Showing 12001 words to 15000 words out of 88612 words

Chapter 5 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

16 Aug 2025

8293

mugun hukunci daga Yarima.

Zama yayi gefan katifarsa yana fad'in.

"Ke !, zo nan".

Aynu ta rarrafa da jan gwiwa ta k'arasa inda ta jiyo muryarsa idonta har lokacin a kulle bata
bud'e ba, cike da tsoro ta haufad'in.

"Kayi hak'uri ka gafarce ni dan Allah !, wallahi tallahi banyi zaton zan tadda kai a haka ba Allah,
dan Allah kada ka kore ni da wannan aikin muka dogara nasha wuya kafin in same shi
amma....!".

Kuka ne yaci k'arfinta ba tare da ta iya k'arasa mganarba ta mak'ale a mak'oshinta.


Yarima kuwa murmushi yayi yana mai k'arewa halittarta kallo yayin da yakeji bugun zuciyarsa
na k'aruwa sosai amma yana jin da d'in kallon nata sosai, musamman yanda take sarrafa
leb'anta wajen magana, sai zara-zaran gashin idonta da suka jik'e da hawaye duk da bai ga
idon nata ba.
"Bud'e idonki babu abin da zanyi miki".

Yayi maganar yana mai kafe idanuwansa bisa nata.

Aynu ta hau bud'e idonta kad'an-kad'an wai dan kada ta kuma ganinsa a yanda ta ganshi d'azu,
tana gama bud'ewa sukayi ido biyu da shi, tayi saurin sauke idonta tana mai rissi nawa da fad'in

"Nagode sosai, Allah yak'ara girma".

"Amin".

Da sauri ta d'ago kai ta dubeshi sabida mamakin yau karo na farko tayi magana ya mayar mata,
murmushi kawai ta ga yayi mata, ta d'auke kanta tana mai shigewa toilet din domin wankewa.

Mintuna kad'an ta fito ta taddashi a inda tabarshi illa wayarsa dake hannu yana daddan nawa,
yanaji ta fito ya d'aga kai yana binta da kallo har ta zo ta durk'usa tana sanar masa ta gama.

Mik'ewa yayi ya fice bai ce da ita komai ba, yana fita Aynu tayi ajiyar zuciya domin ita kanta
kallon da yake mata ya fara bata tsoro sosai, ji take aranta kamar hukuncin da zai yi mata yake
shiryawa.

Ta gama komai ta fito falo ta taddashi zaune, amma wannan karan ya akiye wayar gefansa
yana kallon ball a TV, gefe guda kuma Saima ce zaune Aynu na fitowa ta hau aika mata sak'on
harara ita kuwa bama tasan tanayi ba, ta fara k'ok'arin gyara falon duk abin da ta keyi idon
Yarima akanta shi kansa bai san dalilin da yasa yau d'aya yanajin dad'in kallon yarinyar sosai,
komai takeyi a nutse cikin sanyi kuma hakan na burgeshi sosai.

Sai da ta gama komai yau duk yana zaune, sannan Saima tazo ta jere masa kayan Breakfast
d'insa, yana ci yana faman kallom Aynu yayi mamakin irin abincin da yaci yau sosai, ya gama
Saima takwashe kwanukan ta fice tabar Aynu nan zaune.

Zaman duk ya gun dureta ga kallon da Yarima Fudhal keta jifanta dashi domin lokaci-lokaci data
d'ago kai sai sun had'a ido baki d'aya jinta take yau duk a takure sai take tayin data sanin
zuwanta aikin ma yau baki d'aya.


"Mene sunanki?".

Taji tambayarsa ta jefi kunnuwanta, ta d'an gyara zama tana fad'in.

"AYNU".

"Aynu kuma?, ci kakken sunanki nakeson ji".

Ajiyar zuciya tad'anyi kafin ta bashi amsa.

"AYNUL-HAYAT".

