Showing 39001 words to 42000 words out of 87436 words
Chapter 14 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt
jure duk abinda yake miki. Sorry my daughter kar ki damu da wannan, abu ne ƙarami da mun ci zaɓe shikenan bazai sake ganin koda fuskarki ba. So wipe your tears my dear, i know what i'm going to do."
Narma ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "But Dad if he doesn't stop bothring me and upset me, i will have him arrested wallahi." Dad ya ce, "kar ki damu, ni zan san abinda zan yi. Yanzu kin zuwa dinner ɗin?."
"Na fasa."
"Gobe ƙarfe nawa zaki je arewa 24 ɗin?."
"Zuwa 11am."
"Okay ki kwantar da hankalinki ki huta kin ji? Babu abinda zai sake faruwa." Amsa tayi kawai ta kashe wayar zuciyarta na aiyana mata irin abubuwan da ya kamata ta yi masa wanda zata huce.
Shi kuwa Omar yana fita ya tarar da Bash a machine ya ɗauke shi suka bar wajan zuciyarsa na faɗa masa gwara ya bi shawarar Didi ya ajjiye aikin nan in ba haka ba wallahi zai yiwa ƴar mutane illa. A haka suka je unguwar yana sauka akan machine wayarsa tana yin ƙara, ko bai duba ba ya san Senator ne hakan ya saka kawai ya danna ya kara a kunne.
Kafin Sen ya yi magana ya ce, "batun aikin nan na ajjiye shi bazan yi ba, matuƙar zata dinga ɗaga min murya tana faɗa min magana mara daɗi bazan jure ba, gwara na ajjiye shi a huta kawai. In ban ajjiye ba zaka tarar da abinda bazai maka daɗi ba, ba a ɗaga min murya na ƙyale, ba a yi min ihu a kai, ba a yi min maganar banza. Dan tana ƴarka baza ta yi min abinda bana so na ƙyale ba."
Sen wani takaici ya tokare masa maƙogwaro amma bai nuna ba ya ce, "Tiger ya kamata ka san ƴata ce yarinyar da ku ke tare."
"To dan tana ƴarka sai me? Dan tana ƴarka sai na bari tayi min abinda yake so? Ta tambayi waye ni a garin nan, babu wanda yake ɗaga min murya balle rashin kunya ko zagi. Sanin ƴarka ce ya saka nake faɗa maka, ka ja mata kunne. Senator ba haka Tiger yake ba, Tiger baya jure koda ɗaga murya ne balle maganar baki."
Sen ya danne ɓacin ransa ya ce, "na ɗauka yadda ka ke girmama ni zaka girmama ƴata." Omar ya ce, "in da ta so zamu girmama juna, bata girmama ni ba nima bazan girmamata ba. Shiyasa na ce a bar aikin nan kawai." Numfashi Sen ya sauke ya ce, "na zaɓeka ne saboda na san zaka iya kular min da ita sosai, na zaɓeka akan jami'an tsaro masu bindiga amma na ga kamar hakan bai maka ba."
"Kawai bana tolerating nonsense ne" ya bashi amsa kai tsaye ba tare da wani tunani ba.
Tolerating nonsense, Senator ya maimaita a zuciyarsa cike da mamaki, wai daman har yana da karatun da ya san ne kalmar take nufi, kuma dan bashi da hankali shi yake faɗawa haka akan ƴarsa?. Lallai ya zama dole ya san abin yi, da an kammala zaɓe zai saka a yi masa abinda zai manta ma ya taɓa sanin Sen a duniya.
Sen ya ce, "Amma Tiger meye buɗe mota? Da ka buɗe mata kun tafi da shikenan." Wani murmushi ya yi na rainin hankali kana ya ce, "a kaf duniya Yayata kaɗai zan iya yiwa haka, bayan ita babu wani ko wata a duniya da zan buɗewa mota. Ka faɗa mata indai sai na dinga buɗe mata mota zata shiga ta je inda take so to baza ta je ko ina ba." Duk da ba a zafafe yake maganar ba amma kalamansa ciwo suke yiwa Sen sosai kawai bashi da zaɓi ne.
