Showing 24001 words to 27000 words out of 88612 words
Chapter 9 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
fice.
Yana tsaye jikin katangar gidan nasu hannunsa rik'e da wayarsa yana dannawa d'aya hannun
kuma na cikin aljihun wandon jeans d'insa, aranta ta furta.
"Ko ina dai ba'a gajiya da sana'ar".
Da sallama ta k'arasa wajensa Yarima ya amsa tare da fad'a d'a murmushinsa yana duban ta,
Aynu tayi saurin yin k'asa da kanta sabida irin kallon da Yarima Fudhal yake ji fanta dashi
idanuwanta bazasu iya d'auka ba.
Shiru ne ya ziyarci wajen kafin Yarima yayi k'arfin halin katse shirun da fad'in.
"Ke na keson aura Aynu !, zuciyata tafi aminta dake akan wacce iyayena suka zab'amin
amma...".
Sai kuma yayi shiru yana mai haska fuskarta da hasken wayarsa domin ganin yanayin ta,
Aynu dai kanta yana k'asa amma zuciyarta na bugun uku-uku wanda ta rasa dalilin faruwar
haka.
"Ko bakya so na?".
Taji saukar muryarsa akaro na biyu yana tambayarta, maimakon ta bashi amsa kawai juya wa
tayi tabar wajen ta shige gida ta barshi nan tsaye.
Yarima yabi bayanta da kallo ba tare da yayi yunk'urin da katar da ita ba yanaji zuciyarsa nayi
masa zafi, tare da jin haushin abin da tayi masa.
***
Kwance yake bisa lallausar katifarsa sai faman juyi yake yana son yin bacci amma hakan ya
gagare shi, tunanin abin da Aynu tayi masa d'azu shine yake damunsa, amma babban abin da
yafi damunsa bai wuce jin tsoron kada Aynu tace bata son saba.
Lokacin ya jawo wayarsa ya duba agogo k'arfe biyu da kusan rabi, ya d'an ja tsaki tare da
cigaba da danna wayar da alamu akwai abin da yake nema.
Can ya danna wata number tare da karawa akunnensa, sai da wayar ta kusa tsinkewa
sannan aka d'aga tsaki Yarima yaja tare da fad'in.
"Kai fa d'an rainin wayo ne Anwar !, mai kake nufi ?, da ba zakayi picking bane?".
Cikin muryar bacci Anwar ya amsa da fad'in.
"Kai fa prince kafi kowa matsala wallahi ban da ni wa zaka kira da tsakad daren nan ya d'aga".
Yarima Fudhal yaja dogon tsaki kamar ya yanke wayar sai kuma ya fasa yana fad'in.
"Kaga malam maganace mai muhimmanci ka tashi daga baccin".
"Akan me?, fad'i maganarka kawai ina jinka".
"Mene ma'anar idan ka furtawa mace kan sonta tayi tafiyarta batare data baka amsa ba?".
Daga can b'angaren Anwar dariyace ta kwace masa har da rik'e ciki, ba k'aramin k'ok'ari yayi
ba wajen saita kansa domin tambayar tazo masa a bazata da kuka mamakin wanda yayi
tambayar, bai kai da baiwa Yarima amsa ba yaji ya katse wayar yasan dama za'ayi hakan, kira
ya sakeyi harta katse Yarika yak'i dagawa sai da ya kira sau uku sannan ya d'aga batare da yayi
magana ba.
Anwar cikin dariya ciki-ciki yahau fad'in.
"Am sorry Prince kawai naji mamakin tambayar da kayi min ne wallahi, da gaske soyayya kake
son sanar dani ka fara ko kuwa me?".
"A'a kawai inason jin amsar ne".
Anwar yayi murmushi tare da fad'in.
"To kabari har gobe mayi magana mana".
"A'a yanzu nake so shiyasama na kiraka ai, da naso har gobe ai sai goben zan neme ka".
"Hakane, amma gaskiya a gani na duk macen da kace kana so tayi tafiyarta ta barka nan
batare da amsa ba to d'ayan biyu ne ko kunyar baka amsa take ji ko kuma bata son ka...".
Kafin ya kai da k'arasa maganar Yarima Fudhal ya katse wayar ya wullata can k'arshen
katifarsa tare da yin tsaki, sai kuma yamik'e ya zauna maganar Anwar nayi masa yawo akai.
"Aynu kunyata take ji, ko kuma so nane batayi ?".
Kai ya girgiza yayin da zuciyarsa ta tsinke tsoro ya ziyarce shi, sai ya samu kansa da fad'in.
"Allah yasa kunyace ta hana ta bani reply !".
Hhhhhhh to fa !, su Yarima Fudhal anshiga taskun soyayya, to amma aganinku Aynu zata so
Yarima Fudhal kuwa?.
