Showing 1 words to 3000 words out of 87436 words
Chapter 1 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
_Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai, godiya ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai da ya ba mu aron rai da lafiyar da mu ka kawo wannan lokacin da rai da lafiya. Ina roƙon Allah yadda ya bani ikon fara rubutu littafin nan lafiya da aminci Allah ya sa na gama lafiya, Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfani al’umma baki ɗaya, ya Allah kar ya bani ikon rubutu ɓarna ko abinda ya saɓa addinin mu amin._
_Wannan labari mai suna KIRAN RABO ƙirƙirarre ne, ban yi shi dan wani ko wata ba, in ya yi kama da labarinki ko labarinka ayi haƙuri rashin sani ne._
_Ban yarda a canja min labari zuwa wata siga daban ba, ban amince a juya min labari zuwa wata fuska ba ba tare da izini ba!._
*SHIMFIƊA.*
_*Hausawa suna cewa da mutuwa, aure da arzuƙi ƴan uwan juna ne. Ni kam na ce a haɗa da RABO domin shima yana daga cikin waɗanan ukun. RABO in ya yi kira ko kana cikin mahaifiyar ka sai ka amsa shi ka fito duniya. KIRAN RABO ya kan canja ƙaddara daga baƙa zuwa fara, KIRAN RABO ya kan mayar da wasa ya zama gaske, KIRAN RABO yana mayar da abinda ba zai yu ba ya zama mai yuwa. Wani yana shigowa rayuwar wani dan ya zama silar amsa KIRAN RABON sa, wani yana fita daga rayuwar wani dan hakan ya zama silar amsa KIRAN RABON SA. Ya ake gane rabo ya yi kira? Ba a ganewa, sai bayan Allah ya yi ikon sa a kai ake fahimtar daman can kiran rabon ka amsa. Ana amsa KIRAN RABO a lokacin da ba a san an amsa shi ba, ba a jin kiran da kunne balle a kasa kunne a nutsu dan a saurari lokacin da rabo yake kiran ka. Kamar yadda bawa ba ya sanin lokacin da mutuwar sa, lokacin auren sa, lokacin da ƙaddara ta kira shi haka ba a sanin lokacin da RABO yake kira sai dai ka tsinci kan ka a lokacin da ka amsa. KIRAN RABO lokaci ne dashi kamar dai yadda mutuwa take da lokaci!.*_
https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t
*Book 1*
*P 01*
_"Tsinanne ɗan iska, a haka zaka ƙare rayuwarka. Yara duk sun zama ɓata gari saboda rashin kulawar iyaye"._
_"Ka daina furta irin wannan maganar don Allah, in kana aibata yaran wasu kamar na ka ka ke aikabata. Mun haifa mu ma, don Allah ka daina ba hali ne mai kyau ba."_
Numfashi ta sauke tunawa da abinda ya wuce a shekarun baya, sai yanzu take fahimtar illar da take cikin irin wannan kalamai da iyaye suke yiwa yaran da ba nasu ba. Sai yanzu take fahimtar dalilin mahaifitarta da a kullum take kwaɓar mahaifinsu ga barin aibata ƴaƴan wasu da yake yi. Tabbas yanzu ta fahimta tunda gashi reshe ya juye da mujiya.
A zaune take a ƙaramar harabar gidan akan sallaya babba mai girma. Ita da wani mutum ne a zaune amma gabaɗaya hankalin ta baya tare da shi ta tafi tunanin abinda ya wuce saboda abin ya zo akan gaɓar da zata yi tunanin ne. Kallon farko zaka yi musu ka fahimci zaman taɗi suke yi kamar yadda samari da ƴan mata ke yi, ko yadda zawarawa suke yi.
A yadda take kallon sa yana magana zaka tabbatar da kalaman da yake faɗa basu yi mata daɗi ba sam, fuskarta mai yawan fara'a ta canja gabaɗaya ta cushe waje ɗaya saboda yadda kalaman suke sosa mata rai. Shima kallon ta yake yi cikin ƙarfin guiwar sanar da ita saƙon da yake zuciyarsa, domin abinda yake ransa kenan kuma shi yake faɗa kuma ya zama dole ta sani.
