Showing 51001 words to 54000 words out of 88612 words
Chapter 18 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
numfashinsa da ke barazanar d'aukewa, hakan ya
sanyashi yin shiru ya mai da idonsa ya rufe yana fitar da wani irin numfashi mai zafi.
Sosai tausayin Fudhal ya kama Anwar sai binsa da kallo kawai yake, mutumin da in banda
Mahaifiyarsa bai d'auki mace wani abuba arayuwa, yau gashi mace na wahalar da shi kuma
macen ma ba 'yar gidan kowa ba 'yar talakawa, shi da ya d'auki soyayya kamar shirme ko
hauka yau gashi a kanta yana neman rasa rayuwarsa, dama bahaushe yace komai lokaci ne
abin da kake rainawa wata rana shine zai baka tsoro.
Yarima Jaleel ne ya shigo falon yana fad'in.
"Broda anshirya Jalilah inji Momy".
Sai lokacin Fudhal ya sake bud'e idonsa daya kad'a yayi jajir ya dubi Jaleel tare da fad'in .
"Ku wuce kawai zan biyoku a baya".
Jaleel ya fice daga d'akin cikin sauri domin jiransa suke a mota.
Bayan fitar Jaleel Yarima ya shafe tsayin lokuta ba tare daya mik'e ba, da k'yar dai ya mik'e ya
shige bedroom nasa domin ya d'an watsa ruwa yabar Anwar zaune a falo.
Cikin mintuna kad'an sai gashi ya fito cikin k'ananun kaya duk da cewa ba wani tsayawa yayi yin
gwalli ba hakan bai hana kyawunsa da b'oyayyar damuwar dake kwance k'asan fuskarsa
baiyana ba, Anwar ya jefawa key d'in mota tare da fad'in.
"Tashi mu tafi".
Anwar bai ce komai ba yamik'e yabi bayan Fudhal don shi tuni yayi waje abinsa.
Suna isa asibitin Jaleel da Momy na zaune zaman jiran zuwansa, bai tsaya wani b'ata lokaci
ba ya nufi d'akin da aka kwantar da Jalilah domin gwajin da za'ayi mata.
Sun shafe kusan a wanni uku zuwa hud'u duk abin da ya kamata ayiwa Jalilah anyi amma
hakan bai sanya angano takamai-mai abin a yake damunta ba, abin da result ya bayar kawai
maleria ke damunta.
Ko da Fudhal ya fito ya had'a zufa sosai ga kuma kansa dake matsanancin sara masa, bai bi
takansu Momy ba kawai office nasa ya wuce yana goge gumin da ke tsatstsafo masa, ya zauna
kan kujera tare da k'aro sanyin A.C da ke office d'in, ya kwantar da kansa kan kujerar tare da
lumshe ido yana aikin daya saba.
Turo k'ofar da a kayi ne tare da kiran sunansa ya sanyashi d'ago kai yana mai k'are masu kallo,
Anwar da Jaleel suka zauna akan kujerun da ke gaban table d'in Yarima suna mai binsa da
kallo suma.
"Lafiya Yarima ya jikin Jalilan?".
Anwar ya jefa masa tambaya, Yarima ya gyara zamansa tare da janyo file d'in Jalilan yana
dubawa can ya rufe yana mai mayar da kallonsa kansu.
"Al'amarin ne yake d'auremin kai Anwar duk iya binciken da mukayi maleria kawai result yake
bamu".
Fudhal yayi maganar murya a sanyaye, Jaleel ya gyara zama sosai yana fad'in.
"Maleria kuma?, ba'a gano dalilin da yasa bata magana ba?".
"Wallahi munyi iya yinmu Jaleel nima abin da yake damuna kenan".
Shiru ne ya biyo baya kafin Anwar yace.
"Kuma ban da maleria babu wani ciwo da ke damunta?".
"E".
"Abin da mamaki fa?".
Cewar Jaleel ya fad'a tare da mik'ewa yana mai cigaba da fad'in.
"Bari inje insanarwa Momy to".
