Showing 6001 words to 9000 words out of 87436 words
Chapter 3 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt
an girma dai. Ka gaishe da Aisha mutuniyar kirki."
Bai ce komai ba ya juya suka cigaba da tafiya yana ɗan murmushi jin abinda Hajja ta ce wai a daina rashin ji. Tafiya suke yi har ƙofar gidan Alhaji Yusuf kamar yadda suka yi niya. Ɗaya daga cikin yaran sa ne yayi sallama a ƙofar gida aka amsa daga ciki. Kafin ka ce kwabo mutane sun taru a wajan saboda mamakin ganin Omar a ƙofar gidan a tsaye, wannan dalilin ya saka aka tsaya kallo dan a ga me zai faru.
Alhaji Yusuf ya fito ganin Omar shi kansa sai da gabansa ya yanke ya faɗi dan bai san dame yazo ba. Ya dake bai nuna tsoro ba ya kalli wanda ya yi sallamar ya ce, "Lafiya?." Omar jin maganar sa sai ya ƙaraso yana kallon sa ya ce, "Ka jawa matar ka kunne, kar ta dake faɗar abinda ta faɗa in ba haka ba zata yi dana sani." Alhaji Yusuf ya ce, "me tayi maka?."
"Har gwara ace ni ta taɓa da zata fi zama lafiya, in ka tambaye ta zata faɗa maka. A dai ja mata kunne saboda gudun gamuwa ta gaba" abinda ya ce kenan ya tafi daga wajan. Yaron sa mai suna Tk ya kalli Alhaji Yusuf ya ce, "a ja mata kunne, Tiger gargaɗi ɗaya kawai yake yi. Tunda kaga yazo har nan tabbas Didi aka taɓa, ka tambayi matar ka abinda ya haɗu su zaka fahimta" yana gama faɗa ya bar wajan aka bar Alhaji Yusuf da sakaken baki yana bin su da kallo.
Kamar yadda ya faɗa cikin unguwar Yakasai suka shiga kasancewar magriba gabato garin a cike yake da ƴan kasuwa da ake dawowa. Har inda ya san ƴan dabar yakasai suna zama suka shiga, kai tsaye ya hango wanda yake nema ya ƙarasa wajan su yana kallon su kamar yadda suke kallon sa. Zama yayi a cikin su yana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ya kalli babban su ya ce, "Meyasa akuyar ka ta shiga gidana ta cinye min dusa?."
Kallon sa ya yi ya ce, "Tiger ban fahimce ka ba." Tk da yake tsaye a baya ya ce, "Tiger yana magana akan yaron da aka kashe a nan bayan kun kwace wayarsa, ɗan arear Tiger ne."
Kallon Omar ya yi ya ce, "Tiger afuwa ban mu san na ku bane da hakan bai faru ba. Ka gan shi nan yanzu maganar ma mu ke yi" ya faɗa yana dukan kan yaron. Omar ya kalli wanda aka nuna masa kafin ya dawo da kallon sa ga Jijiya ya ce, "Wanne mataki aka ɗauka akan hakan?."
"Babu abinda mu ka yi a yanzu."
"Ya zama dole a hukunta shi! Bazai kashe banza ba, kai ka san bazan ƙyale ba."
Jijiya ya ce, "Haba Tiger duk an zama ɗaya fa, kuskure ne kuma baza a sake maimaitawa ba." Ya sauke ajiyar zuciya ya sake kallon Jijiya ya ce, "ya san an zama ɗayan ya kashe rai?."
"Tiger kana da abin mamaki, meye aibu a kashe rai kamar yau aka saba?."
"Ko ku bari hukuma tayi aikin ta ko mu mu yi aikin mu, wanne ku ka zaɓa?." Jijiya ya kalli Tiger ya ce, "yadda ka ce haka za a yi." Omar ya miƙe ya ce, "ku tashi mu je wajan ƴan sanda"
Wanda ya aikata laifin yayi tsiru-tsiru da ido jin ana zancen ƴan sanda ya kalli Jijiya ya ce, "Haba Jijiya ai ba a yi min adalci ba." Jijiya ya kalle shi ya ce, "Kenan na bar ka da Tiger ya hukunta ka?." Kai ya sunkuyar cikin rashin abin yi, ya kalli Tiger da yake kallon wani wajan daban.
