Showing 60001 words to 63000 words out of 88612 words
Chapter 21 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
toilet domin ɗauro alwala wayarta tahau ringing hakan yasa tayi
saurin ɗagawa domin ba k'alamin faɗuwar gaba taji ba alokacin aranta ta furta.
"Ko waye ke kirana da asubar nan Allah yasa dai lafiya?".
Tayi maganar tana mai ɗaga wayar tare da karawa bisa kunnanta.
Daga can ɓangaren aka amsa da faɗin.
"Hello Hajiya lafiya kuke kuwa?".
"Lafiya ƙalau Sadiya wani abune ya farune naga kiranki da asubar nan?".
"Wallahi Hajiya hankalina ya kasa kwanciya ne tun jiya da dare nake kiran wayar Fudhal baiyi
picking ba, yanzuma sai da na kira amma bai ɗaga ba".
Fulani take taji gabanta ya tsananta faɗuwa amma ta daure ta bata amsa da faɗin.
"May be yana bacci ne, idan ya farka nasan zai nemeki".
"To amma dai Hajiya kisa adubo shi".
"Insha Allah bari inyi sallah".
Fulani ta katse wayar tare da shigewa toilet a can kasan zuciyarta kuwa addu'a kawai take ta
faman zubawa domin tasan cikin kwanakin nan kaf baya cikin nutsuwarsa ita al'amari nasama
bakaramin tsoro yake bata ba.
A gaggauce ta ɗauro alwalar ta fito ta shimfida abin sallah ta tayar da sallah.
Ta nayin sallama ta fito daga ɗakin domin zuwa dubo Fudhal sabida zuciyarta ta kasa jurewa.
Gidan shiru babu kowa har ta isa part ɗin nasu, kofar ɗakinsa buɗe dan haka kai tsaye ta sanya
kai cikin falon ta nufi bedroom ɗinsa tana sa kai ta hangoshi kwance tsakar ɗakin sai
nunfarfashi yake sama-sama da gudu ta karasa wajen tana faɗin.
"Subhanallahi...! Baka da lafiya Magaji?".
Ta karasa Kansa kenan ta ɗago shi sai ga Anwar ya faɗo ɗakin shima shine ya taimaka mata
ya miƙar dashi tsaye sai lokacin suka lura a she aman jini yake yi da basu lura ba da yake
dumm light ne a ɗakin da sauri sukayi waje da shi Anwar ya sanyashi a mota sannan ya juyo ya
kalli Fulani yana faɗin.
"Bari in wuce da shi asibitin kafin ki sanar da Mai Martaba domin yana bukatar taimakon
gaggawa".
Bai jira jin amsartaba ya shige mota yaja da gudu yabar harabar gidan, Hajiya ta koma ciki da
sauri kai tsaye shashin Mai Martaba ta nufa ta Sanar dashi halin da ake ciki.
Nan da nan aka tashi driver suka bi bayan Anwar.
Anwar bai tsaya a ko inaba sai a NANAH KHADIJAH PRIVATE HOSPITAL kai tsaye
Emergency aka nufa dashi.
Anwar ya kasa zaune ya kasa tsaye sai safa da marwa yake, a haka su Mai Martaba suka
taddashi abinka da masu gari office ɗin Babban Doctor aka kai Mai Martaba ya zauna tare da
Hajiya idan banda addu'a babu abin da ko wanne daga cikinsu yake yi cikin ransa.
Likitoci sun shafe tsayin a wanni biyar akan Yarima Fudhal kafinsu samu nasarar dai-daita
numfashinsa dake barazanar yin bankwana da duniya.
Babban likitan ya fito yana share gumi ya nufi cikin office ɗinsa inda ya barsu Mai Martaba na
zaman jiransa.
Ya bude wani file yayi ƴan rubuce-rubucensa kafin ya ɗago kai yana binsu da kallo ya bude baki
a hankali yana faɗin.
"Ya akayi kuka bari yana wasa da bin ƙa'idojin shan magani?, nasan kunsan illar dake tattare
da ciwonsa, ga kuma damuwa daya sanyawa ransa da yawa Wanda yin hakan na daf da Ku iya
rasashi baki ɗaya".
