Showing 39001 words to 42000 words out of 88612 words
Chapter 14 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
baki a washe tana dubansa tare da fad'in.
"Ina so sosai wallahi !".
"Ok..! Zanyi magana da Babanki sai musan abinyi kafin zuwa lokacin kammalawarki zan san
yanda zanyi inshawo kan Mai Martaba ya amince da auren mu !".
Sosai Aynu taji farin cikin jin wannan maganar, ta d'an risina tare da fad'in.
"Nagode sosai Allah ya k'ara girma da arzik'i...!".
Yarima Fudhal ya sanya ya tsansa d'aya kan leb'ansa yana fad'in.
"Shishshshsh...! bana buk'atar jin godiya daga gare ki, komai zan iya indai akan ki ne Aynu
sabida ke ce mace ta farko dana fara so !, ina jinki sosai cikin raina...!".
Aynu dubansa tayi cike da murmushi kan fuskarta, take taji son Yarima da k'aunwrsa na k'ara
shiga ranta har dai sanda taji yana fad'in.
"Ki gayawa Abbanki nan da kwana biyu zanzo muyi magana kan batunki da karatun da zaki
koma !".
"Da gaske kake ?".
Yarima Fudhal kai kawai ya gyad'a mata tare da lumshe idanuwansa, sabida yanda Aynu ta
wurk'a idonta kafin tayi masa tambayar ne ya sashi jin wani abu tun daga kwanyar kansa zuwa
babban yatsansa, da k'yar ya iya bud'e baki ya bata amsa.
"Na tab'a yi miki wasa ne?".
"A'a".
Ta bashi amsa tare da mai da kanta k'asa, sabida wani irin kallo da taga yana binta da shi.
"Zo muje mota zan baki sak'o ".
Ya fad'a yana mai kafeta da idanuwa, Aynu ta d'anyi jim kad'an kafin tace.
"To".
Yayi gaba yana tafiya ta bishi a baya har zuwa bakin layinsu inda yayi parkin motarsa, ya bud'e
gidan baya ya d'auko wata k'atuwar farar leda ya mik'a mata, tsayawa tayi tana dubansa ba tare
data karb'a.
"Bana son musu kin sani dai".
Aynu tasa hannu tak'arba tare da fad'in.
"Nagode sosai".
Dubanta ya sakeyi tare da zira hannu cikin aljihun wandonsa ya zaro kud'i masu yawa ya
mik'a mata, kai ta girgiza alamun a'a tana fad'in.
"Kabarshi iya hankama ya isa nagode sosai....!".
Katse ta yayi da fad'in.
"Wannan ba daga ni ba ne, daga Abbana ne yace a baki hak'k'in ki ne, na aikin da ki kai".
Aynu tasa hannu takarb'a tana fad'in.
"Ayimin godiya".
"Ni zan koma ki kulamin da kanki !, sai nan da jibi zan dawo, karki manta da maganarmu".
"To insha Allah bazan manta ba, kai ma ka kula da kanka".
Yarima yayi murmushin jindad'i yana mai bin bayanta da kallo har sai da tab'acewa ganinsa,
sannan ya tayar da motar ya bar layin gidan ya nufi gidansu Anwar.
***
"Ranki ya dad'e, sai fa mun dage sosai akan Magaji wajen yi masa addu'a, sabida sharrin
mak'iya !".
"Muna nan munayi Jakadiyya, ke dai kina ji da magaji sosai kullum maganarki bata wuce ta
sa".
Jakadiyya tayi ajiyar zuciya kafin ta ce.
"Ai dole indamu da shi Hajiya, shi d'in ai abin so ne ga kowa".
Fulani Bingel tayi murmushi na jindad'in maganar da Jakadiyya keyi akan Yarima.
Sallama yayi ya shigo tare da neman waje ya zauna, yana mai gaishe da Fulani, ta amsa cike
da fara'a tana dubansa, Jakadiyya ta rissina ta gaishe da shi tare da tamik'e tabar d'akin.