Ta fad'a tana mai gyara zamanta da kyau domin ji tayi k'afafuwanta duk sunja jini sunyi wani iri
babu dad'i sabida zaman d'urk'ushen da tayi.


"Aynul-hayat !".

Taji ya mai-maita cikin wata irin murya da ta sanya tsigar jikinta tashi, ta d'ago kai akaro na biyu
ta dube shi shima ita d'in ya kafe da idanuwa ya jefe ta da murmushi kafin yace.


"Nice Name".


Tayi saurin sauke idonta yayin da bugun zuciyarta ya cigaba da k'aruwa, aranta tana fad'in.


"To me ya zauna yi yau ayanda nasan shi da yana gama cin abinci yake ficewa zuwa wajen
Kakarsa ko Babarsu amma yau ya wani zauna ya tsare mutane".

A fili kuwa ita ma murmushin ta d'anyi duk da bai kai zuci ba.

"Beautiful smile".

Taji yak'ara fad'a ita ta d'auka ma waya yake da turawa dan bata fahimci mai yake fad'i ba.


Mik'ewa yayi ya shige bedroom d'insa mintuna kad'an sai gashi ya fito sanye da jeans bak'i da
T.sheet blue yayi kyau sosai, yazo yad'an rage tsayinta akanta yana fad'in.


"Aynul-hayat !".

Taji gabanta ya fad'i, ta d'ago kai ba tare data amsa ba, shima bai da muba ya cigaba da fad'in.

"Yaushe kuke tafiya gida?".

"K'arfe biyu ko biyu da rabi".

"Ok".

Abin da yace kenan ya kama hanya ya fice ya barta nan zaune tana tunanin abubuwan da
suke faruwa da ita yau.


"AYNU".

Ta sake jin muryarsa ta daki kunnuwanta ta juyo da sauri sai taga ashe Yarima Jalil ne tsaye
bakin k'ofa ya nad'e hannuwansa bisa k'irjinsa yana jifanta da wani mugun murmushi.

Gaishe shi tayi ya amsa yana fad'in

"Mai yasa bakyason sakin jiki da ni, da zaran kin ganni sai kin tsora ta?".

"Babu komai".

"Da wani abu mana fad'i gaskiya dai?".

Ji yayi andafa kafad'arsa ta baya ya juya da sauri sai yaga ashe Yarima Fudhal ne ya kuwa
had'e girar sama data k'asa, ya dubi Aynu yana fad'in.

"Ke...!, tashi ki fita".

Sum-sum Aynu ta fice dama neman hanyar fita ta keyi, Yarima Jalil kwafa yayi yana cijen lab'e
yabar k'ofar d'akin, domin yasan yanzu kome zai yi Yarima Fudhal bazai kulashi ba kuma ba
zai tsaya suyi maganar arzik'iba tunda ya d'aure fuska.




Assalamu alaikum

Nagode sosai 'yan uwa da abokan arzik'i abisa addu'arku agareni Allah yabani lafiya sosai,
masu inbox zuwa call da message ina godiya Ubangiji Allah yasaka da alkhairi amin.

Zaku cigaba da jina insha Allahu kamar ko yaushe.
[18/07, 18:08] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*


Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®



SADAUKARWA:-Namesy ta Pheerdauceey Jeebour.


Wannan page naki ne Tawan ta hannun damana HAFSAT M. ki morewa abinki.



09


Aynu na fita can baya taje ta samu waje babu kowa ta zauna abinta tana nazari a kan
abubuwan da suka faru, a haka Zainab ta tadda ita.

Neman guri tayi kusa da Aynu ta zauna tana tambayarta "lafiya kuwa?".

Aynu bata ji komai ba ta kwashe dukkan abin da ya faru ta sanar da ita sai dai ta b'oye abu
guda bata fad'a mata ba, wato ganin da ta yiwa Yarima wanda aganinta bai dace ta fad'awa
kowa ba.

Zainab tace.

"Haba Aynu wannan d'an abin shine kuma abin da zai ta da hankalinki, ki kwantar da hankalinki
wallahi babu abin da zai faru insha Allahu".

