Showing 3001 words to 6000 words out of 87436 words

Chapter 2 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

kuma yason munafurci da gulma. Bashi da ɓoye-ɓoye kuma girman ka baya hana shi magana, shiyasa gidan kullum shiru sai Didi kawai ita kaɗai saboda kowa tsoron sa yake ji ba a iya zuwa. In kaga mutane a gidan to tabbas baƙi ne, shima haka zai ta cin magani yana zare musu idanu dan ya tsani ya ga anyi baƙo ko baƙuwa.

Hawaye taji yana share mata sai ta kalle shi bayan ya canja kaya zuwa ƙananun kaya ya tsuguna a gabanta ya ce, "duk wanda ya zama silar zubar hawayen ki sai na zama silar zubar jini a jikinsa, Didi kin san bana kisa, ban taɓa kashe rai ba. Amma akan hawayenki zan iya farke maƙworagon ko waye" ya faɗa yana wara idanunsa yana kallon ta.

Murmushi kawai tayi ta miƙe tsaye ta ce, "baza ka ci abinci ba?." Shima ya tashi tsaye yayi yana kallon ta ya ce, "Zamu zo anjima dasu goje mu ci, yanzu zan je na dawo."
"Ina zaka je?."
"Wani ɗan aiki zan je nayi."
"Wanne aiki ne?." Ya kalli idanunta ya ɗauke kai  dan baya yi mata ƙarya kuma shi baya ɓoye mata komai na sa. Ya ce, "mutanen Yakasai ne suka ƙwacewa wani na mu waya sannan suka kashe shi, Ke kin san sai naje mun zauna dasu."

Ta girgiza kai tace, "don Allah Omar...." Ya dakatar da ita ta hanyar faɗim, "Didi sai na je fa, amma nayi miki alƙawari bazan yi faɗa ba indai ba sune suka so hakan ba. Magana kawai zamu je mu yi domin na ja musu kunne akuyar su ta kiyayi ramata."

Kallon sa take yi bata ce komai ba shima haka kafin ya ja baya ya ɗauke idanunsa daga kanta ya ce, "Zan dawo yanzu Didi." Yana faɗa ya fita cikin takunsa na ƙasaita ya bar ta a tsaye tana kallon sa.

Hawaye ta share ta ɗaga kai sama bayan ta ɗaga  hannu ta ce, "Ya Allah ka kiyaye min marayanka, Allah ka kare shi. Ya Allah ka sassauta masa wannan zuciyar da yake fama da ita, ya Allah ka cire masa son wannan ɗabi'ar daga zuciyarsa." Ido ta share tare da sauke ajiyar zuciya ta shiga falo.


•••••••••
*ABUJA*
*SENATOR SAGIR SANI SHATIMA RESIDENT.*

Senator Sagir shine Sanatan Kano ta tsakiya mai ci yanzu, wayeyen mutum ne mai ilimi da kuma son ilimin boko. Kaf ma'aikata gidan sa daga masu degree sai masu master, daƙyar ake samu ya ɗauki mai kwalin diploma aiki, saboda a ganin mai wannan matakin karatu jahili ne bai san komai ba, shi kuma yana ganin aiki da wanda bashi da ilimi ba ya haifar da komai sai dana sani. Kaf masu aikin gidan mata da zama sun iya english, in suna turanci ba ka ce masu aiki ba ne saboda haka ne tsarin mai gidan. Ya raina wanda bashi da ilimin boko, yana kuma ganin wanda bashi da ilimin boko babu inda zai je a rayuwa sai dai ka ƙare a bara.

Ba ya mu'amala da wanda ba shi da ilimin boko, in kuwa ya yi to ta zama dole kuma sai dai a ɓangaren siyasa. Bai damu da ilimin addinin ka ba, shi dai indai kana da na boko ko kafiri ne kai ka fiye masa musulmi.

Matar shi ɗaya tal wacce yake so kamar rai, yana da yara guda uku. Nabil, Narma sai Najwa.

