Showing 3001 words to 6000 words out of 88612 words

Chapter 2 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

16 Aug 2025

8313

"Masha Allah a dage sosai".

"Insha Allahu Ummata".


"Duba cikin kwanun da ke can rufe akwai abinci ki d'auka kici".

"To Ummata".

Tamik'e ta dauko ta zauna har tasa hannu zata fara ci sai kuma ta dubi Ummanta ta da
tambayar.

"Umma kinci abincin kuwa?".

"Ehh naci 'yar gidan Umma, har Babanki shima yaci wannan nakine kici abinki".

Aynu tasa hannu ta ci gaba da cin abincin ta.

"Ummata waye da aikin ladan nan haka?".

"Kema ko ba'a fad'ab ba kinsan wace ai, Tasallah ce Babar Zainabu ta kawo mana d'azu".

"Amma Umma babu abinda zamuce da Maman Zainab sai dai Allah yasaka mata kawai".

"Amin dai, yauwa inkin gama inason magana da ke".

"To Ummata nagama ai, bari in wanko hannuna".

Tafice daga cikin d'akin hannunta rik'e da kwanun data gama cin abincin.
[07/07, 16:15] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*




NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®


FIDDDAUSI S.A (QURRATUL-AYN)©



03


Notes...............kuyi hak'uri nayi mistake a page 1 MAI BABBAN D'AKI ita ce mahaifiiyar Sarki,
UWAR SORO babbar kwarkwara ce, Zakuga nasake post nashi na gyara ne.

*** *** ***


Ta wanko hannunta ta dawo ta zauna kusa da Ummanta, Ummanta ta kamo hannunta
tarik'e kafin ta fara magana.


"Aynu !, kiyi hak'uri abisa yanda kika tsinci kanki a rayuwa, ki sani komai yake faruwa da bawa
haka Allah yatsara masa tun kafin zuwansa duniya, nasan ke mai hak'uri ce Aynu, ina rok'anki
ki k'ara akan wanda kikeyi, domin bahaushe na cewa mahak'urci mawadaci, nasan wata rana
sai labari".
Ta danyi ajiyar zuciya na wani lokaci, kafin taci gaba da magana.

"Mahaifinki shine ya hanamin fita neman na kaina, a cewarsa bazanyi bara ba, kamar yanda
shima bazaiyi ba, amma kuma duk wani hanyar samunsa ta kulle, gashi ni bana da ido bare inyi
koda sana'ar k'arfice a gida, yau Tasallah tazomin da batun idan mun amince zata kaiki gidan
sarki aiki, ana samun abinci sannan da albashi duk wata".

Murmushi ne ya sub'ucewa Aynu duk da 'yar kwallar dake saman idonta, tarik'e hannun
mahaifiyarta ta k'am tana fad'in.

"Amma kun amince ko Ummata?, dannima ba nason bara wallahi gara nayi ko wanne aiki
indai za'a biyani mu amfana".

Ummanta itama murmushin tayi.

"Ya zamuyi Aynu?, ai dole mu amince sabida bamu da wani zab'i daya wuce amincewar tamu".

"Kai amma naji dad'i Ummata kinga yanzu zamu samu kud'i mud'inka kaya musayi ta barma da
katifa da takalmi, sannan kuma ga abinci, yanzu bamu ba yunwa ko Umma?".

"Uhmmm Aynu kenan, sarkin buri arayuwa Allah dai ya warware mana !".

"Amin Ummata".

Daga haka suka cigaba da hira, Ummanta tanayi mata nasiha akan ta kula da kanta tayi
biyayya kada tayi abinda za'a tsa neta ko ta b'atawa wani rai, sannan ta gargad'e ta akan ta
zama mai hak'uri a duk inda tasamu kanta.


WASHE GARI....!

Washe gari tun asuba Aynu ta tashi tayi sallah tad'ebo ruwa ta cika gidan, tayi dukkan
aikace-aikacen data saba kullum, tazo ta zauna gaban Ummanta ta gaisheta taje ta gaida
Babanta ta dawo ta zauna tana jiran gari yad'anyi haske ta fita, domin babu agogo a gidan
nasu.
A nanma nasihar Ummanta tayi ta mata, kafin tayi mata sallama ta lek'a d'akin Baban nata tayi
masa sallama shima ya biyota da addu'a ta fice daga gidan.

