Showing 45001 words to 48000 words out of 87436 words

Chapter 16 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

sama da su ashirin a wajan sun baje wayoyi da atm cards da kuɗi. Wajan banda warin wiwi babu abinda yake yi, ga hayaƙin taba ya cika wajan.

Ganin an shigo suka miƙe duk suka fito da makamai ɗaya daga cikin yana cewa, "wanne mai ƙarar kwanan ne yazo inda bazai fita ba?." Narma ta ɓuya a bayasa gabanta na faɗuwa tana dan sanin shigowa wajan. Haske shi suka yi da fitila shi kuma ya ɗaga pcap ɗin kansa, ganin fuskarsa ta bayyana sai suka haɗa baki suka ce, "Damisa!."

Babban cikin su ya ce, "Allah ya ja zamanın Damisa ƙi sabo, mu je madugu uban tafiya, barkono ka fi ƙarfin shiƙa. Allah ya sa ba laifi mu ka yi ba, na ganka kwatsam babu sanarwa." Omar ya bisu da kallo yana kallon wayoyin da suke ƙasa ya ce, "waye ya ƙwace waya a ƙasan gada?." Ɗaya daga cikin su ya ce, "Madugu ai ƙasan gada da yawa, daidai ina ka ke nufi?." Narma ya juya yana kalla ya ce, "fito." Sai ta riƙe rigarsa tana kwanciya a bayansa jikinta na rawa sosai. Hannunta ya jawo kafin ya saki hannun na ta ya ce, "waye ya karɓi wayarta?."

Wanda ya ƙwace mata wayar ya kalle ta ya ce, "afuwan Jan wuya ni ne." Da hannu ya yi masa alamun da ya zo, ba musu ya taso yazo yana zuwa ya daki ƙewarsa ya ce, "Sai ka ji mata ciwo?." Ya sunkuyar da kai ya ce, "afuwan madugu ban san antyn mu ba ce." Harararsa ya yi ya kalli Narma da tayi tsuru ya ce, "bata haƙuri." Kallon Narma ya yi ya ce, "ki yi hakuri Anty." Firgita tayi da maganarsa jin ta wani iri kana ji ka san a buge ya ke, ta yi tsalle cikin tsoro ta koma bayansa ta riƙe shi jiki na rawa.

Omar ya runtse ido jin jikinta a bayansa a kwance, wani iri yake ji baya so tana riƙe shi ɗin nan, shi in ba Didi ba babu macen da ya taɓa haɗa jiki da ita, ko ita tunda ya girma bai haɗa jiki da ita ba sai dai ya riƙe hannunta ko su gaisa da safe, shiyasa yake jin wani iri a jikinsa in ta riƙe shi. Daurewa ya yi ya ce, "ɗauko min wayar, sannan kar ka naga an taɓa mata komai."

Ba musu ya juya aka fara bincike wayar sai ga iPhone 16 kalar pink da atm ɗinta a baya an ɗauko ya miƙa masa yana cewa, "wallahi Allah ne ya taimaka Magudu da yanzu ba labarin nan ake yi ba, na je inda za a kwashe kuɗaɗen ciki baya nan." Omar ya karɓi wayar yana kallon su ya ce, "sauran wayoyin fa?."

Wanda yake zaune ya ce, "Damisa ganimar yau ce." Ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya kana ya ce, "tattaro min su duka." A tare suka haɗa baki suka ce, "Haba Damisa wannan yawa ka ke yi fa, wannan ba halin ka bane." Fuska ya sake ɗaurewa ya ce, "Ku tattaro min ko na tattara har da ku." Babban ciki ya ce, "gaskiya Madugu hakan bai yi ba, ka san wahalar da muka sha....." kallon da ya yi masa ya saka ya ce, "Kawai dan kaine wallahi, amma da ka san babu wani da ya isa ya saka mu bada wayar nan koda gwamna ne wallahi, ku bashi."