Mai Martaba da Hajiya bin Doctor kawai sukeyi da kallo domin basu fahimci maganarsa ba.
"Amma Doctor mene kake magana akai haka?".
Cewar Mai Martaba kenan yana mai bin fuskan Doctor ɗin da kallo.
"Kamar ya?, kuna nufin kuce bakusan ciwon dake damun ɗanku ba?".
Doctor yayi maganar yana mai jingina a jikin kujerar da yake kai, tare da ƙare masu kallo ɗaya
bayan ɗaya.
"E gaskiya bamu sani ba, amma kada kaga laifinmu abisa hakan domin ba anan ya girma ba".
"OK a takaice dai ɗanku na ɗauke da ciwon zuciya ne wanda ya kai matakin ƙarshe da zai iya
rasa ransa".
A tare Mai Martaba da Fulani Bingel suka mike, Fulani inbanda innalillahi wa'inna ilaihi razi'un
babu abin da yake fita daga bakinta.
Anwar dai na gefe ya rasa abin da zai ce sosai yake jin tausayin Yarima Fudhal cikin ransa.
Doctor ya buɗe baki ya cigaba da faɗin.
"Ku zauna insha Allahu babu wata matsala munsamu dai mun dai-dai ta tsayuwar nunfashinsa,
amma munaso musan dalilin daya haddasa masa wannan ciwon, sannan kuma munaso musan
WACECE AYNUL-HAYAT?, da dukkan alamu soyayyartace ta jefashi cikin wannan yanayin?
sabida bakinsa babu abin da yake furtawa sai ita".
Anwar dake tsaye gefe neman guri yayi ya zauna yana mai lumshe idanuwansa da sukeyi masa
zafi sosai, yanason yin magana amma ya gagara furta ko kalma ɗaya.
"Doctor ciwon ya jimane a jikinsa ?".
Cewar Fulani kenan tana mai goge kwallar dake kokarin zubo mata.
"E to a bincikenmu ciwon ya kai tsayin shekaru goma zuwa goma sha uku".
Shiru office din ya ɗauka naɗan wani lokaci kafin Anwar ya katse shirun da faɗin.
"Nasan dalilin ciwon nasa !".
Nan Anwar ya bawa Doctor labarin dalilin samun ciwon zuciyarsa ya kara da faɗin.
"Aynul-hayat da kaji yana faɗi itace yarinyar da yake so, kuma sonta ne dalilin tsanantar ciwon
nasa".
Doctor yayi shiru tsayin wani lokaci suna kallonsa kafin ya fara rubuce-rubuce cikin file ya
ɗago yana kallon Mai Martaba.
"Duk yanda za'ayi indai kuna son ɗanku to dole ne idan ya farka ya fara tozali da abin da ya
sakashi a cikin wannan halin idan kuwa ba haka ba zan iya cewa sai dai kuyi hakuri da shi !".
Cikin fushi Mai Martaba ya mike yana faɗin.
"Kana nufin inje innemawa Magaji auren ɗiyar mutsiyata?, ina bazai yiyuba duk yanda zakuyi
kuyi amma auren Magaji da wannan yarinyar bazan taɓa lamunta ba".
"Kayi hakuri Mai Martaba halin da yake ciki zamu duba..!".
"Dakata Doctor...! Ni bana magana biyu, ina roka masa Allah ya bashi lafiya amma aure babu
shi da waccan yarinyar ko bayan raina".
Yana faɗin haka ya saka kai ya fice daga office ɗin, Anwar da Doctor suka bi bayansa da kallo,
Fulani kuwa nan tayi zaune tana sharar kwalla.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdausi Jeebour.
36
Doctor ya dawo da dubansa kansu Anwar tare da ajiyar zuciyar yana faɗin.
"Gaskiya Hajiya kusan yanda zakuyi Ku nemawa Yarima Fudhal abin da yake so, domin yin
hakanne kaɗai zai iya taimakawa wajen cetonsa daga halin da yake ciki sai kuma addu'a wadda
ita yafi buƙata a halin yanzu".