Yau wani nishad'i ta keji arayuwarta domin ita dama burinta na rayuwa bai wuce yanda zata
taimaki iyayenta ba, wad'anda sukai d'awainiya da ita tun tana cikin ciki, duk da gararin rayuwa
da taulacin dasuke fama dashi amma hakan bai hana musu ganin sun kyautata mata ba, sai
taci kafin suci, sai ta sha suke sha, intayi kuka suyi kuka idan tayi farin ciki suyi farin ciki, ba dan
yanda rayuwa ta juyewa mahaifinta ba tasan bazai tab'a bari taje wani guri aikatau ba, tasan
iyayenta sun sota arayuwa to itama meyesa ba zata kyautata musu ba?.


Haka ta isa gidan Babah Tasallah tana sak'e-sak'e cikin ranta, da sallamarta ta shiga gidan,
Zainabu dake shara ta amsa mata sallamar tana fad'in.

"Uwar 'yan sammako k'arfe shidda fa? Amma har kinzo!".


Aynu tayi murmushi ta bata amsa da fad'in.

"Amma aikin san da zafi-zafi akan daki k'arfe".

"Da gaskiyarki 'yar gidan Umma".

Babah Tasallah ta fad'a tana mai fitowa daga d'akinta, Aynu ta d'urk'usa ta gaisheta ta amsa
fuskarta fal murmushi tana tambayarta ya ta baro Ummanta ta, Aynu ta bata amsa da.

"Lafiya k'alau take, tace ma agaishe da ke".

"Ina amsawa, shiga d'akin ki zauna kafin da rabin tayi".

Aynu ta shiga ta zauna, Zainabu ta gama shara ta kawo musu abin kari koko da k'osan da
Babah Tasallah tayi tun asuba, suka karya dan kada su tafi da yunwa.


6:30.

Shida da rabi dai-dai suka isa gidan Sarkin tun awaje Aynu ta saki baki tana kallon girman
gidan da tsaruwarsa, sabida ita ba ta yowa nan haka, to mema zai kawota tunda ita dai bayawo
take ba, Zainabu ma tayi nacin suzo tak'i zuwa sai yau da aiki yakawota.

Bata k'ara tsinkewa da al'amarin gidan ba sai da suka shiga soron fad'a anan ta sha kallo kafin
su wuce zuwa ciki gidan, nan kuwa mutuwar tsaye takusa yi, aranta tana fad'in.

"Dama akwai masu irin arzik'inan aduniya?, Allah yabasu kud'i da mulki amma basu damu da
talakawansu ba".

"Ke Aynu!, me kike kallo ne? ki nutsufa, duk abinda kika ga munayi kema kiyi".

Cewar Zainabu kenan tana mai tab'ota, domin taga tad'daga kai sama tasaki baki tana kallo.

Wajen Jakadiyya suka wuce kai tsaye, suka gaisheta anan suka tadda 'yan mata guda hud'u
a tare da ita, 'yan matan suka hauyiwa Aynu wani kallom gani-gani kamar sun ga kashi, ita dai
hankalinta yana ga kallo, bama tasan sunayi ba.


"Ga yarinyar da nake fad'amiki, 'yar gidan Malam Nasiru gurgu ce".

Babah Tasallah ta gabatar da ita wajen jakadiyya.

Jakadiyya ta k'arewa Aynu kallo kafin tace.

"Allah sarki ! Yarinya k'arama da ita kuwa, Allah yasa dai ta samu domin mutum uku ake
buk'ata kuma kinga ga guda hud'u sun zo tun d'azu, ban zaci zaki kawo taba domin kina k'ila wa
k'ala akan zuwan nata, amma dai bari inkaisu wajen Fulani Bingel itace zata zab'a".

Babah Tasallah tace.

"Amin dai insha Allahu zata samu".

Aynu kuwa jin ance Allah yasa ta samu tuni 'ya'yan hanjin cikinta suka murd'a gabanta yahau
bugun sha uku-uku.