"Zaku iya wucewa da ita gida, nima yanzu zan tawo domin nafara jin fever wallahi".
"Ok Allah yak'ara lafiya sai kun dawo".
Ya fice daga office d'in ya barsu.
KUYI HAK'URI DA WANNAN.
NAGODE SOSAI DA SOSAI MASOYANA MASU BIBIYAR LITTAFINA INA K'AUNARKU NIMA
HAR A ZUCIYATA.
[04/09, 05:00] Hassan Atk: *YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey jeebour.
29
Ya shafe tsayin lokaci a zaune a cikin motar ya rasa abin da yake masa dad'i cikin duniya, ji
yayi baki d'aya bazai iya driven ba hakan yasan yashi fara lalub'en wayarsa domin kiran Anwar
ko Jalil wani yazo ya d'aukeshi amma sai bai ganta ba, sai can ya tuna yabarta agida.
Da k'yar ya iya sanyawa motar key ya kunnata tare da barin layin gidan nasu Aynu.
A wannan lokaci Allah ne kad'ai ya kai Yarima gida lafiya, domin tun kafin ya kai ga k'arasawa
yaji idanuwansa na dishi-dishi har dai yayi parking a harabar gidan ya kashe motar kawai ba
tare da ya cire key d'in ba ya nufi part d'insa, yana shiga falo kuwa ya zube k'asa lokacin
agogon da ke falon ya buga k'arfe sha biyu da rabi dai-dai, da rarrafe ya k'arasa cikin bedroom
d'in zuwa wajen drower da yake adana magungunansa ya nufa ya d'auko ya fara had'iyarsu
d'aya bayan d'aya ba tare da ruwa ba, sai da ya tabbatar ya gama had'iya sannan ya rarrafa ya
d'auko gorar ruwan faro mara sanyi ya sha, a wajen ya zube a kwance.
Tsalle tayi tare da fad'awq kan cinyar Fulani Sokoto tana fad'in.
"Na samo Momy na samo burinmu zai cika Momy".
Cike da murna da garin ciki Fulani Sokoto ta karb'i k'unshin k'asar dake d'aure hannun Jalila
tana fad'in.
"Alhamdulillahi...! lallai Jalila kin cika 'yata nayi murna sosai wallahi, ai da nasan zaki iya da
tun farko aike zan sanya aikin".
Jalila tayi murmushi cike da jin dad'in kalaman yaban da Mahaifiyarta ke yi mata.
Sun shafe tsayi lokaci suna hira kafin Jalila ta mik'e ta nufi d'akinta tana fad'in.
"Asuta gari Momy".
"Mu tashi lafiya Jalila".
Ta shige d'akin ta bar Fulani Sokoto zaune falon cike da murna harta matsu taga gari yawaye .
Aynu kuwa tana shiga gida d'aki ta wuce da gudu ta zube kan katifar dake yashe tsakar d'akin
tana shash-shek'ar kuka, a haka Ummanta ta tadda ita ta zauna zaman lalashinta, Aynu ta d'ora
kanta kan cinyar Umman ba tare da ta ce komai ba, illa sharar hawayen da take kawai
Ummanta na aikin bata hak'uri.
Zainab ita dai daga wajen bata koma gidansu Aynu ba gida ta koma jikinta yayi sanyi sosai
tausayin Yarima yake kamata domin ita ayanzu tafi jin tausayinsa akan Aynun.
"Wayyo Allah na Momy...!".
Jalila ce ya farka daga bacci agigice sai faman zufa take baki d'aya ta rud'e, Momy da ke zaune
falo har lokacin ba tayi bacci ba ta shigo d'akin da gudu tana fad'in.
"Lafiya Jalila..!, Mai ya faru?".
Jalila dake faman muzurai ta k'ank'ame Fulani Sokoto tana zubar hawaye.
"Kinga dan Allah karki damu mafarki kikayi ne?".
Jalila ta gyad'a mata kai domin ta kasa d'aga harshenta bare harta furta wata kalma.