       Babban falo ne mai kyau da tsari, kai da ka kalli falon ka san na manya mutane ne na na ƙananun mutane ba, ya tsaru iya tsaruwa duk da babu tarkace a cikin sa. Yanayin tsarin sa zai saka ka tabbatar da falon ba na ƙananun mutane bane ba. Wata kyakykawar budurwa ce fara tas a zaune a falon, sanye take da riga iya guiwa kanta babu ɗankwali hakan sai ya bayyanar da yalwar sumar da take da ita. Tana da kyau wanda a kallo ɗaya zaka fahimta saboda kyawun halittar da Allah ya yi mata.

Barr Narma Sagir Sani shatima kenan wacce ake yiwa laƙabi da Barr Nass. Second born a wajan Senator Sagir, ƴar kimanin shekaru ashirin da shida. Bata da ƙiba daga sama amma Allah ya yi mata baiwar ƙira mai kyau daga ƙasa, tana baiwar sura wacce in ka kalla za ka so ka sake kallo saboda yadda ta tsaru. Barr Nass manager director ce a ɗaya daga cikin kamfanin mahaifin ta. Sananniya a social media musamman a instagram da X.

"Daddy Ina so zan shiga Kano next week" ta furta cikin muryarta irin ta ƴan gayu ƴaƴan Daddy da Mummy.

Kallon ta ya yi a lokacin ta kai abinci bakinta ya ce, "me ake yi a Kano?." Ta ɗan yi farrr da idanu wanda hakan ya zamar mata jiki ta ce, "arewa24 sun yi inviting ɗina then..akwai bikin friend ɗina Samra kamar ma ka san Dad ɗin ta. Bashir na Gwaggo ne babanta."

Dad ya kalle ta yana girgiza kai ya ce, "yes, i knew him. But, how many days are you planing to spend in Kano?." Ta ajjiye spoon ɗin hannunta ta ce, "Uhumm two to three weeks. At least two weeks." Daddy ya girgiza kai bayan ya haɗe fuska ya kalle ta sosai ya ce, "Narma!." Jin yadda ya kira sunan ta sai ta kalle shi ta ce, "Dad."
"You know i don't want you to go to Kano, right?."
"Yes dad, but it's necessary. And dad I'm not a little gril fa, I know what I'm doing. Zan iya kare kaina daga duk abinda ka ke gudu, so just calm down." Kallon ta yake yi kafin ya kalli wacce take zaune a gefe sa ya ce, "Kina Jin abinda take cewa baza ki yi magana ba?."

Mum ta kalle shi ta ce, "wannan maganar tsakanin ku ne babu ruwana a ciki. Ta faɗa min batun zuwa Kano nace sai ta jira umarninka."
Dad ya kalle ta ya ce, "Narma kin san abinda ya faru last a zuwan ki kano ko? An yi attacking ɗinki kin tuna wannan? Ba dan Allah ya kiyaye ba da yanzu bamu san meye ya faru ba."

"Yes Dad ban manta ba, amma hakan ba zai saka na daina zuwa Kano saboda wanda ban san su ba." Dad ya bita da kallo kafin ya ce, "well, I will think about this." Kamar zatayi kuka ta ce, "Dad don Allah kar ka ce bazan je ba."
"I'm not saying that, but sai nayi tunani."
"Okay, thank you" ta faɗa tana tashi ta hau sama tana danna waya.

Senator ya bi ta da kallo bayan ta wuce ya kalli Maman ta ya ce, "Kina ganin ya kamata na barta ta je Kano?." Mum ta ce, "yeah ka barta mana, na san Samra ƙawarta ce sosai bai kamata ace bata je ba. Sai ka bata security su kula da ita." Ya girgiza kai ya ce, "Okay zan san abinda zan yi" ya faɗa yana tashi shima ya saman yana tunani. Anya zai iya barin Narma taje Kano? Garin da aka kusa hallaka masa ƴar da yafi ƙauna a duk duniya?. Ko da zai bari taje sai ya haɗa ta da wanda yake tunanin zai kular masa da ita sosai.