Jakadiyya dai ta d'ebesu su biyar suna binta abaya har b'an garen Fulani Bingel, Aynu har
tuntub'e take tsabar kallo.

Suna shiga Jakadiyya ta zub'e gaban Fulani, suma sukayi yanda tayi suka kwashi gaisuwa,
Aynu ta d'ago kai tana duban Fulani mace kyakykaywa mai haiba tasha ado da wani light blue
d'in leshi dayasha adon stone...., jitayi an mintsineta ta gefanta dayake tana kusa da Jakadiyya

tajuyo taga dukkansu kowa kansa ak'asa itama ta duk'ar da nata.

"An samo guda biyar duk da uku ake da buk'ata sai a azab'a ko?".

Fulani ta gyad'a kai, tare da bada umarnin duk su mik'e tsaye, ba musu suka mik'e kansu duk a
k'asa, ta bisu d'aya bayan d'aya da kallo, kafin tace ta gefan Aynu tayi gefe, sannan ta kuma
zab'ar wata guda d'aya, yarage saura mutum d'aya ke nan?.

Jikin Aynu sai rawa yake ta tsananta addu'a sosai Allah yasa azab'e ta cikon ta ukun, domim
sungama sa rai akan wannan aikin.

Cikin ikon Allah akace Aynu ta koma cikin mutum biyun da aka fara zab'a, tuni ta saki wata
nan-nauyar ajiyar zuciyar.


"Wad'an nan ukun sunyi, biyun ki kai su kicin suyi aiki acan, ku kuma koware kanku".

Ko wacce ta tsaya ita kad'ai aka nuna ta farko.

"Kece zaki dinga kula da abincinsa, wannan kuma ta kula da sharan falo da goge-goge, sai ke
!".

Akayi nuni da Aynu, gabanta yafad'i, tana jiran taji mai za'ace.


"Wannan yarinyace shiyasa nazab'eta, ke zaki dinga kula da gyaran d'akin kwanansa, ki kuma
tsaftace band'aki ko da yaushe, sai kije ki basu kayan da zasu saka ku jira zuwan Yarima domin
yana hanya anje tarbarsa".

Jakadiyya tazube agaban Fulani tana fad'in.


"Angama Fulani".

Muma muka zube tare dayin yanda tayi, muka mik'e da baya da baya muka fice, ashe wai ba'a
juya musu baya sai mutum yaje bakin k'ofa, araina nace ikon Allah wani abun sai gidan sarauta.


Da murnata muka isa inda mukabar su Babah Tasallah nasanar musu an d'aukeni, suma sunyi
farin ciki sosai, Babah Tasallah tayiwa Jakadiyya sallama ta tafi gida, mu kuma akayi wani d'aki
damu.

Muna shiga nan naga abin mamaki, d'akine ciki da falo shak'are da kaya kala biyu pink da blue
sai kace a shago, nan akace mu d'auki blue set biyu tare da abin wuya murjani da abin
hannunsa da 'yan kunne.

Jakadiyya tabarmu cikin d'akin muka sanya kayan, kayan kuwa da Jakadiyya ta nunawa kowa
yad'auka dai-dai jikinmu kamar angwada.

Muka fito d'as damu kowa duk inda muka wuce sai kallonmu ake, ban saniba kyau mukayi ake
kallonmu ko akasin haka?.

Mai makon mu koma cikin gidan sai naga kowa yana fita waje anjeru tun daga bakin k'ofar
shiga gidan har zuwa soron fada, ashe pink d'in unifoam na b'angaren Fulani Sokoto ne,
b'angaren Fulani Bingel blue, sai naga maza sunyi nasu layin mata ma haka, Allah ya taimake
ni na tsaya kusa da Zainabu, mintuna kad'an da tsayuwarmu aka buga wata uwar bindiga data
sanya 'ya'yan hanjina kad'awa, na dank'e hannun Zainabu k'am, ita kuwa tana tamin dariya tana
fad'in.

"Sarkin tsoron tsiya".

K'asa-k'asa take maganar da dariya.

