Showing 69001 words to 72000 words out of 87436 words
Chapter 24 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt
ta fita. Ƙarasowa ya yi ya ganta ta fita a guje ta ƙarasa mota ta shiga ta ja motar da ƙarfin gaske.
"Wai ni za a yaudara" ya faɗa a bayyane bayan motar ta fice daga layin. Sai kuma kalamanta suka dinga dawo masa cikin kansa ya kulle ido ya ce, "ni dai ba sonta nake yi ba, kawai na kasa mantawa da tunanin ta ne. Wannan film ɗin da tazo ta shirya kuma duk zai ƙare."
"Kai kuma kai da wa ka ke magana kai kaɗai?"Didi ta faɗa tana shigowa gidan.
Da sauri ya buɗe ido ya kalle ta ya daidaita nutsuwarsa kana ya ce, "kin dawo?."
"Eh na dawo" ta bashi amsa tana wucewa bata ce masa komai ba. Daɗi yaji da ta bata tarar da Narma ba da bai san me zai ce mata ba.
Bai shiga inda take ba ya koma ɗaki yana tunani kala-kala akan abubuwan da suka faru wanda yake kallon sa kamar a mafarki, tsaki ya yi kawai cikin tunanin da ya rasa wanne zai kama ya yi.
Didi bata sake ganin sa ba sai bayan sallar magriba ya shigo cikin gidan. Duk da yadda yaso ɓoye abinda yake ransa sai da Didi ta fahimta. Ta kalle shi sosai ta ce, "lafiya ka ke kuwa?." Ya girgiza kai ya ce, "lafiya lau." Bata ce komai ba ya zauna yana kallon ta yana ji kamar ya faɗa mata yaji me zata ce, amma kuma yana ji kamar ba sai ya faɗa mata ba yaudara ce kawai ake so a shirya masa.
Didi ganin yana kallon ta kuma bai yi magana ba sai ta ce, "ya dai?." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Didi a misali namiji kamar ni wacce irin mace ce zata iya cewa tana sonsa?." Didi da mamaki ta ce, "kamar ya kenan?."
"Ina nufin ko wacce mace ma zata iya son namiji kamar ni?." Didi ta ce, "ita soyayya ai baka sanin lokacin da ka ke fara ta Omar. A yadda ka ke a haka in ƙaddarar soyayya ta gifta sai ka fara son ƴar gwamnan garin, kuma so bana wasa ba na gasken gaske, kuma dai kaga a zahiri ka san tafi ƙarfinka amma soyayya bata duba wannan Omar. Ko kuma ita ƴar gwamna ta fara sonka so mai tsananin gaske, so na gaskiya ba wai na wasa ba, saboda ba ita ta yi sonka a zuciyarta ba Allah ne da kuma taimakon zuciya. To soyayyar ce yanzu duk ta gaskiya ta gushe sai dai sama-sama, kafin a samu soyayyar gaskiya a yanzu an samu ta ƙarya sau dubu, kuma da yawa yaran manyan mutane yanzu ƙwarya tabi ƙwarya ake yi, me ka kai me za a kawo maka. A dah dai ɗan mai kuɗi ya auri ƴar talaka, ƴar mai kuɗi ta auri talaka kuma an zauna lafiya. Amma yanzu wannan zamani ya gushe Omar."
Yayi shiru jin kalaman Didi sai ya kalle ta ya ce, "misali ace ƴar mai kuɗin unguwar nan ta ce tana sona zaki amince da gaske takr?." Didi ta yi dariya ganin da gaske yake maganar sai bata saka wasa a ciki ba ta ce, "zan amince mana Omar, ai ba ita ta halicci kanta ba, kuma ba ita ta saka son naka a zuciyarta ba, babu yadda Allah baya tsarawa ɗan adam ƙaddara da rabonsa. Allah ne ya kaddara hakan kuma babu wanda ya isa ya canja faruwar sa. Kuma da yawa in yaran masu kuɗi mata suka fara soyayya da wanda bai kai matsayin su ba yawanci soyayyar gaskiya ce, saboda mata rauni gare su, soyayya tana saurin kama zuciyarsu."