Narma ce ta sakko cikin shirin fita, sanye take silk adire kalar ja wanda aka yi masa ɗinki mai ɗaukar hankali. Gabaɗaya ya bi jikinta ya kwanta yana bayyanar da zallar surar da take jikinta, hatta bra ta da saka ana ganin shatin ta komai ya fito kamar bata saka kaya ba. Duk namiji mai lafiya in ya kalli Narma a wannan shiga sai ya ji yanayin da bai shiryawa jin sa ba har ƙwaƙwalwarsa. Ɗauke idanu daga kan Narma a wannan lokaci abu ne mai wahala, sai mai juriyar gaske ne zai kawar da ita daga idanunsa.Ta tsaru a cikin rigar, ta kuma yi mata kyau kamar ka ɗauke ta ka gudu.

Kallon Mum tayi da take zaune ta ce, "Mum zan je shoprite" ta faɗa tana gyara zaman hular kanta. Mum bata kalle ta ba ta ce, "ki taho min da diet stick ɗina ya ƙare."
"Okay Mum" ta amsa tana fita.

A harabar gidan ta tsaya tana ƙarewa motar ta kallo, ta san ta ce a wanke mata amma sai ta ga kamar ba a taɓa ba. Cikin ɗaga murya ta ce, "Ina Kashim!?." Kashim jin maganar ta ya fito cikin sauri da rawar jiki ya ce, "ga ni Ma'am." Nuna masa motar ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ya kalli motar ya kalle ta ya ce, "i'm sorry ma'am, bani da lafiya ne shiyasa......" dakatar dashi ta yi ta ce, "in ka ƙarasa wallahi sai na mare ka." Jin abinda ta ce sai ya kalle ta dan kuwa a shekaru ita ba sa'ar sa ba ce, ko yayanta Nabil ya girma balle ita.

"Who do you think you are...? You won't wash my car, and now you're telling me you're not feeling well?. Damn your sickness!" Ta faɗa cikin ɓacin rai tana kallon sa.

"I'm sorry" ya furta a sanyaye yana kallon ta. Narma ta saka baƙin glasses ɗin hannunta ta ce, "ko mutuwa ce a kan ka kar ka sake aikata wannan gangancin, in na ce ayi kawai ayi in ba haka ba you must regret about it."

"In sha Allah, Sorry Ma'am."
"Zan ƙyaleka saboda wannan ne karo na farko da ka yi haka, kar ka sake maimaitawa" ta faɗa tana barin wajan kafin ta ce, "And make sure you've washed it before i get back" ta faɗa tana karɓar key ɗin motar Mum ta shiga. A guje gate man ya buɗe mata gate ta fita a guje.

Sai bayan ya kulle gate ɗin ya kalli Kashim ya ce, "ka yi sauri ka ƙoƙarta ka wanke kafin ta dawo, yarinyar nan bata da kirki, a iya watan nan masu aiki goma ta kora ta kuma ɗauko guda goma. Ka yi haƙuri ka yi kar ta ci maka mutunci a banza." Kashim ya ce, "wallahi bani da lafiya."
"Haka zaka yi haƙuri. Kuma wallahi ba a wanke musu mota a gidan nan car wash ake zuwa, kawai saboda ta samu hanyar ciwa wani mutunci ne ya saka ta ce ka yi. Dan ita tana so ta ga tana ciwa mutum mutunci. Ta waje guda take da kirki wani lokacin, in ta ga mutum a kwance babu lafiya a nan zata ɗan tausaya masa. Amma sai ciwo ya kai ciwo, bata ɗauki ƙaramin ciwo a komai ba." Kashim ya yi ajiyar zuciya ya wuce jiki a sanyaye. Inda an sabo da wulaƙanci da cin fuska da ƙasƙantar da mutum da yanzu sun saba a wajan Narma.

•••••••••••
*KADUNA STATE*
*ALHAJI ABDALLAH AHMAD RESIDENT.*


Alhaji Abdullahi sannen ɗan kasuwa ne mai ji da kuɗi da iko da kuma alfarma a faɗin ƙasa nigeria. Yana da matuƙar kirki da daɗin mu'amala ga kowa, ko ma'aikatan gidan sa ya ɗauke su kamar ƴan uwan sa baya wulaƙanta su ko tozarci ko yaushe cikin wasa da dariya suke. Mutum ne wanda ya san ya kamata, bashi da wulaƙanci ko kaɗan kamar ba mai kuɗi ba, in ka ga fushinsa akan abu tabbas ransa ne a ɓace.

