Showing 66001 words to 69000 words out of 88612 words
Chapter 23 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
SADAUKARWA:- Namesy Phirdausy Jeebour.
39
***
Al'amarin ciwon Yarima Fudhal da Yarima Jaleel sai dai addu'a ba zaka iya cire guda ba a
cikinsu wanda yafi sauƙi.
Yarima Jaleel tsayin sati biyu kenan ya zama kamar wani zautacce sai dai a yi masa allurar
bacci data sake shi kuwa inya farka ya dinga sambatu da buge-buge kenan har sai Doctor ya zo
ya sake yi masa wata allurar.
Fulani Sokoto ita ce a wajen Yarima Jaleel sai sauran 'yan aikinta da masu zuwa dubiya.
Fulani Bingel kuwa dukkan yaran gidan sun tare a wajen jinyar Yarima Fudhal duk da cewa
suna zuwa dubo Jaleel lokaci zuwa lokaci.
Sarki Ubaiyd baki ɗaya abin duniya ya ishe shi yara biyu, duk suna kwance rai a hannun Allah
! kuma duka waɗanda yake ganin sune magada a bayansa kullum ba shi da aiki Wanda ya
wuce tuanani da neman mafita.
Shi kanshi yasan mafita ɗaya ce akan ciwon Fudhal yaje ya nemawa Fudhal auren Aynu amma
kash hausawa nacewa (Girman kai rawanin tsiya).
Tsananin girman kai da isa, ba zasu barshi yaje ga wadanda yake ganin su maƙas-ƙantane a
gareshi ba.
"Wai Hajiya Mai Martaba ba shi da wani na gaba da shi ne?".
Anwar dake zaune gaban Fulani Bingel yake tambayarta.
"Akwai mana !, Amma me yasa kake tambaya?".
"E to gani nayi gaskiya ya kamata a san abinyi tun da wuri, yanzu haka zamu zuba ido akan
ciwon Magaji ne?".
Fulani Bingel tayi shiru tsayin lokaci kafin ta buƊe baki ta bashi amsar tambayarsa.
"Kayi gaskiya Anwar amma sai dai banajin Magaji Saif zai yarda yazo nan garin har yayiwa
ƙaninsa sarki Ubaiyd wata magana mai daɗi".
"Waye Magaji Saif kuma?".
Suka haɗa baki dukansu wajen tambayar Mahaifiyartasu domin tun farkon tambayar da Anwar
yayi mata suka mai da hankali kacokan a kan Fulani Bingel.
"Magaji Saif yaya ne ga Mahaifinku Uwa ɗaya Uba ɗaya, sai dai abin da ya shiga tsakaninsu
tsayin shekaru shine yayi sanadiyyar raba zumuncin dake tsakanin Mahaifannaku.
"Mene ya shiga tsakaninsu Hajiya?".
Wannan karon Aunty Sadiya ce tayi tambayar.
Ajiyar zuciya Fulani tayi kaɗan kafin ta fara magana.
*MUSAB-BABIN GABARSU*
"Abin da ya haddasa gaba tsakanin Mahaifannaku akan abu biyu ne na farko nice na biyu kuma
al'amarin sarauta ne".
"Ni 'yar asalin garin Bingel ce haifaffiyar can wata rana Mahaifinku da Yayansa sun ziyarci garin
namu tare da iyayensu domin halartar ɗaurin auren ɗan sarkin garin wato Yayana, a wannan
lokaci ne a cikin hidimar bikin muka fara haɗuwa da Mahaifinku ya baiyanamin abin da ke
ƙarƙashin zuciyarsa da sunan yana sona, duk da ban amince ba car lokacin sabida kunya
amma washe garin ranar na baiyanawa ƙawata kuma ta sameshi ta bashi amarsa".
"A ranar ne kuma Yayansa shima yazo min da irin batun da Mahaifinku yazo min da shi, sai dai
ban amince ba anan take na baiyana masa cewa ni Ubaiyd nake so, tun a wannan lokaci faɗa
ya fara shiga tsakaninsu saɓanin da ayanda suke Mahaifannaku suna son junansu tare da
girmama tsakaninsu haka kuma Mahaifinku yanajin maganar Yayansa".
