Showing 48001 words to 51000 words out of 88612 words
Chapter 17 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
ya dubi Anwar cike da
kulawa kafin ya fara magana.
"Me zance to Anwar?, zai nememu fa kawai ya ce da kai, inajin tsoron abin da zai biyo baya ne,
kana da tabbacin ya yarda da abin da ka gaya masa?".
"Ehh mana, ya kamata kayi kyakykyawan zato Yarima".
"Hakane nagode sosai Anwar".
"Haba dai mene abin godiya kuma?, ai ana tare".
***
Baban Aynu ne zaune bisa tabarma da Umma a zaune gefansa suna tattaunawa kan batun
Aynu da Ya Sayyadi.
Baba ya dubi Umma cikin kulawa ya ce.
"Ya kamata a ce da Umar ya fito ayi magana, ko ya kika gani Umman Aynu?".
"Haba dai Malam..! Me zai hana a d'an k'ara kwana biyu, kana ganin yarinyar nan fa yanda ta
koma har yanzu ta kasa mai da walwalar jikinta".
"Ehh haka ne, amma ni ma a son raina dama ba yanzu ba, to wancan yaron ne ke neman
canjamin a kalar maganata ne, kinga idan aka riga akayi baikon ya hak'ura ai".
"Haka ne kuma, amma malam kamarya yana neman canja akalar maganarka?".
"Ehh to d'azu a kasuwa a bokinsa ya zomin da maganar dukkan abin da ya faru a shekarun
baya, ba na so tausayin yaron yayi tasiri araina incanja maganata".
Nan dai ya kwashe komai ya sanarwa Umman Aynu, Umma ajiyar zuciya tayi tana fad'in.
"Allah sarki yaban tausayi sosai wallahi, a she ba shi da laifi laifin duk na mahaifinsa ne?,
yanzu mai ka yanke akan hakan?".
"Maganata babu canji Aynu Umar zata aura, domin shi yafi dacewa damu da rayuwarta, yaron
d'an mutunci wanda ya san mutunci taya zamuyi sake ya sub'uce mana a matsayin suruki?".
"Gaskiyarka Malam domin duk wata uwa ta gari burinta 'yarta ta auri miji nagari, haka kuma
duk wata uwa ta gari burinta d'anta ya auri mata tagari, nima har cikin raina Umar ne zab'ina".
Aynu dake zaune cikin d'aki duk tana jin tattaunawar da iyayenta keyi, tana faman share kwallar
dake zubo mata bisa kan fuskarta a fili ta furta.
"Yanzu ya zama dole inkoyawa zuciyata son Ya Sayyadi Umar, kamar yanda ya zamana dole
in fidda son Yarima a cikin raina..!?".
Ta kifa kai bisa tabarmar da take zaune a kai tana shash-shek'ar kukan da babu mai lallashinta.
BAYAN KWANA UKU.
Zaune yake a office d'insa kamar kullum yayi nisa cikin tunani sosai, ya yin da k'asan
zuciyarsa keta faman azal-zalarsa da son ganin Aynu, har sai da ya kasa jurewa bare ya iya
sarrafa kansa wajen bawa zuciyar tasa hak'uri.
Ya d'ago jajayen idanuwansa dai-dai lokacin da agogon office d'in ya buga k'arfe shida da 'yan
mintuna, sai lokacin ya san irin dad'ewar da yayi a zaune yana aikin tunani, tattara komai yayi
ya mayar inda yake ya fice da sauri zuwa wajen motarsa ya tayar da ita ya fice daga cikin
harabar asibitin.
Kai tsaye gida ya nufa bai tsaya ko ina ba sai cikin d'akinsa yana shiga ya fad'a toilet y
sakarwa kansa sassanyan ruwan shower, wai dan ya d'anji sanyi a ransa amma duk da haka
bai samu yanda yake so ba.
