Showing 72001 words to 75000 words out of 88612 words

Chapter 25 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

16 Aug 2025

8303

suka fita daga cikin
harabar asibitin.


Sai bayan sun hau titi sannna Anwar yake tambayar.

"Abba ina zamu je ne?".

"Gidansu yarinyar da Fudhal yake so zaka kaimu".

Magaji Saif ya bashi amsa, Anwar ya take burki da sauri ba tare daya sani ba domin jin abin da
Magaji Saif ya faɗa.

"Subhanallahi..! Lafiya Anwar?".

Suka tambayeshi a tare.

"Babu komai burkinne yaɗan kwace mun".




***

Tsaye suke jikin bishiyar darbejiyar dake ƙofar gidansu Aynu, sun shafe tsayin lokuta bayan
gaisuwa ba tare da ɗaya daga cikin su ya sake furta ko kalma ɗaya ba, ko wanne yana
saƙe-saƙe cikin ransa.


Ya Sayyadi Umar shine ya katse shirun tare da yin gyaran murya kafin yace.

"Ya shirye-shirye kuma ya gajiya?".

Aynu taɗanyi murmushi tana mai bashi amsa.

"Alhamdullahi".

"Masha Allah, sai dai kamar akwai abin da yake damunki duk naga kin rame sosai lafiya
kuwa?".

"Lafiya ƙalau wallahi, kasan zirga-zirga ma ta ishi mutum ya rame ya fita haiyacinsa".

Ya Sayyadi Umar ya gyaɗa kai kawai, amma a zahiri bai gamsu da amsar data bashi ba.

"Na tambaye ki Aynu".

"Uhm ina jinka".


"Ina so ki faɗamin tsakaninki da Allah kada ki ɓoyemin dukkan abin da yake cikin ranki".

"Insha Allah zanyi ƙoƙarin ganin na gaya maka gaskiya akan abin da nasani akan dukkan abin
da zaka tambaye ni".

"Masha Allah, Aynu dan Allah har yanzu a cikin ranki kina son Fudhal?".


Dammm gaban Aynu ya buga take taji ƙwalla na shirin zubowa daga idanuwanta tayi ƙoƙarin
mai da ita tare da dai-daita nutsuwarta kafin tace.


"Amma me ya kawo wannan maganar?, koma zan so wani ai a dane yanzu dole kai zan so
domin nan da ranar juma'a kai zaka zamo miji agare ni".

Ya Sayyadi Umar yaɗanyi gajeren murmushi kafin yace.

"Haka ne maganarki shikenan Allah ya nuna mana ranar".

"Amin".

"Babu wani abu da kike buƙata ko?".

Aynu gyaɗa kai tayi ba tare data iya bashi amsa da bakinta ba.


Shiru ne ya sake ziyartar wajen tsayin lokaci Ya Sayyadi Umar na kallon Aynu yana karantar
yanayinta yana son yi mata magana akan Fudhal sai dai ya rasa ta Inda zai fara, kuma yana
fargabar yanda zata ɗauki maganar.


Har dai daga ƙarshe sukayi sallama ya tafi, tana tsaye har ya ɓacewa ganinta mai makon tayi
gida sai ta wuce gidansu Zainab sabida gidansu jama'a bazata samu damar sakewa ba.

Tana shiga gidan suka gaisa da Baba Ta Sallah kai tsaye ɗakin Zainab ta wuce ta faɗa kan
katifa tahau rera kuma sosai tsananin son ganin Fudhal da tausayin halin da yake ciki yana taso

mata har bata san sanda Zainab ta shigo ɗakin ba tana yi mata magana.


Aynu ta ɗago jajayen idanuwanta tana duban Zainab ba tare da tace komai ba, Zainab tazo ta
zauna kusa da ita tare da dafa kafaɗarta tana faɗin.

"Haba Aynu har zuwa wanne lokaci ne zaki yi haƙuri ki danganawa Allah komai akan al'amarinki
da Fudhal ne?".


