Showing 87001 words to 87436 words out of 87436 words

Chapter 30 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

Narma. A tabbatar da rayuwarsa ta ƙare a prison" ya faɗa yana kallon Omar da shima shi yake kallo.

Narma ta fincike hannunta daga na Nabil tayi inda Omar yake a gigice, Sen ya riƙeta gam tana kuka tana ƙoƙarin ƙwacewa tana cewa, "A'a Dad! kar ka aikata haka, ka ƙale shi don Allah. Ni nace yazo ba shi ya zo da kansa ba, ni ce nake sonsa Dad, ni nake so na aure shi. Don Allah kar ka yi masa komai Ina sonsa...!!" ta faɗa cikin kuka sosai tana ƙoƙarin fincikewa.

Ƴan sandan wajan Omar suka nufo shi kuma kallon Sen ya ke yi, ya kalli Narma da take kuka ya sake kallon Sen ya ce, "zan tabbatar maka da abinda na faɗa, in har kana so ka tabbatar kar ka bari ka mutu! Ka kasance a raye, sai na shayar da kai mamakin da baka taɓa shiga irinsa ba a rayuwa." Sen a fusace ya ce, "ku tafi dashi daga gidan nan!" Ya faɗa cikin tsawa matuƙa.

Kallon Narma Omar ya yi itama shi take kallo tana faɗin, "please Faruk!." Ɗauke kai ya yi daga kanta, ya sake kallon mahaifinta kafin ya girgiza kai akwai bai ce komai ba. Fita aka yi da su Omar aka saka su a mota, fitar motar daga cikin gidan ya yi daidai da zubewar Narma a ƙasa ta faɗi summiya.

End of book 1!

_To fa Book 1 ya tiƙe a nan!!. Ya ku ke ganin abin zai kasance? Omar zai auri Narma bayan duk abinda ya faru? Nayla fa? Omar zai aureta ko kuma zata cigaba da dakon soyayyarsa?. Burin Maman su Nayla zai cika ko bazai cika ba? Shin Omar zai kai matakin da ya faɗawa Sen ko bazai kai ba?. To wai meye asalin su Omar? Meyasa ya tsani danginsa? Meyasa ya tsani dangin uwa da uba?. Didi zata yi aure ko baza ta yi ba?. Wanne irin rabo ne zai kira Omar? Wanne irin Rabo ne zai kira Nayla? Wanne irin rabo ne zai kira Narma?._

_Duk amsoshin tambayoyin nan suna cikin Book 2&3, labarin yana da tsaho doguwar tafiya ce, zamu shiga jirgin book 2&3 ya lula damu cikin duniyar KIRAN RABO dan jin abinda zai kasance. Free ya ƙare book 2&3 naira 500 for regular group, vip kuma naira 1000 ne kacal. Akwai vip2 zai zo a arewabooks in sha Allah. domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp wa.me/2349030398006 wa.me/234701 809 8175 Dm to subscribe yours._

_Na gode da soyayyarku a gare ni da littafin nan, Allah ya ƙara zumunci. Allah ya sa ku nuna min ƙauna ku gigita ni da shiga paid group._😩❤️❤️

Nana Haleema❤️








Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login