"Yazo masa da batun cewa sai dai ya haƙura ya bar masa ni ai shine gaba da shi, shi kuma
yace bazai yiyu ba hakan ne ya haddasa faɗa atsakaninsu har suka koma gida babu mai yiwa
wani magana domin Magaji Saif yafi Sarki Ubaiyd tsananin fushi da zuciya".
"Ana cikin wannan hatsaniyarne kuma Kakanku ya kwanta ciwon ajali cikin kwanaki biyu yace
ga garinku nan, lokacin munzo gaisuwa a ranar majalisa ta zauna domin tan-tance wanda zai
zamo Magaji a tsakaninsu , Magaji Saif yayi magana kan cewa".
"Indai shine za'a bawa sarauta to dole ne Sarki Ubaiyd ya haƙura da aure na ya barmasa ko
kuma ya fita yabar garin, shi kuma Mahaifinku yace bazai yarda ba ananma sai da sukayi faɗa
haka aka tashi ba tare da samun mafita ba".
"Sai dai kuma abin da kowa bai sani ba a daren 'yan majalisa sun sake zama domin kwance
wannan ƙullin dake tsakanin iyayenku sunyi shawara kancewa Mahaifinku za'a bawa sarauta
tare da aurena inyaso Magaji Saif a bashi waziri domin gudun matsala sabida sun San muddun
suka bawa Magaji Saif sarauta duk yanda zasu so bazasu iya hanashi muzanta Sarki Ubaiyd
ba, domin irin kalaman da yayi sun San zai aikata fin haka dan baya magana ya sake ta, shi
kaifi ɗaya ne koda kuwa zai rasa ransa".
"A washe garin ranar aka haɗa aurena da Mahaifinku tare da naɗin sarauta da kuma sadakar
ukun Kakan ku, nan take Magaji Saif yace baya son wazircin kuma daga ranar Shiba haifaf-fan
garin nan ba ne, kada Wanda yace ma ya taɓa saninsa a duniya daga nan ya fice yabar garin
bamu sake jin labarin saba sai lokacin da aka fara maganar batun auren Magaji da Gimbiya
Safiyya mukaji cewar yana zaune a Sokoto".
Shiru ɗakin ya dauka tsayin daƙiƙu masu yawa kafin Anwar ya nisa yana mai faɗin.
"Insha Allahu zamu sami nasara, zanje innemeshi zai dawo gida cikin farin ciki kuma zasu
manta gabar da suke da yardar Allah".
"Allah yasa ya ɗora ka akansa, domin shi kaɗai ne nake ganin a duniya Wanda zai iya sanya
Sarki Ubaiyd yayi, kuma shine kaɗai zai iya hanashi ya hanu, sai dai kuma meye fa'idar sako
shi a zancen?".
Anwar yaɗanyi murmushi.
"Hajiya kenan kin mance yau saura 2days ayi bikin Aynu kuma duk yanda naso Mai Martaba
yaje ya roƙesu yaƙi, duk wata hanya da zanbi insawa Fudhal farin ciki nabi amma babu nasara
sai dai inaji a raina wannan ce kaɗai nasararmu in Allah yaso".
Fulani Bingel ta murmusa tare da faɗin.
"Allah yayi maka albarka Anwar ya baka abin da kake so duniya da lahira lallai ka cika aboki
kuma amini na gari Ubangiji ne kaɗai zai iya yi maka sakaiya akan abin alkhairin da kake
aikatawa domin mu kuwa bamu da abin da zamu saka maka".
"Hajiya kibar faɗin haka ai Fudhal a guna dan uwane na jini zan iyayin abin da yafi hakama
akansa kedai kawai ki tayani da addu'a".
"Insha Allahu kada ka damu da wannan".
Anwar ya sanya kai ya fita daga ɗakin yayin da suka biyoshi dukkanninsu da addu'ar fatan
alkhairi.
****
Tun ranar da Ya Sayyadi Umar yaje ya dubo Yarima Fudhal ya dawo baki daya ya gaza samun
nutsuwa da kwanciyar hankali a tattare da shi, ji yake kamar yana shirin aikata bab-ban kuskure
ne tare dayin aikin dana sani, sai dai ƙasan zuciyarta na tausarsa da cewa shimafa yana sonta
taya zai iya haƙura ya bawa wani?.