"Bawai rashin dangana bane Zainab ina tausayawa halin da Fudhal ya shiga akai nane, shi
kuma haka ƙaddararsa tazo a kaina?, duk yanda naso daurewa zuciyata kasawa nake Zainab,
wallahi inason sake ganin Fudhal ko da sau ɗaya ne a rayuwata, ina takaici tare da jin haushin
kaina a kan abin da nayi masa nasan duk nice sila..!".
Takai maganar tana mai sake fashewa da kuka, Zainab ta dafa bayanta.

"Kiyi haƙuri Aynu kada ki ɗorawa kanki laifin abin da bake kika aikata ba, kisa a ranki haka Allah
ya ƙaddarowa Fudhal kada kidinga ɗorawa kanki laifi kisa damuwa a ranki har tazo tajawo maki
wani ciwon".





HELLO MY FANS


TEAMS AYNUL-FUDHAL

TEAMS AYNUL-UMAR


Nidai nace AYNUL......! Lol


ASHA KARATU LAFIYA SAI TOMORROW INSHA ALLAH.

BYEEE.


*YARIMA FUDHAL*

Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®



SADAUKARWA:-Namesy Phirdausy Jeebour.







42



Suna isa dai-dai kan layin gidan Anwar yayi parking motar suka fito suka taka da
k'afafuwansu.


Tun da suka shiga layin Magaji Saif da Mai Martaba suke bin gidajen da kallo tunaninsu bai
ta'ba kawowa akwai unguwar da talauci yayi k'atutuba irin wannan unguwar musamman Sarki
Ubaiyd sai gashi yazo da k'afafuwansa nemawa kansa suruka a cikin unguwar da ko a cikin
taswirar garin bai ta'ba tunanin akwai ta ba bare a taswirar kansa.

Suna isa k'ofar gidan Anwar ya nemi yaro ya aike shi domin yayi musu sallama da Baban
Aynu.
Bayan mintuna kad'an yaron ya fito tare da fad'in.


"Wai ance yana zuwa".


Anwar ya zaro Naira d'ari a aljihun wandonsa ya bawa yaron tare da fad'in.

"Nagode kaji".

Yaron ya tafi cike da murna, bayan wani lokaci sai ga Baban Aynu ya fito domin ganin wad'anda
ke sallama da shi, duk jikinsa ruwa da dukkan alamu fitowarsa kenan daga wanka.

Ganin Mai Martaba yasa shi fad'ad'a murmushinsa yana yad'in.


"Ashe kune ?, sannunku da zuwa bari in fito da tabarma ciki mutane sunyi yawa da mun shiga
daga ciki.

Magaji Saif ne ya amsa da.

"Babu komai wallahi ".

Baban Aynu ya koma ciki Jim kad'an sai gashi d'auke da tabarma ya shimfid'a musu k'ark'ashin
bishiyar darbejiyar suka zauna tare da gag-gaisawa, Magaji Saif ya bud'e baki ya fara magana.


"Nasan kayi mamakin ganinmu a dai-dai wannan lokaci, kuma nasan ni ba zaka shaida ni ba,
ni sunana Magaji Saif yaya ne ga Sarki Ubaiyd na wannan gari, mun zone ba dan komai ba sai
dan mu baka hak'uri akan abubuwan da suka faru, ka sani duk abin da yake faruwa bani da
masaniya wallahi kasancewar na shafe tsayin shekaru bana garin nan, sai yau Allah ya dawo
dani kuma ansanar dani komai hak'ik'a Ubaiyd ya biyewa son zuciya da giyar mulki ina fatan
zaka gafarce mu?".


Baban Aynu yad'an gyara zama tare da gyaran murya.

"Babu komai wallahi dama can ban rik'e Sarki Ubaiyd acikin raina ba ko kad'an, kuma naji dad'i
da kuka gane gaskiya dama anaso idan mutum yayi kuskure ya gane kuskurensa hakan yayi
kyau nima na gode sosai".



Shiru ya gauraye wajen har nawasu tsayin lokuta kafin Magaji Saif ya ci gaba da magana.

"Sai dai kuma muna tafe ne da wata buk'ata mai girma ina fatan ba zaka duba abubuwan da
suka faruwa ba a baya ba".

"Insha Allahu ai komai ya wuce wacce buk'ata ce wannan?".

Magaji Saif yad'anyi shiru kafin yace.


