Showing 66001 words to 69000 words out of 87436 words

Chapter 23 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

ya ce, "Yanzu ki shirya ki tafi kasuwar ki yiwa Hajja da Salma siyayya, ko baza ki basu tsaraba ba?."

Sai tayi murmushi ta ce, "zan basu." Ya yi murmushi ya ce, "to maza riƙe twnity ɗinki ku tafi kasuwar." Ta ɗaga kai Abiy ya ce, "ki saki ranki bana son wannan ɗabi'ar da kika ɗauko kin ji." Tayi murmushi ta ce, "To Abiy." Ta kalli Jidda da take kallon ta ta ce, "Twiny mu je?." Jidda ta ce, "Zo mu je ɗaki ɗauko kuɗi sai mu je." Tare suka fita zuwa ɗakin su dan nan wajan Abiy ne, ɗakin suka shiga basu jima ba suka fita. Sai da suka je reception na hotel ɗin sannan Jidda ta riƙe hannu Nayla ta ce, "Twiny."

Nayla ta kalle ta dan ta san daman sai ta tambaye ta, in akwai wanda ya san halinta a gidan su to Jidda ce. Jidda ta ce, "Twiny kin san dai ban yarda da abinda ki ka cewa Abiy ba ko? Ai ba yau kika sana mafarkin Umma ba, Meyasa baki taɓa shiga damuwa ba sai a wannan lokacin?." Nayla ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Jidda ta ce, "Twiny ki faɗa min damuwar ki don Allah."

Nayla ta fashe da kuka ta rungume Jidda tana kuka sosai. Jidda ta riƙe ta tana shafa bayanta a hankali dan ta san ƴar uwarta ta tana da babbar damuwa. Sai da ta bari ta gama kukan sannan ta ɗago tagoge idanun ta ta ce, "mu je mall mu dawo." A haka suka tafi dukka su babu mai walwala a tare dashi, sun jima sosai duk da basu yi wata siyayya ba, sai dan kawai kasuwar da nisa  inda suke.

Ɗakin su ita da Jidda ne kawai sai matar Yaya Anty Halisa dan Jidda babu mijinta suka zo. Da suka dawo Anty Halisa bata nan hakan ya saka Jidda cire mayafi ta zauna kusa da Nayla. Kallon ta tayi sosai ta ce, "Faɗa min damuwarki." Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, "Twiny wani ne." Jidda ta ce, "me wanin ya yi miki?." Tayi shiru bata ce komai ba. Jidda ta ce, "kin faɗa soyayya ko?."

Nayla ta kalle ta sai hawaye ya sakko mata, Jidda ta riƙe hannunta ta ce, "tun a Kaduna naga yanayinki ya yi min kama da wacce ta fara soyayya, kuma na tabbatar a Kano ki ka yi gamo da ƙaddararki. Waye shi? Ya san kina sonsa?."

Kai ta girgiza tana kuka ta ce, "ban san sonsa nake yi ba Twiny, da na san zan fara sonsa da ban je Kano ba, da na yi zamana tare da Mama da Abiy a gida, wallahi da bazan je ba." Jidda ta ce, "ƙaddarar kenan ai. Kuma ita soyayya ai ba kai make sakawa kanka ita ba, Allah ne, kuma yin kanta take yi a zuciyar ɗan adam."

Nayla kuka take yi sosai tana cewa, "ban san ya zanyi ba, kullum cikin kewar ganinsa nake, kullum cikin son jin muryarsa nake amma ko number wayar sa bani da ita Twiny. Meyasa soyayya zata yi min haka? Meyasa zan fara son wanda bani da tabbaci akan zai so ni?. Twiny ko kallo ban ishe shi ba, hasalima maganar minti ɗaya bata taɓa haɗa mu dashi."

Jidda cikin sanyi ta ce, "Waye shi?." Ɗagowa tayi daga jikin Jidda ta ce, "Ki yi haƙuri Twinny, zan faɗa miki amma ba yanzu ba." Jidda ta ce, "kina addu'a?."
"Ina yi sosai."
"Ki sake dagewa kina faɗawa Allah damuwarki, in ba alkhairi bane Allah ya cire shi daga rayuwarki, in kuma alkhairi ne Allah ya daidai ku."

