Showing 54001 words to 57000 words out of 88612 words

Chapter 19 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

8404

***
"Wai ni kuwa Aynu k
ina ya labarin Yarima Fudhal kuwa?".

"Oho ni ina zan sani?, idan nemansa kike kije gidansu mana".

"A a kawai dai tambaya nayi bai kuma zuwa ba?".

Aynu taja guntun tsaki gami da jefawa Zainab harara.

"Wai ke meye naki a ciki akan Yarima nifa nariga na fidda shi daga cikin rayuwata tun ba yau

ba".

"Ni kam bana tunanin Yarima zai manta dake Aynu".

"To ni namance da shi sai me?".

Tayi maganar cike da masifa, Zainab ta fiddo ido waje tana fad'in.

"A a mai da wuk'ar yi hak'uri kada ki rufe ni da duka".

Dariya suka d'anyi a tare, kafin Zee ta sake fad'in.

"Nifa ina ganin abune mawuyaci Yarima ya hak'ura dake tun yanzu".

"To sai kuma gashi ya baki mamaki ya hak'ura ko?".

"Bana tunanin hakan".

"Kinga Zee mubar maganar Yarima dan Allah kina b'atamin rai muyi abin da ya kawo ni kawai".

"To inajinki meke tafe da ke?".

"Au kinma mance abin da nace zanzo muyi magana akai?".

"Ohh yi hak'uri, yanzu tare kuke da Ya Sayyadin?".

"E mana".

"To bari ind'auko hijab muje to, amma kinsan ni banson bidi'a wallahi abarmu mud'anyi
partynmu ko yane, saura kimin buk'ulu".

"A a ni babu ruwana ke da mai bada kud'in".

"E naji dai tashi muje".

Suka mik'e suka fito daga gidan zuwa inda Ya Sayyadi Umar ke tsaye shi da wani abokinsa
suna zaman jiran fitowarsu.

*YARIMA FUDHAL*


Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®



SADAUKARWA:-Namecy Phirdauceey Jeebour.




32


*Mutane da dama na tambayata wai shin Yarima Fudhal ya hak'ura da Aynu ne koya?, nima
dai bani da wannan amsar sai mu jira abin da alk'alamina zai bayar, nagode sosai Masoya iya
wuya ana mugun tare*



***


"Wai ina na sanya wannan abin da aka kawomin ne?, inje inzubar da shi yanzunnan domin
bansan abin da aka k'ullo a ciki ba".

Cewar Fulani Sokoto kenan tana 'yan dube-dubenta, kafin ta sanya wata 'yar k'aramar Yarinya
da ke aiki a wajenta ta kirawo mata Larai.

Mintuna kad'an sai gasu sun dawo tare, Fulani Sokoto ta dubi Larai da fad'in.


"Da kukai gyaran falon nan baku ga wata gorar faro ba?".

"E ranki yadad'e bamu ga komai ba nan falon".

Fulani Sokoto ta cije yatsa tana fad'in.

"Ikon Allah abin da mamaki sosai wallahi, nan fa na tashi na barta jiya namanta shaf ".

Tayi maganar tana mai nuni da gabanta inda take zaune, Larai tace ita dai bata ga komai ba.

"Tashi kuje to".

Suka mik'e suka bar d'akin cikin rawar jiki, Fulani ta dubi Jalilah da duk diramar da ake tana
zaune gefe rik'e da waya tana game.

"Ke !, Jalilah".

Fulani ta kira sunanta, Jalilah ta d'ago kai tana duban Fulani.

"Ba kiga gorar faron ba?".

Jalilah ta gyad'a kai alamu E, tsaki Fulani Sokoto tayi cike da takaici.

Yarima Fudhal ne yayi sallama cikin falon ya shigo, Fulani ta nemo wani munafukin murmushi ta
d'ora akan fuskarta domin danne b'acin ran da take ciki don ka da Fudhal ya fahimci b'acin
komai, Jalilah kuwa ajiye wayar tayi tana mai binsa da kallon fuskarta d'auke da murmushi ta
d'an matsa masa inda take zaune, tana yi masa alamun yazo ya zauna.
Yarima Fudhal ya zauna kusa da ita yana gaishe da Fulani tare da tambayar jikin na Jalilah
yak'ara da fad'in.