Babbar mace ce matashiya wacce a a shekaru zata kai shekaru talatin da biyar a duniya, fara ce irin haske mai ja kaɗan, tana da haske sosai da manyan idanu masu haske da ɗaukar hankali lokaci guda. Tana da dogon hancin da ya ƙarawa fuskarta kyau. Kai tsaye in ka kalle ta baza kace ta kai shekarun da take kai ba saboda ƙaramin jiki ne da ita, sannan ga madaidaicin kyaunta da yake ɗaukar hankali har ba a fahimtar shekarun ta saboda hakan.
Jin Muktar ya gama maganar tasa sai tayi murmushin yaƙe wanda ake kira da yafi kuka ciwo ta kalli wanda yake zaune kusa da ita cikin murya mai sanyi ta ce, "Abinda ka ke tunani kaima a kaina kenan?." Yayi murmushi ya ce, "abu ne a bayyane ai Aysha. Ke kin san da gaske nake ina so na aure ki, amma maganar da take yawo a kan ki bana tunanin iyayena zasu amince da auren ki. Shiyasa na zo ayi ta ta ƙare kawai."
"Yanzu zuwa kayi ka ce min ka fasa aure na kenan?" Ta tambaya tana kallon sa. Duk da ba yau aka saba ba, amma yanayin yadda yake magana yana bata mamaki.
"Kusan Hakan." Ta girgiza kai ta ta ce, "to ka tashi ka koma ta inda ka biyo, saƙon da ka ke son isar min ka isar sai ka je ko?."
Ya bi fuskar ta da kallo ya ce, "ki yi haƙuri ba daga ni bane, in magana tayi yawa akan mutum ko kana son alaƙa dashi dole ka dakata. Na so auren ki amma zancen nan ya zaga ko ina. Har da masu cewa shiyasa baki aure ba saboda duk abinda miji yake yiwa matar sa ƙanin ki OMAR yana yi miki."
Ta rantse ido cikin ɗacin kalmar ta ce, "kar ka sake magana akan ƙanina, kaje tunda dai ka fasa ai shikenan ko?." Ta faɗa cikin rashin damuwa dan ta saba indai fasa aurenta ne. Yayi dariyar rainin hankali ya ce, "Daman an ce bakya son laifinsa, daman an sanar dani ko me za a ce baza ki taɓa ganin laifinsa ba, ke lallai ga mai ɗan uwa. Taƙadarin yaron da ya adabi mutanen Kano gabaɗaya, wai shi ki ke jin haushi dan an faɗi magana a kansa saboda kawai ɗan adam baya son gaskiya."
"Ka gama!?."
Ita dashi a tare suka juya zuwa inda suka ji anyi maganar zuciyar ko wannen su ta buga a take. Wara idanu tayi ganin wanda idanunta suke gani dan gabɗaya bata so yazo ya riski maganar ba, shikenan yanzu ƙaramin abu zai koma gingimeme a wajansa.
Yana zaune akan ɗan tudun ƙofar gidan ya harɗe ƙafafunsa, ga ƙatuwar wuƙa a hannunsa yana shafa ta a hankali yana kallon ƙasa kamar ba shine ya yi maganar ba. Juyo idon sa yayi ya watsa masa wani kallon da ya saka gaban Muktar ya faɗi nan take ya shiga hankalinsa. Wani irin kallon raini da ƙasƙanci yake yi masa yana taune laɓɓansa cikin ɓacin rai. Wuƙar ya fara wasawa a jikin ƙaramin dutse da yake kai a nutse cikin salon mugunta.
Saurayi ne wanda a shekaru bai wuce talatin ba, kallo ɗaya zaka yi masa ka shaida kamar da ya ke yi da Aisha, duk da kyuansa ya fi fitowa akan nata amma suna kama sai dai banbacin halitta ta mace da namiji. Dogo ne mai cikar zati da kuma kyakykyawar halitta, kallon farko zaka yi masa ka shaida kwarjininsa, dan lokaci ɗaya zai cika maka idanu tsoronsa zai mamaye maka zuciya har ya kai mutum ga sauke idanu ƙasa. Namiji ne wanda ake kira na miji, ƙaƙƙarfa kuma mai jikin ƙarafafa, sai ka rantse da Allah Aisha ƙanwarsa ce saboda gabaɗaya ya zama shine yayan itace ƙanwar. Yana da haske sosai, fuskarsa tana da haske irin sosai ɗin nan, yanayin rigar da take jikinsa ƙarama ce zaka hango fatar jikinsa da ta kasance fara tas har tafi fuskarsa haske.
