Showing 57001 words to 60000 words out of 87436 words
Chapter 20 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt
wanne irin yanayi ne?." Babu mai bata amsa, ta sake yin shiru tana kallon bangon ɗakin, ta kulle ido ta buɗe tana jin sautin muryarsa da yadda ya amsa gaisuwarta. Murmushi tayi ta ce, "he's so handsome." Salma da ta shigo ta kalle ta ta ce, "waye ya kama zuciyarki haka?."
Nayla ta kalle ta Salma ta ce, "tun ɗazu na shigo kina tunani kina ta murmushi alamun kin faɗa soyayya, sai naji kina yabon kyaunsa, waye shi?." Gaban Nayla ya faɗi, sai a lokacin ta farga da hakan yana nufin soyayya, kenan son Omar take yi?. Tuna hakan sai ta wara idanu waje Salma ta ce, "meye na buɗe idanu, ai duk wanda yaga yanayinki a kwanakin nan ya san akwai bayani. Kenan ɗan Kano kika samu ko? Yaya Abbas yana can yana haukan sonki wani ya ɗauki zuciyarki."
Nayla ta haɗɗiye yawu ta ce, "Salma ba haka bane."
"To faɗa min ya ne?." Shiru tayi bata ce komai ba, ta juya baya ta kwanta tana tunanin lallai dole ta bar Kano tun kafin dare ya yi mata.
Hajiya Nayla ita soyayya ai duk inda ki ke yana tare dake. lol 😝😂
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t
*Book 1*
*P 17.*
Nayla haka ta tashi sukuku ta rasa abinda yake yi mata daɗi, zuciyar tayi mata nauyi sosai yanayin ta gabaɗaya ya canja. Kallo ɗaya zaka yi mata ka hango canji a yanayinta, kasancewarta ba mace bace mai nuƙu-nuƙu ba, ko ya yanayinta ya canja zaka fahimta, kana ganinta ka san ta canja. Tana zaune a falon Hajja tama juya cokalin a cikin tea ita bata sha ba kuma ita bata daina juya cokalin ba. Hajja ta kalle ta ta ce, “Hauwa’u lafiya ki ke kuwa?.”
Ta kalli Hajja ta ce, “Lafiya lau nake Hajja, Kawai yau na tashi bana jin daɗi ne.” Salma da take gefe tayi dariya ta ce, “ba wani nan, Hajja soyayya ta fara shiyasa yanayinta ya koma haka.” Nayla ta ce, “Samla ki ji tsoro Allah, ni dai ban ce miki ba.” Hajja tayi dariya ta ce, “rabu da ita Hauwa, in ma da gaske soyayyar ki ka fara meye a ciki ai kin kai ki yi ne.”
Nayla ta ce, “balle ma ba haka bane” ta faɗa tana ɗaukar wayarta jin tana ƙara.
Abiyna shine ya bayyana akan screen ɗin, tayi murmushi ta ɗauka ta saka a kunne ta ce, “Abiy barka da safiya.” Daga can ɓangaren Abiy ya ce, “Kin tashi lafiya Mamana?.”
“Lafiya lau nake Abiy, ya su Mama?.”
“Lafiya lau kowa yake, sai kewar ki mu ke yi.”
Tayi murmushi kafin ta yi magana ya ce, “Ya Hajja tana Lafiya?.”
“Lafiya lau Abiy.”
“Ki gaishe ta da kyau.” Ta amsa kafin ya ce, “yaushe zaki dawo ne? Sati ɗaya na ce ki yi amma naga kin yi shiru ban ji kina zancen dawowa gida ba.” Haka kawai gabanta ya faɗi ta ce, “Abiy na ɗauka sai nayi sati biyu.” Abiy ya ce, “A’a baza ki ba Mamana, ki zauna cikin shiri ko yaushe zan iya ce miki zan turo a ɗauke ki. Ki zo gida ki fara aiki ki in makaranta zaki koma ki makaranta in aure zaki yi ki yi aure.”
Nayla da zuciyar take harbawa ta ce, “To Abiy.”
“Yauwa, ki zama cikin shiri zan turo a taho min dake hutun ya isa.” Nayla ta amsa kafin Abiy ya yanke wayar.