"Is okay, ka koma ka kai ta yanzu."
"Bazan iya ba, na riga na dawo gıda sai dai wani lokacin."
"Well, gobe zata je interview ƙarfe sha daya na safe."
"Allah ya kaimu" ya amsa a daƙile dan wallahi gabaɗaya ma aikin ya fita daga ransa, dan ya san cigaba da aiki da ita babbar damuwa zai haifar, tabbas zai iya zama silar komawar sa prison dan wallahi bazan sasssuta mata ba.
Bayan ya kashe wayar gida ya shiga wajan Didi, ganin ta a zaune kamar ba ita ba ya saka shi ya ƙarasa ciki fuskar nan a tamke sosai ya ce, "Didi lafiya?." Ta kalle shi ta ce, "kaina ne yake min ciwo Omar, har zazzaɓi nake ji."
"Mu je a dubaki" ya faɗa yana kallon ta. Girgiza kai ta yi ta ce, "kar ka damu na sha magani zan warke."
"Ki zo mu je a baki magani" ya sake maimaitawa yana kallon ta. Kallonsa itama tayi dan tasan baya ƙaunar ya ji tana ciwo kwata-kwata, yafi so da ta ce babu lafiya ayi maganinsa. Maganin da ta sha ta nuna masa ta ce, "na sha magani."
"Waye ya baki?."
"Jikar Hajja Salma, ka san karatun lafiya tayi." Shiru yayi kawai jin ance jikar Hajja kawai sai fuskar Nayla ta zo idanunsa ba tare da ya san dalili ba, ya kulle ido ya buɗe akan fuskar Didi ya ce, "yanzu da sauƙi?."
"Sosai ma."
"Allah ya ƙara lafiya" ya furta a sanyaye. Ta amsa da amin tana kallon sa tana mamakin abinda ya ɓata masa rai.
"Ki je ki kwanta" ya katse mata tunani yana kashe tv ɗin. "Bana jin bacci Omar, Zaman kaɗaicin nan damuna yake yi sosai, in ka fita sai ni kaɗai, na danna wayar na gaji, nayi kallon na gaji."
Bai ce mata komai ba ya zauna daga nesa da ita yana kallon ta. Gabaɗaya jikinsa yayi sanyi baya so yaji tana yin ciwon kai balle harda zazzaɓi, baya so yaga Didi na rashin lafiya, gabaɗaya sai ya damu kansa kamar shi ya ɗora mata. Didi ta kalle shi ganin yana kallon ta tace, "kar ka damu fa, da nayi bacci na tashi zan ji daɗi." Kai ya ɗaga mata kawai bai ce komai kuma bai daina kallon ta ba.
Ganin ya damu sai ta miƙe ta ce, "ka kashe hasken falon zan je na kwanta." Kai ya ɗaga mata kawai ta shiga ciki dan kawai ta kwantar masa da hankali.
Shiru yayi yana tunani, bai san dalili ba kawai fuskar Narma ta kawo masa ziyara a idanunsa, yadda take kallon sa tana tsaye da mamaki a idanunta na kalaman da take faɗa masa shi yake gani. Tsaki ya yi ya kawar da tunanin daga zuciyar sa yana zaune bai tashi ba.
Bai kashe hasken ba kuma bai tashi ba dan bazai iya tafiya ya bar Didi ita kaɗai ba, in ya tafi sai yaga kamar ciwon zai same ta sosai. A kan kujera yayi bacci ba tare da ya san hakan ba sai dan bazai iya tafiya ya bar ta ba.
Ƙarfe huɗu na dare ta farka kamar kullum, tayi mamakin ganin haske a falo a kunne, ta leƙo ta ganshi a kwance yana bacci hankalinsa kwance. Murmushi tayi ta ƙaraso ta kashe hasken falon ta koma ɗaki ta yi alwala ta tayar da sallah.
Sai da aka kira asuba sannan ta ƙaraso inda yake ta kalli gefen sa taga ya ajjiye ƙaramar wuƙa da wani ƙarfe da alama a jikinsa suke, ta girgiza kai ta tashe shi ya buɗe ido ta sanar dashi lokacin sallah ya yi sannan ta koma ciki shi kuma ya tashi ya fita.