"Akan dai maganar yarinyarka da d'an namu ne Fudhal muna rok'onka ka dubi Allah ka dubi
halin da d'anmu yake ciki ka taimaka ka bamu auren 'yarka".


Baban Aynu ya d'an girgiza kai.


"Amma da kadaina had'ani da Allah Magaji hak'ik'a kazo da batu mai girma kafin kuzo nan basu
sanar maka cewa jibi wato ranar juma'a za'a d'aura auren Aynu ba?".


"Sun sanarmin amma ba wannan za'a duba ba halin da yaron yake ciki shine abin dubawa".


"E hakane amma sai dai kunzo a k'urar-ran lokaci bani da damar da zan iya yi muku wannan
alfarmar kuyi hak'uri Allah ya bawa Fudhal lafiya ya kuma bashi wadda tafi Aynu".


"Amin".

Suka amsa Sarki Ubaiyd dake zaune gefe tun zuwansu ya kasa furta komai haka kawai yau yaji
Baban Aynu yayi masa kwarjini sosai jin amsar da Baban Aynu ya bayar shine ya sanya shi
bud'e baki da sauri yana fad'in.


"Nima bazanyi k'asa agwiwa ba wajen baka hak'uri ba, dan Allah ka ceci rayuwar d'ana ka bashi
Aynu".

"Ai rayuwar d'anka na wajen Allah ba waje na ba, idan yaso ya rayu ko ya auri Aynu ko bai
aurata ba tabbas zai rayu, haka kuma idan lokacinsa yayi koya aure ta Kobe aure ta ba tabbas
zai mutu kama daina danganta rayuwar d'anka da Aynu, idan banyi kuskure ba zan iya cewa
dukkan abin da ya faru da d'an ka Kaine babban mai laifi".
"Ka sani arziki da talauci babu abin da basa bayarwa a rayuwa ka inganta rayuwarka data
iyalinka shine abu mafi ma'ana da mafita ".


"Ka sani bawai ina fad'a maka bane domin in rama abin da kaimin ko kusa wallahi, ina fad'ane
kawai domin intuna maka da abin da ka mance".

"Allah gafururrahim ne idan yaso ya azurtaka babu Wanda ya isa ya hana, haka kuma idan yaso
ka da talauci babu Wanda ya isa ya azurtaka, daraja dan Adam da girmamashi kowanne iri ne
yana da fa'ida sosai domin Allah subhanahu wata'ala da kansa ya fad'a a cikin alk'ur'ani cewa.


"(WALAK'AD KARRAMNA BANIY ADAMA WAHAMALNAHUM FIL BARRI WAL BAHRI
WARAZAK NAHUM MINAL 'DAYYIBATI WA FADDALNAHUM ALA KASIYRIM MIMMAN
KALAK' NA TAFDIYLA)".

Ma'ana:-(Kuma lallene mun girmama d'an Adam kuma muka d'aukesu a cikin k'asa da teku,
kuma muka azurtasu daga abubuwa masu dad'i, kuma muka fifitasu akan masu yawa daga
wad'anda muka halitta fifitawa).


"Hak'ik'a wannnan ayar ko ita kad'ai ta isa mu girmama junanmu mu 'yan adam tare da mutun
tawa , domin agurin Allah bamu da wani ban-banci duk abu d'aya ne mu bayi ne a gareshi dole
ne mu bauta masa indai muna son dace wa da samun cikawa da imani, Allah ya yafemu baki
d'aya abisa laifin da mukayi masa na fili da na b'oye".
"Amin".
Suka sake amsawa.


Sarki Ubaiyd baiyi k'asa a gwiwa ba ya matsa har Inda Baban Aynu ke zaune ya rik'o
hannunsa yana fad'in.


"Mai kake so a duniya? Wanda zanyi maka da zai sanya ka bawa dana auren 'yarka, kud'i ko
mulki? ka fad'i dukkan abin da kake so zanyi maka indai har zaka bawa Fudhal auren Aynu ko
sarautar tawa kake buk'ata zan baka wallahi akan dai in rasa d'ana mafii soyuwa a cikin raina".