Hajja ta kalle ta ta ce, “Hauwa kina son zaman Kano baban ki yana son ki zauna a kusa dashi. Yaushe ya ce zaki tafi?.” Nayla a sanyaye ta ce, “yace na zauna a shiri ko yaushe zai turo a ɗauke ni. Wallahi Hajja bana son tafiya.” Hajja tayi murmushi ta ce, “haƙuri zaki yi ko koma, nima bana son tafiyar ki amma mahaifinki shine yake da iko akan ki sama da kowa, ki koma ɗin wani lokacin sai ki dawo.” Ajiyar zuciya tayi kawai tuna tunanin in ta tafi Kaduna ya zata yi da ganin Omar kenan?.
Ɓangaren Abiy yana yanke wayar Mama da ta shigo ta zauna ta kalle shi ta ce, “Abiy kana son Nayla ta dawo sai, na ɗauka zaka barta ta sake yin kwana biyu.” Ya kalle ta ya ce, “iya hakan da na bari ma nayi ƙoƙari, ke kin san bana barin yara su je wani waje, ba wai dan ba yarda da tarbiyyar wajan da zasu je ba sai dan kawai bana so. In ba Hajja ɗin ba babu inda zan iya barin Nayla ta je yayi wannan kwanakin.”
Mama ta girgiza kai ya ce, “haka ne, amma da ka bari ta sake kwana biyu Itama tana son zaman Kanon. Kuma yanzu bata fara aiki ba kuma ba karatu take ba, tana da lokacin da zata zauna wajan Hajja.” Abiy ya ce, “na yi iya yina ai, gwara ta dawo gida wani lokacin ta koma.”
Mama ta ce, “haƙuri zaka sake yi, itama Naylan tafi jin daɗin zaman can akan zaman nan.” Da mamaki Abiy ya kalle ta ya ce, “Haka Naylan ta ce miki?.” Mama ta ce, “eh haka ta ce. Ta ce min ita da zaka barta ta koma Kano ma tafi son haka.” Abiy ya zuba mata ido yana kallo cikin mamaki kafin ya ce, “na tambayeki.”
“Ina ji.”
“Meyasa bakya son zaman ta a gidan nan ne? Akwai abinda take tsare miki?.” Mama ta wara ido cikin tsoro ta ce, “Abiy yau ni ka ke faɗawa haka? Me Nayla zata tsare min a gidan nan saboda Allah?.”
Abiy ya ce, “to meyasa ko yaushe in ina zancen zata dawo ki ke so na barta ta zauna?.” Mama ta ce, “ba haka bane, kawai ina duba yadda kakarta take sonta ne, da kuma yadda ita Naylan take son kakarta. Kuma kar ka manta Hajja mahaifiyar Nayla ta rasa, Nayla take kallo a matsayin ƴarta da ta rasa shiyasa kawai.”
Abiy ya ce, “nima uwar gidana na rasa, Nayla nake kallo a matsayin matata da muka zauna tare tun auren saurayi da budurwa. Nayla kaɗai Allah ya bata matsayin ƴa kafin ta bar duniya, ita nake kallo nake a madadin matata. Dan haka Zeena kar ki sake yi min magana irin wannan, a duk lokacin da nayi maganar Nayla ta gida dawo in baza ki taya ni cewa ta dawo ba ki kar ki sake saka min baki kin gane?.”
Ganin ya fusata sosai sai ta ce, “Allah ya baka haƙuri, ba da wani abun nake faɗ ba.”
“Na dai faɗa miki” yana gama faɗar hakan ya tashi ya bar mata falon ta bishi da kallo. Kai ta girgiza dan wallahi sai ta samu makamin da zata nisanta Nayla da mahaifinta, dole ma tayi wani abun kafin lokaci ya ƙure mata.
•••••• Omar kuwa da safe wajan Didi ya shiga ya tabbatar da lafiya lau take ya hanata dafa abinci da kansa ya dafa musu noodles suka ci, bayan sun kammala ne ta kalle shi ta ce, “Yaushe zaka gama aiki da Barr Nass?.” Omar ya kalle ta cikin rashin fahimta ya ce, “Wace haka?.” Ta harare shi ta ce, “ban sani ba. Yarinyar da ka ke kaiwa unguwa mana.”
“Oh! Ni in kika ce Barr Nass ɗn nan ɓatar dani ki ke yi. Ban sani ba, amma na san cikin kwanakin nan ne.” Didi ta girgiza kai ta ce, “to Allah ya taimaka, ni so nake ayi a gama lafiya kar a samu matsala da kai.” Ya yi murmushi kawai bai ce komai ba alokacin wayar sa ta ɗauki ƙara.
