Showing 30001 words to 33000 words out of 87436 words
Chapter 11 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt
Ya ce a yi bincike akan rabuwarsu da matar indai akwai damuwa a kansa bazai sake zuwa ba. Ma'aikacin gwamnati ne a wata babbar ma'aikata."
Hajja ya ce, "Alhamdu lillah! In sha Allah komai ya zo ƙarshe. Ai dai ka miƙa lamarinka ga Allah baka da sauran damuwa, Zaɓi na gari Allah ya yi miki shiyasa ya jinkirta miki auren, ko bani da rai zaki ce na faɗa miki Aisha."
Didi ta ce, "Allah ya sa Hajja." Ta amsa da amin Didi ta ce, "Sai dai Omar nake ji, in ya san na kai batun nan wajan Kawu babu zaman lafiya. Ɗazu ma fa shine yazo waje na kawo min katin bikin Ramla ƴarsa shine Omar ya tarar dashi, Wannan tsinin ɓacin ran Nayla ta tarar."
Hajja tayi dariya ta ce, "yayi faɗansa ya gama dole sai an nemi maganatan ki a fannin aure, shi kansa da yake wannan abubuwan bara maganar auren na sa ta zo dole sai ya neme su. Babu mutumin kirkin da zai bashi auren ƴarsa ba tare da ya nemi danginsa ba."
"Hmmm! Ina jin wannan ranar a zuciyata Hajja, ranar da Omar zai je ya nemo dangin mu saboda batun aurensa. Allah Hajja gani nake akan Omar ya neme su zai iya fasa aure, zai iya zuwa ya nemi wacce ba zasu damu da danginsa ba ya aura."
Hajja tayi dariya ta ce, "haka ki ke gani, amma zai neme su da kansa. Ban da abin Omar tunda har suka fahimci a baya basu kyauta ba kuma suke ƙoƙarin gyara laifin su ai ya kamata ya yafe musu." Didi ta ce, "Omar da kafiya, taurin kai, zuciya, riƙo, zafin rai, zafin zuciya ai aminan juna ne, Allah kaɗai ya san yadda zamu kwashe dashi in yaji na tura shi wajan Kawu."
"To banda abin Omar in baki tura shi wajan Kawu ba wajan wa zaki tura shi?." Didi tayi dariya ta ce, "ya ce an faɗa min shi bai yi hankalin da zai bada aurena ba." Hajja tayi dariya sosai ta ce, "a shekaru dai yayi, amma ina hankalin da Ummaru zai bada aurenki?."
Didi tayi murmushi Hajja ta ce, "ki cigaba da yi masa addu'a, kamar uwa ki ke a wajansa, ki ta yi masa addu'a wata rana sai labari."
"In sha Allah Hajja, addu'akullum ana yi masa har taimakon malamai nake nema akansa, in sha Allah canji zai zo. Ba dan malam Salahudden ya rasu ba ai da shine maganin Omar, yana matuƙar girmama malamin." Hajja ta ce, "a yanzun ma zai dawo hankalinsa in sha Allah, nan gaba shima mu sha biki."
Didi ta ce, "wai! Omar da mata." Hajja ta ce, "ba abun mamaki bane, kuma cikin ikon Allah daƙyar in ba ta silar mace zai canja ba." Didi ta ce, "wai ta hanyar soyayya?."
"Kina ganin bazai yu ba ne?."
"A'a, amma lamarin ne akwai firgici, wacce yarinya ce zata so Omar a haka?. Ga halinsa na bayyane ga zafin zuciyar da yake da ita?."
Hajja ta ce, "kadai Allah ya bamu lafiya, Allah ya yafi gaban komai." Didi ta ce, "Haka ne Hajja. Bara na koma magriba tayi in Nayla ta zo a gaishe su" Hajja ya amsa tana sake yi mata addua'a tana amsawa ita kuma ta fita tana jin Hajja kamar mahaifiyar ta saboda kirki da karamcin ta.
Nayla sai bayan i’sha aka dawo dasu daga gidan ƙanwar mahaifiyarta ya wacce suke cewa Mama. Ɗanta mai suna Abbas shine ya dawo dasu har gida sannan suka shiga wajan Hajja tare. Yana yin sallama Hajja ta ce, “wa nake ganin kamar Abbas?.” Yayi dariya ya ce, “ni ne Hajiya Hajja, kin wuni lafiya?.”