Fitowa yayi bayan ya d'auro alwala ya ta da sallar maghriba domin lokacin anata kiraye-kirayen
sallar shi kuma baijin zai iya zuwa sabida yanda yake jin jikinsa, ya jima kan sallah yana jero
tarin addu'o'i wanda zan iya cewa addu'artasa duk a kan Aynu ce, sai a lokacin ya d'anji
dama-dama a cikin ransa.
Yana shafawa ya janyo wayarsa ya kira number Anwar amma switchoff hakan yasa ya wurga
wayar kan katifa ya mik'e ya shirya cikin k'ananun kayan riga T.sheet fara da adon bak'i a jikinta
sai ya sanya bak'in wando jeans bai damu da ya gyara sumarsa ba kamar yanda ya saba ya
d'auki key d'in motar ya fice daga gidan.
Duk a bin da yake Jalila na lab'e tana kallonsa, domin yau taci alwashin sai ta samu abin da
take so, har sai da ya fice sannan ta fito daga mab'oyarta ta koma part d'insu tana zaman jiran
dawowarsa.
A k'ofar layin nasu ya tsaya yayi parking ya fito ya kulle motar ya taka har zuwa k'ofar gidansu
unguwar shiru kamar anyi shara ya shafe tsayin lokuta a tsaye amma babu ita babu labarinta
kuma ya rasa wanda zai aika zuwa gidansu, domin yau yaci alwashin kome zai faru sai yaga
Aynunsa.
Yayi nisa cikin tunani yaji ana fad'in.
"Lafiya dai Yarima?".
D'ago kai yayi da sauri domin a tunaninsa Aynu ce sai dai yaga sab'anin haka Zainab,murmushi
ya saki wanda bai wuce kan leb'ansa ba yana fad'in.
"Alhamdulillahi gara da Allah ya kawo ki".
"Lafiya wani abun ya faru?".
"A'a babu komai, kawai dai wani taimako nakeso kimin dan Allah".
"Taimakon me fa?".
"Ki fitomin da Aynu ".
Zainab ajiyar zuciya tayi kafin ta ce.
"Ai kuwa Aynu bana jin zata fito yanzu, dama dai kayi hak'uri kuma kasan a gida ma ba za'a
bari ta fito ba".
"Please dan Allah ki taimake ni".
Yayi maganar kamar zai yi kuka, sosai tausayinsa ya kama Zainab ta ce.
"To jira mugani Allah yasa ta fito".
Ta juya ta shige cikin gidan ta bar Yarima nan tsaye yanata zuba addu'o'i cikin ransa akan Allah
ya taimake shi ta fito.
Kusan mintuna goma sha biyar suka shud'e ba amo babu labarinsu can dai kamar ance d'ago
kanka ya gansu sun fito tare Aynu na faman turjewa Zainab na rok'onta, cikin d'acin rai Aynu ke
fad'in.
"Kema kin koyi mumafunci ko?, ki ka cemin Ya Sayyadi ne".
"Yi hak'uri dan Allah ki saurare shi".
Aynu ta dubi inda Yarima yake shek'ek'e ta buga tsaki ta juya zata koma, Yarima yayi saurin
kamo hannunta tare da shan gabanta yana fad'in.
"Kiyi ha'uri dan Allah ki saurare ni".
Yayi maganar cikin sanyin murya, Aynu ta tsaya tana kallonsa kawai nan suka hau kallon kallo
tsayin wasu lokuta kafin Aynu ta fizge hannunta tana yi masa wani irin kallo daya kasa fassara
kona mene.
Tsaki taja kafin tace.
"Ka b'acemin da gani Yarima..! Na tsaneka..! Bani son ganinka ko kad'an acikin rayuwata
domin ka jiwa zuciyata ciwon da banajin akwai maganin warkewarta, me ya sa..! Me yasa...!!
Me yasa Yarima?".
Sai kawai ta fashe da kuka, sosai Yarima kejin kukan Aynu har cikin zuciyarsa, a hankali ya cire
hannunsa da ke cikin aljihun wandonsa yakai hannun da niyar share mata hawayen sai kuma
ya sauke hannun da k'yar yayi k'arfin furta.
