Showing 36001 words to 39000 words out of 87436 words

Chapter 13 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

magana yana cewa wai zai ajjiye aikin saboda baya son raini? Just Imagine, wani banza shashasha talaka ne yake faɗawa ƴar senator haka."

Dad ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "kar ka damu Nabil na san abinda nake yi, kar ka samu damuwa, wani lokacin yawo da irin su Tiger yafi amfani akan yawo da police. Na san abinda nake yi fa kar ka samu damuwa." Mum dai kawar da kai tayi zuciyar ta cike da haushin wannan hukunci na senator, gashi wani banza talaka yana wulaƙanta mata yarinya.

     Wayar Narma ce ta sake zuwa ya ɗauka ya saka a speaker muryarta karaɗe falon ta ce, "Dad zan fita da daddare amma an sanar dani ya fita, Dad i'm so done with his attitude, Ko 24 hours ban yi ba ya fara bani cikon kai? Gaskiya i can't." Dad ya ce, "whice time you want to go?."
"By 8."
"Alright, i will let him know, i will send you his number in kina son fita ko yaushe you can give him a call." Narma ta ce, "Dad what's so special about this guy that you're willing to share my contact info with him?."Dad ya ce, "kar ki damu" abinda ya ce kenan ya yanke wayar yana kallon irin kallon da su Mum suke masa amma bai kula su ba dan shi kaɗai ya san amfanin Tiger su baza su gane abinda yake nufi ba shiyasa.

          Shi kuwa Omar ko da ya bar gidan a napep ya koma unguwar su ya sauka a bakin layin ya shiga ciki a ƙafa. Babu wanda yake yiwa magana kamar yadda babu mai yi masa magana tafiya kawai yake yi cikin takun isa da ƙasaita da nuna zallar izza.

"Ummaru wucewa zaka yi? To na gode." Kallon inda aka yi maganar yayi yaga Hajja da hijjabi zata shiga gidan ta da alama dawowar ta kenan daga wani waje. Zai yi magana ta ce, "in baza ka shigo mu gaisa ba na gode" ta faɗa tana shiga cikin gidan.

Shi fa wallahi baya son shiga gidan mutane, ga Hajja yana ganin kırkinta da mutuncinta amma shi gabaɗaya baya son shiga gidan. Ƙaramin tsaki ya yi ya shiga gidan fuskarsa a ɗaure ya yi sallama a car park ɗin gidan. Nayla da ta ji sallama ta amsa tana juyowa ido ta ya faɗa cikin nasa, bata san ta saki tea flaks ɗin da yake hannunta ba sai sautin fashewar kwalba tayi.

Ido ta wara waje tana kallonsa shi kuma kallon sencond biyar ya yi mata ya ɗauke kai ya jiyo muryar Hajja tana cewa, "Ummaru shigo mana." Shiga falon ya yi Hajja tana cewa, "na ɗauka ai baza ka shigo ba, ko gaishe ni ɗin da ka ke yi yanzu ka daina."
"Ina yini" ya furta a taƙaice ta amsa ta ce, "lafiya lau Ummaru, ya gida?."
"Lafiya" ya amsa a taƙaice yana kallon ƙasa.

Hajja ta ce, "Hauwa'u filas ɗin shayin ki ka fasa? Naji ƙarar fashewar kwalba. Ki saka shi a shara kawai, Allah ya sa baki ji ciwo ba" Hajja ta faɗa yadda Nayla zata ji.

Maganar da Hajja tayi ne ya dawo da ita hankalinta, ta ɗauki flakas ɗin ta saka a shara ta taho a hankali zata shiga falon shi kuma zai fito. Ɗifff tayi ta ja numfashi mai nauyi, ƙiris ya rage ƙirjinsu ya haɗu waje ɗaya, ya kalli fuskarta na wasu sacanni murya a can ƙasa ya ce, "ki ƙauracewa ganina" abinda ya ce kenan tayi saurin yin baya shi kuma ya fita yana ji Hajja tana yi masa magana.