Anwar ne yayi ƙarfin halin faɗin.
"Zamuyi ƙoƙarin ganin munshawo kan Mai Martaba insha Allahu, yanzu zamu iya zuwa mu
ganshi?".
"A a sai dai ko zuwa gobe idan Allah ya kaimu munga yanda yanayin jikin nasa zai kasance,
yanzu zaku iya tafiya gida".
Ya kai maganar yana mai miƙewa domin fita daga office ɗin, Anwar da Hajiya suka take masa
baya.
Sai da ya kai Hajiya gida sannan ya wuce gidansu.
Tun kafin Hajiyarsu Fudhal ta dawo labarin ciwon Fudhal ya baza cikin gidan, tana Shiga
falonta aka fara zuwa gaisuwa tare da gamba tambayar jikin Fudhal.
Ɓangaren Fulani Sokoto kuwa bazaka iya tantance halin da take ciki ba farin ciki ko baƙin ciki
?, amma anawa hashashen zan iya cewa Fulani Sokoto farin ciki ne fal cikin ranta akan ciwon
Fudhal domin tana ganin kamar mutuwa zaiyi idan kuwa babu fudhal magajin sarauta dole
Yarima Jaleel ne , sai dai tsananin damuwar da Yarima Jaleel ya jefata shike danne farin cikin
da take ciki.
Mai Martaba kuwa ranar ko fada bai zauna ba idan banda safa da marwa babu abin da yake a
falonsa, a wannan halin ne Fulani Bingel ta taddashi ta nemi guri ta zauna shima ya zauna ba
tare da kowanne daga cikinsu ya furta ko kallama ɗaya ba.
Daga can Fulani Bingel ta katse shirun tana faɗin.
"Amma ina ganin kamar hukuncin daka yanke akan ɗanka yayi tsauri, kada ka zamo ɗaya daga
cikin iyaye masu tauye haƙƙin ƴaƴansu daya rataya a wuyansu, kasan dai Magaji yaro ne mai
ladabi da biyayya Wanda baya tsallake dukkan dokar da muka kafa masa, amma ya kamata
sau ɗaya dai shima ka bashi dama ya samu farin cikinsa, kamar yanda ya kasance yana faranta
mana tsayin shekarun, kayi hakuri idan na faɗi kalma ɗaya data ɓata maka rai ka gafarce ni na
barka lafiya".
Fulani ta miƙe tana mai ficewa daga ɗakin, tabar Mai Martaba nan zaune kamar ta jona masa
wutar lantarki, a can kasan zuciyarsa yasan gaskiya ta faɗa sai dai shi bayajin a ransa zai iya
jure haɗa zuri'a da jinin talaka".
Al'amarin Yarima Jaleel kuwa ranar wuni yayi a ɗaki baiko leƙo waje ba inbanda bankawa
Kansa kayan maye babu abin da yake yi ya zama tamkar wani mahaukaci hakan yasaka bai
San wainar da ake toyawa ba a cikin gidan.
" Wai Hajiya mai yasa Magaji ba zai iya haƙura da yarinyar nan bane?, tunda Abba ma baya
so sai kace dole?".
Cewar Sa'ida kenan, Aunty Sadiya dake zaune gefe tana shirya 'yan biyunta tayi murmushi
kafin ta bata amsa.
"Kema dai Sa'ida kamar baki san al'amarin so ba?, ko kaɗan bana ganin laifin Magaji ina
tausayawa rayuwarsa sosai wallahi, Abba mahaifine agaremu amma shine da laifi daya hakura
anyi auren nan da duk hakan bata kay ba da nasan babu wanda zai san Magaji nada ciwon
Zuciya".
"Ni kuwa kinsan abin da yake bani mamaki Aunty Sadiya?".
"Aa".
"Cewa da akai sanadin ciwon akan matsalarsa da iyayenta ne, abin da yafaru tsayin shekaru
dasu ka wuce sai kuma gashi ya mace akan son ɗiyarsu".