Nan dai tayi ta jan Aynu da hira har ta samu ta war-ware daga damuwar da take ciki, kafin su
mik'e su koma ciki domin k'arasa ayyukansu, Zainabu tayi b'an garen Fulani Bingel ita kuma ta
nufi b'an garensu Yarima.


***

"Ni kuwa mai Martaba dama akwai wata shawara da nakeson baka akan Magaji !".

Mai Martaba dake kishin gid'e kan kusun ya d'an sake gyara kwanciyarsa, Fulani Sokoto ta
mik'o masa yan kakken tufa d'in da yake ci yakarb'a ya kai bakinsa yana fad'in.

"Ina jinki, wacce shawara ce wannan?".

"Kan batun auren Magaji da kake taso yayi shi kuma kaga har yanzu baice komai ba, wata k'ila
baiga wacce yake so ba, shi ne nace mai zai hana anema masa auren Gimbiya Safiyya !".

Mai Martaba yayi shiru yana duban Fulani Sokoto cike fa nazari bisa maganar da tayi yanzu
can ya gyad'a kai yana fad'in.

"Shawara mai kyau Safiyya 'yar Sarki Maina yarinyace mai tarbiya ai babu wanda zai ganta
yace batayi masaba, gaskiya naji dad'i sosai akan wannan zab'in da kika yiwa d'an namu".

"Mai Martaba kenan ai nima d'ane a wajena inda abin da yafi hakama zanyi masa".

"Gaskiya ne aikuwa zamuje nema masa aurenta batare da b'ata lokaci ba".

Tuni wani sanyin dad'i ya ziyarci zuciyar Fulani Sokoto domin tarkonta ya kama, addu'arta d'aya
Allah yasa kada ta samu matsala da Yarima Fudhal kuma?.

***


Kwance yake falo kan d'aya daga cikin kusun d'in dake falon rawar sanyi yake sosai amma ya
kasa tashi ya nufi d'aki ko ya nemi abin da zai rufa dashi gashi wayarsa ma tana cikin d'akin, bai
jin zai iya d'aga ko da dai-dai da yatsansa d'aya bare ya bud'e baki yayi magana.

A haka Aynu tayi sallama cikin falon ta taddashi, k'ara sawa tayi da zauri zuwa inda yake tana

tambayarsa lafiya? ganin da tayi jikinsa sai rawa yake yasa ta fahimci cewa sanyi yakeji.

Mik'ewa tayi ta nufi d'aki ta d'auko masa k'aton bargon da yake rufa dashi ta zo ta rufa masa
sannan ta koma ta fara aikin ta mintuna kad'an da gama wankin toilet tana gyara cikin d'akin ta
dinga jiyo kakarin amansa, ta fito zuwa falo taga yayi aman bisa carpet ne kawai amma ban da
jikinsa .
"Ko inkirawo maka Yarima Jalil ne?".

Kai ya girgiza mata alamun a'a, Aynu tayi shiru tana dubansa shima ita d'in yake kallo.

"Ko a kira Hajiya?".

"Bana buk'atar kowa".

Abin da yace da ita kenan kawai, tayi shiru na tsawon lokaci kafin ta sake fad'in.

"To koma d'aki in gyara falon".

Dubanta ya tsayayi yana k'ok'arin bud'e bakinsa domin yin magana amma kuma maganar tak'i
fita, a hankali ya dafa bango ya mik'e yana tafiya har ya isa d'akin toilet ya wuce ya watsa ruwa
a daddafe tare da wanke baki ya fito ya sanya jallabiya ya kwanta.

Aynu ta gyare falon tas tasanya turare aranta tana jin tausayin Yarima domin tasan
bak'aramin ciwo ne zai kwantar dashi har haka ba.

Lokaci-lokaci takan lek'a tayi masa sannu ta dawo ta cigaba da aikinta, sai da ta gama komai
sannan ta koma ta tambayeshi koyana buk'atar wani abune?, Ruwan tea kawai ya buk'ata ta
kawo masa.