Bayan an idar da sallah ya dawo har ɗakin ta ya shiga kamar yadda yayi tunani tana kan sallaya ya ce, "Didi ina kwana." Murmushi ta yi ta ce, "ka tashi lafiya mai bacci a falo?." Murmushi shima ya yi sannan ya ce, "ya jiki?."
"Na ji sauƙi sosai. Yau baka tashi sallar dare ba, ko baccin ne?."
"Kawai ban tashi ɗin bane, Allah ya ƙara lafiya" abinda ya ce kenan ya wuce ya fita daga falon nata.
Kamar yadda Sen ya ce masa ƙarfe sha ɗaya bai jira sha ɗayan tayi ba ya tafi dan shi mutum ne mai girmama lokaci, baya son african time kwata-kwata, shiyasa in kace masa ƙarfe goma to tabbas goman zaka ganshi, in ka san ƙarya ka ke ma gwara kar ka faɗa masa. Tare da Tk suka je har cikin gidan ya nemi waje ya zauna bayan suka gaisa sama-sama da masu aikin gidan.
Su kam mamaki suke yi ganin da alama ba a kore shi ba akan abinda ya yi jiya, suna jinjina ƙarfin hali da kuma sa'ar da yake da ita, in ba haka ba waye zai yiwa Narma haka ya kwana lafiya. Yahya ne ya zo zai zauna kusa dashi Tk ya ce, "kai yanee?." Yahya ganin Tk da yanayin sa ya saka shi yin sak ya miƙawa Omar hannu ya ce, "Omar barka da safiya." Kallon sa ya yi suka gaisa Tk ya ce, "to kama gabanka."
Kallon sa Omar kawai ya yi sai Tk ya yi shiru shi kuma ya kalli Yahya ya ce, "ka zauna." Ba musu ya zauna ya ce, "ban ɗauka ma zan ganka kazo yau ba duba da abinda ya faru jiya, na ɗauka shikenan kwantiragin aikinka ya ƙare." Omar bai amsa masa ba sai agogo da ya kalla sha ɗaya saura mintina goma sha biyar. Numfashi ya sauke ya ce, "tana da sauran mintina sha biyar."
Yahya ya ce, "don Allah Omar na tambayeka." Kallon sa kawai yayi alamun ina ji shi kuma ya ce, "don Allah ne ka ke taƙama dashi ka ke yiwa ƴar sanata haka?." Omar ya ɗauke kai daga kallon sa ya ce, "ka tambayi sanatan."
Zai sake magana kawai suka ga an taho a guje an zube a gaban Omar yana cewa, "Madugu uban tafiya, madugu uban matsiyata, a hauka a zame ka hau mutum ka zauna daidai. Gadon ƙaya ka ke wallahi duk wanda ya hauka babu shi babu bacci, wando ƙarfe ka ke saka ka sai wanda ya shirya. Ba ayi maka wargi ka ƙyale, jan wuya jinin Didi, Allah ya ja da ran yayar mu."
Kallon wanda ya zube a gaban na sa ya ke yi ya kalli Tk sai Tk ya ce, "Damisa ai kunama ne ɗan yankin su Jijiya." Kai ya girgiza kawai ya kalli yaron da ya miƙe ya ƙaraso wajan Tk yana cewa, "kai ashe babbar giwa ce da kanta a wajan nan, ina na sani ina can ina shirme."
Yahya ya maimaita sunan Damisa yana kallon Omar Tk ya ce, "eh Damisa, shine dai wanda ka ke jin labari a radios shine a zaune a gaban ka! Kayi hattara domin taken Damisa ƙi sabo." Yahya ya girgiza kai yana mamakin to me ya haɗa shi da Sanata kuma? Lallai dole ya yi jiji da kai, wannan kirari dake kwarara masa, kuma ga sunan sa da yayi tambari kusan kowa ya san shi, ko baka san shi ba kasan sunan sa.