"Babu wani abin mamaki da ikon Allah Sa'ida, domin Allah baya yafe laifin wani akan wani,
mahaifinku yayi kuskure Sosai awancen lokacin sakayyace kawai take bibiyarmu amma har
yanzu ya gaza fahimtar hakan, ".
Fulani Bingel ta bata amsa tana mai share kwallar dake kokarin zubowa daga befan idonta,
Jalilah dake zaune gefe tana jinsu tana son cewa wani abu amma babu dama, hakanne ya
sanyata fashewa da kuka musamman idan ta tuna irin ƙiyayyar da suke masa su da
mahaifiyarsu sai gashi shine yafi kowa damuwa da ciwonta.
Mikewa tayi da gudu ta fice daga falon ta nufi part ɗinsu tana Shiga kai tsaye ɗakinta ta wuce
ta faɗa kan gado tana mai cigaba da rera kukanta sai da tayi kuka mai isarta kafin ta mike ta
shige toilet ta wanko fuska ta dawo tana mai zama gefan katifarta tayi ta gumi tana aikin
tuananin neman mafita akan wannan al'amarin.
A can ƙasan zuciyarta tana son warwarewa Abban nasu wata sarkakiya sai dai tana gudun jawa
mahaifiyarsu tsana a gun Mai Martaba da kuma yan'uwansu tare da tsoron yanda Mai Martaba
zai ɗauki batun.
Tun da aka kwantar da Yarima Fudhal ko dan yatsansa baya iya motsawa domin baima San a
duniyar da yake ba, yana rayene amma kamar matacce ban-bancinsa da matacce ɗaya ne
shine numfashi ko numfashinma ta computer dake gefansa ne kawai zaka kalla kasan yana da
rai.
Ranar dasu Aunty Sadiya sukaje babu wanda baiyi kuka ba cikinsu musamman Jalilah
rungumeshi tayi tana aikin kuka har sai da aka janyeta.
Ranar suna dawowa basu wuce ko inaba sai part din Abbansu domin su roƙeshi ya sauko daga
dokin naƙin da ya hau, amma fafur yaƙi daga ƙarshema korarsu yayi dukansu suna kuka suka
baro falon nasa, sai bayan fitarsu kuma jikinsa yayi sanyi sosai hardai daya tuna maganar
Aunty Sadiya ta ƙarshe kafin ya koresu.
"Abba kayi hakuri dan Allah bawai munzo ne akan dole ka yarda Magaji ya auri wacce baka so
ba, munzone akan ka taimaka kaje ka ganshi koda sauɗayane domin yana bukatar addu'arku
sosai, ya kamata ka janye daga fushin da kake da shi ko yasamu wani sassaucin na ciwon
nasa, sabida fushin iyaye babbar masifa ce ga ɗansu".
"Bayan haka Abba ka gafarce ni abisa abin da zan fada yanzu duk da nasan dole maganar
zata ɓata maka rai".
Shiru tayi naɗan wani lokaci kanta a ƙasa kafin ta cigaba da faɗin.
"Abba mene dalilinka naƙin talaka haka?, talaka baya da gata aduniya ne?, shin talaka ba
mutum bane kamar kowa?, Shifa Ubangiji babu ruwansa da talaka ko mai kuɗi, sarki ko malami
shugaban kasa ko gwamna yaro ko babba duk ɗaya suke a wajen Allah ban bancinsu kawai
shine Wanda yafi tsoransa, Abba kasani shifa arziki da mulki ba madogara bane domin ko babu
mutuwa akwai tsufa Abba, a matsayinka na shugaba idan baka kyautatawa al'ummar da kake
mulkaba taya kai ma zakayi tunani Allah zai kyautata maka, Abba......".
"Ke...! Dakata kinfi ni sanin haka ne?, ko kuwa kinaso ki nunamin kinfini sanin ya kamata,
Fudhal ɗa nane nike da iko inyanke dukkan hukuncin da naga dama akansa, Ku tashi Ku
ɓacemin da gani sha-shan yara kawai...".
