Showing 45001 words to 48000 words out of 88612 words
Chapter 16 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
da kowa a cewarsa kafin dawowata an mance da komai nima kuma na
mance, amma bai san hakan babbar matsala ya jawomin ba, sabida ni kai na tun da naje k'asar
tsayin shekaru goma sha shida kenan abin yana raina wallahi Anwar k'arshema sanadin hakan
ne ya jawomin ciwon zuciya..!".
"What...!, ciwon zuciya fa kace?".
"Yes...kana mamaki ne?".
Anwar mik'ewa yayi a rud'e ya fara duba magungunan da Yarima kesha domin bai tab'a dubawa
ba bare har yasan abin da yake damunsa.
"Ban da kai a yanzu nan gida babu wanda yasan abin da yake damuna sai doctor Mansur da
ya zo ya duba ni farkon dawowata time d'in da nayi fama da fever shima na rok'eshi kada ya
sanarwa kowa kuma bai fad'a d'in ba".
Shiru ne ya biyo baya kowa yana tunani a cikin zuciyarsa, can Anwar ya nisa tare da duban
Yarima.
"Kayi hak'uri komai zai wuce insha Allahu !, zanyi k'ok'ari wajen shawo kan Mahaifin Aynu !,
tun da ai abisa kuskure abubuwan suka faru ina ganin idan yasan gaskiya zai sauko !".
Yarima ya dubi Anwar kamar zai ce wani abu sai ya fasa, ya mai da kai kawai bisa katifa ya
kwanta.
***
"Me ki kace Aynu !, ki na so ki cemin Yarima Fudhal ne yayi sanadin mutuwar yayanki?, yayi
sanadiyyar rasa k'afar Baba tare da rasa idon Umma?".
"Ehh haka ne Zainab!, nima ajiya nasan wannan al'amarin".
Zainab tayi shiru tana duban Ayn cike da tausayawa, kafin ta dafa kafad'arta.
"Kenan ya zama dole ki rabu da Yarima kenan?, ko badan hakan bama iyayenku basa son
had'in?".
"Ehh".
"Bani da abincewa daya wuce addu'a Aynu, Allah yayi maki zab'i mafi alkhairi!".
"Amin summa amin".
Aynu ta fad'a tana mai share kwallar da ta taru cikin idonta.
***
"Ina son ganin Aynu !, Anwar dan Allah ka raka ni!".
"Kana son ganin Aynu kuma Fudhal?".
"Ehh haka nace".
"Amma taya zaka ga Aynu yanzu a cikin wannan halin, kuma da dare haka?, ka da ka mance
da a bubuwan da suke faru wa ?".
"Na sani Anwar amma ko ta wanne hali inason ganinta !, dan Allah muje ka raka ni Allah idan
ban ganta a yau ba zan shiga wani hali....!".
"In baza kaba kaga tafiyata".
Yarima Fudhal ya mik'e cike da k'arfin hali ya zari key d'in mota zai fita bai ko damu da yanayin
jikinsa ba.
Ganin da Anwar yayi tabbasa da gaske tafiya zai yi, kuma a cikin halin da yake ciki, shi yasa
Anwar ya mik'e da sauri ya bi bayansa tare da kiran sunansa.
Tafe suke a mota Anwar ne ke driven d'insu babu mai cewa da wani komai, har suka isa
unguwarsu Aynu Anwar yayi parking dai-dai layin gidan nasu, Yarima har ya riga Anwar fitowa
sai da Anwar ya d'an taka da gudu kafin ya taddashi yana fad'in.
"Wai kai lafiyarka kuwa?".
Yarima bai ko kalleshi ba bare ya kulashi.
Tsaye take k'ofar gidan nasu tare da Ya Sayyadi Umar suna hira, galabin hiran shine domin
Aynu daga uhmmmm sai uhm-uhmm abin da take furtawa kenan domin ko kad'an hiran ba tayi
mata dad'i, Allah-Allah takema taji yace zai tafi.
Tana wannan halinne taji k'irjinta ya tsananta bugu da sauri, k'amshin turarensa taji ya daki
hancinta kamar ance ta d'ago kanta, tana d'agowa suka had'a ido duk da garin da d'an duhu
amma akwai hasken farin wata, a tare zuciyoyinsu suka buga lokaci guda Aynu ta mai da kanta
k'asa da sauri ba tare data sake marmarin sake kallon inda yake ba!.
Ya Sayyadi Umar ne ya lura da cewa wajenta suka zo, kuma ya gane Yarima ne ya dubi Aynu
yana fad'in.
"Zo muje mu gaisa da alamu wajenki ya zo?".
"Kaje kawai ni babu inda zanje!".
"A'a kada kiyi haka Aynu bak'onka fa Annabinka, kinsan kuma babu kyau wulak'anci, ki
taimaka dan Allah ki saurareshi ki ji da abin da ya zo kinji?".