"Da fatan dai tana shan rubutun nata?".

Yak'e Fulani tayi tana fad'in.

"E tana sha mana, abin da babu d'aci bare barci".

Jalilah kuwa kallon Fulanin kawai take yi, Fulani ta mik'e tana fad'in.

"Bari inbarka da k'anwartaka ind'anje Shamaki".

"To a dawo lafiya, nima office zanje yanzu".

Fulani ta fice ta barsu nan zaune, tana fita Jalilah ta d'auki waya tare da shiga wajen text
message tayi rubutu kamar haka.

"Yaya Mama fa bata son insha maganin nan".

Ta mik'a masa wayar tare da mik'ewa ta nufi d'aki, mintuna kad'an sai gata d'auke da gorar
rubutun ta fito, tana murmushi Fudhal ya tsare ta da tambayar.

"Me yasa bata so kisha?".

Shiru Jalilah tayi domin ta rasa amsar da zata bashi, tana ji a ranta ba zata iya tonawa
mahaifiyarta asiri ba, domin tana gudun b'acin sunan mahaifiyarta a idon Fudhal.

Karb'ar wayar tayi ta sake rubuta masa.

"Wai bata yarda da maganin ba zubarwa za tayi, amma dan Allah kada ka nuna mata kasan
haka, zan b'oye maganin indinga sha ko wanne magani zaka kawo ka dinga bani zanyi".

Yarima Fudhal ya karanta tare da yin murmushi yana mai duba agogon dake d'aure bisa
tsin-tsiyar hannunsa kafin ya dawo da dubansa kan Jalilah yace.

"Karki damu ki dinga sha ab'oyen rubutun nada matuk'ar muhimmanci a tare da ke, lokaci ya
k'ure domin nayi late sai na dawo".

Yakai maganar yana mai dafa kanta ya fice da sauri, ajiyar zuciya Jalilah tayi mai k'arfi kafin tayi
maza ta koma d'aki ta b'oye gorar rubutun ta dawo dalon ta zauna inda Fulani ta barta.


Sosai Yarima Fudhal ya mai da hankali kacokan kan ciwon Jalilah kullum yana jigilar
karb'o mata magani duk da cewa a b'oye yake bata Fulani Sokoto bata sani ba, wasu kuma
wajen Fulani Bingel yake a jiyewa kullum idan lokacin sha yayi sai taje ta sha ta koma.


Sai dai tana cike da kokwanto da mamakin yanda a kayi Yarima Fudhal ya yarda da abin da ta
fad'a masa ba tare da yayi tunani ko tambaya akan dalilin da yasa Fulani Sokoto ba ta so Jalilah
tayi amfani da magungunan da yake karb'o mata ba.

Amma sai dai ta gaza tambayarsa domin gudun zargi da tsoron wani abu da zai iya zuwa ya
dawo.


Cikin sati biyu da fara ciwon nata sosai sauk'i ya fara samuwa sai dai matsalar rashin maganar
da tafi damun kowa, amma Fulani Bingel takance ya kwantar da hankalinsa ya cigaba da
addu'a sauk'i yana daga Allah.


***

A b'angarensu Aynu kuwa shirye-shiryen biki ake gadan-gadan domin bikin ya rage saura sati
biyu a shiga cikin hidimar bikin, su Aynu anraba anko tare da taimakon Zee domin ita Aynu da
cewa tayi kowa yasa kayansa amma Zee ta ce ina bazai yiyu ba dole ayi anko kamar yanda ake
yi a kowanne biki, INA RUWAN ZAINAB MANYA, K'IRJIN BIKI KENAN.

*(Ni FA BAN GANE BA, ZEE TA KOMA B'ANGAREN YA SAYYADI UMAR NE?, YA ABIN YAKE
NE?).*


"Yadai lafiya kuwa kake ta faman kirana a waya?".