Mutum ne mai kyautatawa iyalan sa da matuƙar ƙaunar su, baya bari iyalan sa su yi kukan babu ko ya ya abin yake. Haka kawai zasu kulle gidan a bar ƙasar kawai dan jin daɗin ƴaƴan sa da walwalar su. Babu abinda iyalan sa suka nema suka rasa, kuɗi, mota, fita ƙasashen waje da sauran kayan more rayuwa ya tanadar musu dashi. Shiyasa suka kasance ƴan gata gaba da baya.

Matar sa ɗaya mai suna Zeenatu, uwar gidan sa mai suna Bilkisu Allah ya yi mata rasuwa shekaru masu yawa da suka wuce. Yaran sa shida, biyar daga wajan Zeenatu ɗaya tal daga uwar gidansa. Ahmad shine babba, Jawad, Jidda, Nayla, Jalila, Jalil. Yara ne masu tarbiyya da sanin ya kamata, dukkan su sun tashi a turbar tarbiyya mai kyau, ilimi, addini da kuma kyakykyawar rayuwa.

          Kyakykyawar farar budurwa ce ƴar kiminin shekaru ashirin da huɗu zaune a ƙasaitaccen falo mai kyau da girma tana danna waya. Falon yana da girma sosai ya kuma tsaru matuƙa, kana ganin falon ka san na masu kuɗi ne ba na talakawa ba. Tana da haske da kyawawan idanu da ƙaramin baki mai ɗaukar hankali, tana da ƴar ƙiba kaɗan ba mai yawa ba, yanayin jikin ya dace da ita sosai dan komai ya yi daidai da halittar ta.

Tana zaune tana danna waya fuskarta ɗauke da kyakykyawan murmushin da yake bayyanar da dimples ɗinta, kana kallon ta ka san duk abinda take kallo a wayar yana bata nishaɗi sosai. A yanayin ta zaka hangi tsantsar nutsuwa da kuma fara'ar da take da ita. Hauwer Abdallah Ahmad kenan, wacce ake yiwa laƙabi da NAYLA.

         "Nayla me ki ke kallo haka ki ke dariya?." Juyawa tayi ganin wacce tayi mata magana sai tayi dariya cikin murya mai daɗin saurare ta ce, "Mama ina kallon comady ɗin ƴan TikTok ne. Abiy ya fito?." Wacce ta kira da Mama ta zauna a kusa da ita tace, "Yanzu zai fito."

"Gani na fito." Jin muryar mahaifin nata mafi soyuwa a gare ta sai ta miƙe tsaye tana murmushi ta ce, "Abiy sannu da zuwa." Ya dafa ta ya ce, "Yauwa Mamana. Ya aka yi ki ke nema na?." Zama yayi bayan ya zaunar da ita tana murmushi ta ce, "Ina so daman zan je Kano cikin gari wajan Hajja na yi kwana biyu." Nan da nan annurin fuskar sa ta gushe ya ɗago ya kalle ta ya ce, "Nayla!." Gabanta ya faɗi jin a yadda ya faɗi sunan ta, kasancewar bai cika faɗa ba sai dai ya ce Mamana. Ta kalle shi ta ce, "Na'am Abiy."

"Meyasa ki ke son zuwa Kano ko yaushe? Meyasa bakya son zaman gidan nan?." Nayla ta kalle shi bayan ta rausayar da kai ta ce, "Ba haka bane ba Abiy, waya mu ka yi da Hajja tace min yaushe zan zo shine nace mata sai na kammala nysc. Kuma yanzu Abiy na gama services, tahfiz ɗin ma da na shiga na gama shiyasa nake naje" ta faɗa cikin yanayi na shagwaɓa wanda zai tabbatar da ita ɗin ƴar gata ce.


"Amma kin san bana son zuwan ki Kano ko yaushe ko?."
"Na sani Abbiy, amma Hajja kakata ce tana so na je na dinga gaishe ta. Kuma duk dangin Ummana a can suke, suna jin daɗi in naje na gaishe su."