Lokacin k'arfe bakwai da mintuna arba'in da yake tazo da wuri yau burinta bai wuce ta samu ta
koma gida da wuriba sabida wani dalili nata.

Kitchent ta nufa ta sanar da buk'atar Yarima nan da nan aka mik'o mata flast da cofuna da
sauran tarkacen kayan tea.

A gabansa ta ajiye ta zuba masa ruwan tea d'in kawai da sugar domin yace baya buk'atar
komai da k'yar yamik'e ya karb'i tea d'in yana sha, ita kuma ta fice daga d'akin ta nufi wajen
Fulani Bingel wato mahaifiyarsa domin ta sanar da ita halin da yake ciki.


Tare suka tawo da ita da sauran ma'aikatanta, sukayi masa sannu suka fice ni dama falo nayi
zamana muna shigowa, Yarima Jalil ne ya shiga yayi masa sannu shima ya fito ya koma

d'akinsa, cikin k'ank'anin lokaci ciwon Yarima Fudhal ya bazu ko ina sai faman dubiya ake zuwa
abin har ya bani mamaki, sai na tuna da ni kaina idan zamuyi wata nawa muna ciwo sai wanda
ya zama dole yake zuwa dubamu, Allah sarki arayuwa idan a kace kud'i da mulki angama
komai.

Fulani Bingel ta jima a tare da shi komai ta tambayeshi yana so sai yace A'a daga k'arshema
cewa yayi baya buk'atar masu zuwa duba shi suna k'ara masa ciwo ne, mu dai muna zaune
falo munyi jugum, can sai ga Fulani sokoto tazo duba shi sai da tak'are mana kallo tana wani
yatsina sannan ta wuce ciki.

Tare suka fito da Fulani Bingel tana fad'in.

"Aynu ki kula dashi yace baya buk'atar kowa likita zai zo nan da anjima ya dubashi ".

"To angama Fulani".

Abin da nace kenan na koma na zauna, Fulani Sokoto ta bini da wani mugun kallo tana mai
ficewa, suma sauran ma'aikatan suka takewa Fulani Bilgel baya suka fice, suka barni ni kad'ai
zaune falo kamar wata mayya.


Har doctor yazo ya dubashi yayi masa allurai sannan ya kirani yayimin bayanin
magun-gunansa da yanda za'a dinga bashi ya tafi, na nemi guri na zauna ina kallon yanda yake
fitar da numfashi da kyar hucin zafin jikinsa kuwa ina daga inda nake ina jiyo zafin.


Ganin alamun yana magana nayi na k'arasa da sauri zuwa dai-dai kansa domin idan ba haka
kayi ba ba zakaji mai yake cewa ba, sai ji nayi ya kamo hannuna yarik'e kam ya had'a da
hannusa, har sai da naji zafin rik'on ga kuma zafin jikinsa, a haka na zauna ina kallon ikon Allah
domin da nayi k'ok'arin janyewa zai hud'e ido yana girgiza kai alamun kar incire, araina nace.
"Sai kace wani k'aramin yaro, kome yake damunsa ma oho?".


A haka har bacci mai nauyi ya d'aukeshi sabida allurar da akai masa na samu na cire hannuna
na dawo falo na zauna ina kallom TV films d'in india ne ake duk da bana fahimtar abin da suke
cewa amma kallon yana min dad'i sosai, na jima a zaune sai ga Yarima Jalil ya shigo ya zauna
na gaishe shi yana tambayar mai jiki nace.
"Yayi bacci ma".

Da haka yayi ta jana da hira jefi-jefi har na mance a tare da waye nake ga Yarima Jalil akwai
ban dariya tuni na ware yana bani labaran abin dariya ina dariya, abin da yake burgeni dashi
kenan ba ruwansa da girman kai illa abu biyun da sukaiwa rayuwarsa illa ban dasu na fahimci
Yarima Jalil na da kirki sosai har yafi Yarima Fudhal ma anawa ganin kenan.