Nabar muku wannan amsar Reader.
Kuyu hkr da wannan page d'in babu yawa, nagode sosai masoyana kuna raina koyaushe.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATIONS®
15
8:00am
Zaune Anwar yake gefen kusun yana duban Yarima Fudhal cike da tsokana yake fad'in.
"Amma dai kowa ya ganka yaga wanda yajik'e da mayen so, amma kace min kai ba soyayya
kake ba?".
Yarima dake kwance gefe ya dora hannunsa na dama bisa fuskarsa kamar bacci ko motsi
baiyi ba, bare ya kula da maganar da Anwar yake masa.
Aynu ce ta fito daga cikin bedroom hannunta rik'e da moopa ta d'an risina tana fad'in.
"Na gama zan gyara nan".
Yarima ya mik'e ba tare daya dubeta ba ya wuce cikin d'akin yana fad'in.
"Sai ka ta so ko".
Anwar yabi Yarima da kallo kafin ya dawo da dubansa kan Aynu yana fad'in.
"Mene sunanki".
"AYNU".
Ta bashi amsa kai ya gyad'a tare dayin murmushi yana fad'in.
"Nice name, a wacce unguwa kike?".
Yarima ne ya banko labulan d'akin ya fito cike da b'acin rai, kallon daya watsawa Aynu shine
yasa ta shan jinin jikinta tayi k'asa da kai ba tare data baiwa Anwar amsa ba.
Anwar ya sanya dariya mai sauti tare da mik'ewa yabi bayan Yarima cikin d'akin yana fad'in.
"Abin da nayi zato ya tabbata Prince, wai me yasa kake b'oyemin ne?, tun da nazo nake
karantar yanayin ka akan yarinyar nan".
"Sabida kamai da zancena gist mana !, kasan ni bana wasa a cikin al'amura na".
"Ehh to zancen wasa ya wuce, amma ka da dai kacemin wannan Yarinyar kake so?, domin
naga kishinta k'arar bisa fuskarka".
"Ehh ita nake so !, wani abun ne?".
"A'a amma fa yarinyar tayi wallahi, duk da dai kanta ba'awaye yake ba".
"Ehh naji koma dai mene, amma kasan wani abu ?".
"Menene fad'amin inajinka".
Saima ce ta shigo da Sallama tare da fad'in.
"Breakfast d'inka yayi ready".
"Ok ina zuwa".
Ta juya tafice, Anwar ya dubi Yarima tare da fad'in.
"Ina jinka".
"So nake kajawo hankalin wata yarinya, ma'ana kayi soyayya da ita".
"Ban fahimce kaba?".
"Ok abin da nake nufi, inaso kasa wata yarinya ta soka, ni so nake hankalinta ya tashi daga
kaina ya koma kanka, Yarinyar tana so nane hakan na neman jawomin matsala ".
"Wacce matsala kenan?, amma kuma wacce yarinya ce?".
Yarima Fudhal yayi murmushi tare da kau da kansa gefe.
"SAIMA 'yar gidan Alhaji Buba, ita nake so kayi soyayya da ita, so nake kamar yanda ta furta
tana sona inaso ta furta da bakinta bata so na !".
"Amma mai yasa ka yanke wannan hukuncin, Yarinya kamar Saima mai tsada tace tana
sonka amma kace a'a?".
"Yes bana ra'ayin 'yan mata irin tane, jiya da Yamma Mai martaba ya kira ni ya sanarmin
Baban ta Alhaji Buba da kansa yazo nan wajen Mai Martaba akan yana so ya had'a zuri'a da
mu, wato dai yana so ya auramin 'yarsa, bayan kuma anmin zab'in Safiyya, amma kasan amsar
da Mai Martaba ya bawa mahaifinta?".
"A'a sa ka fad'a".
"Cewa yayi ai namiji mijin mata hud'u ne, babu komai sai a had'amin mata biyu in aura aini
Yarima ne kuma magajin gobe, wannan dalilin yasa na kasa daure zuciyata har sai da naje na
furtawa Aynu ina sonta, sai dai bata bani amsa ba har yanzu, hakan namin ciwo sosai jiya ko
bacci kasa yi nayi".
"To ka had'asu duka ukun mana".
"Bana ra'ayin hakan, kawai ka yimin abin da nagaya maka".
"To amma idan Saima ta dawo kaina, ita Safiyyan ya zakayi da ita?".
"Banyi tunani akan taba, sai na gama da wannan".
"Amma kuma idan ta furta bata sonka ni take so, rabuwa zanyi da ita kome?, dan nima gaskiya
ba lallai ya kasance in so ta ba".
