne?".

Shiru yayi na wani lokaci kafin yabud'e baki a hankali ya fara magana kamar wanda ake yiwa

dole.

"Kije falo".

Aynu tamik'e ta fito falo ta zauna tana jiran fitowarsa, ya shafe kusan mintuna talatin kafin ya fito
falon sai faman tashin k'amshi yake cikin wani farin yadi mai shara-shara ana iya hango singlete
d'insa ta ciki baisa hulaba illa taje sumarsa da yayi takwanta luf yaune karo na farko data ganshi
cikin kayan hausawa tun dawowarsa.
Ya zauna gefan kusun yana duban Aynu, can ya kau da kansa ya mai dashi kan screeng d'in
wayarsa da ke ringing.

SAIMA DARLING


Yagani bisa screeng d'in wayar tasa yasa hannu ya d'aga ahankali tare da sanyata a headfree.

Daga can b'an garen tanaji ya d'aga tahau fad'in.


"Haba Yarima !, ashe yanda na d'auke ka baka d'aukeniba!, mai yasa kake wulak'anta mai son
kane?".

"Sabida banayin abu a rufe".

Ya bata amsa, cikin d'aga murya kad'an tace.

"Kamar ya kenan?".

"Kamar yanda ki kaji na fad'a".

"Ok amma mai yasa tun ran birthday d'inka baka nemeni ba, ni ina nan ina zaman jiran
kiranka".

"Na manta ne".

Daga can b'arin Saima ajiyar zuciya tayi, domin ba kad'an takejin ciwon maganar da Yarima
keyi mata ba duk da tanajin dad'in sautin muryarsa, ya katseta da fad'in.

"In kin gaji zan aje wayar?".

"A'a kawai banajin dad'in reply d'in kane".

"Time d'in breakfast d'ina yayi zaki iya kira anjima?".

Ya kashe wayar ya ajiye gefe, duk maganar da yake idonsa na kan Aynu yana karantar
yanayinra, ita kuwa kanta na k'asa tana wasa da wani d'an k'aramin zobe kod'ad'd'e dake
hannunta.


Duk tanajin maganganun da suke amsar k'arshe daya bayar da kuma kashe wayar shi yafi
komai bata mamaki da Yarima, amma data tuna waye shi?, sai mamakinta ya kau domin tasan
zaiyi fiye da abin da yafi haka indai Yarima ne, b'an garan jiji da kai, girman kai da d'agawa ga
shegen miskilanci da wulak'anci tun da take bata tab'a ganin mutum irin yarima ba abin nasa
yayi yawa.

Ya katseta da fad'in.


"Yau wannan banjin zata zo?, inaga zan koreta aiki ne kawai !, jeki kawomin breakfast ".

*YARIMA FUDHAL*


Na
FIRSAUSI S.A(QURRATUL-AYN).



NAGARTA WRITES ASSOCIATION®


SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.


Wannan page d'in naki ne *Ashnurpyar* Nagartacciya Allah yabar zumunci amin.



14


BAYAN KWANA BIYAR


Zaune take can gefe daga inda yake yanata aikin danne dannan wayarsa, tafiya take sonyi

amma ya hanata ko da fita cikin gidan ne.


"Zo nan Aynu".

Taji muryarsa yana kiranta tamik'e ta k'arasa wajen da yake zaune nesa da shi kad'an.

"Matso mana".

Ta d'an kuma matsawa kad'an, murmushi yayi yaga alamun bata da niyan zuwa kusa dashi
mik'ewa yayi yazo daf da ita ya mik'a mata wayar hannunsa yana fad'in.

"Kalli ki gani".

Aynu takai dubanta bisa screeng d'in wayarsa wata farar mace ta gani kyakykyawa ajin farko
tana sanye cikin alkyabba pink data k'ara bayyanar da kyanta.

"Gimbiya Safiyya kenan".

Ya fad'a yana mai duban fuskarta.

Murmushi tayi Aynu tare da furta.

"Amma ta had'u sosai tayi kyau wallahi".

Yarima Fudhal ya kafeta da idanuwa yana dubanta kafin yad'anyi murmushi kad'an.

"Ita ce ake son had'ani aure da ita !, nan da 3days zatazo gidan nan, amma ni gaskiya bana
sonta !".

"To amma kuma kake ajiye hotonta?".

"Meye ra'ayinki akanta?".

Ya tambayeta ba tare daya bata amsar tambayar ta ba, Aynu ta dube shi da murmushi saman
fuskarta.

"Ta dace da kai sosai kuwa".


"Uhmmm haka ki kace?".

"Ehh mana".

"Wannan zab'in iyayena ne, amma ni bata daga cikin zab'ina".

"Sai kabi zab'in iyayen naka ai, domin nasan basuyi maka zab'in tumun dare ba".

Tsaki Yarima Fudhal yaja yana mai duban Aynu cike da takaicin amsar da take bashi, dubanta
ya sakeyi a karo na biyu yana fad'in.

"Bawai na nuna miki bane domin ki bani shawara akan zab'in da zanbi, na nuna miki ne
domin.......".

Sai kuma yayi shiru maganar ta tsaya a mak'okwaronsa, dai-dai da shi gowar Saima ya d'auke
dubansa daga kan Aynu ya karb'i wayarsa tare da fad'in.

"Tashi kije".

Aynu ta mik'e da sauri ta fice dama ta takura da al'amarin Yarima sosai, Saima ta bi bayanta da
kallon tuhuma, har sai da Aynu ta fice sannan ta dawo da kallonta kan Yarima tana fad'in


"Kana buk'atar wani abu ne?".

"A'a jeki kawai".

Ya bata amsa batare daya dubeta ba.


DARE
8:20PM


Da dare misalin k'arfe takwas da mintuna ashirin Aynu na zaune bisa tabarmar da tayi sallah
gama cin abincinta kenan akai sallama tare da fad'in.

"Wai Aynu tazo inji Yarima".

Dammm gabanta ya buga har sai da tad'an lumshe ido tare da karanto addu'a cikin ranta afili
kuwa ta furta.

"Yarima kuma !, me zaiyimin da daren nan?".

"A'a tashi kiji tunda kiga mutum ya tako har inda kike yazo yana da abun da yakawo shi mai
muhimmanci ne musamman manyan mutane ai sai da babban dalili suke zuwa wajen mutum".

Umma ta fad'a tana mai duban inda 'yar tata take zaune duk da ba gani take ba.

Aynu tayi ajiyar zuciya gami da tashi daga cin abincin dama ta gama ta wanko hannu ta zari
hijabi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login