Anwar ya fad'a yana mai zama a d'aya daga cikin kujerun da ke gaban table d'in Yarima Fudhal.


"Babu komai rakiya nake so kamin".

"Zuwa ina kenan?".

Yarima ya kafe Anwar da shanyayyun idanuwansa ba tare daya bashi amsar tambayarsa ba ya
mik'e tsaye tare da fad'in.


"Kai dai tashi muje kawai".

Anwar ya d'anyi jim kafin shima ya mik'e yad'an zunkud'a kafa yana fad'in.

"Muje to amma fa kamai da ni d'an rakiya wallahi, ko ina nake kome nake yi sai ka kira ni inraka
ka wani waje, na kusa samawa kaina mafita nima dai".

Yarima najinsa baitanka masa ba domin yasan duk surutun banza yake yi bazai iya aikata abin
da yake ikirarin zai yi ba.

"Kana jina kayi shiru?".

Anwar ya jefa masa tambaya dai-dai sanda suka isa jikin motar Anwar d'in.

"Au wai a motata za'aje ma?".

Ya sake jefawa Yarima Fudhal tambaya.

"E da a motar wa za'aje?, idan ba taka ba".

Ya bashi amsa yana mai shigewa cikin motar ya zauna, tsaye Anwar yayi yana binsa da kallo.

"Ka shiga muje mana".

"Wai driven d'inma ni zanyi?".

"Kaga malam kafiya k'orafi da surutu dan Allah ka shigo kaja mota muje".

Anwar yayi murmushi a can k'asan ransa yana mamakin hali irin na Yarima, yau ka ganshi fari
gobe ka ganshi bak'i kullum da salon halin da zai nuna maka.


"Matarka zatayi fama wallahi".

Anwar yayi maganar yana mai sanyawa motar key, idan kujerar da yake kai tayi magana to
shima ya tanka, kwanciyarsa yayi jikin kujerar motar tare da lumshe ido kawai yana sauraron
abubuwan da zuciyarsa take raya masa.


Sai da Anwar ya hau babban titi sosai sannan ya juyo fuskarsa ya dubi Fudhal da har lokacin
yana kwance ido a lumshe.

"Wai ina zamu ne?, ka barni sai faman tafiya nake".

"Unguwar kwari".

Ya bashi amsa ba tare da ya bud'e idonsa ba.

"Unguwar kwari kuma?, kana nufin gidansu Aynu zamu je?".

Yarima Fudhal ya bud'e ido tare da gyara zamansa kafin ya bashi amsa da fad'in.

"E unguwar kwari zamu je, amma ba gidansu Aynu ba".

"To wajenwa zamuje a unguwar kwarin?".


"Kai dai muje kawai zaka ga wajen wanda zamu je".


Anwar bai kuma cewa komai ba ya juya kan motarsa ya hau titin da zai sada shi da unguwar, a
dai-dai bakin layin sukayi parking motarsu, Fudhal ya fito ya tsaya jikin motar yana mai k'arewa
layin kallo har Anwar d'in ya fito shima ya kulle motar yana fad'in.


"Sai ina kuma?".

"Ka fiye tambaya ka...!".

Maganar ta mak'ale a dai-dai sanda ya hango Zainab na fitowa daga cikin layin, Fudhal ya
fad'ad'a murmushinsa tare da fad'in.

"Yauwa ga Zainab d'innan ma".

Zainab ba k'aramin mamaki tayi ba sanda idonta ya sauka kan Yarima Fudhal, k'arasawa tayi
da fara'a tare da sallama.

Fudhal ya amsa yana fad'in.

"Ina Aynu?, wajenta muka zo".

Zee ta d'anyi jim kafin ta bud'e baki ta fara magana.

"Ai nad'auka ka hak'ura da ita wallahi".

"Kamarya kenan, mai yasa kika ce haka kuma?".

"Naga tun randa kukayi rabuwar babu dad'i baka sake nemanta ba, ko layinan ka daina zuwa".

"Aiki ne ya tsare ni".