"Yanzu zancenka muke sai kuma gaka ka shigo".
Yarima ya d'ago kai daga daddanna wayar da ya ke tare da duban Mahaifiyartasa.
"Wai kai kullum babu abin da kake jin dad'ine da ya wuce danna waya?".
"Hajiya kenan...bazaki gane bane".
Ya bata amsa cike da murmushi, itama murmushin tayi tana fad'in.
"Taya zan gane ba'ayi min bayani ba?, daga ina kake ne haka?".
Yarima Fudhal ya dubi Mahaifiyartasa shi dai baya yi mata k'arya kuma baya so ya fara yi mata
ayau.
"Naje gidansu Aynu, daga nan naje wajen Anwar".
Fulani Bingel kafe Yarima Fudhal tayi da ido cike da mamaki, domin yau karo na farko tana
ganin tirjiya tare da kaucewa umarnin mahaifinsa.
"Kenan baka bar yarinyar ba?".
Yarima ajiyar zuciya yayi tare da duban Fulani Bingel yana fad'in.
"Kada kimin gurguwar fahimta, ki tayi da addu'a Hajiya, ni kaina na kasa kaucewa abin da
zuciyata take so, na rasa yanda zanyi incire yarinyar a raina ne".
"Karka damu na fahimci damuwar da ka ke ciki, zan tayaka addu'a sosai insha Allahu kaima ka
dage da addu'a kaji?".
"To Hajiya ina nan inayi dama".
"Amma Hajiya Aynu taban tausayi sosai wallahi duk sai naga ta rame, kawai na yanke
shawaran mai da ita makaranta inyaso ki tayani shawo kan Mai Martaba !".
A jiyar zuciya Fulani tayi tana fad'in.
"Ka san halin Mahaifinku dai al'amarinsa sai dai addu'a Magaji, amma zanyi k'ok'arin ganin na
shawo kan nasa".
"Yauwa Hajiyata !, haka ya kamata ki fad'a ai tun da farko, Allah yak'ara girma".
"Amin".
Ya kwanta bisa cinyarta, d'an bugun bayansa tayi tana fad'in.
"Wai kai yaushe zaka girma ne ?, kai da ake shirin yiwa aure !".
Fudhal yayi dariya yace.
"Ai a gunki bazan girma ba Hajiya, tunda nine auta !,, kinga ai dole kiji dani".
Fulani ta tureshi tana fad'in.
"Yau dai ka girma agun nawa".
Yarima ya zauna yana fad'in.
"Wai ina Aunty Sadiyya ta shige ne?, kwana biyu bata zuwa?".
"Ina zata zo?, tana fama da jikinta, ta kusa haihuwa fa, kai dai kam Allah ya shiryamin kai baka
son zumunci ko kad'an tun da ka dawo babu gidan wacce ka taka bare har ka zaga dangi".
"Ayya Hajiya karki damu zanje ne insha Allah, kinsan tun da nadawo busy nake ne".
"To naji amma gobe kaje ka dubota".
"Allah ya kaimu goben lafiya".
"Amin".
***
Ya Sayyadi Umar ya durk'usa ya gaishe da Umma, ta amsa cike da fara'a tana fad'in.
"Munata ganin abubuwan alkhairi mungode sosai, Allah k'ara bud'i".
"Amin, Babu komai Umma, karku damu, Baba baya nan kenan?".
"Ehh bai shigo ba tukun".
"A gaishe dashi ni zan koma".
"Zaiji insha Allah, Allah kiyaye mungode sosai".
Ya mik'e ya fita, Aynu ta bi bayansa har zuwa k'ofar gida inda ya tsaya yana jiranta.
Dubanta yayi kafin yace.
"Har yanzu kink'i sakin jiki dani !, ko wani abun ke damun ki?".
"A'a babu komai".