Yana zuwa nan ya runtse ido sosai yaji ransa na suya da ɗaci akan abin da ya aikatawa ƴaƴan
nasa, sai dai shima baya da masaniya akan dalilin da yasa yake musu hakan, amma har ga
Allah yasan gaskiya ta faɗa.
"Mene dalilina akan tauyewa ƴaƴana haƙƙin abin da suke so?".
"Son zuciya...!".
Ya bawa kansa amsa, girgiza kai yayi cike da takaici, yana daga idonsa kasan carpet yayi to zali
da wata takadda yasa hannu ya ɗauka ya buɗe a hankali rubutu ya gani ciki da bayan
takaddar, haka kawai yaji aransa ya kamata ya karanta domin ya ji abin da ta kusa.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S. A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-NAMESY PHIRDAUSY JEEBOUR.
37
Ga abin da wasiƙar ta ƙunsa.
"Assalamu alaikum.
Abba ina mai baka haƙuri akan abin da zan faɗa bana fatan ko kalma ɗaya tasanyaka fushi sai
dai fatan ka fahimce ni, kayi hakuri Abba ka yafewa Fudhal kasa ni shi dan Adam ajizine baya
da masaniya akan abin da zai aikata domin komai ya faru ga bawa dama can rubutacce ne,
Abba ni na sani dukkan abin da yake faruwa tsakanin Fudhal da Jaleel akan Gimbiya Safiya
wallahi Abba sa hannun maƙiya ne kayi haƙuri ka fahimci ko wanne daga cikin su ka daure kaje
ka dubo Fudhal kaga halin da yake ciki bawai ina faɗin ka amince masa da auren wacce baka
so ba a'a fatana kaje kaga halin da yake ciki may be zaka iya sanin hukuncin da zaka yanke
akan haka.
BISSALAM".
Sarki Ubaiyd ya karanta wasiƙar kusan sau biyar tare da shafe tsayin lokuta yana jujjuya
wasiƙar sosai jikinsa yayi la'asar, yayin da ƙasan zuciyarsa ke azalzalarsa da ƙin yarda da batun
sai dai yayi nasarar yaƙar kasan zuciyartasa ɗari bisa ɗari.
WASHE GARI
Washe gari tun misalin ƙarfe bakwai Fulani Bingel da Fulani sokoto suka shirya domin zuwa
dubo halin da Yarima Fudhal yake ciki.
Jalilah ma ba'abarta a baya ba, domin da kanta ta Shiga kitchent ta ɗanyi masa girki mai
ruwa-ruwa yanda mara lafiya zai iya ci.
Fulani Bingel ta dubeta sai faman tiri tiri take da kwandon kayan abinci guntun murmushi tayi
kafin ta dafa ka faɗarta.
"Jalilah girki ki kayi masa ne?".
" E Hajiya ".
"Ayya baki San haryanzu bai dawo haiyacinsa ba?, baya cin komai Jalilah mai da abincin kizo
mutafi".
Takai maganar dai-dai sanda driver yayi parking a gabansu suka shiga Jalilah kuma ta bawa
ɗaya daga cikin dogarawan dake yawo a farfajiyar gidan kwandon kayan abincin ta shige mota
itama suka tafi.
Ko da suka isa asibitin can suka tadda Aunty Sadiya tuni ta jima da zuwa ma, Aunty Sa'ida ce
sai bayan da sukaje sannan ta je ita ma.
'Yan dubiya ne suka fara sallama daga wannan ya fita sai kaga wasu sun shigo duk da cewa
ba'a aganinsa sai dai ka leka ta glass ɗin windown ɗakin da yake kwance kamar gawa ansanya
masa oxygen babu wani abu dake motsi a jikinsa sai saitin zuciyarsa da ake iya ganin
bugawarta ya rame sosai kai kace yayi shekaru irin biyun nan a kwance.
Mai Martaba na kishingiɗe bisa kusun Jakadiyya tayi sallama a ruɗe ta shiga tana mai zubewa
kasa tare da faɗin.
"Mai Martaba Yarima Jaleel fa na daf da rasa hankalinsa yayi Marisa sosai Yallaɓai...!".
Mai Martaba miƙewa yayi bai jira