Hakan yasa yake samun ƙwarin gwiwa tare daji aransa bazai taɓa iyayin SADAKAR SOYAYYA
ba.
Shi kaɗaine a motarsa yake driven yayin da ya sanya kira'ar sudais a motar yana tuƙi yana bi
hankalinsa kwance kai kace babu abin da yake damunsa a duniya, sai dai ƙasan zuciyarta
cunkuce take da tarin damuwa da tunanin abin da zaije ya tarad duk da cewa yana yiwa kansa
fatan alkhairi tare da saran samun nasara domin yasan aikin alkhairi yake shirin aikatawa bare
kuma al'amari na zumunci Allah zai bashi nasara.
Ko da ya isa cikin Sokoto birnin shehu ya shafe tsayin a wanni hudu yana fafutuwar neman
Magaji Saif kafin Allah ya haɗashi da wani al'amajiri mai wanki da guga shine yace ya sanshi ai
shi yake bawa wanki da guga duk sati, gidansa a can (kalan baina) yake yazo suje ya rakashi.
Haka suka tafi yaron na nunawa Anwar hanya shi kuma yana bi har zuwa bakin gate ɗin wani
tamfatse-tsen gida sukayi hon gateman ya buɗe ƙofar wangagememan gate din gidan suka
sanya kai.
Almajirin yace wa Mai gadi ya sanarwa Alhaji yayi baƙo, ba musu Mai gadin ya wuce cikin gidan
da sauri domin sanarwa ahaji dake yasan almajirin sosai, mintuna kaɗan sai gashi ya dawo
tare da amsar su shiga yana jiransu.
Su Anwar suka sanya kai zuwa cikin gidan, shi dai Anwar kallon gidan kawai yake domin yasan
ko a turai da yayi karatu bai taɓa ganin gida mai girma da haɗuwa kamar wannan gidan ba,
faɗin haduwar gidanma ƙauyanci ne sai dai masu karatu ku ƙiyassata a cikin ranku.
Yana zaune falo kan wata luntsumemiyar kujera 'yar ubansu shaddar dake sanye jikinsa ita
kanta kukan kuɗi take bare kuma azo batun takalmi da hula zuwa uwa uba agogon hannunsa,
yana zaune a hannunsa kuma news paper ce yake karanta sukayi sallama ya ɗago kai cike da
fara'a yana mai amsa musu.
Tsan-tsan kamar Sarki Ubaiyd da Anwar yagani a tare da fuskar Magaji Saif shine abin da ya
daure masa kai ainun ya kuma tabbatar tabbas wannan shine Magaji Saif yayan Sarki Ubaiyd.
Suka gaisa Anwar yayiwa almajirin godiya tare da alkhairi mai yawa ya tashi ya tafi.
Yana fita Magaji Saif yabi Anwar da kallo yana faɗin.
"Sai dai ban shaida fuskarka ba, ko zaka iya yimin bayanin waye kai?, mene kuma ya kawoka
gidan nan?".
Anwar yayi murmushi kafin yace.
"Abu mai sauƙi dama hakance ta kawo ni".
Nan take Anwar ya fara bashi amsar tambayarsa dalla-dalla tare da faɗin abin da ya kawoshi da
kuma dalilin zuwansa.
Magaji Saif ya haɗe girar sama data ƙasa tamkar bashi ne yake murmushi ba yanzu sai kace an
aiko masa da saƙon mutuwarsa haka ya miƙe tsaye yana mai mid zuwa wajen Anwar tuni
hantar cikin Anwar tahau kaɗawa tsoro ya ziyarceshi take ya fara karanto addu'a cikin ransa
domin ya gama hasko irin cin mutunci da tozarcin da zai fuskanta yau a hannun Magaji Saif.
KOMA DAI MENENE KU BIYO NI........! Smile kuna raina fa.
Nagode sosai da sosai da ɗunbin tarin addu'arku a agare ni Allah ya biyaku amin.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:- Namesy Phirdausy Jeebour.
39
***
Al'amarin ciwon Yarima Fudhal da Yarima Jaleel sai dai addu'a ba zaka iya cire guda ba a
cikinsu wanda yafi sauƙi.