      Nayla ta shiga tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "na shiga uku, Hajja daman yana shigowa gidan nan?." Hajja ta ce, "yana shigowa mana." Nayla ta ce, "Allah ya taimaki Salma da take bacci bata ganshi ba, wai har da ce min na ƙauracewa ganinsa. Ni dai ban san ƙaddarar da take haɗa mu ba wallahi, gabana sai faɗuwa yake yi."

Hajja ta ce, "shiyasa ki ka fasa min filas ɗin shayi ai, sai ki kira babanki Daddy ya bayar a kawo mana sabo saboda gobe zaki azumi." Nayla dai numfashi take sauke a hankali, abinda yake bata mamaki faɗuwar gaban da take ji ba ta tsoro ba ce kamar wacce take ji farkon haɗuwarsu, muryarsa take ji a kunnenta tana hango yadda ƙirjinsu da ya kusa haɗewa da na juna. Lumshe ido tayi ta buɗe a bayyane ta ce, "Allah mai iko." Hajja ta kalle ta sai tayi tsaki ta cigaba da kallon tv tana kallon tashar saudia.

           Omar yana shiga gidan a tsakar gidan ya samu Didi ta juyo tana kallon sa ta ce, "shigowa ba sallama kuma Omar?." Bai amsa mata ba ta kalle shi ta ce, "ina kaje ne?." Bai ce komai ba ya shiga falon ya zauna, itama bata bi bayan sa ba sai da ta gama abinda take yi sannan ta shiga ta samu yana cin abinci.

Bata yi masa magana ba har ya gama dan ta san shi ba mutum ne mai son yin magana in yana cin  abinci ba, sai da ya sha ruwa ya sauke numfashi kaɗan sannan ta kalle shi ta ce, "ina ka je?." Kallon ta yayi ya tashi zaune sosai ya ce, "na fara wani aiki ne, amma ina ganin dole na ajjiye shi kafin na shaƙe yarinyar." Didi ta ce wanne aiki ne?."
"Zan faɗa miki, na karɓi aikin saboda ke ne kawai, na san aikin zai kawo kuɗi sosai ga hidimar bikin ki tana zuwa."
"Waye ya ce maka hidimar bikina tana zuwa?."
"A jikina naji hakan."
"Allah ya sa. Amma ka faɗa min wanne irin aiki ne?."

Bai ɓoye mata ba ya faɗa mata komai da kuma wacce aka haɗa shi da ita, ya ɗora da cewa, "ni wai yarinyar nan zata yiwa tsawa" yayi wani murmushi ya ce, "ko babanta bana tunanin zai yi min tsawa na ƙyale shi balle ita, a kaf duniya ke kaɗai zaki aike ni naje bayan ke babu wata halittar."

Didi da ta saki baki tana kallon sa cikin mamakin da ya sumar da ita a wajan ta ce, "Omar Senator Sagir ɗan takarar gwamnan Kano kuma sanata mai ci yanzu! Omar Meyasa ka kai kanka irin wannan wajan don Allah?. Na san halin ka baka da haƙuri ko kaɗan, kar zuciyarka ta kai ka ga aikatawa yarinyar nan wani abun na shiga uku."

Ya kalle ta ya ce, "kema kin san bazan ɗauki raini ba ai ko? Kuma bazan ɗauki iskanci ba. Ko Wacece ita daidai nake da ita wallahi, dan ubantq sanata ne hakan bazai hana na tsaga mata fuska ba da aska ba. In ta ja mutuncinta zamu zauna lafiya, in bata ja ba sai dai ko yi haƙuri kawai zaki ji labarin ina prison."

Didi a ruɗe ta ce, "Omar don girman Allah ka ajjiye aikin nan ka rufa min asiri, shi uban yarinyar wanne ganganci ne ya saka ya haɗa ka da ita? Omar ya san halin ka kuwa? Ya san baka da juriya kuwa? Ya san kana ɗaukar makami kuwa Omar?." Ganin Didi ta ruɗe hankalinta ya tashi sai ya ce, "kar ki damu Didi, babu abinda zai faru, in kin ga wani abu ya faru yarinyar tazo da rainin hankali ne wanda kin san bazan jure masa ba. Ko da ita nake yiwa aiki bata isa ta yi min abinda bai yi min balle babanta nake yiwa aiki, Kuma shima baban nata alfarmata ya nema a wannan ɓangaren, sai da na amince zan yi sannan ya turota."