Shiru ya yi kawai bai ce komai ba yana tunanin kenan dai da gaske Narma zata iya fara sonsa ko dai hasashen Didi ne kawai?.
Didi ta ce, "kai dai ka bar so kawai Omar, nima ba wai sanin soyayyar na yi ba, amma so babban abu ne. Kai ta addu'a Allah kar ya ɗora maka son wacce tafi ƙarfinka, daga lokacin da ka fara son wacca tafi ƙarfinka daga lokacin zaka san meye azabar so. So ai mugun abu ne wani lokacin."
"Ni ai Didi na faɗa miki bana tunanin akwai wacce tafi ƙarfina a duniya, in har akwai ɗin sai dai in bata sona." Didi tayi dariya tana jinjina maganar sa ta ce, "ko tana son naka iyaye da ƴan uwa sai sun dakusar da soyayyar."
Ya yi shiru bai ce komai ba yana ɗan girgiza kai ba dan ya yarda ba. Disi ta ce, "wai me ya kawo wannan maganar ma yau?."
"Zan faɗa miki" ya fɗa yana tashi ya fita ya barta da tunani dalilin yin wannan maganar, ita da ta san baya magana akan soyayya, ko akan mace baya magana balle irin wannan ta soyayya. Ko tsokanarsa ta yi wani lokacin ko tanka mata baya yi, amma tunda ta ji ya yi wannan maganar tabbas akwai dalili.
Yana fita yaga message ɗin Narma ta rubuta, _Daman na san baza ka zo ba, in na rasa raina kaine sila Faruk! Da Ina da iko da na cire son da make maka tuni na ajjiye shia a gefe. Amma babu komai na gode._
Sai yaji wani irin abu ya tsirga masa mai kama da tausayi sosai, ya sauke ajiyar zuciya yana jin zuciyarsa na bugawa sosai cikin rashin sanin dalili. Shi dai bazai je inda Narma take ba gaskiya, in ya je dagula masa lissafi zata yi ya rasa abinda zai ce mata gwara ya ƙyale ta in ta gaji ta koma gida.
"Kenan in da gaske so na take su masu kuɗi babu ruwan su da cewa in mace ta fara cewa tana son namiji zubar da aji ne? Tunda gashi tun daga Abuja ta ɗauko ƙafa tazo Kano saboda ta furta min tana sona. In kuma yaudarata take yi ta taro match wallahi, za tayi dana sanin aikata abinda ta aikata. Amma taya zan gane soyayyar gaskiya ce ko ta ƙarya?." Shafa kansa yake yi ya kasa gane inda zai kama dan ya kamo bakin zaren.
"To wai ni me nake ji a kanta?" Ya faɗa yana shafa ƙirjinsa daidai inda zuciyar take, yana jin wani irin abu yana fizgarsa daga ta ciki. Da wannan tunanin ya kwanta yana ta juyi ya rasa abinda yake damun sa.
Narma yanayin ta babu daɗi, raba dare tayi tana kuka zuciyarta ma bata shawara kala-kala, har shawarar kashe kanta tayi ta fasa, tayi shawarar fita taje gidan su Omar ta kasa. Ta jima tana kuka daƙyar ta samu bacci ya ɗauke ta.
Ya jima yana bacci har goma na safe sannan ya tashi, bai fito ba sai da ya yi wanka jikinsa duk a sanyaye yake ya rasa abinda ya kamata ace ya yi. Lokacin da ya shiga wajan Didi ta idar da sallar walha ta kalle shi ta ce, "yau ka sha bacci, da fari na ɗauka ka fita ashe kana nan." Ya girgiza kai ya ce, "na jima ban yi bacci ba ne jiya, daƙyar na iya tashi sallar asuba."