Tattaro wayoyin suka yi suka zuba a wata jaka aka miƙa masa ya karɓa yana kallon su duk sun ɗaure fuska alamun basu ji daɗin hakan ba. Ya sake kallon su ya ce, "Ku riƙe kawai" ya faɗa yana miƙa musu.
" ka je dasu kawai, amma kawai dan babu yadda zamu yi da kai ne."
"Ban son wannan ɗabi'ar da ku ke yi, in ba ku daina ba...." Sai ya katse maganar ya karkaɗa musu yatsansa. Ya motsa zai bar wajan ta sake riƙe shi gam.

Tsaki ya yi ya ce, "Malama ki sake ni!." Yadda ya yi maganar a kausashe ya saka ta sakinsa amma duk da haka tana rike da gefen rigarsa suka fita daga wajan. Bayan motar ta shiga a tsorace ya cilla mata wayar ta ya ce, "Kano ba Abuja bane ki san inda zaki dinga shiga." Bata ce komai ba ya ja motar kai tsaye police station ya wuce.

Nan ma sai da ta bishi ya samu dpo yana niyar fita suka gaisa ya bashi wayar ya ce, "wayoyin da aka ƙwace yau ne, ku saka a duniya a mene masu su a basu wayar." Dpo ya kalle shi ya ce, "ina wanda suka ƙwace wayoyin su ke?."
"Ni dai wayoyin na kawo maka in na mayar shikenan." Ya karɓa ya ce, "amma samun masu aikata laifin ya fi samun wayoyin amfani. Tiger da zaka taimaka a kama su da kayi babban aiki."

Ya kalli Dpo ya kafin ya ce, "a fara bawa kowa haƙƙinsa tukunna, zan faɗa maka inda zaka same su wani lokaci, amma ba yau ba." Dpo ya ce, "babu damuwa. Da za a samu shugabanni kamar ka ai da Kano ta zauna lafiya. Ga ka dai kowa ya san ka amma baka ɓarnar da ƴan uwanka suke yi, ban san meyasa ake kiran ka da ɗan daba ba, dai kai ba shi ba ne." Bai ce komai ba ya fito ya shiga mota itama ta shiga ya ja motar ya nufi gidan da Narma ta sauka.

Yana tsayawa a harabar ta buɗe motar ta fito jiki a sanyaye dan kanta ciwo yake yi mata matuƙa saboda kukan da tayi. Fitowa Shima ya yi tana niyar shiga ya ce, "kin ga." Ba musu ta tsaya cak ta jiyo tana kallon sa ya tako inda yake ya miƙa mata key ɗin motar. Ta kalli key ɗin da yake bata ta kalle shi ta ce, "kaje da ita."
"Karɓi" ya sake faɗa yana miƙa mata fuskarsa a ɗaure yamau.

A shagwaɓe ta ce, "hannuna yayi nauyi bana iya ɗaukat komai, maganin ma wahala nake sha wajan riƙewa." Ledar hannunta ya buɗe ya saka mata key ɗin ya juya ya fita daga gidan. Ajiyar zuciya tayi bayan ya fita tana kallon sa ta ce, "kamar wani mai hankali, ba dan shi ba da waya ta ta tafi kenan" ta faɗa tana shiga falo.

Kunna wayar tayi tana ajiyar zuciya kiran Dad ya shigo, ɗauka tayi daga can Dad ya ce, "Narma ina kika saka wayarki? Ina ta kira tun ɗazu bana samun ki." Narma ta ce, "Dad!" Sai ta saka kuka hankalinsa ya tashi ya ce, "me ya faru? Tiger ne ya sake miki wani abun?. Talk to me mana kin saka ni a ruɗani."

"Dad tare ni aka yi a under the flyover, they snatched my phone and my atm card. Dad sun yanke ni a hannuna jini yana ta flowing" ta faɗa tana jan kalmar ƙarshe tare da fashewa da kuka.
"Innalillahi! Daughter me ki ke cewa? A ina haka ya faru? Ina shi Tiger ɗin yake?." Ba ta yi magana ba sai kuka, kawai ya yanke wayar ya kira ta video call ta ɗauka ta ganshi a zaune shida Mum harda Najwa a rikice suke ce mata ne ya faru.