"Wannan ya rage naka karabu da ita ko ka aure ta, inkaso zaka iya son ta bai dame ni ba,
amma nidai buk'ata ta tace bata so na".
Anwar ajiyar zuciya yasaki mai k'arfi yana mai kallon Yarima cike da tunanin al'amarinsa,
shikam yasan tun yana yaro tare suka taso da Yarima amma har yanzu ya gaza fahimtar
halayyar Yarima, shi wani irin murd'ad'd'an mutum ne, sai ka kasa gane inda yasanya gaba.
"Kayi shiru ko kana buk'atar lokaci ne?".
"A'a zanyi yanda kace, amma kana ganin ita wannan Yarinyar zata so ka?".
"Ban dai sani ba?, amma shirun ta na bani tsoro".
Anwar ya girgiza kai da murmushi saman fuskarsa yana fad'in.
"Babu komai Allah ya shige mana gaba".
"Amin".
Suka mik'e suka fito zuwa falon, komai ready kai tsaye wajen abinci suka nufa sukayi
breakfast, suna ci suna tattaunawa domin falon babu kowa sai su kad'ai.
Zaune take bisa da kalin dake farfajiyar Shamaki babu kowa wajen sai ita, tayi zurfi cikin
tunani domin ba tasan ma Yarima Fudhal na tsaye bisa kanta ba, ya kira sunanta yafi sau a
k'irga amma bata amsa ba.
Hakan ya sashi zama kusa da ita tare da sanya hannu yad'an girgiza kafad'arta, firgigit ta farka
tare da mik'ewa da sauri tana duban Yarima, Yarima Fudhal murmushi yayi mata yace.
"Zauna mana".
Aynu ta koma ta zauna amma duk ata kure take jinta.
"Me kike tunani?".
Ya tambayeta Aynu tayi k'asa da kanta tana duban tafin hannunta.
"Babu komai".
Ta bashi amsa, girgiza kai yayi alamun bai yadda ba.
"Bana son k'arya kodai tunani na kike?".
"A'a !".
Ta kuma bashi amsa, Yarima yayi ajiyar zuciya tare da kafeta da idanuwa har lokacin
murmushin fuskarsa bai d'aukeba.
"Aynul-hayat !".
Ya kira sunanta da wata irin murya wadda tasanya tsigar jikin Aynu tashi, har tad'an rintse ido
kad'an, hannunsa ya sanya bisa tafin hannunta yarik'e, ya cigaba da fad'in.
"Ki fad'amin mana, ko kunyata kike ji?".
Aynu ta girgiza kai, tana mai k'ok'arin janye hannunta amma yarik'e kam.
"Bafa zan cika ki ba, har sai kin bani amsar tambayar da nake miki".
Aynu dai tayi shiru sai motsa bakinta take amma kuma maganar tak'i fitowa, su Zainab ta
hango suna nufo wajen kusan su biyar da dukkan alamu sungama aikin sune sunzo su huta
domim duk a wajen suke hutawa.
Ta kafe su da idanuwa tsoro ya k'ara kama ta, jikinta har wani rawa yake Yarima ya juya yana
duban inda take kallo murmushi yayi yana fad'in.
"Indai baki bani amsa ba sai dai su taddamu ahaka, danni kinsan babu ruwana !".
Aynu tahau girgiza kai kawai, bai zata ba sai jin saukar ruwa yayi akan hannunsa ya kalleta da
sauri yana mai sanya hannu ya d'ago fusakarta, afili ya furta.
"Kuka kuma?, Yi hak'uri share hawayen kada suzo su gani wasa nake maki fa n".
Ya cika mata hannun yana murmushi, ya mik'e tsaye ya zuba hannuwansa cikin aljihun
wandonsa yana kallon yanda taketa k'ok'arin share hawayen amma wasu na zubowa, sosai
abin yake burgeshi sai yaji dama su dauwama haka yana kallonta.
K'arasowar su Zainab ce tasan yashi barin wajen yana fad'in.
"Zaki zo kisame ni ne".
Zainab tak'arasa wajen Aynu tana fad'in.
"Lafiya Aynu?".
Harara ta sakar mata tare da juyar da kai gefe, sosai take jin zafin rik'e hannunta da Yarima
yayi.
"Wai ke mene yake damunki ne?".
"Babu komai".
Ta bawa Zainab amsa, Zainab tace.
"A'a wallahi nasan da wani abun, yanzufa naga Yarima yabar wajen nan, wannan ruwan
hawayen kuma fa?".
Tsaki Aynu taja tana fad'in.
"Ke kam kin shiga uku da tambaya".
"Ehhh naji, ai ni dake iya wuya muna tare".
Aynu tayi murmushi ta juyo ta kalli Zainab tana mai bata labarin abin da ya faru, ajiyar zuciya
Zainab tayi tare da fad'in.