“Lafiya lau mara kunya, baka zuwa ka gaida mutane sai dai in zaka kawo babbarka sannan ake ganinka, yanzu ma na san saboda Nayla ne ka shigo ko?.” Yayi ƴar dariya ya ce, “Haba Hajja, ni da nazo ki bani dambun nama sai ki fara ƙorafi?.”
Hajja ta ce, “nayi ɗin, baka zuwa gidan nan kai kwata-kwata sai da dalili.” Yayi murmushi ya kalli Nayla da take jona chaji kasancewaar an gyara musu wutar gidan. Hajja ta bishi da kallo tana kallon abinda yake kallo ta ce, “ya ƙannen naka da Yayar?.”
“Lafiya lau Hajja, kowa yana gaisheki.”
“Ina amsawa da kyau.” Daga nan suka yi shiru ya sake kallon Nayla da take aikinta ba ta shi yake yi ba.
Hajja ta ce, “Hauwa ga saƙo ki can Aisha ta kawo miki tun yamma.” Nayla ta kalli Hajja ta ce, “to.” Abbas ya miƙe ya ce, “Hajja ni zan koma, sai Allah ya dawo dani.”
“Allah ya kiyaye.” Ya kalli Nayla ta ya ce, “Hawwa zan tafi.” Ta kalle shi ta ce, “To Yaya Ab ka gaida gida.”
“Bazaki raka ni ba?.” Ta shagwaɓe fuska ta ce, “na gaji Yaya.” Yayi murmushi ya ce, “ki huta.” Itama murmushin tayi ya fita daga falon.
Salma ta bi shi da kallon ta kalli Nayla ta ce, “Nayla anya Yaya Abbas bai ƙyasa dake ba?.” Nayla ta wara idanu ta ce, “rufa min asiri ki bar zancen nan.”
Hajja ta ce, “babu zancen a rufa miki asiri ai gaskiya ta faɗa, ni kaina na lura da yana sonki Hauwa’u.” Gabanta ya faɗi ba tare da ta san dalili ba ta kalli Hajja ta ce, “don Allah Hajja ki daina faɗar haka, ni ɗan uwana ne babu wannan batun a tsakanin mu. Kuma kun san shi yana da wasa da dariya babu lallai abinda ki ke zargi ne. Ga su Yaya Muhmmad da su Yaya Aliyu, da Yaya Khaleed duk ba a ce haka ba sai shi?.”
Hajja tayi murmushi ta ce, “Mai Babban suna da Ali babu wanda ya nuna wani abu a kan ki kamar yadda Abbas ya nuna, daman ni ina son auren zumunci kuma in sha Allah a cikin zuri’ata sai an yi auren zumunci ba ɗaya ba ba biyu ba. Da kaina zan cewa Abbas ya samu Daddyn ku da maganar ki.”
Nayla kamar tayi kuka ta ce, “Don girman Hajja ki bar zancen nan, wallahi ni bana so” ta faɗa tana tashi ta shiga ɗaki dan ita in akwai abinda ta ƙi jini bai wuce auren zumunci ba. Haka kawai baya burgeta balle tayi tunanin zata yi nan gaba. Balle ma kuma Abbas da ya kasance mai ƙirar mazan da ta tsana, bana son namijin da gym ya nuna shi, ita ta fito son mai normal ƙira ba murɗaɗɗe ba.
Didi tana zaune har takwas na dare Omar bai shigo ba duk sai ta damu ta ɗauko waya tana kiransa amma wayar ma taƙi shiga. Ba jimawa sai gashi ya shigo da sallama ta amsa tana kallonsa ganin fuskarsa tana nan kamar ɗazu a ɗaure tamau. Didi ta ce, “ina ka shiga ina ta jiran ka tun dazu?.” Kamar ba zai ce komai ba sai daga baya kuma ya ce, “ina nan.”