Tayi maganar kanta ak'asa.
"Ina ganin kamar ya kamata inturo iyayena ayi magana ko?, domin zance babu tsayay-yiyar
magana bata da amfani".
Dammm gaban Aynu ya buga, tuni yanayinta ya sauya har Ya Sayyai Umar yaso fahimtar
hakan.
"Yadai ko bakyaso inturo yanzu?".
"A'a kawai gani nayi zaifi dacewa ka bari ad'an k'ara kwana biyu".
Ya Sayyadi Umar yayi shiru nad'an wani lokaci kafin yace.
"Babu damuwa !, Allah ya kaimu lokacin ni zan koma ankusa kiran sallah ki gaida Baba idan
ya dawo".
"Zai ji insha Allah".
Ta fad'a tana mai juyawa ta koma cikin gidan tabarshi nan tsaye.
BAYAM SALLAR MAGHRIBA...!
Baban Aynu ne zaune bisa tabarma yana cin abinci, Umma na daga gefansa, Aynu na waje
d'aya a zaune, sai sak'a take tana warwarewa a cikin ranta, tana son sanarwa iyayen nata
maganar Yarima Fudhal amma ta kasa tana jin nauyi sosai.
Har Baban nata ya kammala cin abincin ya wanke hannu tare da alwala yana fad'in.
"Zanje masallaci ankusa shiga sallah".
"Adawo lafiya".
Suka had'a baki da Ummanta wajen fad'i.
Sai bayan fitarsa Aynu ta matsa wajen Ummanta tana fad'in.
"Umma dama wata magana nake son fad'a miki".
"To inajinki Aynu".
Aynu ta d'anyi shiru kafin tace.
"Umma dama...! dama..!! dama !!!".
"Dama me?, kiyi magana mana Aynu".
"Dama Yarima ne yace wai...".
Sai kuma tayi shiru.
"Yace me Aynu?, fad'i ina jinki".
"Cewa yayi fa wai jibi zai zo wajen Baba suyi magana, wai za biyamin inkoma makaranta !".
Umma shiru tayi na zuwa wani lokaci, Aynu kuwa ta zuba mata ido tana jiran taji abin da zata
ce.
"To Allah ya kaimu !, zan gayawa Baban naki".
Umma tayi maganar asanyaye, kamar akwai wani abu ak'asan ranta.
Ita dai Aynu bata ce komai ba illa.
"Amin".
Data furta kawai, acan k'asan ranta kuwa farin ciki ne fal wanda ba zai fad'uba, tamik'e ta
d'auro alawala domim gabatar da sallar isha'i.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
24
*BAYAN KWANA BIYU*
Yarima Fudhal ne tare da Anwar tsaye jikin k'ofar gidansu Aynu, Anwar sai bin gidan yake da
kallo Yarima kuwa kansa na bisa screen d'in wayarsa yana dad-dannawa, fitowar Aynu daga
cikin gidan shine ya sanyashi mai da wayar cikin aljihun wandonsa yana binta da kallo.
Ta k'araso inda suke tsaye tare da gaishesu tana fad'in.
"Baba yana ciki !, ku shigo mana?".
Ta juya zuwa cikin gidan suka take mata baya, da sallama suka sanya kai cikin gidan, yaune
karo na farkon shigar Yarima gidansu Aynu.
Ummanta na zaune gefe kan kujera da sandarta agefanta, Babanta shima na waje d'aya kan
tabarma, sai wata tabarma ba kowa akai ita ce akayiwa su Yarima nuni da su zauna.
Aynu kuwa tuni ta wuce can k'uryar d'aji ta baza kunnuwa, k'asan zuciyarta kuwa cike ya ke da
fargaba data rasa dalilin sa.
Zama sukayi tare da gaishe da iyayen Aynu, Yarima ya sake duban Baban nata karo na biyu a
zuciyarsa yana tunanin kamar ya tab'a saninsa, sai dai yana so ya tuna amma ya kasa tunawa.