"To ke mene ra'ayinki akan Yarima Fudhal, son shi ne ba kyayi ?".
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
16
Hello makaranta
Hope na sameku lafiya?
Ya komai, ya kowa?
Kuyi hak'uri dan Allah zaku dinga ganin post d'ina ko yaushe insha Allah amma ban da ranar
Friday sabida wani dalili.
Nagode sosai da sosai.
"wai ni ya zanyi ne Zainab !, Yarima ya matsamin akan lallai sai yaji ina sonsa ko bana
sonsa?".
"To wai ke mene ra'ayinki akansa ne !, nima kaina na kasa gane maki ko son sane bakyayi?".
Aynu ta girgiza kai cike da jimami.
"Nima har yanzu nakasa tan-tancewa ina sonsa ko bana sonsa, abin da kawai nasani ina jin
tsoro ne sosai?".
"Tsoson me kuma?".
"Yarima yafi k'arfina Zainab !, mai Yarima zaiyi da ni?, 'yar miskinai kuma baiwarsa niba 'yar
kowa bace Zainab !, Yarima yana tak'ama da kud'i da mulki mafiya yawan al'ummarmu na
yanzu musamman masu kud'i da masu mulki sunfi son AURE KWARYA TABI KWARYA, ina jin
tsoron abin da zaije ya dawo ne".
Zainab dogon tsaki taja cike da takaicin maganganun da Aynu ta fad'a.
"Toke mene zai dame ki, bafa ke kika ce kina son saba shine yace yana sonki, ni dai
shawarata agare ki kada ki bari damarki ta wuce ki, kiyi 'kok'arin yin amfani da damarki, ki
sanarwa Yarima kina sonsa, sauran lamarin ki barwa Allah komai kiyi ta addu'a da yardar Allah
komai zaizo cikin sauk'i".
Zainab ta nisa tana mai kallon Aynu dake share kwallar dake k'ok'arin zubo mata bisa fuskarta
ta cigaba da fad'in.
"Aynu kina son Yarima !, ki yarda da hakan kuma, kawai tsoro da fargaba ne sukafi tasiri a
zuciyarki shiyasa kika kasa fahimtar cewa kina son sa !".
Aynu murmushi tayi tana mai duban Zainab, Zainab kai ta gyad'a mata itama fuskarta d'auke
da murmushi ta dafa kafad'ar Aynu tana fad'in.
"Zan tayaki da addu'a sosai, amma kada ki bari Yarima ya sub'uce miki, domin ke kikafi
dacewa da Yarima Fudhal".
Sosai Aynu taji dad'in shawaran Zainab agareta, rik'o hannun Zainab tayi tana fad'in.
"Nagode ! Nagode !! Nagode !!! Zainab Allah yabar mutare".
"Amin".
Shela aka hauyi a cikin gidan na cewar tawagar Gimbiya Safiya ta sauka aje a tarbota.
Da sauri su Aynu suka mik'e suka nufi waje.
Jerin motoci goma ne sukai parking a k'ofar gidan, wani dogari ya taka da gudu yaje ya bud'e
k'ofar motar, cike da tak'ama da izza Gimbiya Safiyya ta sako k'afa ta fito, mace doguwa fara
kyakykyawa ajin farko tana sanye da farar alkyabba wacce ta rufe dukkan jikinta, inbanda
hannunta da k'afarta sune kawai a waje, takalimin k'afarta mai gashine shima fari iya had'uwa ta
had'u k'arshe.
Aynu sai taga tafi kyau afili ma fiye da a hoto data ganta, take taji wani abu ya ziyarci zuciyarta
taji ta raina kanta sosai domin babu abin da zata nunawa Gimbiya Safiyya indai kyaune zai sa
aso mutum to tabbas da Yarima baice yana sonta ba, domin Gimbiya Safiyya kyakykyawace ta
k'arshe.
Tana fitowa aka hau yi mata ruwan fure tare da tawagarta bayi mata biyar ke biye da ita, kai
tsaye wajen Mai Martaba dake tsaye ta nufa tayi gaisuwa, sannan muka rufa mata baya zuwa
cikin gidan.
Kai tsaye muka nufi b'angaren Fulani Sokoto da ita, tana tafe anayi mata ruwan fure tare da
kirari har zuwa cikin falon Fulani Sokoto.
Yarima Jalil da Jalila duk suna zaune falon tare d ma'aikatan Fulani, muna shiga Fulani ta fito
daga cikin d'akinta tana yiwa Gimbiya Safiyya sannu da zuwa, rungumeta Gimbiya Safiyya tayi
tare da yinn kiss d'in kuncinta tana fad'in.
" I Miss u my Mom !".
Ta juya kan Yarima Jalil