Narma ta ce, "Dad ba da shi ne fita ba, ni kaɗai na fita."
"Are you mad Narma? Nace baki da hankali ne. Me na faɗa miki akan fita ke kaɗai? Ban yi miki warning akan haka ba?." Ganin yana faɗa sai Mum ta ce, "My dear ka yi mata a hankali baka ganin tana da ciwo ne?. Daughter calm down ki faɗa mana abinda ya faru."

Narma ta ce, "na jira shi bai zo ba sai na hau mota na fita, ina cikin tafiya sai motar ta tsaya na fito daga motar sai ga wani ya saka min wuƙa ya ce na bashi wayata, da zai ƙwace wayar ne ya yanke ni....!" Ta faɗa tana hawaye.

Dad ya ce, "oh my god! Yanzu ya jikin naki?. Kin je asibiti?." Mum cikin faɗa ta ce, "'ni banga amfanin wannan banzan Tiger ɗin ba, ban ga amfaninsa da ka bashi ragamar kula da yarinya ta ba. How com yana matsayin driverta ya barta ta fita ita kaɗai?. Gaskiya dear bazan iya tolerating wannan shirmen na sa ba, zan tura mata da poliçe da zasu kula min da ita. Kalli hannunta fa, kalli girman ciwon da ka ji mata akan wayar one million."

Narma ta goge ido ta ce, "No Mum, ya taimake ni. Ban san ya aka yi ba ina wajan sai na ganshi yazo, he took me to the hospital and had my wound dressed, then muka je har inda masu ƙwacen wayar suke zama ya kaɓo min wayar har suka bani haƙuri. Sai da ya dawo dani sannan ya tafi."

Jin haka gently Mum ta ce, "kina nufin har inda wanda suka ƙwace miki wayar ya je ya karɓo miki?."
"Yes Mum, har da atm card ɗina ma an bani. Ba ma iya phone ɗin ba duk wanda aka karɓawa waya yau ya karɓa ya kaiwa police station za a neme masu shi." Dad ya kalli Mum ya ce, "Now you understands why I have trusted him right? You should see the benefit of being him with Narma?." Narma ta yi shiru ya kalle ta ya ce, "na tabbatar da ace tare ku ke babu wanda zai ce zai miki wani abun."


"I see, Dan suma bashi respect sosai har mamaki nayi."
"You see. Kina ji, yanzu ki je ki huta ki yi bacci sosai da safe sai mu ƙarasa maganar."

Narma ta ce, "but Dad I'm scared wallahi, please can you convince him to come and stay with me? In yana kwana a nan zan fi samun tsaro sosai." Dad ya ce, "don't worrry, yanzu ki kwanta." Amsawa tayi ta kashe wayar ta tashi ta sha magani ta kwanta.

Dad bayan ya kashe wayar ya kalli Mum ya ce, "kin ga abinda nake faɗa miki ko?. Ɗan iska sai da ɗan iska irinsa ake zama lafiya." Mum ta ce, "na fahimta, amma ya cika zaƙewa ne da yawa baya bata girmanta." Dad ya yi murmushi ya ce, "ƙyale ni dashi, tunda har ya taimake ta ai komai ya yi kyau."

Omar kuwa a haka ya koma gida jikinsa duk babu ƙarfi, ƙhamshin turaren Narma ya gama kama kayan jikinsa gaba da baya. Duk ya takura ya kuma damu saboda turaren ya ishe shi duk da yana da daɗin ƙamshi sosai, amma ya takura masa so yake ya cire kayan ya huta.

Yana shiga gidan ya ga Didi a tsaye, ta ƙaraso inda yake ta ce, "Tun ɗazu nake jiran dawowaka, ko abinci baka ci ba." Kallon rigarsa tayi kasancewar ta blue mai haske ta ce, "Omar me nake gani a jikinka kamar jini?." Kallon rigar ya yi ya kalle ta zai yi magana ta ce, "Omar kar ka ce min faɗa ka yi."