Yahya ya sake kallon sa ganin maza buyu suna gefensa a tsaye shi kam sai aikin danna waya yake yi yana kuma kaɗa ƙafa, in ka shigo gidan sai ka ɗauka mai gidan ne a zaune saboda yadda ya kame kai baza ka ce ma shi bane.
Mamaki Yahya yake yi sam bai yi kama da ƴan daba ba sai ma kama yake yi da jaruman gaske, kallo ɗaya zaka yi masa kayi tunanin babban hamshaƙin mai kuɗi ne ko ɗan mai ƙudi saboda yanayin fatarsa da kyaun da Allah ya bashi, in ka sake kallon sa sai ka ɗauka soja ne, saboda kwarjini da ƙirarsa. In ka kalli fuskarsa kaga yalwar gashi sai ka ɗauka wani babban ma'aikacin gwamati ne ko hamshaƙin ɗan kasuwa. Dan ƙananun kaya ya saka harda takalmi sau ciki, kai baza ka kalle shi kace Damisan da ke zance bane.
Narma kuwa tsaf ta shirya cikin riga da siket ɗnkin straight siket, ya kamata sosai ɗakyar take jefa ƙafarta saboda yadda ya kamata, ta yafa mayafi babu laifi ta saka da ɗan saka mai girma amma chantily ne gabaɗaya ana ganin jikinta. Wayarta taji yana ƙara ta duba ganin mai kiran sai ta ɗauka aka yi mata magana ta kashe ta ɗauki wayar ta ta sakko daga saman.
Harabar gidan ta fito duk ma'aikatan gıdan suka ƙarasa suka gaishe ta maza da mata, shi kam yana zaune abin sa gefensa Tk shida kunama. Kallon agogo ya yi yaga saura mintina biyar a lokacin da ya bata ya tashi ya tawo wajan Tk da kunama suna take masa baya, ya buɗe motar ya shiga ya yi mata key bai ce mata komai ba.
Narma sai da gabanta ya faɗi ganin yanayinsa a yau ya saka taji wani iri a zuciyarta, gudun kar abinda ya faru jiya ya faru ya saka ta buɗe bayan motar ta shiga Tk ya shiga gaba shi kuma ya ja motar suka fita. Ƙhamshin turarenta ya gama cika motar, ga ƙhamshin mai daɗi da tsayawa a rai bai ce mata komai ba itama bata ce masa komai ba.
"Tk."
"Allah ya ja da zamanin Madugu."
"Ina ne Arewa24?."
"Nan gaba ne babu nisa." Bai sake magana ba ya cigaba da tafiya Tk na nuna masa.
Yadda ya furta magana ta biyu sai ta kalle shi tana mamakin wai shine ya yi maganar ko ba shi ba, ganin shi ne yake maganar sai ta girgiza kai tana tunanin anya wannan ɗan daba ne kamar yadda Dad yake faɗa? Anya shine Tiger ɗin da ake faɗar tsagerancinsa a duniya?. Kai gaskiya da sake tana tantama akan sa.
A bakin gate suka tsaye ta kalle shi kamar zata yi magana sai kawai ta fasa dan so take taga iya gudun ruwan sa. Fita tayi ta shiga ciki kamar yadda bata yi magana ba babu wanda ya kula ta.
Suna zaune shi da Tk duk da ba magana suke yi ba kowa harkar gabansa yake yi, shiru babu ita babu alamun ta kusan mintina talatin. Agogo ya kalla ya ga sha biyu na rana har ta kusa ya sake kallon inda ta shiga ya yi tsaki. Mintina goma ya ƙara mata in bata fito ba zai yi tafiyarsa ai ba driver bane ba shi da zata ajjiye shi a waje bata fito ba. Ita kuwa an jima da gama interview tana sane tayi banza dashi tana so taga ƙarfin iskancin sa shiyasa tayi zaman ta.