Yarima Jaleel tsayin sati biyu kenan ya zama kamar wani zautacce sai dai a yi masa allurar
bacci data sake shi kuwa inya farka ya dinga sambatu da buge-buge kenan har sai Doctor ya zo
ya sake yi masa wata allurar.
Fulani Sokoto ita ce a wajen Yarima Jaleel sai sauran 'yan aikinta da masu zuwa dubiya.
Fulani Bingel kuwa dukkan yaran gidan sun tare a wajen jinyar Yarima Fudhal duk da cewa
suna zuwa dubo Jaleel lokaci zuwa lokaci.
Sarki Ubaiyd baki ɗaya abin duniya ya ishe shi yara biyu, duk suna kwance rai a hannun Allah
! kuma duka waɗanda yake ganin sune magada a bayansa kullum ba shi da aiki Wanda ya
wuce tuanani da neman mafita.
Shi kanshi yasan mafita ɗaya ce akan ciwon Fudhal yaje ya nemawa Fudhal auren Aynu amma
kash hausawa nacewa (Girman kai rawanin tsiya).
Tsananin girman kai da isa, ba zasu barshi yaje ga wadanda yake ganin su maƙas-ƙantane a
gareshi ba.
"Wai Hajiya Mai Martaba ba shi da wani na gaba da shi ne?".
Anwar dake zaune gaban Fulani Bingel yake tambayarta.
"Akwai mana !, Amma me yasa kake tambaya?".
"E to gani nayi gaskiya ya kamata a san abinyi tun da wuri, yanzu haka zamu zuba ido akan
ciwon Magaji ne?".
Fulani Bingel tayi shiru tsayin lokaci kafin ta buƊe baki ta bashi amsar tambayarsa.
"Kayi gaskiya Anwar amma sai dai banajin Magaji Saif zai yarda yazo nan garin har yayiwa
ƙaninsa sarki Ubaiyd wata magana mai daɗi".
"Waye Magaji Saif kuma?".
Suka haɗa baki dukansu wajen tambayar Mahaifiyartasu domin tun farkon tambayar da Anwar
yayi mata suka mai da hankali kacokan a kan Fulani Bingel.
"Magaji Saif yaya ne ga Mahaifinku Uwa ɗaya Uba ɗaya, sai dai abin da ya shiga tsakaninsu
tsayin shekaru shine yayi sanadiyyar raba zumuncin dake tsakanin Mahaifannaku.
"Mene ya shiga tsakaninsu Hajiya?".
Wannan karon Aunty Sadiya ce tayi tambayar.
Ajiyar zuciya Fulani tayi kaɗan kafin ta fara magana.
*MUSAB-BABIN GABARSU*
"Abin da ya haddasa gaba tsakanin Mahaifannaku akan abu biyu ne na farko nice na biyu kuma
al'amarin sarauta ne".
"Ni 'yar asalin garin Bingel ce haifaffiyar can wata rana Mahaifinku da Yayansa sun ziyarci garin
namu tare da iyayensu domin halartar ɗaurin auren ɗan sarkin garin wato Yayana, a wannan
lokaci ne a cikin hidimar bikin muka fara haɗuwa da Mahaifinku ya baiyanamin abin da ke
ƙarƙashin zuciyarsa da sunan yana sona, duk da ban amince ba car lokacin sabida kunya
amma washe garin ranar na baiyanawa ƙawata kuma ta sameshi ta bashi amarsa".
"A ranar ne kuma Yayansa shima yazo min da irin batun da Mahaifinku yazo min da shi, sai dai
ban amince ba anan take na baiyana masa cewa ni Ubaiyd nake so, tun a wannan lokaci faɗa
ya fara shiga tsakaninsu saɓanin da ayanda suke Mahaifannaku suna son junansu tare da
girmama tsakaninsu haka kuma Mahaifinku yanajin maganar Yayansa".
"Yazo masa da batun cewa sai dai ya haƙura ya bar masa ni ai shine gaba da shi, shi kuma
yace bazai yiyu ba hakan ne ya haddasa faɗa atsakaninsu har suka koma gida babu mai yiwa
wani magana domin Magaji Saif yafi Sarki Ubaiyd tsananin fushi da zuciya".