"Kiyi hak'uri Aynu...!, Ki sani ina sonki har cikin raina wallahi, dukkan abubuwan da suke faruwa
har yanzu ban fidda rai da ke ba, domin inajin a raina ke tawace har abada kuma zamu rayu
tare, amma yau she ne wane lokaci ne abubuwan zasu dai-daita ban sani ba?".
Aynu ta d'ago jajayen idanuwanta tana kallonsa cike a takaijin jin maganar da yake yi.
"Kama daina wannna mafarkin, domin Aynu nan da wasu watanni matar wani ce, kalamanka
banjin zasuyi ta siri a raina Yarima, kamar yanda kuka so yi da farko sai dai Baba ya taka muki
burki, to nima inaso kamanta da ni...!".
Kafin ta kai ayar maganarta sai ganin Yarima Fudhal tayi tsugunne a gabanta bisa gwiyoyinsa
idanuwansa fal da hawaye.
"Kiyi hak'uri dan Allah da Annabinsa nasan nayi kuskuren da babu abin da zanyi domin
gyaransa amma ki sani Aynu babu wani bawa da zai iya kaucewa k'addararsa, nasan na
zalunce ku ke da iyayenki amma ki sani komai muk'addari ne daga Allah, dan Allah ki janye
daga batun auren wani bani ba, Aynu inasonki wallahi zan iya rasa raina Ayn...!".
"Naji kana so na..!, amma duk kai kaja dukkan abubuwan nan suke faruwa, Babana bawai
yana da burin d'aukan fansa bane, haka ni ma bana da burin fansa cikin raina, amma me yasa
Yarima kayanke shawaran azurtamu da kud'inka kamance Allah ke azuratawa ba bawa ba, kai
ma da kuke tak'ama da kud'i da mulkin ai duk Allah ne ya baku ayau in yaso sai ya karb'e
abinsa, mai yasa kazo wajen Baba da fuska biyu?, mai yasa baka zo kanka tsaye ba domin
kafuwar soyayyar da kakemin idan har gaske ne?, ina ji a raina bani kake so ba akwai dai abin
da kake so, domin idan har ni kake so ba zaka yi tunanin amfani da kud'i ba zakayi ne domin
yak'ini da zuciyarka".
Yarima kamo hannun Aynu yayi yarik'e k'am ba tare da ya lura da hakan da yayi ba.
"Ki fahimce ni Aynu, sonki shine yafi tasiri a zuciyata fiye da komai, sonki ne ya sanya zuciyata
ta rufe, tunani na ingyara kuskuren da nayi, amma mai makon in gyara sai in k'arawa kaina wani
laifin ba tare da nasan hakan ba, ki ga farce ni dan Allah ka da kiyar da ki auri wani ba ni ba
Aynu zanyi k'ok'arin ganin na gyara kuskure na...!".
"Taya zaka gyara kuskuren naka?, Kuskure ka riga kayi ai sai dai ka kiyaye gaba , amma ka
sani har yau ba zan dai na fad'a maka ba, gobe za'ayi bai kona da Ya Sayyadi nan da watanni
ni mata ce a gare shi, ina so ka manta da ni kasa wa ranka tamkar mafarki na kayi ka farka...!".
Aynu ta fizge hannunta ta shige gida da gudu tana kuka, Yarima zaman dirshan yayi a wajen
zuciyarsa na zafi da k'una, har ya naji dama Allah ya d'auki ransa a dai-dai wannan lokaci akan
yana ji yana gani Aynu ta auri wani ba shi ba, duk abubuwan da suke faruwa Zainab na gefe
tana kallo har sai da suka sanyata zub da hawaye ita ma.
Yarima da k'yar yayi k'arfin halin mik'ewa yana jan k'afa cike da tangad'i kamar wani d'an
shaye-shaye ya bar layim gidansu Aynu zuwa inda yayi parking motarsa ya bud'e ya shiga ya
zauna tare da kifa kai bisa sitiyarin motar.