Ya tuna kwanaki da wani ya aikata irin abinda ya aikata yaƙi yarda ya kai kansa ga ƴan sanda, aka bar shi da Omar yana da ƙafafunsa basa takuwa saboda sun tashi aiki. Omar ba ya kisa, amma za a yi maka abinda zaka gwammace kashe ka aka yi.
Ajiyar zuciya yayi ya ce, "mu je ga hukumar." Omar ya koma gefe kamar ma bai san ana yi ba, tare suka tafi police station aka gabatar da mai laifi kamar yadda maganar ƙwace wayar ta zaga duniya saboda irin kisan da aka yiwa wanda aka ƙwacewa wayar. Video aka yi masa aka yaɗa a duniya ana tabbatarwa da mutane wanda ya yi kisan ya shiga hannu, kuma za a yi masa hukunci daidai da abinda ya aikata.
A nan suka yi sallar magriba gabaɗaya, DPO yana ta yabawa Omar akan abinda ya yi, duk da an saba ire-iren wannan laifin ya kan kawo wanda ya aikata don a hukunta shi. Shi kuwa ko maganar kirki samu daga gare shi ba burinsa a hukunta shi in ba haka ba shi ya ɗauki mataki. Ya tsani yadda ake ƙwacewa mutane waya kuma a cutar dasu, kai da abin ka a ƙwace maka kuma a cuce ka saboda tsabar zalinci. In da iya ƙwacen ne ma da sauƙi, amma bayan a ƙwace sai an cutar da kai. Shiyasa baya ɗagawa kowa ƙafa akan ƙwace, ko da kana daga cikin yaran ka aikata sunan da ake kiran sa zai yi tasiri a kan ka. Damisa ƙi sabo!.
Suna idar da sallah suka koma unguwar su kamar yadda suka saba. Waɗanda suka kalli video da aka yaɗa sai kallon Omar suke yi suna mamakin yadda wani lokacin yake yin aiki irin na masu hankali wani lokacin kuma ya yi aiki irin na ƴan daba.
Tare suka shiga gidan da yaran sa su uku har shi na huɗu. A lokacin Didi tana zaune akan sallaya a tsakar gidan tana sauraron abinda ake faɗa a video da aka yaɗa na yaron da Tiger ya saka aka kama. Ganin shigowar su sai ta kalle shi ta ce, "ka ɗauko mu ku abinci." Bai ce komai ba ya nemi waje ya zauna dan sun san bazai dauƙo ba. Goje ne ya ɗauko abincin da kansa dan gidan ba baƙon su bane, babu inda basa shiga dan sune kamar ƴan aiken ta. Abincin ya kawo kowa ya zuba abincin yana ci.
"Omar amma abinda ka yi ka kyauta sosai, ina nan ina fargabar kar ka ɗauko min magana ashe gyara ka je kayi. Da haka ka ke yi da ba ayi maka wani kallo na daban ba" Didi ta faɗa tana kallon sa.
Numfashi kawai ya sauke bai ce komai ba sai tayi murmushi bata damu da shirun na sa ba ta ce, "Tukur meyasa bakwa yiwa mai gidan ku faɗa ne? Meyasa bakwa faɗa masa gaskiya?." Tk ya kalli Didi yana murmushi dan itace kawai take ce masa tukur a zauna lafiya, Tk shine sunansa ba Tukur ba. Ya ce, "Didi Tiger fa ba yadda ki ke tunani ya ke ba, mutum ne mai son zaman lafiya in kinga an samu matsala dashi akasi aka samu."
"Ba wani nan, kawai kana kare mai gidan ka ne, kuma bakwa faɗa masa gaskiya" ta kalli sauran da suke cin abinci suna murmushi ta ce, "Sai murmushi ku ke yi babu mai faɗa masa gaskiya a cikin ku, na tabbatar in Omar ya watsar da makaman sa kuma za ku watsar, domin kuwa ya zamar kamar shi ne komai na ku, in ya ce ayi kuna yi, In ya ce a bari kuna bari. Da tattara ku ya yi ku ka koma kasuwa duk da hakan bai faru, da nima na huta da ɗauko min maganar da ku ke yi." Ƴar dariya suka yi dukkan su dan in da sabo sun saba da wannna maganar ta Didi. Shi kam ko motsin kirki bai yi ba balle yayi magana abinci kawai yake ci.