Da jajayen idanun ta ce, "gwara na yi addu'ar Allah ya cire min shi ɗin, dan ko yana sona bana tunanin Abiy zai amince."
"Me zai hana ya amince?." Nayla ta girgiza kai tana aiyana dan bata san waye bane shiyasa take faɗar haka.

Jidda ta ce, "yanzu dai tashi mu je mu shiga mataf ki sake faɗawa Allah damuwarki, zama bai kama mu ba ai Twiny." Nayla ta miƙe tsaye Jidda ma ta miƙe sai Nayla ta ce, "yau ban ji kina waya da Baby ba." Jidda tayi murmushi ta ce, "yana can Kano yana neman gida, ya dage sai unguwa ɗaya yake so kuma gidan sai wanda ya yi masa wai ai kuɗinsa ne, siya zai yi ba haya ba." Nayla tayi dariya ta shiga tayi alwala Jidda ma tayi suka fita zuwa masallaci.

        A ɓangaren Abiy bayan fitar su Nayla kowa ya fita ya zama daga shi sai Mama ya yi shiru bai ce komai ba. Mama cikin ƙarfin hali ta ce, "ka yarda da abinda Nayla ta ce maka?."

Abiy ya kalle ta ya ce, "koda abinda ta faɗa yana damunta to tabbas akwai wani abun da yake damunta bayan wannan." Mama tayi murmushi ta ce, "ka fahimta kenan, nima na ga haka a tare da ita sosai."
"Amma me kike gani yana damunta?."
"To in na faɗa sai ka ce ba haka ba, gwara nayi shiru kawai." Abiy ya ce, "kina nufin Hajja?."

Kafin Mama tayi magana ya ce, "kinga mu bar zancen nan, domin bazan amince son zaman Kano ne ya mayar da Mamana haka ba. Akwai dai abinda yake damunta amma ba wannan ba." Mama ta yi shiru kawai bata ce komai ba amma ya zama dole ya nemo damuwar Nayla ko dan ta san meye in zata amfane ta tayi amfani da ita.


••••••••

Narma gabaɗaya ta susuce soyayya tayi mata mugun kamun da bata yi tunani ba, ta koma wani iri ko yaushe cikin tunani take da faɗuwar gaba. Yanzu gashi in ta kira Omar ɗin ma baya ɗauka, gabaɗaya sai ta sake shiga damuwa ta yi wani iri kamar ba ita ba.

Iyayenta duk sun lura da yanayin ta ranar Mum tayi nufin sake tambayarta. Ɗakin ta ta shiga ta same ta tayi tagumi ta zauna a gefen ta ta ce, "Narma." Narma ta kalli Mum ta ce, "faɗa min abinda yake damun ki kika zama haka." Narma ta ce, "Mum nima ban sani ba, amma Ina sonsa sosai Mum, Ina ji in ban aure shi ba zan iya mutuwa." Mum ta riƙe fuskar ta tace, "Waye shi? A Ina yake?."

Narma ta ce, "A Kano yake, kuma yanzu na samu labarin baya jin daɗi Ina so naje na duba shi Mum." Mum ta bita da kallo mamaki ta ce, "anya shima yana sonki kuwa?."
"Yana sona sosai Mum, yana sona. Tunda Dad baya nan gobe da safe zan je Kano zuwa jibi sai na dawo kin ji Mum?." Mum ta bita da kallo cikin tausayin yanayin da take ciki ta ce, "is okay, sai Najwa ta rakaki."

"No Mum bana so kowa ya ganshi mamaki nake so na baku, ni kaɗai zan je." Mum ta ce, "shikenan dai. Amma jibi zaki dawo da safe, kuma ban amince da wannan Tiger ɗin matsayin driver ba. Ki kira drivern Kano su zo su ɗauke ki ki gama abinda zaki yi ki dawo kin gane?." Jin abinda Mum ta ce sai gabanta ya faɗi, amma da yake an barta zuwa Kano bata damu ba ta amince da hakan.