"Ayya amma ba kada labarin aurenta ko?".

"What..! Aure kuma?, wa zata aura?".

Fudhal ya jero tambayoyin cikin rud'u da tashin hankali.

"Ya sayyadi Umar zata aura, nan da sati biyu masu zuwa".

Yarima Fudhal yayi sauri ya jingina a jikin mota bai sake furta ko kalma d'aya ba, sabida ji da
yayi bugun zuciyarsa na k'ara tsananta da bugu fiye da kima.

Zainab bata lura da yanayin da yake ciki ba ta cigaba da fad'in.

"Gaskiya nima banji dad'i ba wallahi, naso a ce aurennan da kai za'ayishi amma babu yanda
muka iya haka Allah ya tsara".


"E hakane dama ai matar mutum k'abarinsa inji malam bahaushe, mungode sosai Zainab".

Anwar yayi maganar yana mai dafa kafad'ar Yarima, Zainab tace.

"To ni zan koma gida dama sak'o na kaiwa Aynu sai anjimanku".

"To sai anjima ki gaida Mamanku".

Cewar Anwar kenan, yayin da Zee ta juya tabar wajen.

Anwar ya bud'e mota ya zaunar da Yarima yana fad'in.

"Please ka sanya ranka salama dan Allah kada ka jawa kanka matsala fa?".

Yarima Fudhal ya dubi Anwar da jajayen idanuwansa da suka rine daga fari zuwa ja tsabar
d'acin rai.

"Yanzu Aynu zata iya auran wani ba ni ba?, why Anwar mai na aikata haka a rayuwata da SO
yake wahalar da ni haka?, wanne zunubi na aikata wa Ubangiji ya jarance ni da irin wannan
SO?, har zuwa yaushe ne zan samu muradin raina?, har tsayin wanne lokaci ne zuciyata zata
samu abincinta, har yaushe ne idaniya zata samu haskenta?, yaushe ne rai zai huta daga
fuskantar barazanar yin bankwana da duniya?, Anwar ka taimake ni dan Allah ina son Aynu
wallahi inasonta kamar raina ita ce dukkan burina na duni...! ".

Bai samu damar k'arasa maganarba sabida kukan daya sark'e masa murya, sosai Yarima
Fudhal ya bawa Anwar tausayi, yasan zafin so amma bai san zafin yakan kai har wannan
matakin ba, ya rasa kalmar da zai lallashi Fudhal da ita hakan yasa kawai ya sanyawa motar
key suka bar layin gidan domin ya fuskanci Yarima Fudhal baya cikin haiyacinsa a wannan
lokacin.

*YARIMA FUDHAL*




Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).



NAGARTA WRITERS ASSOCITION®


SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey jeebour.

32



Ganin halin da yake ciki ne ya sanya Anwar mai makon ya kai shi gida sai suka nufi
gidansu Anwar d'in, ko da yayi parking motar a parking space ya shafe tsayin mintuna amma
Yarima Fudhal ko motsi bai ba ganin da yayi ba shi da niyar fitowa ya sanya shi bud'e
b'angaren da yake zaune ya kamo hannunsa ya fito da shi suka nufi part d'in Anwar.
Suna shiga falo Fudhal ya nufi frige kai tsaye ya d'auki gorar faro mai sanyi zai sha Anwar ya
karb'e da sauri yana fad'in.

"Kanka k'alau kuwa Yarima ka shiryawa kanka bankwana da duniya ne?".

Fudhal bai kulashi ba ya koma kan kujera ya zauna yana mai da numfashi, ya shafe kusan
mintuna talatin a haka Anwar na tsaye gefe yana kallonsa cike da tausaya shi yama rasa mai
zai yi masa da zai samu zuciyarsa tayi sanyi a yanzu.