“Ka zauna kaci abinci.” Kai ya girgiza alamun baya ci sannan ya ce, “meyasa baki kira ni ba lokacin da baƙonki yazo ba?.” Ta kalle shi ta ce, “na san ba zaka dawo ba saboda ranka a ɓace yake sosai, Yanzu ka zauna kaci abinci.”
“Bana son cin komai.”
“Ko abincin rana baka ci ba na san kuma kai ba mai son abincin waje bane, ka zauna na kawo maka awara nayi maka da kaina.”
Jin yadda take magana murya a sanyaye sai ya ɗago ido ya kalle ta ta ƙaraso inda yake ta ce, “ka zauna don Allah, ba don ni ba.” Ba shi da mafita dole ya zauna ta wuce kitchen sai gata ta dawo da lafiyar jollof rice da kuma ƙaramin plate na awara ta ajjiye masa. Kallon shinkafar ya yi ya ce, “bazan ci shinkafa ba, wannan ya isa” ya faɗa yana ɗaukar ƙaramin plate ɗin awarar ya riƙe a hannunsa ya ɗora ƙafa akan ɗaya.”
Fara ci yayi kusan mintina biyar kafin ya kalle ta ya ce, “Amma ya yi daɗi sosai, kuma babu yaji.” Didi tayi murmushi ganin ya sake ta ce, “na san baka son yaji ai shiyasa sauce ɗin ma babu abinda zai saka ta yaji.” Kai ya girgiza cikin izza da ƙasaita ya kalle ta ya ce, “ina jinki.”
Didi ta ce, “Kamar yadda kaji sunansa haka sunansa yake, ma’aikaci ne ya taɓa aure amma basa tare da matar. Kuma alamunsa ba da wasa yazo ba gaskiya.” Ya girgiza kai ya ce, “haka ake so. Yanzu ya maganar ta tsaya?.” Ido ta zuba masa sannan ta ce, “ka san ba ni zan bayar da kaina ba ko? To na tura shi wajan Kawu.”
Cak ya dakata da abinda yake yi ya kalle ta suka haɗa ido tayi sauri ta ce, “babu yadda na iya ne, ya nemi ganin dangin babana dole na yi masa kwatancen gidan Kawu. Kai ka san ai ba ni zan aurar da kaina ba dole a nemo ganin dangina.” Ajjiye plate ɗin hannunsa yayi bai ce mata komai ba ya miƙe tsaye ya fita.
Daman ta san ƙarshen cin abincin na sa yazo kenan tunda ta ambato maƙiyansa, taji daɗi da bai yi magana ba dan ta san da faɗa zasu yi dashi. Su Bashir ta kira ta basu abincin sannan ta shiga tayi shirim kwanciya. Tunanin baya ne yake dawo mata dawo mata cikin kanta, ta yi ajiyar zuciya tana tuna abinda ya wuce.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 09.*
Ranar asabar da daddare Omar da Didi suna zaune a falo yana aikin danna waya ita kuma tana kallon tv, bata ce masa komai ba ganin ya ƙi ya saki rai, sai ɗaure fuska yake yi ba kamar jiya ba, bata so ta yi masa wata maganarta tsokano shi hakan ya saka ta yi shiru. Shirun ne yayi yawa hakan ya saka ta kalle shi ta ce, "Omar." Ya ɗago manyan idanunsa ya kalle ta sai ta langwaɓar da kai ta ce, "don Allah ka daina buɗe idanunka akan fuskar mutane, wannan idanu naka sai ya firgita mutum cikin dare."
Bai yi magana ba ta ce, "zan faɗa maka wata magana amma kar ranka ya ɓaci don Allah."
"To" ya amsa a taƙaice kafin ta ce, "Ɗazu Kawu ya kira ni, maganar AbdulHamid ce. Ya samu Kawu ɗazu da yamma, shi kuma ya ce ya bashi lokaci zasu ɗan yi bincike a akansa."
Ta ɗauka da ta kira sunan Kawu ransa zai ɓaci kamar kullum amma sai taga yayi murmushi mai ƙayatarwa da daɗin kallo. Murmushi yana yi masa kyau matuƙa, yana fitowa da asalin kyaunsa da kwarjininsa. Ya ce, "Allah ya tabbatar da alkhairi."