Didi ta ce, "ga idanunka nan har yanzu da sauran bacci. Ga abinci can in zaka ci." Ya girgiza kai ya ce, "bana son cin komai gaskiya."
Didi ta ce, "na lura gabaɗaya a sanyaye ka ke, me ya faru ka koma haka?." Ya bita da kallo yana tunani. Bashi da aboki a duniya sai ita, babu mai bashi shawara sai ita, babu wanda yake iya faɗawa damuwarsa sai ita, babu da wanda ya saba sai ita ɗin dai. Itace kawai mafitarsa, dole ya faɗa mata abinda yake faruwa ko zai samu wata makama a wajan ta.
Niyar zama yake yi aka shigo falon sai ya fasa zama yana kallon wacce ta shigo. Didi ta miƙe tsaye ganin wacce ta shigo cike da mamaki, shi kansa sai da gabansa ya faɗi balle Narma da take kallon sa. Didi ta ce, "Barr Nass."
Wajan Didi ta ƙarasa ta ce, "Sister laifi ne dan mace ta fara soyayya? Laifi ne dan ma fara son wani a lokacin da ban shirya ha? Laifi ne dan na fara son wani ba tare da na san hakan ba?."
Didi da mamaki take jin abinda take cewa ta girgiza mata kai ta ce, "A'a." Ta nuna mata Omar ta ce, "Amma Faruk ya kasa gane da gaske ina sonsa, wallahi sister daga Abuja na taho nan akwai dan na furta masa kalmar Ina sonsa. Ina sonsa da gaske, ki faɗa masa ba yaudararsa nake yi ba. In ya cigaba da tafiyar dani a haka a yadda nake jin sonsa zan iya mutuwa!" Ta ƙarasa faɗa a sanyaye tana kwantar da kanta a kafaɗar Didi.
Didi suman tsaye tayi tana jin sautin kukan Narma a kunnenta, tunani take yi wai ko dai mafarki take yi? Sai kuma taga ai ko a mafarki abinda take ji bai kamata ace yazo gare ta ba. Omar ɗin ta ake magana akai, kuma ƴar Senator ɗan takarar gwanma ce take wannan maganar. Tabbas wannan maganar indai ba mafarki bane to tabbas wasan kwaikwayo ne.
Bata iya bata amsa ba ta ji Narma ta ɗago daga jikin ta ta ce, "Sister bazan yi ƙarya dan na yaudare shi ba, ki kalli idona wallahi da gaske Ina son sa. Tun farkon ganina dashi na fara jin wani abun a kansa, da ya zo ɗauka na a Airport a nan na sake jin abinda naji. Da ya taimake ni a lokacin da aka ƙwace min waya a nan na tabbatar da ya shiga zuciyata. Ba wasa nake yi ba, ba yaudara na shirya ba, gaskiya nake faɗa Sister."
Shi dai Omar yana tsaye kaiwa bai fita ba kuma bak ce komai ba yana kallon ikon Allah. Didi sai a lokacin ta samu damar kallon Narma ta ce, "Wai Omar ɗina ki ke so?." Ta ɗaga mata kai alamun eh, Didi ta zuba mata ido kafin ta kalli Omar da yake kallon su sannan ta ce, "Narma kalaman naki ne kamar a mafarki, Omar ɗin ki ke so?" Ta faɗa tana sake nuna mata shi da yake tsaye.
Narma tayi murmushi ta lura sun kasa gane abinda yake ji a kansa, ta ce. "Shi nake so, saboda son da nake masa aka fasa maganar aurena da Ashraf ɗan gov katsina state, na faɗawa iyayena Ina da wanda nake so su bani lokaci, yanzu sun bani lokaci suma jira na kai musu shi matsayin wanda nake so. Wallahi a yadda nake ji bazan iya auren wani in ba shi ba, ki taimaka min, kece kawai hope ɗina Sister. Nazo har nan jiya na bayyana masa amma ya ce min A'a!."