Ana gama buga bindigar kuma sai ga jiniyar kwanon motoci tana tana kawo kai.
[07/07, 16:15] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®


FIDDAUSI S.A (QURRATUL-AYN)©.



04



•••


Sarki ne da muk'arrabansa suka fara sau kowa fadawa suka ke wayesu suna yi musu kirari.

Babban abinda yabani Mamaki ya kuma d'auremin kai, shine sauran fadawan da suke tsaye

bisa layi sai naga kowan ne mutum ya kwanta bisa cikinsa, Sarkin yataka yabi takan bayansu,
har sai da yashiga cikin fada, suka mik'e suka kewayeshi yazauna bisa karagarsa, sanna suka
dawo suka tsaya jiran fitowar yarima.

Ya ziro k'afarsa guda d'aya sai da yad'au mintuna sama da biyar kafin ya sake ziro d'aya k'afar
cike da izza da k'asaita yafito yanda mahaifinsa yayi shima haka yayi takan bayan bayin fada
yabi.

Sai da yashiga soron fada shima sannan sauran 'yan uwansa mata masu aure da su Jalil da
Jalila suka fito suma suka nufi fada, amma su bata kan mutane suka bi ba.

Ni kuwa abin ya tsaya min arai sosai, haka muka juya muka nufi cikin fadar zuciyata cike da
wasi-wasi da ko kwanton al'amura na wannan masarauta, na fahimci wani abu guda d'aya ga
masarautar tun yanzu, wato dai basu d'auki wani talaka abakin komai ba.

Sai da yarima yayi gaisuwa ga mahaifinsa Sarki Ubaiyd ya rungume d'an nasa cike da so da
k'auna, kafin yamik'e yashige cikin gidan mu kuma mu da wasu mazan fada muka take masa
baya.

Kai tsaye wajen Mai Baban d'aki muka nufa wato mahaifiyyar Sarkin kuma Kaka a
wajensu Yarima, nan muka zube tsakar d'akin tana zaune abinta tasha irin shigarnan ta mutan
da wadda suke kira da suna b'anti-b'anti, asa riga a d'aura zani har saman k'irji sannan a kawo
wani zanin ad'aura k'asan wanan zanin, abun hannu da na wuyanta duka azurfa ce, mace mai
fara'a, anan sun shafe kusan awa guda suna gaisawa cike da barkonci, kafin su fito su nufi
b'angaren Fulani Sokoto.

Fuskarta wasai ta karb'esu, har da rungume Yarima wai sabida murna, muma kanmu dake
sabbin zuwa ne mund'auka da gaske tana farin ciki da dawowarsa sab'anin yanda sauran
mutan gidan suka sani.

Muka fito muka nufi b'angaren Fulani Bingel wato mahaifiyarsu Yarima Fudhal.

Muna shiga muka zube muka sake d'iban gaisuwa, ni kuwa da man nagaji da tsayuwa ina zama
sai naji wata rahama ta ziyarce ni, musamman da naga sunyi kaman basu san muna wajen ba,
araina nace.

"Ma huta ma wannan azaba har ina ?, da man haka aiki yake a gidan saraunata?".


Sun shafe kusan a wanni biyu suna gaisawa, suna hira cike da so da k'aunar tare da murnar
dawowarsa lafiya, amma shi abin mamaki wayarsa ce a hanunsa yana danna-dannesa.

Sai idan sun tambayeshi abu ya basu amsa da ehh ko a'a, amsar bata wuce haka abin ya bani

mamaki sosai, na lura su basa damuwa darashin ko inkula d'insa, ko haka halinsa yake? Oho.

Mik'ewa yayi alamun yana buk'atar yaje ya huta sukayi sallama, mu kuma muka dafo masa
baya muka fito.

Yana shiga part d'insa yayi kwanciyarsa bisa lallausan carpet d'in dake shinfid'e tsakar d'akin ya
ta da kansa da kusun, Jakadiyya ta zube a gabansa tana fad'in.


"Fulani taba da umarnin canja maka bayi, gasu nan guda uku".

Ta nuna ta farko.

"Wannan sunanta Naja'atu, wannan kuma Saima".