Sai taji daɗi sosai a ranta ta har hakan ya bayyana a fuskar ta ta ce, "Amin Habibin Mama. Yaushe zaka nemo taka matar? Kaga in Allah yayi aurena dashi sai a haɗa gabaɗaya ko?." Kallon ta yayi tare da ɗaga yalwatacciyar gashin girarsa ya ce, "Tare mu ka zo duniyar da zamu yi aure tare?."
"Ba tare muka zo ba, amma zan so mu yi aure tare."
"Ke kika fara zuwa duniya, ke zaki fara aure."
"Ai abin ba daga nan yake ba, yara nawa aka haifa a bayana duk suna yi aure har yaran su duk sun girma?."
"Su daban Omar daban" ya faɗa yana kallonta.
Didi ta ce, "to naji, Amma ya kamata dai kaima ka fara neman matar aure, kaga in nayi aure gidan nan bazai maka daɗi ba, waye zai maka girki ka ci da sauran su?." Omar ya ce, "kin san dai na iya girki ko?."
"Na sani, amma yadda baka zaman nan zaka so ace kana dawowa abinci zaka ci ba sai ka dafa ba."
"Ni wannan bai dame ni ba, ki yi auren dai kawai yafi komai a yanzu." Tayi murmushi cikin tsokana ta ce, "faɗa min wacece budurwarka, baka ɓoye min komai amma baka taɓa faɗa min wacce ka ke so ba." Murmushi ya saki mai sauti yana kallon ta ya ce, "Ni aka ce miki ina da budurwa?." Didi ta harare shi ta ce, "Santalelen saurayi mai kyau da kyaun zati kamar ƙanina ai bazai rasa budurwa ba. Ina jin ka ya sunanta."
"Aisha" ya faɗa cikin gatse yana kallon ta da murmushi. Dariya tayi jin sunan da ya faɗa ta ce, "ka ce takwara ta ce ma, Yaushe zata zo na ganta?." Bai ce komai ba kuma bai daina murmushi ba ta ce, "Wai! zan so naga mace da Omar zai so, zan so naga lokacin da Omar zai fara soyayya. Allah ka bani aron rai da lafiyar da zan ga Omar na matuƙar son wata mace bayan Didinsa. Wacce kalar mace ka ke so? fara ko baƙa?."
Kallon ta yake cikin mamaki ganin yadda ta saka shi a gaba tana yi masa wannan tambayoyi kamar wanda ya ce mata neman aure yake yi. Murmushi ya yi ya ce, "ni wai na ce miki aure zan yi ne?."
"Ko baka ce ba na san zaka yi."
"To ba yanzu ba." Tayi murmushi tana kallon sa ganin shima murmushin ya ke yi ta ce, "Allah ya kaimu lokacin, Allah ya kawo macen da zata gyara min kai ka hau kan hanya mai kyau ka sauka daga wacce ka ke kai."
"Hmmm" shine abinda ya furta kawai amma murmushi yake yi. Sai kuma tayi ajiyar zuciya alamun akwai abinda ta tuna amma bata ce komai ba.
Ganin yanayinta ya canja sai ya so ya kawar da damuwarta ya ce, "ai ki kiyaye ganin matar da zan aura, sai na baki mamaki." Jin abinda ya ce sai fara'arta ta dawo ta ce, "Allah ya nuna mana lokacin, Allah yasa baza a samu matsala a aurenka. Allah yasa kar ka nemi wacce za a ce tafi ƙarfin ka."
Ga mamakin ta sai taga yayi dariya kaɗan ya ce, "har akwai macen da tafi ƙarfin namiji ne a duniya?." Didi ta ce, "sosai ma kuwa, akwai inda kai baza kaje kace ma a baka aurenta ba, saboda matsayin ku ba ɗaya ba ba." Ya girgiza kai ya ce, "ni kam ban ga macen da za a ce tafi ƙarfina ba, sai dai in bana sonta." Kallon sa take yi jin da gaske yake yi ta ce, "kai dai Omar ayi shiru kawai, amma akwai matan da sun fi ƙarfin ka nesa ba kusa, tazarar ku kamar tazarar sama da ƙasa. Kyaun da ka ke dashi ba komai ba ne."