Yana da manyan idanu sosai wanda ake kira kwala-kwala masu ban tsoro, idanunsa zagayayyu ne masu girma, in ya wara su yana magana kamar zasu fito saboda girman su. Kallo ɗaya in ka yiwa idanunsa baza ka so ka sake kallon idon ba musamman in ransa a ɓace ya ke. Yana da hanci amma ba irin mai tsayin nan sosai ba kuma ba gajere ba ne, yana da zagayye cikakken baƙin gashi a fuskarsa, wanda suka ɓoye ƙuruciyar sa suka bayyanar da kwarjini a tare dashi.
Yana da kwantaccen gashi a kansa wanda ya tara, in ka kalli gashin lokaci ɗaya zaka fassara shi a gashin buzaye ko fulani, dan yadda ya ke a kwance baƙi zai saka ka tabbatar ba gashin hausawa ba ne. Yana da yalwar gashin gira irin wacce take a cushe gata baƙa sosai. Haka fuskar sa itama a cike take da gashi mai yawa wanda kana gani ka san baya samun gyara yadda ya kamata.
OMAR kenan! wanda ake yiwa laƙabi da DAMISA wasu kuma su ce MADUGU, wasu kuma ce JAN WUYA.
Ɗan daba ne lamba ɗaya, ɗan daba ne mai lasisi wanda ya samu goyan baya daga iyayen ƙasar wato ƴan siyasa. Duk da dabancin ta sa mai tsari yake yi amma yana daga cikin ƴan dabar da ake matuƙar tsoron su a faɗin Kano. Kaf yankin ƙofar nasarawa shine shugaba, babu wani ɗan daba da zai aikata ba daidai ba a wannan area sai Damisa ya sani. Kuma saboda shine kawai ake jin tsoron yin faɗa a arear saboda in ya tashi ɗaukar fansa bai iya ba, shiyasa ba a cika koda sace-sace a unguwar ba saboda ya zama kamar kura da nama ya shigo zai kama. A shekarun baya ya yi faɗace-faɗace duk da bai taɓa kisa ba amma ya yi ƙanin kisa, a yanzu ne ya canja tsari da salon dabancin shiyasa wasu mutanen suke gani kamar ba ɗan daban gaske bane.
Aisha da take zaune ganin Muktar ya firgita da ganin ƙanin nata cikin bada umarni ta ce, "Omar ka tashi ka shiga gida babu ruwan ka." Jin abinda Yayar ta sa ta ce sai ya miƙe tsaye yana kallon ta, shigowa ciki yayi sosai yayi kamar zai wuce ta kawai ya ɗuka ya damƙi wuyan Muktar ya miƙar dashi tsaye.
Nan take jikinsa ya soma, yana kallom Omar yana karkarwa dan daman an faɗa masa Omar indai akan Yayarsa ne babu abinda bazai yi ba. Omar ya kalli cikin idonsa cikin dakakkiyar muryarsa irin ta jarumai mazajen gaske ya ce, "maimaita abinda ka faɗa mata naji." Jikin Muktar rawa yake yi sosai, ji yake kamar ya yi fitsari saboda tsoro ya kasa furta komai saboda tashin hankali.
Aisha da take tsaye itama t ce, "Omar meye haka ne? Ka sake shi!?" Ta faɗa cikin ɗaga murya. A fusace ya kalle ta ya ce, "DIDI ki matsa baya, babu abinda zai hana ban farka bakin wannan mutumin ba. Nan gaba na ga da wanne bakin zai furta irin abinda ya ce yanzu" ya dawo da kallon sa ga Muktar shi ya ce, "Tunda ya tako har cikin gidan mu babu abinda zai hana ban ɗauki mataki a kansa ba. Ko na datse masa harshe, ko na farka cikinsa."