"Kar ki damu Daughter, zaki auri wanda ki ke so kin ji?." Kai ta ɗaga cikin farin ciki Mum tayi hugging ɗinta tana rarrashi kafin ta fita barta. Narma tana fita ta tashi ta kalli kanta a madubi tana so ta gane itace ko kuwa ba ita bace, domin ta san ta canja, halayya ta da kamanninta duk sun canja saboda Omar. Mamaki take yi wai daman zata iya fara soyayya da wanda bai ma san tana yi ba? Soyayyar ma kuma da mutum irin Omar. Itace fa Narma da maza suke so ta yi musu replying message balle kuma ta yi magana dasu, amma ga Omar ya haukata ta lokaci ɗaya ta fita daga hankalin ta.


Ajiyar zuciya ta yi ta lumshe ido tayi tana sake buɗe ido a bayyane ta ce, "Faruk gani nan zuwa."

        Washe gari.

Jirgin ƙarfe takwas ta hau dan haka da wuri ta shiga kano, tana fitowa taga Yahya wanda ya san da zuwan ta tun a daren jiyaa. Gida aka kai ta daƙyar ta iya haƙura aka yi sallar azahar ta hau mota ta nufi gidan Didi kai tsaye. Sai da taje ƙofar gidan sannan ta kira Omar a waya.

A lokacin yana kwance a ɗaki abubuwa sun yi masa yawa, ya kasa gane abinda ya damunsa gabaɗaya wani irin yanayi ya damu zuciyar shi da gangar jikinsa.

Kiran ta ya shigo wayarsa ya kalli wayar, bai yi saving ba amma ya gama haddace ƙarshen number ta ko dan kiransa da take yawan yi a kwanakin nan ne bai sani ba. Kai ya dafe bai ɗauka ba yana kallo har ta katse, wani kiran ya sake shigowa kamar bazai ɗauka ba sai ya ɗauka.

Narma da ta fara kuka yana ɗauka ta ce, "Faruk Ina ƙofar gidan ku." Da hanzari ya miƙe zaune ya ce, " ki ka ce?."
"Uhum, Ina ƙofar gidan ku."
"Me kika zo yi gidan mu?."
"Ina kiran ka baka ɗauka shiyasa nazo." Kasa magana ya yi ya tashi ya fita ya kuwa hango motar ta a ajjiye a gefe, ganin sa sai ta buɗe motar ta fito.

Kallon ta ya yi itama shi take kallo ta ɗauki wayar hannunta sake kiransa ya ɗauka ta ce, "na ƙaraso ko zaka zo mota mu yi magana?." Omar yace, "meyasa kika zo?." Narma tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Da yake yana kallon ta tana kallonsa sai ya ce, "ki koma gida zan zo."
"Na san ba zuwa zaka yi ba" ta faɗa tana yanke wayar ta nufo gidan, yana kallon ta tana tahowa zuciyar sa cike da tsoro da kuma tsantsar mamakin zuwan ta gare shi.

Sai da ta shigo gidan sannan ta zuba masa ido tana kallon sa ko kofta ido bata yi. Numfashi ta sauke ta kawar da kai gefe tana jin haushin zuciyarta da ta saka ta fara son wannan mutum mai shegen shariya da nuna ko in kula kamar sa.

Narma ta kalli gidan ta ce, "Sister fa?."
"Bata nan" ya bata amsa babu ɓata lokaci dan ya ƙagu ya ji abinda tazo dashi. Tayi shiru bata ce komai ba, hakan ya saka ya ce, "Ina jinki, me ya kawo ki Kano har kika zo nan?. Kar ki ɓata min lokaci ki faɗi abinda yake ranki."

"Babu abinda ya kawo ni Kano, na zo Kano saboda kai kuma saboda kai zan koma." Narma ta gyara tsayuwa tana kallonsa ta ce, "ban san me zan ce maka ba, ban iya ɓoye-ɓoye ba haka zalika ban san wani abu tsoro ba indai a kan abinda yake zuciyata ne. Abinda na sani kawai Ina sonka Faruk! Ina sonka so na Aure!."