[04/09, 05:00] Hassan Atk: *YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour
30
Am so sorry abisa jina da kukayi shiru kwana da yawa wlh fever ya rik'eni...amma yanzu
Alhmdlh ngd sosai da call naku zuwa text message ubangiji Allah yabar kauna amin kuna raina
any time ana mugun tare.!
***
"Haba Yarima ka da ka mance kaima Doctor ne?, amma ya kake k'ok'arin jawa kanka
matsala ne?, ka fini sanin illar da ke tattare da ciwonka fa...!, Please Yarima kayi k'ok'arin
cirewa kanka damuwar da ke tattare cikin zuciyarka tun da wuri domin kana dab da fuskantan
babbar matsala?"
Yarima Fudhal bai ce komai ba illa kafe Doctor Mansur da yayi da shanyayyun idanuwansa
babu ko k'iftawa, Anwar ne ya dubi Doctor Mansur cike da kulawa yana fad'in.
"Insha Allahu zamuyi k'ok'arin kiyayewa Doctor zan fahimtar da shi da yardar Allah komai zai
yi normal".
"Ok babu damuwa tun da kai ka fahimce ni zaka iya fahimtar da shi, Allah ya k'ara lafiya ni zan
koma?".
Sukai sallama da Anwar ya fice daga d'akin ba tare daya sake duban Yarima ba.
Yana fita aka sake turo k'ofar Yarima Jalil ne ya shigo cikin shiga irin ta Yarima Fudhal farar
T.sheet da bak'in wando Jeans har adon rigar da komai iri d'aya.
Zama yayi a gefan da Fudhal ke kwance bayan ya mik'awa Anwar hannu sun gaisa yana fad'in.
"Ya dai Bro bakajin dad'i ne?".
Yarima Fudhal ya gyad'a masa kai alamun E .
"Ayya am sorry..! Jalila ma nacan kwance da alamu ko magana bata iyayi amma ta matsa a
kirawo mata kai".
Yarima Fudhal ya kafe Jalil da ido yana fad'in.
"Meke damunta?".
"Waya sani?, Momy dai ta ce tun dare ne tayi mafarki shikenan take ta aikin kuka har safe bata
koma bacci ba, amma kuma tak'iyin magana ".
"Subhanallahi...bari intashi muje to !".
Yarima Fudhal ya mik'e da k'yar suka fito daga d'akin dukansu a hanyar zuwa part d'in Fulani
Sokoto ne yake tambayar Yarima Jalil.
"Wai kai ina kake zuwa ne? ina lura da kai kusan 2week kenan baka gidannan, yaushema ka
dawo ne?".
Yarima Jalil sosa k'eya yayi tare da wata 'yar guntuwar dariya.
"Naje hutu ne kawai, jiya da dare na dawo na shiga d'akinka baka nan ai".
Yarima Fudhal ya watsa masa wani mugun kallo kawai ya d'auke kansa, a can k'asan ransa
bak'aramin ciwo yakeji ba akan munanan halayen Jalil bai san meya sa baki d'aya ya gama
lalacewa shine shaye-shaye neman mata duk ya had'a kamar ba jinin sarauta ba?.
Suna shiga falon babu kowa kai tsaye d'akin Jalila suka nufa da sallamarsu Momy ce zaune
gefan Jalila ita ce ma ta amsa musu sallamar, dukansu suka gaisheta tare da tambayar jikin
Jalila, ita kuwa Jalila tun da suka shigo take bin Fudhal da Jalil da wani irin kallo kamar yau ta
fara ganinsu.
Yarima Fudhal ya zauna gefanta yayin da Anwar da Jaleel suka nemi gefe guda suka zauna
Momy ta mik'e ta fice daga d'akin.
Fudhal ya rik'o hannunta yana fad'in.
"Ya jikin naki?".