Sannan ta nuna ni.

"Ita kuma wannan Aynu, sune zasu dunga kula da nan wajenka yanzu".

Idanmu da muke tsaye munyi magana to shima yayi magana, ko d'ago kai bai yiba bare ma
yasan suwaye ke zaune awajen, kawai danna-dannenta yake abinsa a wayarsa mai kama da
littafi danni banko tab'a ganin irin taba sai yau a hannun yarima.

Jakadiyya bata damu da amsawarsa ba ko rashin ta, ta dubemu tana fad'in.

"Ku biyoni muje".

Muka fice da sauri muka bi bayanta, kicin muka nufa kai tsaye aka mik'o mana tire guda uku
manya ko wacce a cikinmu ta d'auki d'aya, Naja tad'auki mai kuloli manya, Saima ta d'auki mai
k'ananun kuloli da flat -flat da kofuna akai, ni kuma aka bani mai kayan mar-mari aciki (Fruit).

Muka d'auka muka kai d'akin Yarima yana nan inda muka barshi, muka ajiye a gefensa Naja
tad'auki flat ta zuba masa wani had'ad'dan farfeson kayan ciki, sannan ta zuba soyayyar hanta
a cikin wani flat da ban, ta sake d'auko flat ta zuba masa da faf-fan naman kai, sannan ta koma
gefe ta zauna.
Ita Kuma Saima a she duk kulolin data d'auko dambun nama ne aciki kala-kala ta zuba masa
itama ta koma gefe.

Ni kuwa nayi diri-diri na rasa ya zanyi masa da kayan fruit d'in dana d'auko, na dubi su Naja
naga ko kallon inda nake basuyi ba, na d'ago ka na dubi Yarima, da niyyar tambayarsa gabana
yayi wani mummunar fad'uwa, sai a lokacin naga irin tsan-tsar kyawun da Allah ya zuba masa,
domin duk shige da ficen da muke kai na ak'asa yake ban yarda ko kad'an na kalleshi ba.

Farine amma ba can ba mai matsakaicin tsayi ne, sumarsa bak'ace har zuwa sajensa da
gashin baki, yana da manyan idanuwa mai cikar gashin girane daka ganshi zaka san ma'abocin
son k'amshi da tsafta ne kuma masoyin son ado ne, zan iya cewa yafi kama da Fulani Bingel
domin kamanninsa da ita sunfi fitowa fili mutum ne mai haiba da kwarjini sosai.

Da sauri na mai da kaina k'asa nafasa tambayar tasa, nima na koma gefe kamar yanda naga su
Naja sunyi.


Mun shafe wajen mintuna talatin a zaune har zaman yafara gundura ta, sannan naga yamik'e
ya zauna, yajawo flat d'in farfeson kayan ciki, Naja tamik'e da sauri ta d'auki Spoon ta mik'a
masa yasaka cokalin a hankali ya d'ebi kad'an yakai bakinsa, ya hau taunawa kamar mai cin
magani, ya ture gefe haka yayi ta bin farfesun ko wanne flat cokali d'aya ya keyi ya ture, kafin
ya koma kan dambun daman shinema naga yad'anyi cokali uku zuwa hud'u, ya ture su gefe ya
k'urawa kayan marmari ido na wani lokaci can yaja tsaki, sai jin kakausar muryarsa mukai ta
daki kunnuwanmu .


"Wace takawo kayan fruit?, Je ku kiramin Jakadiyya".

Yayi maganar kamar mai koyan magana, kuma umarni da tambaya duk a lokaci guda, hanjin
cikina naji yak'ulle cike da tsoro na k'arasa inda yake na durk'usar.


Mai makon yasake magana sai gani nayi yamik'e tsaye, ban zata ba sai ji nayi ya jefe ni da tire
d'in kayan marmarin duk sukayi kaca-kaca afalon Allah yasoni babu wanda ya tab'a jikina,
amma duk da haka na takure waje d'aya jikina nab'ari.


Jakadiyya ta shigo da saurinta ta durk'usa tana nema min afuwa, nima ganin yanda tayi yasa
nima na durk'usa kanmu a k'asa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login