Baban Aynu ya girgiza kai yana mai k'arewa Sarki Ubaiyd kallo domin ya tabbatar da gaskiyar
abin da yake fad'a, tabbas yaga tsan-tsan nadama sosai a idanun Sarki Ubaiyd, Baban Aynu
yayi hamdala cikin ransa afili kuwa ya furta.


"Bana buk'atar komai naka Mai Martaba, sai dai abin da bakina ya furta d'azu har a yanzu shi
d'in zai sake furtawa kayi hak'uri zan taya d'anka Fudhal addu'ar samun macen da tafi Aynu tare
da fatan samun lafiyarsa s...!".

Maganar Baban Aynu ta katse a dai-dai sanda suka tsinkayi sallamar mutum a kusa dasu ko
wannansu ya d'aga kai sama domin ganin mai Sallamar.


Ya Sayyadi Umar ne ya cire takalminsa ya nemi guri d'an nesa da su ya zauna akan tabarmar
tare da gaishesu dukansu suka amsa.


Ya Sayyadi Umar ya bud'e baki zaiyi magana Baban Aynu yq katse shi da fad'in.


"Wannan shine yaron da zai aureta ai".


Magaji Saif da Sarki Ubaiyd sukabi Ya Sayyadi Umar da kallo.


Ya Sayyadi Umar yad'anyi gyaran murya.


"Baba daman nazo ne kan wata magana".


"To intaso kenan ".

"A a muyi maganar anan, dama maganar nan ne huruminta".


"To masha Allah ina jinka Mallam Umar".


Cewar Baban Aynu kenan yayin da dukansu suka bada a tension wajen Ya Sayyadi Umar
domin jin abin da zai fad'a.


"Baba nasan zaku ji maganar da baku tab'a zata ba kuma bakuyi tsammani ba, na riga na
yanke hakan kuma inaji a raina alkhairi ne yin hakan banajin zanyi kuskure ko kad'an, Baba tun
ranar da abokin Fudhal yazo ya d'auke ni wato Anwar ya kaini na dubo Fudhal tun daga ranar
zuciyata ta kasa samun nutsu inaji araina kamar nine na yiwa rayuwar Fudhal karan tsaye a yau
inajin dad'i tare da godiya ga Allah har cikin raina zanyi abin da ba duk wani masoyi ne zai iya
ba, bantab'a tunani ko ji araina zan iyayin sadakar soyayata ba amma ayau ni UMAR FARUK
na SADAUKAR GA SOYAYYATA GA YARIMA FUDHAL, Ma'ana na barwa Fudhal Aynu ya aura

duniya da lahira ina fatan nima Allah yayi min zab'in mafificin alkhairi...;".


"Kai Umar..! Kasan me kake fad'a kuwa?".


"Na sani Baba.!, Idan banyi hakan bane banajin kona auri Aynu zuciyata zata zauna lafiya
domin Aynu babu Wanda take so aduniya fiye da Fudhal ni nasan hakan, Aynu ta yarda zata
aure ni ne kawai domin yin biyayya agareku amma bawai dan tana so naba".


"Amma Umar kana ganin hakan ya dace?".


"Sosai ma Baba kayi musu fatan alkhairi kawai, sai dai ina rok'on wata alfarma Baba".

"Ina jinka Umar".


"Kamar yanda aka sanya d'aurin auren nan banaso a fasa a d'aura auren Aynu wa Fudhal ranar
juma'a dan Allah Baba kayimin wan nan alk'awarin".


Baban Aynu yayi shiru tsayin lokaci yana kallon fuskar Ya Sayyadi Umar yama rasa abin da
zaice domin ya Riga ya d'aure shi da jijiyoyin jikinsa akan dole yace.


"Nayi maka alk'awari Umar kamar yanda kace insha Allahu ranar juma'a za'a d'aura auren
Fudhal wa Aynu bi iznillahi ta'alah, Allah yayi masa albarka yasa ka gama da duniya lafiya ya
baka dukkan farin ciki duniya da lahira kamar yanda ka faranta rai kaima ".


"Amin Baba babu komai ai".


Magaji Saif, Sarki Ubaiyd, Anwar sakar baki da hanci sukayi suna kallon Ya Sayyadi Umar tare
da jinjinawa tsananin jarumtarsa wajen iya sadaukar ga soyayyarsa lokaci guda haka.