Bata kuma cewa komai ba tabi bayansa, Ya Sayyadi Umar ya mik'awa Anwar hannu sukayi
musabiha ya mik'awa Yarima Fudhal amma Yarima ko kallon inda yake baiyi ba, Ya Sayyadi ya
sauke hannunsa cike da murmushi yana mai da kallonsa kan Aynu.
"Zan jira ki".
Haka yace da ita ya koma inda suke tsaye ya tsaya yana zaman jiran Aynu.
Aynu ta kau da kanta gefe ba tare da ta ce da su komai ba, har tsayin wani lokaci shi Anwar
yama rasa ta inda zai fara domin Aynu ayau sai yaji tayi masa kwarjini da yawa gashi kuma ta
had'e girar sama da ta k'asa alamun babu wasa, Yarima kuwa ya kafeta da ido babu ko k'iftawa
sai faman doka murmushi kawai da ya keyi wani sanyin dad'i na ratsa dukkan sassan jikinsa,
Anwar ne yayi k'arfin halin fad'in.
"Sannu Gimbiyarmu, kina lafiya?".
"Lafiya k'alau".
Hakan da tace ne ya bashi damar ci gaba da fad'in.
"Kina neman zauta Yariman mu da soyayarki ko?, yanzu dai gashi nan ya tasomu cikin daren
nan ya ce inbai ganki ba babu zaman lafiya....!".
Kallon data watsa masa ne ya sanya shi tsuke bakinsa tun kafin ya k'arasa maganarsa.
"Yanzu ai ya ganni ko?, to zaku iya tafiya daga yau bana k'aunar sake ganinku k'ofar gidanmu
har a bada !, wancen shine wanda zan aura nan da lokaci k'ank'ani fatan kun gane?".
Bata jira mai zasu ce ba tajuya abinta, ba Anwar ba hatta Yarima mutuwar tsaye yayi a wajen,
yama rasa ta cewa domin dama kasa furta komai yayi sabida bai san mai zai ce da ita ba,
amma ko babu komai ya d'anji sanyi a cikin ransa domin yaga farin cikin rayuwarsa
Qurratul-aynun sa (Sanyin idaniyarsa).
Anwar ne ya ja shi har zuwa mota suka shiga Anwar ya tada mota suka bar layin.
"Yanzu kenan Aynu ta san komai?".
Cewar Yarima kenan yana mai duban Anwar, Anwar bai dube shi ba ya fara fad'in.
"Ai ba sai ka tambaya ba, daga maganganun da take da irin kallon da take jifanmu da shi
wannan kawai ya isa ka bawa kanka amsa...!".
Yarima Fudhal yayi a jiyar zuciya tare da kwantar da kansa bisa kujerar motar ya lumshe ido sai
ga hawaye na bin gefan idonsa a hankali ya furta.
"AYNUL-HAYAT fountain of life.....!".
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
27
BAYAN SATI 'DAYA...!
Cikin satin abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da d'an samun sauk'in jikin Fudhal,
hakan ya sanya aka gudanar da bikin bud'e sabon asibitin Yarima Fudhal da mai martab'a ya
gidana masa, an fara aiki gadan-gadan kwararrun likitoci aka d'auka domim taya Yarima Fudhal
gudanar da asibitin yanda ya kamata.
Duk irin dauriya da dannewa da Yarima ya keyi amma hakan na neman fin k'arfinsa, domin
wani lokacin yakan kasa daurewa zuciyarsa daga abin da take muradi, har sai ya d'auki mota
yaje layin gidansu Aynu ya tsaya har lokacin zuwa islamiyyarta sai ya ganta sannan yakan d'anji
dama-dama cikin ransa, Aynu da Zainab basu tab'a gane shine a cikin motar ba domin yakan
d'auko d'aya daga cikin motar abokan aikin sane baya d'aukar motarsa sabida gudun kada su
gane shi.
Al'amarin Aynu kuwa a kullum burinta bai wuce tamance da Yarima Fudhal ba, tana so tasa
aranta tamkar mafarkinsa tayi ta farka, sai dai hakan ya gagara a gare ta, sau tari idan suka zo
wuce wa ta inda Yarima ke tsaye Aynu takanji bugun zuciyarta ya tsananta sosai kuma tanajin
k'amshin turarensa sai dai Zainab takance ba shi bane kawai dai har yanzu tana son sane
shiyasa takeji kamar shine a motar, batun turare kuma ai bashi ka d'ai ne ke amfani da irin
saba, ba shi kad'ai campany suka yiwa ba, ita dai Aynu tana barin zancen ne kawai domin
Zainab ba ta yarda amma tanaji a cikin ranta tabbas Yarima ne.