Ganin ya miƙe tsaye Didi ma ta miƙe ta ce, "Omar ka yi masa waya ka ajjiye aikin nan."
"Didi ki nutsu don Allah, babu abinda zai same ni."
"Wallahi a jikina nake ji haɗuwarka da ita bazai zama alkhairi ba wallahi, don Allah ka ajjiye aikin nan." Ya bita da kallo ya ce, "Didi yarinyar da ki ke gani ce a social media fa, wacce ki ke cewa tana burge ki kin ganeta?." Didi ta wara ido waje ta ɗauki wayarta da sauri ta dubo page ɗin Barr Nass ta nuna masa ta ce, "wannan ce?."

Hoton Narma ya gani cikin kayan lauyoyi sun yi mata kyau matuƙa fuskar ta sai sheƙi take yi da annuri, wani iri yaji a jikinsa ya janye idanunsa ya kalli Didi ya ce, "ina faɗa miki itace kuma kina nuna min hotonta."

Didi ta ajjiye wayar ta ce, "na shiga uku, Omar don Allah ka ajjiye aikin nan ka ji? Yarinyar nan kowa ya yi mata shaidar bata da kunya, a social media ma faɗa ake yi da ita balle kuma a zahiri, kuma kai ka ga tana ganin a ƙasanta ka ke aiki."

Murmushi ya yi ya ce, "Didi kar ki damu babu abinda zai faru." Didi a sanyaye ta ce, "Tsoro nake ji Omar, bana son wani abu ya same ka shiyasa."
"Babu komai." Shiru tayi bata ce komai ba shi kuma ya fita ya bar mata falon tana kallon sa. Tana mamakin wannan ƙarfin hali na Omar, yarinya kamar wannan ƴar manya ita yake cewa in tayi masa wani abun sai dai ta samu labarin yana prison kenan bazai ƙyaleta ba, ta san daman bazai ƙyale ɗin ba wallahi sai dai a kulle shi. Ita dai duk fargaba ta gama cika mata zuciya, saboda babu wanda ya san halin Omar kamar ta, tsaf zai jawo mata maganar da zata kwana tana kuka. A haka ta koma ta zauna jiki babu ƙwari.

      Narma kuwa bacci ta yi sosai bata tashi ba sai magriba tayi sallar la'asar sannan tayi magriba, sakkowa tayi ƙasa ta samu har mai aiki ta haɗa mata abinci ta zauna taci abinci, ta ɗauki waya tana amsawa kafin ta tashi ta koma sama.

Ta window ta leƙa ta ga Yahya a zaune ta ɗaga murya ta ce, "kai!." Ɗago kai yayi ya kalle ta ya ce, "Hajiya." Narma ta ce, "ina sabon driver nan yake?." Yahya ya ce, "Hajiya ai tun ɗazu da ya tafi bai dawo ba." Kai ta girgiza ta koma tana mamakinsa da ƙarfin hali irin nasa. Shi ba kowan kowa ba amma ya dinga yi mata iskanci kala-kala.

Sai da tayi sallar i'sha sannan ta fara shiri, sun yi da ƙawayenta zasu ne yawo hakan ya saka ta shirya cikin doguwar riga wacce jikinta take kamar roba mai tsaga a baya, daga hips ɗin akwai wani maɗauri kamar mayafi daka ɗaure shi aka ɗaura a tsakiyar rigar. Rigar baƙa ce hakan ya saka ta haska jikinta sosai, ta ɗauki hula ta saka sannan ta ɗauko ƙaramin mayafi ta ɗora akan hular. Kallon kanta take yi, dan ta kanta san tayi kyau itama sosai, ta fesa turare masu daɗin gaske sannan ta sauka falon ƙasa a lokacin takwas daidai.