Fuskar Sarki Ubaiyd tuni ta jik'e da hawaye yama rasa mai zai cewa Ya Sayyadi Umar da k'yar
dai ya iya furta.

"Mungode Umar Allah yayi maka albarka yayi maka sakayya kan abin da ka aikata na alkhairi
nayi alk'awari dukkan abin da kake so a duniya ka fad'amin zanyi maka kada kaji nauyi ko
kunya domin bani da abin da zan saka maka dashi nan duniya sai dai Allah ya saka maka".


Anwar kuwa mik'ewa tsaye yayi ya rungumeshi yana fad'in.

"Mungode.! Mungode..!! Mungode...! Sosai Umar bani da bakin da zan iya yi maka godiya kayi
abin da wad'anda zasu iyayin hakan basu da yawa a duniya Allah ya baka wadda tafi Aynu
Umar mungode".

"Amin ya Allah".


Magaji Saif kuwa murmushi kawai yake dokawa domin yama rasa bakin magana daga k'arshe
dai yace.


"Babban albishir d'in da zan iya yimaka kawai shine ni Magaji Saif na bawa Umar auren Jalilah
'ya ga k'anina Sarki Ubaiyd sauran tukwicinka kuwa sai mun zauna".


Ba Ya Sayyadi Umar ba hatta Anwar da Baban Aynu basu san sanda murmushi ya kufce musu
ba dan tsabar farin ciki da jindad'i jin wannan babban tukwici da Magaji Saif yayi masa, Sarki
Ubaiyd kuwa girgiza kai kawai yake hawaye ne a fuskarsa amma kuma murmushi yake.






YAU DAI NASAN TUKWICINA NA MUSAMMAN NE AGAREKU *AYNUL-FUDHAL* INA JIRA
NA CIKA MUKU BURIN KU YAU.



TO AYNUL-UMAR YA KOMA JALILAH-FARUK

KU KUMA WANNE IRIN TUKWICI ZAKU BANI INA JIRA


BYEE..!

*YARIMA FUDHAL*

NA
FIRDAUSI S.A(AURRATUL-AYN).

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®

SADAUKARWA:-NAMESY PHIRDAUSY JEEBOUR.

43


Ya Sayyadi Umar ya durƙusa yayi godiya duk da cewar bai san wacece Jalilah ba? bai taɓa
ganinta ba amma ba zai iya cewa baya so ba, a kan dole ya amince kenan da auren Jalilah?.


Su Mai Martaba sukayi addu'a tare da roƙon Allah ya sanyawa auren albarka Ya Sayyadi
Umar yayi musu sallama ya tafi amma kafin ya tafi ya roƙesu akan kada asanarwa Aynu komai
har sai anɗaura auren kuma ko wanne daga cikin su ya amince da wannan batun.

Sannan suma sukayiwa Baban Aynu sallama suka tafi kowa zuciyarsa cike fal da farin cikin
wannan rana.

Suna komawa asibitin kai tsaye Magaji Saif da Sarki Ubaiyd office ɗin doctor suka nufa, Anwar
kuwa ɗakin da Fudhal yake jinya ya nufa yana shiga su Hajiya da Aunty Sadiya suka tsare shi
da tambayar abin da ya faru.

Bai wani tsaya tunanin komai ba ya sanar musu duk kan abin da ya faru zuciyar Fulani Bingel
da Aunty Sadiya suka cika da farin ciki Sa'idah kuwa ba zaka iya shaida yanayin da take ciki ba
farin ciki ne ko akasin hakan.


"Doctor ya jikin Fudhal ɗin kuwa?".

Cewar Magaji Saif kenan tare da tsare Doctor da idanuwa domin jin amsar da zai basu.

Ya cire farin glass ɗin dake manne bisa idonsa yana kallonsu fuskarsa wasai.

"Jikin Fudhal alhamdulillahi kullum yana ƙara samun lafiya may be nan da Friday muna saran
farfaɗowarsa sai dai abin da nake ƙara tuna muku idan har ana son ɗorewar samuwar lafiyarsa
dole ne idan ya farka ya fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login