Taɓe baki yayi kawai bai ce komai ba, amma shi kam a wajan sa bai ga macen da za a ce tafi ƙarfinsa ba, in dai yana sonta tana sonsa to bata fi ƙarfinsa ba.
A wannan lokacin Nayla tana ƙofar gidan Hajja hannunta har rawa yake yi wajan kiran number Salma, tana ɗauka ta ce, "Salma ya naga gate ɗin gida a kulle?." Daga can ɓangaren Salma ta ce, "Wallahi mun fita, mun je dubiya kuma bamu taho ba."
Nayla ta ce, "Innalillahi na shiga uku, Salma fitsari nake ji kamar nayi hauka. Yanzu ina zan shiga? Kin san ba kowa na sani a unguwar nan ba." Salma ta ce, "Wallahi bamu taho ba, ki shiga gidan Didi kawai."
"Gidan Didi kuma? Ni ce zan shiga gidan Didi?."
"To ba lalaura ba ce? Ita kaɗai ki ka sani a unguwar kawai ki daure ki shiga." Tsabar haushi Nayla kashe wayar tayi ta fara zaga wajan saboda fitsarin da take ji kamar zai zubo.
Haka kawai ta shiga gidan Didi Omar ya ganta yayi mata tsawar da zata yi fitsarin a wando, me ya kai ta shiga gidan Didi..? ai gwara ta yi fitsarin a wando ta san a wandon ta yi. Runtse ido tayi saboda yadda take a matse sosai, kawai sai ta fara hawaye cikin matsuwa da rashin mafita. Hango ƙofar gidan Didi take yi daga inda take, kamar wacce aka bawa umarni ba shiri ta kwasa a guje ta afka gidan.
Kamar a cilla ta ta shiga falon da sallama, idon ta bai faɗa kan kowa ba sai Omar da ya kalli ƙofar yana kallon wacce tayi sallama. Idanunta ne ya faɗa cikin nasa, ga mamakinta murmushi yake yi kuma ganin ta bai saka ya daina ba sai ma ɗauke kai da yayi daga kallon ta.
Didi ganin ta ƙame a jikin ƙofa sai ta miƙe ta ce, "Nayla lafiya na gan ki a firgice haka?." Nayla a wahale ta ce, "Didi fitsari nake ji." Didi ta ce, "maza shiga ki ciki mana" da sauri ta wuce ta shiga ɗakin Didi.
Didi ta koma ta zauna tana kallon Omar da har lokacin fuskarsa a sake take bai yi wani abu da zai tsorata Nayla ba. "Ita wannan yarinyar kullum sai ta shigo ne?." Jin abinda ya ce sai ta ce, "Eh mana, tana sona ne nima ina sonta, tana girmama ni nima ina girmamata." Kai ya girgiza kawai, yana tuna a gaban ta Didi ta dinga yi masa faɗa harda cewa zata mare shi.
Sallamar Nayla ya saka bai ce komai ba ta fito falon kamar munafuka tana kallon Didi. Didi ta ce, "ƙaraso ki zauna." Zama tayi a tsorace ta kalli Didi ta ce, "Su hajja ne basa nan, ni kuma naje gidan ƙanwar Abiy sai yanzu na dawo." Didi ta ce, "Ayya. To ki shiga kitchen ki zuba abinci in zaki ci."
"Na ƙoshi" ta faɗa kanta yana ƙasa dan har lokacin yana zaune bai tashi ba.
Didi ta kalli Omar da ba su yake kallo ba ya dai hakimce ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana kaɗawa. Murmushi tayi tace, "Yayanki Omar ya ci awarar da kika dafa yana ta santi." Nayla ta ɗago tana kallon Didi haka kawai gabanta yake faɗuwa, babban abin mamakin faɗuwar gaban da take ji ta banbanta da irin wacce take ji in ta ganshi. Nayla dai bata ce komai, Didi tayi murmushi ta kalli Omar da yake murmushi sosai da alama akwai abinda ya bashi dariya a wayarsa.
Didi ta ce, "Omar!." Ɗago idanunsa yayi ya kalle ta suka sake haɗa ido da Nayla tayi saurin kawar da kai jin faɗuwar gaban da take ji tana neman wuce tunaninta. Hasken idanunsa kawai take a gani