"Aiba komai bane yi shiru kinji, mafarki ba gaskiya bane maza koma kiyi baccin ki babu abin da
zai faru".
Fulani ta kwantar da ita tare da rufa mata bargo tana fad'in.
"Kiyi baccinki 'yata karki damu, da safe mayi magana".
Ta juya ta fice daga d'akin tare da ja mata k'ofa ta rufe, Jalila ta kalli inda agogon d'akin yake
kafe agogon ya nuna k'arfe uku da 'yan mintuna na dare, amma sam Jalila ta kasa komawa
baccin da take sosai tsoro yake ratsata tasan da wuya Mahaifiyarta ta fahimceta.
"Meke shirin faruwa ne?".
Ta furta hakan cikin ranta tare da mik'ewa zaune tana karanto addu'a cikin ranta.
Yarima kuwa tun da yayi wannan zubewar ya kwanta bai tashi farkawa ba, sai da garin Allah
ya waye kusan k'arfe goma na safe ya bud'e ido tare da k'arewa d'akin kallo ya sauke dubansa
kan Anwar dake zaune gefansa ga kuma Doctor Mansur yanata faman aunashi.
K'ok'arin mik'ewa Yarima Fudhal ya hauyi hakan ya saka suka fahimci ya farka, kamashi
sukayi tare da jinginashi jikin pillow, Doctor Mansur ya zauna gefansa yana k'aremasa kallo
kafin ya bud'e baki ya fara magana.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
31
*BAYAN SATI 'DAYA*
Cikin satin abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da kawo kud'in auren Aynu da Ya
Sayyadi Umar yayi kimanin dubu talatin tare da sanya ranar biki wata guda mai zuwa domin
Baban Aynu yace baya son wasu bidi'o'i, shima Ya Sayyadin a nasa b'angarensa abin haka
yake, hakan yasa bak'aramin dad'i yaji ba da yaji hukuncin da Babannata ya yanke a kan batun
auren.
A cikin wannan lokaci ba zaka iya tantance halin da Aynu ta ke ciki ba farin ciki ko bak'in ciki
Allah ne ya baiwa kansa sani sai kuma Aynun kanta.
Yauma kamar kullum tsaye yake jikin bishiyar darbejiyar dake k'ofar gidansu, yana zaman jiran
fitowarta mintuna kad'an sai gata ta fito tana sanye da doguwar riga ta atamfa purple mai ratsin
pink da adon fari ajiki sai ta sanya hijab pink mai hannu bak'aramin kyau kayan sukayi mata ba
duk da cewar ita bak'ace amma hakan bai hana baiyanuwar kyawunta a cikin kayan ba.
Cikin takunta kamar bazata taka k'asa ba ta tako zuwa gareshi fuskarta babu yabo babu fallasa
ta tsaya d'annesa dashi kad'an tare da yin sallama.
Ya Sayyadi ya amsa yana fad'in.
"Barka da fitowa".
"Yauwa barka kana lafiya yasu Umma?".
"Duk suna lafiya sunce a gaishe dake".
"Ina amsawa sosai kuwa".
Tayi maganar tare da yak'e har fararen hak'oranta na baiyana a waje.
"Kinyi kyau sosai Amaryata".
Aynu tad'an rufe idonta da tafukan hannunta tana fad'in.
"Nagode sosai".
Ya Sayyadi Umar ya cigaba da fad'in.
"Yanzu hankalina ya kusa kwanciya Aynu kina daf da zama mata a gare ni dama shine babban
fatana a kodayaushe, gashi kuma inaji araina Allah ya amsa addu'ata".
Aynu tad'anyi murmushi kad'an ba tare da ta ce komai ba illa wasa data hauyi da yatsun
hannunta tana sauraren kalaman da ke fita daga bakinsa wanda a nata b'angaren bazata iya
tan-tance ya matsayin kalaman suke aranta ba.
***
"Wai lafiya kake kuwa Magaji, tun dawowarku ka kwanta anan ka kasa motsi?".
"Wallahi Hajiya ina fama da fever ne kawai".