"Wayyo Allah na shiga uku!. Aisha don girman Allah ki taimake ni, ki ce ya ƙyale ni, ki taimaka min kar......" maganar da ta maƙale saboda wuƙar da ya kawo kusa da wuyan sa ya ce, "kana cigaba da magana wallahi sai dai uwar ka ta haifo wani."
Ɗif ya yi ya kulle bakinsa da jikinsa yana karkarwa sosai nan da nan hawaye suka fara ambaliyya daga idanunsa saboda tsoro. Didi ta ƙaraso wajan ta riƙe hannunsa ta ce, "Omar ka ƙyale shi ya tafi na ce ko?."
"Bazan ƙyale shi ba. Ba shi yana da zarrar zuwa har gidan nan yake cewa ya fasa aurenki ba?
Inda iya wannn kalmar ya faɗa da sauƙi, amma har magana mara daɗi ya faɗa a kanki. Didi ko duniya ce zata taru yau babu abinda zai hana ban farka cikin mutumin nan ba."
"To ba ni aka faɗawa magnar ba ina ruwan ka...? Malam ka cika shi ya tafi bana son wannan ɗabi'ar" Ta faɗa da ƙarfi tana son cire hannun Omar daga wuyan Muktar amma ta kasa.
Kallon Muktar ɗin ya yi da yake hawaye kamar ƙaramin yaro jikinsa na rawa sosai ya ce, "ka ci albarkacin ta a yau ka sha, amma kar ka sake idanuna ya sake ganin fuskar ka, In kayi wannan gangancin zaka yi dana sanin zuwan ka duniya." Kai yake ɗaga kamar ƙadangare saboda tsoro Omar ya ce, "baka da baki!?." Yadda yayi maganar cikin tsawa ya ake firgita shi ya ce, "na....ji....ka yi....ha...ku....ri."
Omar ya cika masa wuya ya kalle shi ya ce, "durƙusa ka bata haƙuri." Babu ɓata Lokaci ya zube a ƙasa ya ce, "Ki yi haƙuri Aisha, na tuba ki yafe min." A fusace Omar ya ce, "sunan ta ka ke faɗa kai tsaye babu girmamawa? Sa'ar ka ce?." Jiki na karkarwa Muktar ya ce, "ki yi haƙuri Mama, Allah ya wuci zuciyarki."
"Haifar ka tayi da zaka ce mata Mama!?" Ya sake faɗa yana cakumar rigarsa. Muktar ya fashe da kuka mai sauti ya ce, "Ki yi haƙuri Anty, ki yi haƙuri don Allah." Omar ya sake shi ya nuna masa ƙofa ya ce, "bar nan." Ai bai sake magana ba ya fita a guje ko takalman sa bai ɗauka ba saboda tsoro.
Omar ya kalli inda Didi take ganin bata wajan ya san ta shiga gida ya kalli yaransa da suke ƙofar gida ya ce, "duk ranar da ya shigo area nan kar ya fita da lafiya." Dukkan su suka haɗa biki suka ce, "An gama Damisa, a fito Lafiya Magudu uban matsiyata." Ya jiyo idanunsa masu ban tsoro ya kalle su ya ce, "Zaku iya wucewa anjima sai ku zo" yana gama faɗa ya shiga gida yana jin su suna amsawa.
Yana shiga tsakar gidan Didi ta tare shi ta ce, "Omar me yasa ka ke min haka ne? Omar me yasa ka ke son saka min ciwo ne wai?." Zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta ce, "kar ka ce komai sai na baka dama. Ya ka ke so nayi ne? Me ka ke so ka zama ne Omar? Yau gabaɗaya satin ka biyu da fitowa daga prison bayan ka shafe kwana goma a ciki, so ka ke ka kuma komawa ne?."
"Didi...." Ta katse shi ta ce, "ba wani Didi, babu wani Didi kar ka ƙarasa. Omar me ka ke son zama ne don girman Allah? Ɗan ta'adda ka ke so ka zama ko me? A gaban idona ka dinga zancen zaka farkawa wani ciki?."