Da kansu suka kwashe mata kayan aka shiga dashi kitchen kafin su miƙe tsaye Goje ya ce, "Tiger zamu wuce." Shima tashi yayi suka fita gabaɗaya ta bisu da kallo tana yi musu fatan shiriya. Sallah i'sha tayi bayan ta idar ta kunna tv kasancewar suna da wutar solar, rana tsaka ta ga Omar da masu haɗawa aka haɗa a gidan. Da ta takura masa da tambayar inda samu kuɗi sai ya ce sadaka aka bashi. Ta kuma san gatse ya yi mata, kawai bazai faɗa bane shiyasa ta haƙura.
Babu jimawa ya shigo da sallama ta amsa ya samu waje ya zauna ta kalle shi ganin yayi shiru yana kallon hoton da yake kafe a falon. Hoton su ne shida ita da mahaifiyar su a ranar da ya cika kwana bakwai a duniya. Ganin abinda ya ke kallo ya saka ta kalle shi ta ce, "ko dan saboda ita nake so ka gyara rayuwarka ka koma mutum kamar kowa saboda tayi alfahari da kai a ranar tashin qiyama. Ko dan saboda Mama da Baba...." Kafin ta ƙarasa ya kalle ta ya ce, "iya Mmaan dai, ki cire na ƙarshen."
Da mamaki take kallon sa ta ce, "wai tsaya! Omar Baba ba shine ya haife ka? Meyasa baka so a dinga zancen sa kamar ba uban ka ba?."
"Bai cancanci na dinga tunawa dashi ba ko kaɗan."
"Mahaifin?."
"Shi fa" ya bata amsa kai tsaye.
"Me ya yi maka?."
"komai ma" ya bata amsa yana ɗora ƙafa kan ɗaya.
"Omar ko dan saboda ƙasa da ta rufe idanunsa ya kamata ka manta da abubuwa da suka wuce a baya. Kuma abinda ka ke fushi a kai baka san an yi ba labari aka baka, amma ka ara ka yafa." Ya sauke ajiyar zuciya bai yi magana ba, ganin hakan sai ta canja batun ta ce, "Baba Adamu ya yi min waya ɗazu yana tambayarka na ce baka nan."
"Waye haka?" Ya faɗa yana danna waya.
Ta sake kallon sa ta ce, "Baba Adamu fa nace maka." Ya kalle ta yana ɗaga yalwatacciyar gashin girarsa ya ce, "Shine nace waye haka?."
"Yayan mahaifiyarka." Ya girgiza kai ya ce, "ban san shi ba." Banza tayi masa bata sake magana ba dan in ta biye masa ranta ne zai zo ya ɓaci da irin waɗanan kalaman na sa marasa control. Jin ta yi shiru sai ya girgiza kansa ya ce, "ba dan ba dan ba ko....hmm." Jin abinda ya ce sai ta kalle shi suka haɗa ido ya ce, "bani da dangi a kaf duniyata, ke kaɗai ce dangina a kaf rayuwata."
"Hmmm Omar kenan!." Ta faɗa kawai bata tanka masa ba, in ta biye masa taurin kansa ɓacin rai zai jawo mata, shi kuma ko a jikinsa gaskiyar abinda yake zuciyarsa ya ke faɗa. Tv take tana kallon a lokacin aka hasko fuskar wacce ta kunna tv domin ta a daidai lokacin tana cewa, "Sunana Narma Sagir Sani wacce ku ka fi sani da Barr Nass."
Murmushi Didi tayi ta ce, "haka kawai Allah ya ɗora min soyayyar yarinyar nan a zuciyata. Bana kallon shirin nan amma saboda a shafin ta na instagram na ga ta ce yau za a saka interview ɗin da aka yi da ita ya saka na zauna." Kallon wacce take kallo yayi yana mamakin ko meye abin so a yarinyar nan da Yayarsa take son ta oho. Kallon sa tayi ta ce, "yarinyar nan bata burge ka?. Tana ƙoƙari wajan karɓar cases na ƙananun yara, sannan an ce bata taɓa yin rashin nasara ba a duk case ɗin da zata yi." Kallon tv ya yi ya kalli Didi ya ce, "Tunda ke tayi miki shikenan ai."