Gajiya tayi da zaman ita kanta, bacci take ji hakan ya saka ta fito a lokacin ya kunna motar zasu bar wajan kenan. Ganin ta fito ya saka shi ya dakata ta buɗe ta shiga tana cewa, "wai da ban fito ba kenan tafiya zaka yi?." Tk ya ce, "to Damisa yaron ki ne da zai zauna yana jiran ki?." Narma ta ce, "kai ba da kai nake magana ba, kayi min shiru kafin na ɗauki mataki akan ka."
"Mataki akan wa? Wai ni Tk? Gaskiya....." Kallon sa Omar yayi hakan ya saka ya ce, "Tuba nake Madugu ta zo ta rainin hankali ne." Narma ta zo iya wuya saboda ɓacin rai cikin masifa ta ce, "Kai wai waye kai? Me ka ke dashi da ina magana zaka yi min banza?. Me ka ke dashi da zaka tafi ka barni a kan titi iyeee!" Ta faɗa da ƙarfin gaske wanda hakan ya saka Omar taka burki da ƙarfi.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 12.*
Yadda ya taka burki da ƙarfi sai da tayi gaba kamar zata kifa kafin ta koma daidai ta zauna, ya jiyo ya kalle ta suka haɗa ido bata ɗauke idonta shima bai ɗauke ba ya ce, "in kika sake yi min magana a motar nan wallahi sai kin sauka, ki aikata ki gani." Mamaki yake bata da tsoro, ita da motar gidan su shine yake cewa in ta yi wani abun ba daidai ba sai ta sauka? Lallai wannan anyi ɗan rainin hankali, rainin hankali mana, in ba haka ba ita zai kalla ya ce in bata yi shiru ba sai ta sauka daga motar da babanta ya siya.
Sai kuma ta kasa magana tayi shiru ya cigaba da jan motar yana aiyana wallahi in ta sake masa magana sai ta fita daga motar sai dai ta hau abin hawa ta koma. (Omar akwai ƙarfin hali).
A haka suka koma gida motar tsitt babu wanda yake magana a cikin su sai ƙhamshinta da ya cika motar gabaɗaya. Yana tsayawa a gidan ta buɗe motar ta fita, ta kalle shi bayan ta fita shima ya fito ta ce, "zan ga abinda ka ke taƙama a duniyar nan, zan ƙure maka gudu, zaka fahimci ni ba sa'ar wasan ka bace ba." Tk ne ya zabura ya yi kanta Omar ya ɗaga masa hannu alamun ya ƙyale ta, ya juyo ya kalle ta ya ce, "cigaba."
Wani irin baƙin ciki ya zo ya tokare mata a maƙogwaro, kenan ya mayar da ita shashasha mara hankali kenan ta cigaba da magana mahaukaciya. Juyawa tayi a fusace ta shiga cikin gidan ta cillar da mayafin jikin ta a haukace. Wayarta ce tayi take ƙara ganin sunan Ashraf ya saka bata ɗauka ba ta tashi ta hau sama a guje raina a ɓace matuƙa.
Da wannan ɓacin ran tayi sallah sannan ta yi wanka ta kwanta bacci zuciyarta nayi mata saƙa da kwancewa akan abinda zata yiwa Omar dan ta huce. Bata farka ba sai bayan la'asar, ta tashi ta sake sabon wanka ta sako riga da wando na shan isaka ta sakko ƙasa da niyar cin abinci. Kamar yadda ta zata mai dafa mata abinci ta dafa abinci ta ajjiye, ta a dining table zauna ta zuba abinda take so ta fara ci.
Wayar ta ce ta sake yin ƙara ganin mai kiran sai ta ɗaula ta ce, "ina ciki." Abinda tace kenan aka yanke wayar ba jimawa aka shigo falon.
Kyakykawan saurayi ne fari tass siriri mara jiki ya shigo yana kallon ta daga inda take zaune tna cin abinci. Kallon sa tayi sai ta miƙe ta ɗauko plate ɗin abincin ta shigo cikin falon tana cewa, "Welcome Baby." Ƙare mata kallo yake yi dan shigar da tayi ta yi masa kyau a idanunsa sosai. Surar Narma tana daga cikin abinda yake ɗaukar hankalinsa a kan Narma, duk lokacin da zai yi arba da ita sai