"Ayya sannu !, Allah ya k'ara lafiya".
"Amin Hajiyata".
"Wai kuwa ya batun ciwon Jalilah?".
Yarima Fudhal yad'anyi ajiyar zuciya kafin yace.
"Nidai narasa gane inda matsalarta ta dosa domin duk iya gwaje-gwajenmu bamu gano taka
mai-mai abin da yake damunta ba result d'inmu kawai maleria yake bamu".
Fulani Bingel tayi shiru tana kallon Yarima cike da kulawa, kafin ta bud'e baki ta fara magana.
"Anya kuwa Jalilah ba gamo tayi ba?, sati guda abu yak'i ci yak'i cinyewa, kasan mutanan
b'oyannan sune ke rik'ewa mutum baki ko k'afa ko hannu ko su toshewa mutum kunne".
"Gamo kuwa Hajiya?".
"E kana mamaki ne?".
"E to zai iya kasancewa, nima abin da nake tunani kenan, amma Hajiya yakike ganin za'ayi?".
"Kuje wajen Mallam Kallah may be a samu addu'o'in da za'a dingayi mata ko Allah yasa a
dace bakin ya bud'e".
"Ok hakanma za'ayi bari zuwa gobe da safe idan Allah ya kaimu sai muje ni da Anwar".
"To Allah ya nuna mana goben lafiya, kaje ka kwanta yanzu ka huta kaji ko".
"To Hajiya sai da safe?"
Yarima Fudhal ya fad'a yana mai mik'ewa tsaye ya nufi b'angarensa domin lokacin k'arfe goma
na dare ne, gidan shiru kowa yayi makwancinsa sai kukan tsuntsaye kawai da ke tashi.
***
Malam Kallah ne zaune bisa buzunsa yana rubuce-rubuce gefe guda kuma almajirai ne
rukuni-rukuni suna tak'ara(karatu).
Yarima Fudhal da Anwar sukai parking motarsu dai-dai rumfar suka fito dukansu zuwa inda
Mallam Kallah ke zaune, sallama sukayi suna masu cire takalmansu suka shiga cikin runfar tare
da rissinawa suka gaishe da shi, Mallam Kallah ya amsa fuskarsa fal murmushi yana mai aje
allon da yake rubutu ajiki ya mai da hankalinsa kacokan kansu Yarima, tare da tambayarsu
mutanan gida da kowa, Anwar yace.
"Duk suna lafiya Mallam".
"To masha Allahu, ya Mai Martaba kuma kwana biyu yajini shiru ko?".
"Yana nan lafiya amma ba shine ya aiko mu ba, munzo ne kan batun Jalilah".
Cewar Yarima Fudhal kenan yana mai gyara zamansa ya fuskanci Mallam Kallah, Mallam
Kallah ya d'anyi shiru kafin ya bud'e baki ya fara magana.
"E nima ina da niyar ziyartar Mai Martaba domin sanar da shi batu a kan ciwonnata amma tun
da kunzo Alhamdulillahi".
"Jalilah zan iya cewa ta taka *SAWON B'ARAWO* ne (littafin Noorieyya), abin da yasa nace
haka kuwa jifa aka binne domin wani ya tsallaka sai akayi rashin dace ta tsallaka a daren ita
kuma ".
Anwar da Yarima suka dubi juna cike da mamaki, yayin sa Mallam Kallah ya katse mamakin
nasu da fad'in.
"Zan baku rubutun AYATUSSHIFA ta d'inga sha tare da shafe jiki insha Allahu da yardar Allah
(S.W.A) koma mene zai karye, sannan kai kuma abin da zan fad'a maka".
Yayi nuni da Yarima.