"Tirƙashi!" Didi ta furta tana sake kallon Narma dan ta tabbatar a hankalin ta take, sannan ta kalli Omar da yake jin su bai ce komai ba.
Motsawa yayi zai fita Didi ta ce, "Ina zaka je?."
"In na tsaya me zan yi Didi? Me zan ce in na tsaya? Gwara na tafi" ya faɗa yana kallon ta.
Narma ta kalle shi ta ce, "kana ganin kamar wasa nake yi ko?" Sai tayi murmushi ta ce, "dole zaka ji haka saboda a saba namiji ne yake bayyana cewa yana son mace kafin ita tace, ni kuma sai gashi nice nazo ina yin abinda mazan ma baza su yi ba. Ni ban iya ɓoye abinda yake raina ba, in dai akwai zan faɗa ne kawai na huta. Kuma ban ɗauki dan nazo har gidan ku na ce ina sonka da wani abun ba, gaskiya na faɗa ba ƙarya ba. Amma wallahi ko dm namiji ya yi min a social media sai na shekara ban buɗe ba, namiji sai ya shekara biyu yana so nace masa hii amma ban ce ba. Duk wannan ajin da nake dashi soyayyarka ta kawar da ita Faruk!. Kuma har yanzu kace kana tantama? Didi kina ji fa" ta faɗa tana kallon Didi da take ganin abun kamar almara.
Didi ta ce, "Ko da gaske ki ke, ko da wasa kike Narma kin fi ƙarfinki ce kina son Omar, ke ba irin matan da ya kamata ace suna son Omar bace. Kuma amsar da ya baki ta a'a itace daidai Narma, dan ke ba daidai dashi bace, ki tuna matsayin ki dana mahaifinki."
Narma ta ce, "ni dai in har yana sona duk wannan ba damuwa ta bace, iyayena suna son duk abinda nake so, ko yanzu na kai musu shi nace shi nake so zasu yi maraba da zuwan sa. Kuma na sanar dasu ma fara sonsa kuma sun yi min fatan alkhairi." Didi ta ce, "Omar ɗin ki ka ce kin fara so?." Narma tayi murmushi ta ce, "Didi kema ɗauka ki ke ƙarya nake ko?."
"A'a Narma ban ce ba, amma maganar ce dole ta saka mana shakku a zuciyar mu."
Narma ta ce, "me zan yi da zai goge shakkun? Na shiga social media nayi video ce Ina sonsa? Ko gidan tv zan je ma bada labarin yadda ma fara son sa?. Ko kuma na sanar da iyayena su zo su nemana min auren sa?. Wanne zan yi da zai tabbatar da ba ƙarya nake ba?."
Didi ganin Narma ta gigice sai ta kwantar da murya ta ce, "Ki kwantar da hankalin ki Narma, yanayin matsayin da kike dashi ne dole ya saka mu tantama a kan ki."
"Shiyasa nace me zan yi ya goge?." Didi ta ce, "babu ko ɗaya da kika lissafa. Na amince da gaske kina son Omar so na gaskiya kuma so na aure."
Narma a sanyaye ta ce, "Amma shi ya ce ƙarya nake yi." Didi ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Narma ban san me zance miki ba a yanzu, amma ki koma gida zan yi ƙoƙari na shawo kansa ya faɗa min abinda yake ji ransa a kanki, in yana ji zai karɓi soyayyar ki shikenan, in baya ra'ayin hakan sai dai ki yi haƙuri."
Narma ta goge idon tana murmushi ta ce, "Hakan ma na gode. Amma Didi in kika samu labarin wani abu ya faru dani wallahi Faruk ne sila, soyayyarsa itace silar da zata jefa ni ko wanne irin yanayi. Yin acting ɗin ƙarya akan soyayya ba ajina bane, bazan taɓa iya furta ina son mutum ba indai ba da gaske nake ba Didi. Abu ɗaya kawai na sani, ina sonsa koda shi baya sona, zan rayu dashi koda baya sona."