Dariya tayi ta dafa kafaɗar sa ta ce, "ɗazu da safe da baka nan Oga Mansur ya sake zuwa gidan nan. Don Allah Omar ka daure ka koma harkar aikin kayan nan, aikin ya karɓe ka kana da nasibi sosai akai meyasa baza ka dogara da kanka ba?."
"Bayan Allah akwai wanda na dogara dashi ne?" Ya tambaya ba tare da ya kalle ta ba. Ta girgiza kai ta ce, "Babu, amma in da sana'ar aikin yin takalman nan ka ke yi sai an fi ganin girmanka da martabarka, saboda kowa ya san harkar sa'anarka ka ke yi babu mai yi maka wata magana ta banza. Aikin ya karɓe ka, ka iya fiye da tunanin mai tunani, meyasa ba zaka riƙe iyawar ka ba?."
"Ni da ba sarki ko gwamna ba martaba da girman me zan nema? Tunda ina girmama kaina hakan ya ishe ni. Kuma ko a yanzu babu wanda ya isa ya yi min maganar banza, ai na wuce a kalli idona a yi min maganar da bata kwanta min ba. Ai ko kura ta rame ta wuce rainin karnuka, kuma duk lalacewar giwa ai tafi ƙarfin suya, balle giwar da lafiyar ta babu abinda ya same ta." Zata sake magana ya ce, "Didi zaki ɓata bakin ki ne kawai, na wuce zama a ƙarƙashin wani, in zan yi sai dai nawa na kaina."
Ta girgiza kai ta ce, "Tunda kai ba kowa bane zama a ƙasan wani ya zamar maka dole, kuma waɗanda ka ke so ka bawa haushi a rayuwa baza ka taɓa ɓata musu rai da ɗaukar wuƙa ko adda da zaman prison ba. Murna ma zasu yi in suna ganin har yanzu kana cikin wannan ƙasƙantacciyar rayuwar. Amma in ka gyara rayuwarka ka koma makaranta, Allah ya ɗaukaka duk mai son ganin ka wulanƙanta a wannan gaɓar ne zai ji haushi." Kallon idanun ta yayi na wani lokaci sai kuma yayi murmushi wanda fararen haƙoransa da suke a jere reras suka bayyana ya ce, "Didi baza ki gane ba."
Kallon sa take yi ta ce,"Kar na gane Omar, Sai aukin iya karin magana kamar goyan Kaka." Murmushi ya sake yi ta sake kallon sa ta ce, "Murmushi yana sake fito da asalin kyaun ka Omar, Meyasa baka son yin murmushi sai wa ni kawai?."
"Ba kowa ya cancanci ya gani ba."
"Sai ni sai matarka?." Kallon ta ya yi jin kalmar mata da ta saka, ya ɗan sosa walwatacciyar girar sa kamar yadda ta zama al'adar sa na ɗora yatsu biyu akan goshin sa ya ɗan murza kaɗan amma bai ce komai ba.
Didi ta ce, "Hmm! Zan ga matar da zaka aura dai Omar."
"Au za a samu wacce zata aure ni?." Ta wara ido da mamakin kalaman sa ta ce, "Meyasa ka ce haka?."
"Haka nan" ya bata amsa a taƙaice.
"Za a samu mana Omar. Shiyasa nake so ka ajjiye wannan ɗabi'ar ta ka, in kana a haka ba ko wanne uba ne zai baka auren ƴar sa ba." Ya taɓe baki ya ce, "nima ba a wajan ko wanne uba zan nemi aure ba." Murmushi ta sake yi jin abinda ya ce dan kuwa ba a kayar dashi a bada amsa. Bata sake cewa komai ba sai sauraron muryar Narma da ake hira da ita akan yadda take gabatar da aikin ta da sauran rayuwar ta.