Ya gama bani wani labari ina cikin dariya sai ganin mutum kawai mukayi a kanmu kamar
mala'ikan mutuwa haka muganshi a tsaye.

Yarima Jalil ya washe baki yana fad'in.

"Sannu broda ka tashi kenan, ya k'arfin jikin?".

Idan TV d'in dake d'akin tayi magana to shima yayi magana, nima na durk'usa inayi masa
sannu wani kallo ya watsomin daya sanya hanjin cikina k'ullewa ba k'aramin k'ok'ari nayi ba
wajen rik'e fitsarin da yayi shirin zubomin a wando.
[19/07, 17:42] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*



Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®



SADAUKARWA:- Namesy Pheerdauceey Jeeebour



Wannan page d'in naki ne FIRDAUSI SODANGI A cigaba da suburbud'a mana cakwakiyar
KWAD'AYI MABUD'IN WAHALA muna tare da ke har zuwa inda al'kalamin ki zai tsaya.


10




Na mik'e tsam na koma waje guda na zauna ina jiran umarninsa.

"Sannu Broda Allah yak'ara lafiya".

Cewar Yarima Jalil kenan yana mai ficewa daga d'akin.

"Ke zo nan".

Na mik'e da sauri na k'arasa wajensa ya kafeni da sexy eyes d'insa da bana iya juran kallonsu,
ya jima a haka kafin ya bud'e baki ya fara magana.

"Kada insake ganin ki tare da Jalil".

"To".

Na sake mik'ewa na nufi cikin d'akinsa na d'auko magun-gunansa na d'auko ruwa a robar faro
na kawo na ajiye, ina mai b'alli maganin na mik'a masa ya karb'a yasha ya jawo kusun ya koma
ya kwanta, sai lokacin na lura k'arfe biyu tayi ashe dubansa nayi ina fad'in.

"Zan iya tafiya?".

Bak'aramin k'arfin hali nayi ba wajen tambayarsa domin bansan amsan da zai bani ba.

Kai kawai ya d'agamin alamun ehh, na mik'e da sauri ina k'ara yi masa Allah sauwak'e na fice
daga d'akin duk da ban juya ba amma nasan ni yake kallo.

Kitchen na nufa kai tsaye naje na juye abincin nayiwa Jakadiyya sallama na tafi gida, araina ina
tunanin rashin zuwan Saima yau.

"Ko da yake jiki da jini a kace".


***

5:00pm


"Assalamu alaikum wai Aynu tazo".

Aynu dake shara tsakar gidan ta ajiye tsin-tsiyar tana tambayar.

"Waye ya aiko ka Mallam?".

"Ya Sayyadi ne fa na Islamiyya !".

"Au kace ina zuwa".

Yaron da ta kira da Mallam ya fice domin isar da sak'onta.

Aynu ta shige d'aki ta d'auko hijab d'in islamiyyarta tana mai duban Ummanta.

"Umma bari inje wai Ya Sayyadinmu ke kira na".

"To sai kin dawo a kula dai da kyau".

"To Ummata".

Aynu ta sanya ta mutsats-tsan silifas d'inta ta fice.

Yana tsaye jikin bishiyar darbejiyar k'ofar gidan, fari ne d'an siriri mai doguwar fuska sai saje
bak'i da yayiwa fuskarsa k'awanya da ka ganshi ka ga tsan-tsan bafulatani, yana sanye da
jallabiya fara har k'asa da hula fara da ake kira tashi ka fiye naci.

Aynu ta k'arasa wajensa fuskarta cike da fara'a kamar yanda tasa take, ta d'an rissina ta gai
dashi ya amsa yana fad'in.

"Malama Aynu kwana biyu na jiki shiru bakya zuwa makaranta?".

Aynu ta d'anyi murmushi tana mai gyara tsayuwarta tare da fad'in.

"Wallahi Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login