"Ana cikin wannan hatsaniyarne kuma Kakanku ya kwanta ciwon ajali cikin kwanaki biyu yace
ga garinku nan, lokacin munzo gaisuwa a ranar majalisa ta zauna domin tan-tance wanda zai
zamo Magaji a tsakaninsu , Magaji Saif yayi magana kan cewa".
"Indai shine za'a bawa sarauta to dole ne Sarki Ubaiyd ya haƙura da aure na ya barmasa ko
kuma ya fita yabar garin, shi kuma Mahaifinku yace bazai yarda ba ananma sai da sukayi faɗa
haka aka tashi ba tare da samun mafita ba".
"Sai dai kuma abin da kowa bai sani ba a daren 'yan majalisa sun sake zama domin kwance
wannan ƙullin dake tsakanin iyayenku sunyi shawara kancewa Mahaifinku za'a bawa sarauta
tare da aurena inyaso Magaji Saif a bashi waziri domin gudun matsala sabida sun San muddun
suka bawa Magaji Saif sarauta duk yanda zasu so bazasu iya hanashi muzanta Sarki Ubaiyd
ba, domin irin kalaman da yayi sun San zai aikata fin haka dan baya magana ya sake ta, shi
kaifi ɗaya ne koda kuwa zai rasa ransa".
"A washe garin ranar aka haɗa aurena da Mahaifinku tare da naɗin sarauta da kuma sadakar
ukun Kakan ku, nan take Magaji Saif yace baya son wazircin kuma daga ranar Shiba haifaf-fan
garin nan ba ne, kada Wanda yace ma ya taɓa saninsa a duniya daga nan ya fice yabar garin
bamu sake jin labarin saba sai lokacin da aka fara maganar batun auren Magaji da Gimbiya
Safiyya mukaji cewar yana zaune a Sokoto".
Shiru ɗakin ya dauka tsayin daƙiƙu masu yawa kafin Anwar ya nisa yana mai faɗin.
"Insha Allahu zamu sami nasara, zanje innemeshi zai dawo gida cikin farin ciki kuma zasu
manta gabar da suke da yardar Allah".
"Allah yasa ya ɗora ka akansa, domin shi kaɗai ne nake ganin a duniya Wanda zai iya sanya
Sarki Ubaiyd yayi, kuma shine kaɗai zai iya hanashi ya hanu, sai dai kuma meye fa'idar sako
shi a zancen?".
Anwar yaɗanyi murmushi.
"Hajiya kenan kin mance yau saura 2days ayi bikin Aynu kuma duk yanda naso Mai Martaba
yaje ya roƙesu yaƙi, duk wata hanya da zanbi insawa Fudhal farin ciki nabi amma babu nasara
sai dai inaji a raina wannan ce kaɗai nasararmu in Allah yaso".
Fulani Bingel ta murmusa tare da faɗin.
"Allah yayi maka albarka Anwar ya baka abin da kake so duniya da lahira lallai ka cika aboki
kuma amini na gari Ubangiji ne kaɗai zai iya yi maka sakaiya akan abin alkhairin da kake
aikatawa domin mu kuwa bamu da abin da zamu saka maka".
"Hajiya kibar faɗin haka ai Fudhal a guna dan uwane na jini zan iyayin abin da yafi hakama
akansa kedai kawai ki tayani da addu'a".
"Insha Allahu kada ka damu da wannan".
Anwar ya sanya kai ya fita daga ɗakin yayin da suka biyoshi dukkanninsu da addu'ar fatan
alkhairi.
****
Tun ranar da Ya Sayyadi Umar yaje ya dubo Yarima Fudhal ya dawo baki daya ya gaza samun
nutsuwa da kwanciyar hankali a tattare da shi, ji yake kamar yana shirin aikata bab-ban kuskure
ne tare dayin aikin dana sani, sai dai ƙasan zuciyarta na tausarsa da cewa shimafa yana sonta
taya zai iya haƙura ya bawa wani?.
Hakan yasa yake samun ƙwarin gwiwa tare daji aransa bazai taɓa iyayin SADAKAR SOYAYYA
ba.
Shi kaɗaine a motarsa yake driven yayin da ya sanya kira'ar sudais a motar yana tuƙi yana