Kai kawai ta gyad'a amma babu bakin magana.
"Bakya iya magana ne?".
Nanma kan ta sake d'aga masa.
Yarima Fudhal shiru yayi kawai yana dubanta tausayin k'anwar tasa ya kamashi yama rasa mai
ya kamata yayi mata?.
Mik'ewa yayi ya fito daga d'akin zuwa falo dai-dai lokacin da Momy ke fad'awa Larai baiwarta.
"Kiyi maza ki kai masa sak'on dan Allah bana son a samu kuskure kice a yi aikin cikin gaggawa
dan Allah...!".
Maganarta ta katse dai-dai sanda Fudhal ke fitowa zuwa falon, Fulani Sokoto tayi wani
mayaudarin murmushi tana fad'in.
"Har ka fito Magaji?".
Fudhal ya nemi guri ya zauna ba tare daya bata amsa ba, Larai kuma tamik'e da sauri ta fice
daga d'akin.
"Momy ta fad'a miki abin da tayi mafarki ne?".
"A a nidai ihunta kawai naji cikin dare ina shiga d'akin na lallasheta tayi bacci na koma d'akina
da nufin da safe na tambayeta amma da safen duk yanda naso tabud'e baki tayi magana amma
abu ya faskara".
Yarima Fudhal yayi shiru nad'an wani lokaci kafin yace.
"Bari musan abinyi to a tafi da ita hospital d'inmu domin akwai kayan aiki sosai, zamu gano inda
matsalar take".
Fulani Bingel ce tayi sallama dai-dai wannan lokacin Fudhal ya amsa fuskarsa fal murmushi ya
durk'usa ya gaishe da ita, suka gaisa da Fulani Sokoto tana tambayar.
"Ina mai jikin?, naji ance Jalila ba taji dad'i ba".
"E tana d'aki ".
Cewar Fulani Sokoto kenan, Fulani Bingel ta mik'e ta nufi d'akin yayin da Fudhal da Fulani
Sokoto suka take mata baya.
"Allah sarki !, Sannu kinji Jalila Allah k'ara sauk'i".
"Amin".
"Amma mene yake damunta?".
Fulani Sokoto ta d'anyi dariya tare da bata amsa.
"Mafarki ne tayifa shine baki d'aya ta koma haka".
"To a san abinyi tun da wuri mana".
Fudhal ne yayi saurin bata amsa a wannan lokacin.
"E muna kanyin hakan kika shigo, nace a kaita hospital namu sai induba inda matsalarta take".
Fulani Bingel ta gyad'a kai tare da mik'ewa suka fito daga d'akin dukansu, tayiwa Fulani
Sokoto sallama ta fice daga part d'in yayin da Fudhal da Anwar suka tako mata baya.
Sai da suka raka ta har cikin falonta sannan suka fito suka koma d'akin Fudhal domin ya d'an
kwanta ya huta sabida shima ba lafiyarce gareshi ba.
Kwanciya yayi bisa carpet tare da d'ora kansa kan kusun, Anwar ya zauna kusa da shi yana mai
k'are masa kallo kafin ya bud'e baki ya fara magana.
"Wai Fudhal mene matsalarka ne?".
Fudhal ya bud'e ido a hankali tare da saukesu kan fuskar Anwar yana mai jifansa da wani
guntun murmushi da bai wuce kan leb'ansa ba.
"Tambayarka nake, wai ina kaje ma jiya da dare ne?"
"Wajen Aynu".
Ya bashi amsa a tak'aice.
"To amma meye dalilin tashin ciwonka, kasan a halin da nazo na tadda kai kuwa?".
"Koma a wanne yanayi ne nasan zaka iya tadda ni, sabida abin da ya faru ajiya bana sonma ina
tunashi ko kad'an".
"Aynu da bakinta tace bata sona ta tsanane ita bazata aure ni ba, tariga ta tsai da wanda zata
au...!".
Maganar ta mak'ale a mak'oshinsa sabida