"Wai Uwar soro har yanzu aikin yak'i samuwa ne?".
Uwar soro ta d'an risina tana fad'in.
"Wallahi ranki ya dad'i duk iya k'ok'arin da nakeyi abin ya faskara na rasa yanda zanyi
insamo...!".
"Kinga idan kawai bazaki iya ba ki sanar dani tun da wuri !, abu kusan wata guda amma ya
gagara?".
"A k'ara hak'uri dai ranki ya dad'e insha Allah cikin satin nan komai zai kammala".
"To babu damuwa amma fa kiyi aiki da nutsuwa da kulawa".
"Babu matsala ranki ya dad'e kada ki damu".
"Shi kenan tashi kije".
Uwar soro ta mik'e tabar d'akin, Jalila dake zaune gefan Fulani Sokoto tana faman danne
dannan wayarta tayi tsaki tare da wurga wayar kan kusun tana fad'in.
"Aikin banza!, Wallahi Mama ke ki ke yarda da aikin wasu bare, ni da kin yarda da tuni anyi
komai ya wuce munriga munsan matsayar da muke".
Fulani tayi murmushi tare da fad'in.
"Jalila kenan !, Ke fa yarinya ce har yanzu , amma bazank'i ta taki ba, me kike ganin zaki wanda
bazamu iya ba?".
Jalila gyara zama tayi tana fuskantar Mahaifiyarta sosai.
"Yauwa Momy abin da ya kamata ki ce kenan tun d'azu, ki bani kwana biyu cikin kwanakin
tabbas zan samo maki takun k'afar Fudhal".
"To amma ta yaya?".
"Momy...! Ke dai kawai ki zuba ido".
"Bawai nak'i ta taki ba ne, inajin tsoron al'amarin ne kawai, amma dai kiyi komai cikin nutsuwa
da taka tsan-tsan, domin kinfi kowa sanin yanda Fudhal da d'an'uwanki suke, ban-bancin
kamanni ma kad'anne haka wajen kayansu zuwa takalmi kinsan abune da sai mutum ya lura
sosai da kulawa sabida ka da a samu miskila".
"Haba Momy...!, Ni har sai anmin wannan baya ni, idan ni ban iya tan-tance Fudhal da Jalil ba
waye zai gane?".
"Uhmm to haka ne kuma Jalila".
"Yauwa wai Mama ina Jalil kuwa?, kusan 2week fa kenan bana ganinsa cikin gidan nan?".
Fulani tayi ajiyar zuciya tare da tab'e baki tana fad'in.
"Ni ina zan sani Jalila..! komai ina yi ne domim gobenku, amma shi baya fahimta kullum
al'amarin nasa k'ara gaba yake yi, shi da ya kamata ace yana girma yana hankali amma ina...!,
waye zai yarda abashi ragamar Sarauta a cikin wannan halin nasa?".
"Ka da ki damu Momy komai zai dai-dai ta".
"Fatana kenan Jalila".
***
Dawowarsa kenan daga asibiti lokacin kusan k'arfe biyar da mintuna na yamma ya zauna
gaban Fulani Bingel tare da fad'in.
"Wash Hajiya wallahi nagaji yau sosai".
"Kai dai ka shigesu da lalaci kamar ba namiji ba?".
"Namiji baya hutu kenan Hajiya?".
"Ni dai bance ba, amma kai kullum ka dawo wash ne sallamarka cikin falon nan tun da ka fara
aiki".
Yarima Fudhal yayi murmushi wanda ya baiyana hak'oransa waje, amma daka kalli fuskarsa
zaka san yana k'ok'arin danne damuwar da ke kwance bisa fuskarsa ne.
"Au.. Magaji ai kuwa zama bai ganka ba, yanzu akayimin waya Sadiya ta haihu ".
"Masha Allah mai ta haifa Hajiya?".
"Yan biyu ne aka samu mace da namiji".
"Allah ya rayasu yanzu kuwa zanje, fatan tana lafiya dai ko?".
"Lafiya k'alau ta haihu har an sallamesu daga asibitin sun koma gida".
Yarima Fudhal ya mik'e yana fad'in.
"Bari inje inshafo maki kan jikokin naki".
"Ko dai kaje ganin 'ya'yanka dai?".
Nan ma dariya sukayi a tare, tana bashi sallahun ya gaishe da su tare da mik'a masa wata
k'atuwar leda fara ta ce ya kai mata, Yarima Fudhal ya amsa ya fice, Fulani Bingel ta bishi da
fad'in.
"In kaje ka samu kaci abinci dai".
Ya amsa da "to Hajiya".
Bayan fitarsa Fulani Bingel murmushi tayi a fili take fad'in.
"Ina ruwan Magaji...! shi dai yana son yara sosai, Allah dai ya nunamin ranar da zanga naka
yaran kai ma".