"Aynu ta gayamin kan cewa zaka zo muyi wata magana !, to yanzu gashi Allah ya kawomu, ina
jinku mai ke tafe da ku?".
Baban Aynu ya katse Yarima daga dogon tunanin daya fad'a, Anwar ya gyara zama yana fad'in.
"Baba munzo ne kan maganar 'yarka Aynu !, Yarima Fudhal ya ganta yana kuma son ta !, sai
dai ya yanke hukuncin zai mai da ita makaranta domin cigabanku da rayuwarta kafin zuwan
lokacin da iyaye zasu shiga tsakanin maganar !".
Baban Aynu ya gyad'a kai cike da gamsuwa da maganar Anwar, kafin ya mai da kansa kan
Yarima Fudhal yana binsa da kallo cike da nazarin yanayinsa, Baban Aynu yayi murmushi na
wani lokaci kafin yace.
"Yaro ya sunanka?".
"Anwar, shi kuma Yarima Fudhal d'an Sarki Ubaiyd, nasan zaka sanshi ai?".
"Kwarai kuwa ni nasan Fudhal !, inajin duk cikar garinnan akwai wanda zai kai ni sanin waye
Yarima Fudhal?".
Anwar ya dubi Baban Aynu cike da mamakin jin maganar da yayi, shima kansa Yarima Fudhal
kallonsa yake yayin da gefe guda kuma zuciyarsa sai bugun uku-uku take.
Baban Aynu ya cigaba da fad'in.
"Naji duk kan abin da kuka zo dashi sai dai ina mai baku hak'uri abisa maganar da zanyi
yanzu".
Shiru ya biyo baya na wani lokaci, yayin da Anwar da Yarima suke jiran suji abin da zai ce.
"Na riga nayiwa Aynu miji !, kayi hak'uri nagode sosai abisa taimakon da kukayi niyar yi mana
!".
Zuciyar Yarima tsananta bugu tayi lokaci guda yaji kasala da mutuwar jiki sun ziyarce shi,
Anwar ya dubi halin da abokin nasa ya shiga, ya mai da kai kan Baban Aynu ya bud'e baki zai yi
magana Baban Aynu ya da katar da shi tare da fad'in.
"Kuyi hak'uri kawai !".
Aynu dake tsaye cikin d'aki tana sauraronsu ta zube k'asa zaune tana share kwallar dake shirin
zuba kan fuskarta.
"Baba muna baka hak'uri muma !, amma naga ai bakayi mata baiko da kowa ba, ka taimaka
Baba abokina nasonta sosai wallahi !".
"Nasan da hakan !, amma kusan wani abu guda d'aya ko da ban yiwa Aynu baiko ba, nariga
na gama magana bazan canja ba, ko da ace babu wanda nayiwa alk'awarin aurawa Aynu
bazan tab'a yarda Aynu ta auri Fudhal ba !".
Cike da firgici Yarima Fudhal ya d'ago kai ya dubi Baban nata yana fad'in.
"Me yasa Baba ?, kataimaka kada ka yimin yankan k'auna dan Allah kayarda ka bani Aynu!".
"Sai yanzu kasan da haka Fudhal !, ni nasan ba zan tab'a yi maka yankan k'aunar da ka yimin
ba !, shin zaka iya tuna MALAM ABDALLAH, Tsohon malamin makarantar primary mai ritaya ?".
Yarima Fudhal fiddo ido yayi waje yana duban Baban Aynu take hawaye ya fara zarya bisa
fuskarsa, wani abu yaji na fizgar zuciyarsa ya mik'e da sauri ya dubi Anwar ba tare da ya ce
komai ba yayi hanyar waje.
Anwar ya biyo shi da sauri yana kiran sunansa amma bai kulashi ba, har ya shiga mota ya
zauna ya jingina da kujerar maotar yana mai kwantar da kansa, idanuwansa ya lumshe take
hawaye suka fara zarya kan fuskarsa.