Abiy yayi shiru bai ce komai sai kallon ta da yake yi ganin haka sai ta sunkuyar da kai tana addu'ar Allah ya sa ya barta ta. Abiy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "zan bar ki ki je amma baza ki jima a can ba, sannan ban yarda da yawo ba." Nan take tayi murmushi mai bayyanar da kyaun ta da ƙuruciya tace, "in sha Allah Abiy. Na gode sosai." Ganin tana farin ciki shima sai ya yi murmushi sannan ya tashi ya yi musu sallama ya fita.

Nayla ta kalli Mama da farin ciki ta ce, "Mama bara naje na fara shirin tafiya Kano." Mama tayi murmushi ta ce, "to sai kin dawo. Sannan kar ki damu da yace kar ki jima, in kika tafi ba sai ya gan ki ba?." Nayla tayi dariya ta ce, "Kuma fa haka ne Mama, bara naje na dawo" ta faɗa tana tashi da sauri ta shiga ciki.

Da muguwar harara Mama ta bita bayan ta ja tsaki ta ce, "na rantse da girman Allah sai kin bar gidan nan, yadda uwar ki ta barshi kema sai kin bari. Wannan soyayyar da yake nuna miki sai ta koma ƙiyayya nan ba da jimawa ba. Sai na saka kin zama abin ƙyama a idanun mahaifinki. Irin wahalar da uwarki ta bani a gidan nan sai kin an ninka miki ita a gidan aurenki. Bazan taɓa bari samarin da suke tururuwar son auren ki su aure ki ba, in suka aure ki ai ban yi riba ba, ɗiyar Bilkisu ta rayu a cikin gidan aure mai ɗauke farin ciki bayan ni ta wahalar dani a nawa gidan auren?. Hmmm ai duk wanda ya ci tuwo dani miya ya sha, wallahi sai kin gwammace ba a haifo ki ba. Mu je zuwa Nayla!."

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Tsakanin Narma, Nayla da Omar waye zai amsa KIRAN RABO..?🤩

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t

Book 1
P 02

           Omar ko da ya fita a ƙofar gida ya tarar da yaran sa su uku suna jiran fitowarsa, suna ganin ya fito sa suka miƙe ya ƙaraso cikin su yana kallon su sannan ya ce, "ehmm matan Alhaji Yusuf na wa?." Ɗaya daga cikin su ya ce, "Alhaji Yusuf nan baya?." Ya ɗaga masa kai alamun eh ya sake cewa, "Matar shi ɗaya ce." Omar ya girgiza kai bayan ya saka hannu a aljihu ya ce, "mu je gidan."

Tafiya suka fara yi yana tsakiyar su fuskar nan tashi a tamke matuƙa, babu alamun fara'a a tare dashi gabaɗaya babu damar kawo wasa ko raini a kan fuskarsa. Duk inda ya wuce kallon sa ake yi amma babu damar ayi masa magana saboda kwarjinin da yake dashi.

        "kai Ummaru!."

Aka faɗa daga bayansa ya tsaya cak tare da juyawa dan ya san kaf unguwar mace ɗaya ce ke ɓata masa masa ta kira shi da Ummaru. A hankali ya juya kamar yadda ya yi tunani kuwa ita ce ya sake haɗe fuska ya ƙarasa wajan ta yaran sa suka rufa masa baya ya kalle ta ya ce, "Omar sunana, in baza ki faɗa ba ki ce Tiger."

Ta harare shi ta ce, "bazan faɗa ba, ko zaka saka ni na faɗa ne?. Na faɗa Ummaru." Ɗan kawar da kai ya yi ya ɗan saki fuska kaɗan domin yana matuƙar girmama tsohuwar da babu abinda zai hana bai yi mata warning ɗin da baza ta sake ganganci ce masa Ummaru ba. Hajja ta kalle shi ta ce, "Kwana biyu baka shigowa mu gaisa ko?." Ya kalle ta ya ce, "zan zo."
"Allah ya kawo ka, a daina rashin ji a san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login