Wunin ranar Yarima Fudhal gidansu Anwar yayi shi haka ya wuni babu ci babi sha, har dai
b'arawon bacci yayi a won gaba da shi, bai farka ba sai bayan sallar maghriba, ko da ya farka
kaso talatin na daga damuwar da yake ciki a cikin d'ari ya ragu, mik'ewa yayi ya nufi toilet yayo
alwala yana fitowa ya shimfid'a sallaya yahau jero salloli bayan idarwarsa ya shafe tsayin lokuta
yana addu'o'i fuskarsa cike da hawaye yana nemawa kansa sauk'i a wajen Allah, a haka Anwar
yayi sallama ya taddashi , Yarima Fudhal ya sallame daga addu'ar da yake ya dubi Anwar da
fad'in.

"Muje ka ajiye ni a gida".

"Ka bari har gobe mana".

"A a yanzu nake so zansha maganina ne".

"To kaci abinci mana, mai za'a kawo maka?".

"Bana buk'atar komai yanzu idan naje gida zanci".

Anwar yasan tunda ya kafe ba zai zauna ba garama kawai ya tashi ya kaishi gidan, Anwar yace

"To shikenan tashi muje".

Domin yasan halin Yarima tunda yasa kanshi tafiya babu yanda za'ayi ya zauna kome zai ce
masa kuwa.

A tare suka fito Yarima ya shiga mota ya zauna Anwar yaja suka bar harabar gidan.

Ko da suka isa gidan Anwar yaso sanarwa su Hajiyar Fudhal abin da yake damunsa amma
Yarima Fudhal ya kafe a kan kada ya fad'awa kowa, akan dole Anwar yayi shiru da bakinsa
sukayi sallama ya koma gida tare da fad'in da safe zai dawo insha Allahu.


Anwar na tafiya a mota wayarsa tayi ringing baiyi niyar d'agawa ba amma ganin number da ke
kan screen d'in wayar ya sanya shi d'agawa tare da sanya wayar a handfree.

Daga can b'angaren a kayi sallama tare da fad'in.

"Dan Allah idan babu damuwa ko takura kazo gidanmu yanzu".

Anwar ya d'anyi jim kad'an kafin yace.

"Lafiya dai ko?".

"Lafiya k'alau wallahi, kazo dai kawai".

"Ok ina kan hanyar zuwa gida ne yanzu amma bani mintuna goma sha biyar yanzu zaki ganni a
k'ofar gidanku insha Allah".

"To sai kazo, Allah kawo ka lafiya".

Aka katse wayar, Anwar yabi screen d'in wayar da kallo cike mamaki tare da wani guntun
murmushi daya mak'ale gefan fuskarsa afili ya furta.

"Yau SAIMA da kanta tana nemana...".

Ya d'an daki sityarin motar yana fad'ad'a murmushinsa cike da jindad'in wannan lokaci.

Kafin ya hau tunanin abin da ya faru tsakaninsa da ita sati uku da suka wuce.


*MUD'AN KOMA BAYA KAD'AN*

SATI UKU DA SUKA GABATA KAFIN WANNAN RANA !.


Zaune Yarima yake cikin office d'insa yana ta faman duba wasu file-file da ke gabansa, Anwar
ya turo k'ofa ya shigo tare da sallama Fudhal ya amsa ba tare daya d'ago kansa ba, Anwar yaja

kujera ya zauna yana fad'in.

"Kaga Mallam ajiye aikin nan magana zamuyi mai muhimmanci".

Yarima Fudhal ya rufe wani file daya bud'e ya d'ago kai yana fad'in.

"To Oga ina jinka".

Anwar yayi murmushi kafin yace.

"Koma dai mai zaka ce naji, wani tunani nayi akan Saima".

"Tunani kamar name fa?".

"E to naga Yarinyar ta yarda dani sosai, sai nake ganin kamar infad'a mata gaskiyar abin da
yake faruwa kafin k'urewar lokaci ta zo ta sani abubuwa kuma sukwab'e".

Yarima Fudhal yayi shiru kafin ya gyad'a kai.

"Ra'ayinka ne wannan in kaso ta san gaskiyar to, idan kaga baka buk'atar ta sani shikenan,
amma zanfi so ka saurari zuciyarka akan abin da take raya maka".

"Nidai nafi aminta da sanar mata ".

"Ok babu damuwa Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login