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 20.*


Wani irin dumm Omar yaji a zuciyarsa, ya zubawa fuskarta ido yana kallo ba cikin mamakin da ya gama ɗaure masa jiki. Ya kasa motsi sai kallon idanunta da yake yi kamar yadda take kallon sa. Narma tayi murmushi tare da hawaye ta ce, "kayi mamaki ko?." Sai ta girgiza kai ta ce, "nima kwana nake Ina mamaki, kwana nake Ina tambayar kaina Narma ta ya hakan ya faru. Kullum tambayar kaina nake yi Narma meyasa ki ka shiga wannan rayuwar, meyasa ki ka fara son wanda bai damu dake ba. Da wannan tunani nake kwana nake tashi tunda na bar garin nan har yau da nake tsaye a gabanka."


Narma ta ce, "Ina sonka, Ina sonka!. Ban san me zan ce maka ka yarda ba amma abinda nake ji a raina kawai Ina so nayi rayuwa da kai a matsayin mijina, ban damu da abinda zai biyo baya ba, ina so na rayuwa da kai daga nan har a tashi duniya. Ban damu da abinda kowa zai ce ba, kawai Ina so na dinga duba gefena na ganka a tare dani ko yaushe, ban damu da kowa ba, ban damu da komai ba. Da zuciyata kawai na damu, abinda yake cikinta kuma soyayyar ka ce, Ina son ka!" Ta faɗa tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta.

Kai ta girgiza tace, "ba wasa nake yi ba wallahi, zan iya aurenka na zauna da kai a ko wanne yanayi. Please Faruk! ka amince dani as your life partner, wallahi ina sonka!" Abinda take faɗa kenan kamar zata zubar da hawaye. Bai yi zato ba, bai yi tsammani ba, ya tafi duniyar tunani kawai yaji ta kwanta a jikinsa ta rungume shi sosai tana kuka.

"Innalillahi!" Ya furta a bayyana yana riƙe hannayenta ya janye ta daga jikinsa ya ce, "Narma!."  Kallon sa tayi karo na farko da ya kira sunan ta, bata ɗauka ya san sunanta ma tunda bata taɓa ji ya faɗa ba sai yanzu. Hasalima bashi da sunan da yake faɗa mata tunda ba magana yake yi mata ba.

Ganin irin kallon da yake mata ya yi kama da na fushi da fusata sai jikinta ya yi sanyi. A kausahe Omar ya ce, "Ki bar wannan abin da kike yi, Ko da wasa kar ki sake kuskuren cewa zaki riƙe ni, bana son wannna shirmen kin fahimta!?" Ya faɗa a fusace yana nuna ta da yatsa. Kai ta girgiza ta ce, "I'm sorry!."

Omar ya ce, "Sannan ki koma gida, ki bar cikin gidan nan yanzu. Abinda ki ke so baza ki same shi daga gare ni ba." Narma ta narke fuska ta ce, "Kana nufin baza ka iya sona ba?." Ya ɗaga mata kai alamun eh kana ya ce, "in ma wasan kwaikwayo kika shirya ki dakatar dashi bazai yi tasiri a kaina ba. Kar ki sake zuwa cikin gidan nan ba tare da kin sanar dani ba, bana so na sake ganinki, ki fita daga gidan nan kafin na nuna miki asalin waye ni."

Kallon sa kawai Narma take yi jin yana ambatar wasan kwaikwayo, yanzu kenan soyayyar da take yi amsa ce ya ɗauka wasan kwaikwayo ko bayyana masa ɗin da tayi ne ya zama wasan kwaikwayo?.

Narma murya na cracking ta ce, "Wallahi Ina sonka, wallahi i'm ready to marry you. Ban damu da abinda zai biyo baya ba indai zan samu cikar burina na amince zan zauna da kai a ko wannan yanayi."