"Gobe zan je Abuja." Kallon sa tayi jin abinda ya ce ta ce, "Abuja? Me ake yi?." Ya ɗora ƙafa kan ɗaya wani baƙin zare da yake ɗaure a ƙafarsa ya bayyana, yana ɗaure a tsintsiyar ƙafarsa kamar sarƙar ƙafa ta mata. Ya yi masa kyau sosai ya haska farar ƙafarsa matuƙa. Ya ce, "aiki." Didi ta ce, "wanne irin aiki ne haka? Wai me yake kai ka Abuja akai akai haka Omar?. A mota zaka je ko a jirgi?."
"Hmmm Didi kenan" ya faɗa yana ƴar ƙaramar dariya kana ya ce, "ai na wuce zuwa Abuja a mota tun tuni." Ta fuskance shi sosai ta ce, "Omar me yake kai ka Abuja haka? Daga fitowar ka daga prison ka je Abuja sau uku kenan. Me ka ke yi a can?."
"Aiki ne yake kai ni."
"Wanne irin aiki?" Ta faɗa tana yi masa kallon tuhuma kafin ya yi magana ta ce, "yaushe ka fara aiki babu labari? Yaushe ka fara ɓoye min abu?."
Shiru yayi bai amsa mata ba ta ce, "Omar da kai nake fa, yaushe ka fara aiki babu labari sannan wanne irin aiki ne haka?." Kallon ta yayi ta ƙasan ido ya ce, "kin san ni ba ɗan kidnapping ba ne ba ko?."
"Nima ban ce ba, amma me yake kai ka Abuja haka?."
"Aiki ne yake kai ni can Didi." Wayarsa da take ƙara ya saka bata sake magana ba shi kuma ya miƙe ya fita. Mamaki take yi wanne irin aiki ne ya kai shi Abuja haka? Anya babu abinda yake ɓoye mata game da rayuwar sa?. Babu mai bata amsa sai shi ta kuma san babu lallai ya amsa mata.
Bai jima ba ya dawo ya koma inda ya tashi ta ce, "tunda baza ka faɗa min ba kaje ka kulle mana gidan kar a shigo mana." Kallon ta ya yi a kaikaice ya ce, "ai ko shekara gidan nan zai yi a buɗe babu halittar da zata iya shigowa da niyar cutarwa. Ko aljani sai dai wani gidan ba dai wannan ba."
"Har da aljanu a masu tsoron na ka kenan?."
"Hmmm!" Shine abinda ya furta kawai yana ɗan sakin fuskar sa kaɗan.
"Ko bara almajiri baya shigowa saboda kawai ana jin tsoronka, ni dai ina nan ina yi maka addu'ar canji daga wajan Allah, wannan ɗabi'a har ina? In sha Allah canji yana nan zuwa rayuwarka. Ina yi maka fatan ka amsa kiran ƙaddararka da kuma rabo. Maƙota babu mai shigo min saboda kai, kowa tsoron ka yake ji."
Bai ce komai ba yayi shiru muryar Narma na tashi a falon hakan ya saka ya sake kallon Tv kafin ya yi tsaki ya ɗauka kansa zuciyarsa na wani tunani daban.
Babban burinsa a rayuwa bai wuce Didi tayi aure ba, amma auren ya gagara saboda baƙin fentin da yake ganin mahaifin su ya shafa musu. Shekarar ta talatin biyar amma bata taɓa aure ba, da an fara batun auren sai ya lalace, ya rasa meye dalilin hakan. Shi ba ya hango lamarinsa yana daga cikin dalilin da ya hana Didi aure, kawai abinda yake hange daban kuma ya tabbatarwa kansa da shine silar da ya hana Yayar sa yin aure.
Numfashi ya sauke da ƙarfi hakan ya saka ta kalle shi ta ce, "ka je ka kwanta, Nima gobe ina da aiki zan yi jollop rice ta mutane ɗari, bacci zan yi." Tashi tayi ta barshi a falon ta shiga ɗaya daga cikin daƙuna da yake falon guda biyu.
Tana shiga ta tsaya a jikin ƙofa tana goge idanunta cikin tausayin ƙanınta da ita kanta, Tabbas mahaifin su shine silar