Omar ya ce, "Ban yi faɗa da kowa ba Didi, taimako nayi, kar ki damu." Kallon fuskarsa tayi sai taga bai yi kama da wanda ya yi faɗa ba, dan ta san in faɗa ya yi jiyoiyin kansa ma zasu tona masa asiri saboda ɓacin rai.

"Wa ka taimaka haka?."
"Wata yarinya aka ƙwacewa waya kuma aka yanke ta a hannu shine na taimaka mata." Da mamaki take kallonsa ta ce, "ƙhamshin turarenta nake ji a jikinka haka?." Ɗan kulle ido ya yi ya buɗe dan bai so ta ji ƙhamshin ba ya ce, "shi shine."

"Wanne irin taimako ne wannan da ƙhamshinta zai dinga tashi haka a jikinka?." Ya kalle ta ganin tana kallon sa kamar bata yarda ba ya ce, "kin san bazan miki ƙarya ba ko?." Didi ta ce, "na sani, ban ce kana ƙarya ba, ina so na tabbatar ne kawai."
"To ki yarda" ya furta mata a taƙaice ya wuce ya kyale ta. Mamaki abin yake bata, taimako ya yi, taimakon ma mace ya taimaka kuma ga ƙhamshinta a jikinsa, wanne irin taimako ne wannan haka?. Babu mai bata amsa hakan ya saka ta ƙyale shi da tambaya ta shiga ciki.


Washe gari.

Da labarin abinda Tiger ya yi aka tashi, kusan duka mutanen da aka ƙwacewa waya a daren jiya an basu kayar su, musamman wanda aka ƙwacewa a arear da ya karɓa. Ana ta saka masa albarka dan an faɗi sunan sa ance Omar wanda aka fi sani da Tiger.

Nayla na zaune kusa da Hajja tana kallon labaran tana murmushi. Hajja ta kalle ta tace, "ke lafiya ki ke murmushi?." Ta kalli Hajja ta ce, "Hajja Omar ƙanin Didi shine ya karɓo wayoyin da aka ƙwacewa wasu jiya, Wallahi shine abin ya yi min daɗi sosai."

Hajja ya ce, "indai irin wannan abubuwan ne ya saba, inda iya haka yake tsayawa da ya zama mutumin kirki sosai, to shima shegen kansa ne. Lokacin da yake cikin ƴan daban kaca-kaca baza ki so ki ji irin abinda yake yi ba, ya zubar da jinin mutane da yawa ba kaɗan ba. Allah sarki Aisha, ya wahalar da baiwar Allah nesa ba kusa ba, itace zuwa wajan ƴan sanda, itace zuwa prison, ita zuwa inda yake zama. Kaii...sai dai Allah ya biyata kawai, amma Omar ya wahalar da ita har yanzu yana kan bata ciwon kai." Nayla tana ji tayi shiru amma Allah ya sani ya yi bala'in burgeta, haka kawai taji tana so ta ganshi ko da kuwa zai yi mata tsawa.

Hajja ta sake kallon ta taga sai murmushi take yi ta ce, "Wai murmushin ne har yanzu?." Nayla ta ce, "wani abun na gani a wayar." Hajja ta ɗauke kai sai Nayla ta ce, "Hajja an ce Didi ma tayi rashin lafiya, bara naje na duba ta." Hajja ta kalle ta ta ce, "Keda bakya son shiga gidan?."
"Hajja ai lalura ce kuma tana da kirki sosai."
"Ki jira Salma ta dawo sai ku je."
"A'a Hajja, kamar wata baƙuwa?, bara naje dai" ta faɗa tana ɗaukar hijjabi ta saka, ta ɗauki wayarta fita Hajja ya bita da kallon mamaki.


*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

             ©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

https://www.tiktok.com/@nanahaleemawriter?_t=ZS-8zaZqblsrGp&_r=1

*Book 1*
*P 14.*


Nayla sai da tazo ƙofar gidan Didi sai kuma gabanta ya faɗi matuƙa, ta runtse ido tare da ajiyar zuciya ta shiga gidan da siririyar sallama. Yana tsaye a tsakar gidan dube-dube da alama akwai abinda yake nema, jin anyi sallama ya juya kai tsaye suka haɗa idanu da Nayla.