Kallon Omar Narma tayi ta matso kusa dashi ta ce, "zan koma gida, zan je na samu likitoci naji zasu canja min zuciya. Indai zasu iya zan amince a cire tawa a saka min wata indai zan rabu da abinda nake ji. In kuma baza su iya ba ina tabbatar maka wani abun zai same ni akan abinda nake ji a kanka. Na tafi, amma ka sani zan dawo, zan dawo dan jin amsarka. Bazan iya rayuwa da wani in ba kai ba, bazan taɓa iya rabuwa da kai ba" ta faɗa tana ficewa a guje kamar walƙiya.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 21.*
Didi tana kallon ta har ta fice ta dafe ƙirji ta kalli Omar da yake tsaye har lokacin ta ce, "wai da gaske ba mafarki nake yi ba?." Ƙoƙarin fita ta ga yana yi ta ce, "Ina zaka je?" ya juyo yana kallon ta ta ce, "Dawo, ai fita bata kama ka ba Omar. Daman shine silar magangangun da kayi min jiya? Daman akan Narma ne Omar?."
Yana daga wajan da yake tsaye ya ce, "na rasa abinda zan ce ne Didi, ban san me zan yi ba, ban kuma san a wanne matsayi zan ajjiye hakan ba."
Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Omar ni na amince da gaske Narma tana sonka." Ya kalle ya ce, "ta ya kika tabbatar a lokaci ɗaya haka?."
"Kalamanta, yanayinta, matsayinta. Omar a matsayin da Narma take dashi a Nigeria baka kai matsayin wanda zata yiwa wasa da hankali ba, ko ta yaudare shi ba. Soyayya bata duba cancantar mutum ko kuɗi ko mulki, dan zuciyarta faɗa a soyayyarka abu ne mai sauƙi tunda ba itace tayi kanta ba. Mace kamar ta baro Abuja kawai saboda ta zo ta ce maka tana sonka daga ji ka san wannan abin ya kai zuciya."
Kallon Didi yake yi har ta gama magana kana ya ce, "in kuma film aka shirya fa? Ni Ina ganin kamar da wata manufa hakan ya faru. Ta ya za a ce lokaci ɗaya ta baro garin su tazo ta ce tana sona? Har yaushe ta sanni? Yaushe muka yi sabon da zata fara sona? Yaushe muka yi mu'amala tare da hakan zai faru?."
Didi ta murmusa ta kalle shi ta ce, "Wacce manufa kenan? Me ka ke dashi da Narma zata yaudare ka Omar? kai waye a Nigeria da za a yi amfani da ita wajan yaudararka?. Da gaske na san ana amfani da mace a yaudari mutum amma sai mutum ya kai inda ya kai ake aika masa haka. Allah na tuba kai wanne matakin rayuwa ka taka da za a yi amfani da ita a cuce ka? Ai in ma cutar taka za a yi sai dai ayi amfani da mata irin na lunguna ba dai ita ba."
Ganin ya yi shiru bai ce komai ba ta kuma cewa, "Zancen yaushe ta fara sonka duk daga baya ne, zuciya tana fara son wanda mutum bai taɓa gani ba, ana fara soyayya a iya jin murya kawai. Mace na fara son namiji in taji muryarsa a tv ko radio, haka namiji yana fara son mace in yaji muryar ta koda a hanya ne."
Shi Omar mamaki abin yake bashi shiyasa ya kasa magana, ya sake kallon ta ya ce, "wai da gaske yana faruwa a gaske ko sai a film? Ni ban amince da soyayyar ba, ban amince akwai wani abu soyayya a duniya ba. Ina jinta tamkar tatsuniya, ina jin labarin soyayya kamar iska da zata zo ta wuce ba tare da ka ganta ba, ina jin labarinta tamkar tafiyar ruwa. Ban amince akwai soyayya ba Didi, ni ban yarda akwai ta ba balle har na yarda da son da wata take min."
Didi