A daidai wannan lokacin Omar ya shigo cikin gidan ya kalli Yahya suka gaisa yana cewa, "yanzu Hajiya yake tambayarka." Omar ya ce, "gani ai, tana ina?."
"Tana ciki bata fito ba." Omar ya kalli agogon wayar sa ya ce, "ƙarfe takwas aka ce min, yanzu kuma takwas da mintina biyu, In takwas da sha biyar tayi wallahi babu inda zan je."

Shi dai Yahya kallon sa yake yi da mamaki, ganin sun haɗa ido sai Yahya ya ce, "ban san ko sunanka ba amma ƙarfin halin ka yana bani mamaki." Omar ya kalle shi ya ce, "Omar sunana."

"Koda na ji, yanayinka da maganarka da ta masu suna Omar ka yi kama, Daman da wahala ka ga masu suna Omar ba irinka ba, ko kaɗan ba sa lamuntar raini." Ɗan murmushi Omar ya yi kawai amma bai ce komai ba.

Narma ce ta fito tana duba waya tana cewa, "wai ina driver nan yake ne? Bana son wulaƙanci da iskanci fa, dan ya raina ni ni ce zan zauna ina jiran sa?."

Inda yake ta kalla ta ga ya kalle ta ya ɗauke kai kafin ya ƙarasa wajan motar ya buɗe mazaunin driver ya shiga ya zauna ita kuma ta ja ta tsaya. Ƙwanƙwasa glass ɗin gaban motar tayi ya sauke glass ɗin ƙasa. Wani irin kallo take masa na raini da ƙasƙanci ta ce, "Malam ka sakko ka buɗe min, ko kana so kace ni zan buɗe?."

"Baki da hannu?" Ya faɗa ba tare da ya sake kallon ta ba.
"Ina dashi, kai nake so ka buɗe min."
"Ashe baza ki je" ya sake kallon agogo ya ce, "kina da mintina bakwai in lokaci ya cika babu inda zan je."

Kallon sa take yi shi kuma ya kalli glass ɗin gaban motar kamar motar sa, fuskarsa ɗaure matuƙa ga wani kwarjini da fuskar take fitarwa. Duk da tana jin tsoronsa musamman yadda ya ɗaure fuska amma hakan ya saka ta kuma cewa, "ni kuma indai baka buɗe min ba bazan je" ta faɗa tana komawa gefe ta ja ta tsaya tana so ta ƙure shi iskancinsa.

Shi kuwa kallon ta yayi zuciyarsa a sama matuƙa, abu ɗaya kawai ya sani ko zata mutu ta dawo wallahi bazai buɗe mata mota ba sai dai kar ta je. Zama ya cigaba da yi a cikin motar sai kace motar ta Didi ce. Agogo yake kallo yana jira lokacin da ya bata ya cika ya fita ya bar gidan. Su dai ma'aikatan gidan kallon ikon Allah suke yi, mamakin Omar su ke yi ɓangare ɗaya suna jin daɗi an samu daidai da Narma, suna tsaye suna so su ga waye zai ci wasan.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 11.*


Kowa a wajan kallon ta yake yi ana kuma jira a ga Omar zai fito ya buɗe mata motar ko bazai fito ba. Ga mamakin su Omar bai fito ba yana zaune a cikin motar kamar motarsa, ita kuma tana tsaye har lokacin tana jira ya fito ya buɗe mata. Mamakin sa take yi ganin bai sauko ya buɗe mata ba kenan bazai yi ba? In haka ya faru wacce irin kunya zata ji a gaban ma'aikatan gidan?. Wayarta ce tayi ƙara ta ga ƙawayenta da suke jiran ta zasu fita ne, ta buga uban tsaki ta kashe wayar tana sake kallon sa babu alamun ma zai fito dan ko kallon inda take ma baya yi.

Shi kuwa Omar ƙoƙarin daidaita ɓacin ransa yake yi dan in ya fita a yadda yake jin zuciyarsa tsaf zai sharara mata maruka masu zafi, shi kuma ba haka yake so ba, yana so su rabu lafiya ko dan alƙawarin da ya yiwa Didi, sannan yana so su rabu lafiya ko dan kuɗin mahaifinta da ya karɓa. Shiru na kusan mintina biyar hakan ya yi daidai da saursa minti biyu ya kama gaban sa.