Sanye yake da riga mai siririn hannu kamar singlet amma tafi singlet girma da rufe jiki. Sai dogon wando mai jikin Damisa dan sai ka ɗauka da fatar Damisa aka yi shi. Murɗaɗen jikinsa duk a bayyana haka farar fatansa a bayyane take tana ɗaukar ido, ga wanda bai san shi ba dole in yaga fatarsa sai ya tsaya yana kallo saboda haskenta.

A cikin sakan biyar ta ƙare masa kallo har lokacin kallon ta yake yi duk da tana jin tsoro amma ta daure ta ce, "ina kwana." Bai amsa ba bai kuma daina kallon ta ba yana mamakin wannan yarinya da shegen naci take, bata jin magana duk da ya yi mata warning bata daina zuwa gidan ba.

Janye idanunsa ya yi bai ce komai ba, jin bai amsa ba sai ta ce, "Didi tana nan?." Nan ma yayi mata banza sai jikinta ya ɗan yi sanyi, daman gashi a tsorace take dashi gashi yayi mata banza. Kallon inda take ya yi yaga tana tsaye ya ce, "in zaki shiga ki shiga, in fita zaki yi ki bani waje!" Ya faɗa da ƙarfi bata san ta wuce shi a guje ba sai sautin tsakinsa taji tayi ajiyar zuciya.

Bata tarar da Didi a falo ba sai ta zauna kamar munafuka ta kasa sakewa, motsin shara taji ana yi sai ta miƙe ta kalli window ga mamakin ta shine yake share gidan a nutse, sai ta tsaya tana kallon sa tana murmushi wanda bata san tana yi ba. Didi da ta fito ta ga Nayla na kallon window sai ta yi murmushi tana daga bayanta ta ce, "Nayla." Firgigit tayi ta kalli Didi ta ce, "Didi yaushe ki ka fito?."

"Ta ya zaki san lokacin da na fito kina kallon mutumin ki yana shara? Ya baki mamaki ko?" Ta faɗa suna zama a kan kujera. Nayla sai taji nauyi kallon sa da ta tsaya yi amma bata nuna ba ta ce, "Sosai ma kuwa, kawai ji na yi ana shara sai na leƙa ashe shine, kawai sai na tsaya ina kallonsa."

Didi tayi dariya ta ce, "ai dole ki tsaya, In ya so ya ga dama shi yake yin komai a gidan nan hatta girki, har inda na kwanta shine zai gyara kuma baza ki ce namiji ne ya yi ba. Amma in bai ga dama ba abinda ya ci abincin ma ni zan ɗauke." Nayla tayi murmushi tana kallon Didi ta ce, "shi dai sai ka rasa ka gane wanne iri ne, in ya yi gabas sai ya karkace."

Didi ta ce, "shiyasa nake faɗa miki yana da kirki fiye da tunaninki, yana da hira sosai. Kawai bashi da saurin sabo ne kuma baya son baƙi kwata-kwata."

Nayla daɗi take ji a zuciyarta ana hirar Omar hakan ya saka ta sake gyara zama ta ce, "ina fa kirki a nan Didi, har gaishe shi nayi yayi min banza." Didi ta ce, "bazai amsa ba ai, in kinga ya amsa to tabbas kun sana dashi matuƙa. Naga alama dai tsoron na sa ya ɗan ragu a zuciyarki."

Nayla ta ce, "hmm ina fa, wallahi akwai daurewa nayi nazo na gaishe ki, kwana biyu kin yi rashin lafiya." Didi tayi dariya ta ce, "ai kuwa na gode sosai Nayla, Naji daɗi matuƙa Allah ya bar zumunci." Nayla ta amsa da amin amma a zuciyarta kawai so take a cigaba da zancen Omar. Ƴar hira Didi take janta da ita akan labarin mutanen Kaduna da Hajja tana amsa mata da lafiya kowa yake.

Shigowarsa suka gani ya canja kaya zuwa jeans blue da farar riga mai layi-layi a jikinta, riga ta mai dogon hannu ce, sai ya tattare hannun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login