Kuka take yi mara sauti duk sai ta sake dagula masa lissafi, shi bai san da wacce makama zai ɗauki maganarta ba dan shi gani yake kamar akwai abinda ta shirya shiyasa ta zo masa da wannan maganar. In ba haka ba kai tsaye tazo ta furta tana son shi kamar ba mace ba? Macen ma irin ta mai aji da kuɗi da mulki na siyasa? Ta ya zai amince da wannan tatsuniyar mai kama da wasan yara?. Kuma shi wata mace bata taɓa kallon sa ta furta masa wannan kalma ba, bai taɓa tsayawa da wata mace na adadin mintinan da yake tsaye da Narma ba. Shifa Didi kawai ya sani, itace komai na sa, Bai taɓa alaƙantuwa da ko wacce mace ba in ba ita ba. Shiyasa yake jin kansa uncomfortable saboda ita ce mace ta biyu a rayuwarsa da ya samu kusanci da ita, da ita ya taɓa haɗa jiki, da ita ya taɓa tsayawa suna doguwar magana, da ita ya fara zama waje ɗaya shida mace, itace ta fara furta masa kalmar so a rayuwarsa. Jin kansa yake yi yayi nauyi, nauyi yake a zuciyarsa dan yanayin ya zama baƙo a gare shi.

Da wannan tunanin ya ce, "kina ji.....!" Baya tayi tana kuka kamar wacce ta rasa hankalinta ta ce, "ba wasa nake maka ba, ba ƙarya nake maka ba, ba yaudararka nake ba, ba plan na shirya maka ba. Wallahi Ina sonka da gaske ba da wasa nake ba. Dama ana cire zuciya da na cire zuciyata na nuna maka abinda nake ji a kan ka. From the moment i saw you in our house fell in love with you, saboda zuciyata bugawa ta dinga yi da na ganka, na ɗauka kwarjini kayi min a lokacin, amma a yanzu na fahimci sonka nake yi. I'm not joking about my feeling, it's not a game or drama or whatever you think about it. I truly love you" ta haɗe hannayenta waje ɗaya ta ce, "Please believe me" ta faɗa tana zubewa a wajan tana kuka sosai.

Kama ƙugu Omar ya yi yana kallon ta, wai shi Omar wata mace take ɗuke a gabansa take kuka da sunan tana sonsa. Ya kasa banbance yanayin da yake ciki, tausayinta yake ji ko haushi take bashi shi kam bai sani ba. Bugawar zuciyarsa yake ji na tausayinta ne ko na meye dai shima ba sani ba.

Ba ya so Didi ta dawo ta tarar da ita a wannan yanayi, hakan ya ya buɗe baki zai yi magana amma ya kasa. Shi bai san ya ake rarrashin mace ba har ta daina kuka, bai taɓa ganin kukan mace a gaban idanun kamar haka ba sai a wannan lokacin, bai san ta ya zai fara ba kwata-kwata. Ya sake kallon ta ya ce, "ki bar kuka ki tashi daga wajan nan."

Bata daina kukan ba amma ta miƙe tsaye ya ce, "na ce ki bar yi min kuka bana so!" Ya faɗa cikin tsawa kaɗan wacce ta sakata haɗɗiye kukan nata. Ya kalle ta ya ce, "Yanzu ki je gida zan zo zamu yi magana anjima."

A sanyaye ta ce, "ka tabbatar zaka zo?." Ya ɗaga mata kai alamun eh. Ta kalle shi ta ce, "in ma baka zo ba zan dawo, Ina so naji amsar ka akan abinda na faɗa maka. Bazan koma Abuja ba sai na ji amsar ka." Bai ce komai ba sai cize bakinsa da ya yi, ya kalli fuskarta ya ga ta koma ja sannan da gaske ta ɗan rame kaɗan.

Wuce shi tazo yi ta sake kallon shi ya ce, "Faruk ka kawar da duk tunanin da ka ke yi a kaina, da gaske nake Ina sonka." Kulle ido ya yi ya buɗe sai yaga ta bar wajan da alama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login