"Kana da mak'iya da yawa a cikin gidanku da waje yawanci jifan da ake yi kai ake yiwa sai dai
kuma da taimakon Allah da taimakon Ayatul-kursiyyun da ka rik'e da kuma al-azkar sune suka
zamo makami daga gareka don haka kak'ara dagewa wajen al-azkar da tsayuwar dare, domin
abin da mu mutane bama ganewa ayanzu wannan Ayatul-kursiyyun da muke rainawa gata dai
aya d'aya ce amma maganin da zatayi maka yafi dubu domin ita babbar kariya ce ga duk wani
muminin da yarik'eta yana karanta ta ko yaushe dare da rana, sannan abu na gaba azkar muna
shagala da yawa tare da barin damarmu a kodayaushe al-azkar nada matuk'ar kariya da
muhimmanci a tare damu, domin idan kayi shi da safe Allah Ubangiji (S.W.A) zai sanya
mala'iku suyita gadinga tun daga safiyya har zuwa yammaci, idan kayi shi da yammaci za'a
sanya mala'iku suyita gadinga daga yammaci har zuwa asuba kagani mutum na cikin kariyar
Ubangiji taya tuggun wani bil'adama zai ci shi?, koma mene mutum ya nufoka da shi sai dai ya
koma kansa amma ba dai yazo gareka ba, Allah yasa mu da ce yasa mufi k'arfin zuciyarmu ya
karemu daga sharrin mak'iyanmu".
"Amin ".
Su yarima suka amsa tare yayin da kowa acikin zuciyarsa yake tunani na daban akan batun da
Mallam Kallah yayi musu yanzu.
Sun d'an tab'a hira kad'an, wanda dukkan hirar wa'azi ne gami da nasiha Mallam Kallah keta yi
musu, basu bar wajensa ba sai da jikinsu yayi la'asar sosai nasiharsa ta shigesu, sukayi masa
sallam tare da karb'an rubutun Jalilah suka nufi gida.
***. ***. ***
"Ina fatan kinsanar masa ayi aikin nan da gaggawa ko?".
"Ehh ranki yadad'e, yace ma cikin satinnan komai zai kammala".
"Yauwa haka nake son ji, domin bahaushe ya ce da zafi-zafi akan daki k'arfe, tashi kije sai kin
jini".
Larai ta mik'e da tsumar jiki tabar falon Fulani Sokoto, tana fita su Yarima na kawo kai, zama
sukayi gefan Fulani sokoto tare da gaisheta sannan suka fara sanar da ita dukkan abin da
Mallam Kallah ya fad'a musu dangane da ciwon nata.
Fulani sokoto najin cewa Jalilah ta taka asirin da akayiwa wani ne, haba wa sai tamik'e zaune
ta fara sababi da masifa.
"Ai wallahi duk ma mai hannu a ciki narantse da Allah da kansa zai bayyana kasan, har ni
za'anunawa asiri?, ai ko da guraye mutum yake yawo yayi kad'an yamin haka, karku damu
nasan waye yayimin hakan kubar komai a hannuna".
Yarima da Anwar suka saki baki kawai suna kallonta cike da jimamin jin batun da ke fita daga
bakinta.
Anwar ya mik'a mata gorar rubutun yana fad'in.
"Gashi ta dinga sha inji Mallam Kallah ta shafe jikinta, Fulani sokoto takarb'a tare da binsu da
wani irin kallo da suka kasa fassara kona menene?.
Mik'ewa sukayi tare da yimata sai anjima suka fito daga falon, suna fita Fulani sokoto taja tsaki
tare da dariya tana fad'in.
"Aikin banza aikin wofi har ni za'a nunawa bariki?, ayo asirin sannan a biyo ni da wani
munafikin rubutu wai inji Mallam kallah, kuji wani rainin wayo wato a biyo ta hanyarsa a k'arasa
kashemin 'yartawa to ba dani ba wallahi Fulani Bingel da ni kike zancen dan nasan wannan duk
tuggun ki ne burinki kawai kiga bayana ni da yarana to kafin kiga nawa sai naga naki, wannan
abin kuwa zubar da shi zanje inyi wallahi abin da kuka k'ulla sai dai ya koma kanku".
Haka Fulani sokoto ta shafe tsayin lokuta tana ta faman sambatu kamar wata tab'ab'b'iya Jalilah
na d'aki tana jinta.