Baki har kunne ya shiga cikin gidan, da sallama ya sanya kai cikin falon mijinta ne zaune
shi da yaransa guda biyu mata kusan kansu d'aya ga kuma mugun kama da suke yi, yaran
tubarkalla gasu da kyau, da gudu yaran suka taso suna fad'in.
"Oyoyo Uncle..!".
Suka rungumeshi ya tsunna ya rumgumosu jikinsa yana fad'in.
"Saleema da Saleena anyi k'anne kuma baki ba rufuwa".
Dariya suka yi atare suka sumbaci kumatunsa, shafa kansu yayi yana fad'in.
"Nagode yara na !".
Ya mik'e ya k'arasa wajen Baban nasu suka gaisa, yana tambayarsa .
"Ina Maman tasu?".
"Suna ciki ka shiga ku gaisa mana".
Yarima Fudhal ya kama hannun yaran suka shige cikin d'akin, Aunty Sadiya na kwance bisa
gado sai jariran agefan ta, gefe guda kuma Aunty Sa'ida ce da wasu mata su biyu, suka gaisa
da matan suka fice.
Yarima ya gaishe dasu Aunty Sadiya ya d'auki yaran yana mai k'are musu kallo, kafin yayi
murmushi yana duban Aunty Sa'ida.
"Aunty na sai nakejin yaran nan kamar Aynu d'ita ce ta haifamin wallahi, shi yasa Hajiya na
gayamin na kasa daurewa sai nazo na gansu".
Aunty Sa'ida ta tab'e baki kawai tana dubansa cike da takaicin maganar da yayi.
"Au wai kai har yanzu baka bar maganar yarinyar nan ba?".
Cewar Aunty Sadiya kenan tana daga kwance.
"Taya kuwa zan barta Aunty na, baki san yanda nake jinta ba a cikin raina Allah".
"Sai kayi kuma, iska na wahal dame kayan kara".
Aunty Sa'ida ta fad'a tana mai jan hannuwan Saleema da Saleena suka fice daga d'akin, Yarima
Fudhal ya bita da kallo ko kad'an bayajin dad'in yanda take yi masa akan Aynu, Aunty Sadiya ta
dafa hannunsa tana fad'in.
"Kar ka damu k'anina, komai zai wuce soyayyarka ta gaskiya ce insha Allahu zaka sameta
idan har matar kace, idan kuma Allah bai k'addara matar ka bace kayi hak'uri kaji sai Allah ya
musanya maka da mafi alkhairi".
Yarima Fudhal murmushi yayi cike da jin dad'in maganar Auntyn tasa, bai ce komai ba illa mai
da kallonsa kan 'yan Jariran da yayi yana mai kai musu kiss a goshinsu cike da so da k'auna
sosai yakejin yaran cikin ransa.
Hello
Kuyi hak'uri da wannan dan Allah babu yawa rashin chaji yaja nayi muku typng kad'an dan kada
kuji ni shiru.
Nagode sosai da sosai masoyana kuna raina ko da yaushe.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
28
"Wannan shine gaskiyar abin da ya faru, please Baba..! Dan Allah ka taimaka kajanye
hukuncin da ka d'auka, ka san gaskiyar abin da ya faru yanzu wallahi Yarima yana son 'yarka
da gaske so na tsakani da Allah".
Baban Aynu shiru yayi kansa na k'asa, tsayin lokaci ya shafe yana tunani kafin ya d'ago kansa
ya kalli Anwar dake zaune yana jiran yaji amsar da zata fito daga bakinsa.
"Yaro kayi hak'uri kuje ku sake wata shawaran wannan ba zata samu karb'uwa ba, domin
nasan ka zo ne da silar yaudara kamar yanda kuka zo da farko".
"Baba wallahi dukkan abin da na fad'a a yanzu gaskiya ne, idan da farko munzo da yaudara
wallahi tallahi Allah d'aya ne Baba bazan yi rantsuwa akan k'arya ba dukkan abin da na fad'a a
yanzu babu haufi a cikin sa".
Shiru ne ya sake biyowa baya kafin Baban Aynu yace.
"Shikenan kaje zan neme ka".
Anwar yayi godiya tare da mik'ewa ya bar wajen zuwa cikin motarsa ya tada ita ya bar bakin
kasuwar, Baban Aynu ya shafe tsayin lokaci zaune yana nazari a kan maganar da Anwar ya
sanar da shi yanzu, kafin ya mik'e ya nufi gida zuciyarsa cike da wasi-wasin al'amarin.
***
"Kayi farin ciki Yarima na sanarwa Baban Aynu gaskiya da dukkan alamu kuma ya yarda
damu yanzu, ya kayi tsaye kana kallona baka farin ciki ne?".
Yarima ya ajiye wayarsa dake rik'e a hannunsa kan table d'in gabansa