"Duk abinda ya faɗa miki naji, in ya fasa auren ki ya faɗa cikin magana mai daɗi mana sai ya faɗa da wulaƙanci?. Na rantse da girman Allah ba dan ke ba sai na yiwa bakinsa illa."
"To waye zai aure ni bayan kowa tsoron ka yake ji? Da irin wannan dabi'ar taka ka ke so na yi aure Omar?. Wanne iyaye ne zasu amince ɗansu ya aure ni bayan ina da ƙani irin ka?." Ganin idon Yayar tasa ya fara kuka da hawaye sai ya lumshe idanunsa ya buɗe ya kalle ta ya ce, "Didi don ina so ki yi aure ba haka yana nufin zan juri ko wacce kalma a kanki ba, Wallahi ko waye yayi ƙoƙarin ɓata miki rai shima sai nasa da na danginsa ya ɓaci."
Didi ta ce, "waye yace maka raina ya ɓaci?Gaskiya ya faɗa Omar kowa a unguwar nan kallon da suke min kenan. Ban taɓa aure ba muna zaune da kai a gida ɗaya gani suke kamar ni da kai wani abun mu ke aikatawa mara kyau shiyasa rashin auren baya damuna. Shekaran jiya matar Alhaji Yusuf ni da ita ta faɗa min ido cikin ido. Kaga na damu...? Ban damu ba saboda ni na san ba haka bane, suna yiwa abun kallon baibai ne, kuma babu wanda ya isa ya ce zamana da kai a gidan nan akwai haramci, sai dai su yi tunanin banza su daina. Aurena kuma lokaci ne kawai bai yi ba."
Bai yi magana ba kallon ta yake yana kuma hakaito kamannin matar da ta ambata a idanunsa yaji ta ce, "kowa tsoron zuwa ya ce zai aure ni yake yi saboda kai Omar, kaf ƙofar nasarawa da kewaye tsoronka suke ji iya kallon idanunka ma tsorota su yake yi balle ka yi musu magana. A haka ka ke cewa burin ka nayi aure?."
Ya sauke numfashi yana kallon ta kafin ya dafa kafaɗarta ya ce, "Didi lokaci ne kawai bai yi ba, in yayi zaki yi aure. Kawai bazan yarda ki auri ɗan kutmar uba bane, dan ko kina auren nasa ya raina miki hankali ni mai iya ganin bayan sa ne."
Ta cire hannunsa daga kafaɗarta ta ce, "Omar ka daina furta wannan kalmar, ka daina cewa zaka ga bayan mutum don Allah ka daina."
Leɓensa ya ciza ya kalle ta ya ce, "Didi kamar uwa ki ke a wajena, in na kira ki da uwata ban yi laifi ba. Ina so ki sani babu wani ƙato ɗan ƙatuwa da ya isa ya ɗaga miki yatsa ban karya shi ba, kuma shi wannan da ya fita na ƙyale shi ne yanzu saboda ke amma ai zamu haɗu ko da sanayya ko da ganganci. Itama matar Yusuf ɗin zamu gauraya" yana faɗa ya juya ya shiga wata ƙofa da take farko a cikin gidan.
Idanu ta wara waje jin abinda ya ce cikin ɗaga murya ta ce, "Omar kar ka yiwa matar nan komai fa, matar aure ce kar ka sake ka yi wannan gangancin!." Bata ji maganar sa ba daman ta san bazai ce komai ba.
Waje ta samu ta zauna tayi tagumi hawaye na sakkowa daga idanunta. Tana matuƙar son ƙaninta Omar, tana matuƙar ji dashi bata so taga wani abun ya same shi. Amma Omar ya wuce tunanin mai tunani, duk yadda ka ke tunanin rashin jin Omar ya wuce haka. Baya ji tun yana yaro, baya bari in aka ɓata masa tun bai kai haka. Yana da zafi sosai, iya kallon idanun Omar zai saka ka firgice balle ka buɗe bakinsa ko ya yi maka barazana.
Kaf unguwar tsoron sa ake ji ko almajiri baya iya shigowa gidan yayi bara saboda dashi. Babu maƙociyar da take shigowa gidan saboda shi, baya ɗaukar raini