Yahya ne ya ƙaraso wajan motar  a sanyaye ya ƙwanƙwasawa glass ɗin gefen Omar, Omar glass ya sauke yana kallon sa ya ce, "Omar don Allah kazo ka buɗe mata ka huta." Omar ya kalle shi ya ɗauke kai dan babu amfanin ma yi masa magana.

Yahya ya juya ga Narma ya ce, "Hajiya bismillah" ya faɗa yana buɗe mata amma sai ta bishi da banzan kallo na wulaƙanci ta ce, "Wallahi shi zai buɗe min, in kuma bai buɗe min ba daga yau ya bar aiki a gidan nan, sai naga waye ubansa a Kano da yake min wannan wulaƙanci. Shashasha dashi ƙazami."

Buɗe kofar taga an yi sai tayi murmushi ta ɗauka zai buɗe mata ne, ga mamakin ta kai tsaye inda take ya nufa fuskarsa a ɗaure, yana zuwa ya kalle ta ya ce, "in kika sake furta abinda kika furta ɗazu sai kin yi dana sanin haɗa ido dani a rayuwarki, in kuma kina ganin wasa nake yi ki maimaita abinda ki ka ce yanzu" ya faɗa ciki tsawa yana tsare ta da idanunsa masu ban tsoro da kwarjini.

Ɗiff Narma tayi tana kallon idanun sakamar yadda ita yake kallo, da sauri ta ɗauke kai daga kansa, ganin ta yi shiru ya cize baki yana karkatar da baki irin yadda ƴan daba suke yi ya nuna ta da taysa ya ce, "ki san irin maganar da zaki dinga faɗa min in kina so kan ki da zaman lafiya, In kuma kina so na huda cikin ki sai ki cigaba."

Yahya ya kalla ya cilla masa key ɗin motar shi kuma ya chafe, Omar bai ce komai ba ya juya ya fita daga gidan.

Wata uwar ƙara Narma tayi ta shiga cikin gidan a guje ta faɗa kan kujera ta fashe da kuka mai ƙunar rai. Wai ita Narma wani banzan ɗan daba, ɗan shaye-shaye ya yiwa wannan wulaƙacin a gaban ma'aikata, kawai saboda Dad ya bashi damar haɗa ido da ita shine yake zaƙewa. Ita Narma mai capacity wani ɗan tasha ya wulaƙanta a gaban masu aiki a ƙarƙashin ta.

Hannu na rawa take kiran Dad, yana ɗauka kawai ta fashe masa da kuka. Dad ya ruɗe sosai ya ce, "Oh Narma, what wrong? Why are you crying like this?." Kuka take yi sosai cikin baƙin cikin da take ji a zuciyarta. Sai da tayi kukan ta gaji murya na rawa ta ce, "Dad i was really disrespected by that guy in front of the maids, Dad ƙawayena suna can suna jira na amma yayi tafiyarsa. Dad gaskiya ni bana son aiki dashi, ka barni da wanda muke tare dasu a nan."

Dad ya ce, "stop crying and talk to me, what happened?." Narma ta bashi labarin abinda ya yi mata sannan ta ce, "Dad wai waye shi da yake min haka ne?."

Dad ya ce, "ba kowa bane fa ce ɗan daba kuma ɗan tasha, ba kowa bane fa ce ƴan bangar siyasa wanda mu ke amfani dasu wajan cikar burin mu. Bana son yin wasa da Tiger shiyasa kika ga ina biye masa duk abinda ya ce, zaɓen gaba nake ji ke kin san kujerar da nake nema, irin su Tiger makami ne sosai a tafiyar mu shiyasa ki ka ina biye masa. In ba dan haka ba shi waye? Ko inda motarki take bai isa yazo ba, lafiyarsa nake so ya bani wajan kare ta ki shiyasa nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login