Anwar ya k'araso da gudu ganin halin da Yarima ya shiga yasan yashi tsayawa turus yana
dubansa, tare da bud'e murfin motar ya shiga mazaunin driver ya zauna, yana mai dafa kafad'ar
Yarima.
Yarima ya bud'e ido a hankalin yana duban Anwar tare da bud'e baki yace.
"Shikenan yanzu ya zama dole inbar Aynu !, Anwar rabuwata da Aynu tamkar rabuwa da
rayuwata ne, zuciyata zafi Anwar!".
Tausayin Yarima ya kama Anwar sai yake ji kaman shima zaiyi kukan da k'yar yayi k'arfin halin
fad'in.
"Kai ne kab'ata komai ai, mai makon kabari mushawo kansa mu bashi hak'uri sai kawai ka tashi
ka fito !".
Yarima yayi murmushin da yafi kuka ciwo tare da duban Anwar.
"Bazai tab'a hak'ura ba !, ka sani yana son yayi amfani da wannan damar ne kawai wajen
d'aukar fansarsa a kai na!".
"Kamarya kenan!, ban fahimce kaba ?".
"Malam Abdallah, tsohon malamin makarantar primary ba kowa bane illa mahaifin Aynu !".
"To amma wani abu ya tab'a had'aku ne?".
Yarima ya dubi Anwar natsayin lokaci batare da ya bashi amsar tambayar da yake yi masa ba.
"Muje gida Anwar insha magani zuciyata zafi ".
Anwar bai kuma cewa komai ba ya tada mota suka bar layin gidansu Aynu zuwa gida.
***
"Ka da kace min kana son d'aukan fansar abin da yafaru ne tsayin shekaru?".
"Ko kusa Umman Aynu, bana da burin fansa cikin rai na !, kawai ina son yin amfani sa wannan
damar ne wajen mai da Fudhal cikakken mutum domin shi har yanzu bai san waye shi ba?,
sabida shi duk da tarin shekarunsa amma bai cika mutum ba !, har yanzu yana matsayin rabin
mutum ne !, ina son in nuna masa muhimmancin mutum da darajar da d'an adam yake da shi a
wajen Allah da cikin dukkan halittu !, inaso in nuna masa abin da mahaifinsa ya kamata ace ya
nuna masa tsayin shekaru amma ya gaza yin hakan !, ka da ki yiwa maganata gurguwar
fahimta domin kinfi kowa sanin mai ya faru?, taya zan yarda Aynu tayi aure a gidan da basu san
darajar d'an adam ba?".
"Kina tunanin sarki Ubaiyd zai yarda Fudhal ya auri 'yar talaka ne?, shima kanshi Fudhal d'in
da abu biyu yazo wajena a yanzu, nasan abin da shi kanshi Fudhal d'in bai san nasani ba, haka
kawai Fudhal bazai k'ask'antar da kansa a garemu ba !, da a ce ya zomin a cikakken mutum da
fuska d'aya da bazan tab'a ta da abin da ya riga da ya wuce tsayin shekaru ba, sai dai ya zomin
da fuska biyu ne ba akan gaskiyarsa ya zomin nan ba !, nariga da nasan wannan tun ba yanzu
ba, kawai addu'a ce taki cikin wannan al'amari domin bamusan abin da Allah ya riga ya b'oye ba
!, sannan kuma kada ki sa damuwar wannan abin da ya faru aranki dan Allah kinji?".
Umman Aynu kai kawai ta gyad'a tare da fad'in.
"To, Allah ya shige mana gaba".
"Amin, ni zan fita, sai zuwa anjima zan dawo".
"Allah kiyaye a dawo lafiya".
"Amin".
Yana fita Aynu dake cikin d'aki ta fito da gudu ta fad'a kan cinyar Ummanta tana mai rushewa
da kuka mai cin rai.