Number ce ya kalli wayar sosai kamar ya santa number hakan ya saka ya ɗauka ya saka a kunne, “Hello Tiger.” Narma ta faɗa daga cikin wayar, lumshe ido ya yi jin muryarta mai daɗi a kunnesa ya ce, “ina ji.” Narma tayi murmushi ta ce, “Daman na san abinda zaka ce kenan. Na kira ka ne in kana da time zuwa bayan azhar zamu fita.”
“Okay, Allah ya kaimu.”
“Amin. A gaishe da Sister ace ina yi mata ya jiki.”
“Okay” ya sake furtawa a taƙaiice, Narma tayi dariya ta kashe wayar.
Kallon Didi ya yi da take kallon sa kafin ya yi magana ta ce, “Omar kafin ita ka taɓa waya da mace kuwa?.” Ya girgiza kai ya ce, “Gaskiya ban taɓa ba Didi, sai dai masu rubuta wrong number su kira ni suna neman wani. Itace mace ta farko da na taɓa waya da ita gaskiya.” Didi ta ce, “koda na ji, shiyasa ka ke mata magana a daƙile kamar kai ne oga itace driver ta ka.”
“Bana son rainin wayo ne, kin fi kowa sanin haka.”
“Nafi kowa sani kam Alhaji Omar.” ya yi murmushi mai sauti kafin ya tashi ya bar mata wajen.
Sai da yayi sallar azahar ya shirya cikin ƙanunun kaya masu kyau wanda suke masa jikinsa sosai. Kiran Narma ne ya sake shigowa wayarsa ya kalli number dan daga ɗazu zuwa yanzu ya gane number, ya ɗauka ya saka a speaker ya ajjiye a kusa dashi bai ce komai ba. Narma ta ce, “Tiger ina jira.”
“Okay” ya amsa a taƙaice kafin ta kashe wayar ma ya yanke wayar.
Wajan Didi ya shiga ya samu bacci take yi ya fito ƙofar gidan yana ƙoƙarin kiran Bash a waya. Ba jimawa Bash ya zo ya ɗauki shi a machine suka wuce gidan. A ƙofar gidan ya ajjiye shi ya ce yaje kawai zai taho ya tafi shi kuma ya shiga cikin gidan.
Da su Yahya ya gaisa da masu gadin gidan kamar ko yaushe, bayan sun gaisa ya hakimce a inda yake zama. Ga mamakinsa sai gata ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tana nufo shi.
Kasa ɗauke ido ya yi daga kanta, tayi matuƙar kyau cikin lace ja mai adon duwatsu. Riga da siket ne a jikinta ta yafa mayafi a kafaɗa ɗaya da wayarta a hannu. Kafin ta ƙaraso ƙhamshinta ya zo inda take, ya miƙe ta kalle shi ta ce, “Zamu iya tafiya?.” Kai ya ɗaga mata ta bashi key ɗin wata motar daban ba wacce suke hawa ba ya ƙarasa ya kunna motar yana jira ta shiga.
Ga mamakin sai yaga ta buɗe gaban motar ta shiga, bai yi magana ba ya ja motar suka fita ma’aikatan gidan sai kallon ikon Allah suke yi. Titi ya hau ba tare da ya san inda zasu je ba,
kallon fuskar sa take yi cikin tsantsar shauƙin da bata san daga inda yake zuwa ba, wani irin bugu zuciyar ta take yi ba tare da ta san dalili ba.
A haka ta kwana ta tashi cikin wannan yanayi na bugawar zuciya, tsananin kewarsa da take take ji ya saka ta ce zasu fita da wuri ba dan ta san inda zata je ba, yanzu gashi gata amma sai take jin yanayin kamar ya fi na baya shiga rai.
“Ina zamu je?.” Jin muryarsa ya saka ta janye ido daga kansa ta jingina da kujera ta sauke ajiyar zuciya tare lumshe ido, a hankali ta buɗe ta ce, “nima ban sani ba.” Kallon ta ya yi da mamaki suka haɗa ido sai ta ce, “mu je gaba akwai wani restaurant sai mu shiga, yunwa nake ji.”
Bai sake magana ba ya cigaba da tafiya har suka zo inda take nufi. Shiga suka yi ya ajjiue motar yana jira ta fita. Kallon sa yake ji tana ji a jikinsa shiyasa yaƙi kallonta, bai san meyasa ta canja haka ba. Narma ta ce, “mu je tare.” Kai ya girgiza bai kalle ta ba ta ce, “Don Allah.” Kallon ta yayi ya rasa meyasa ta canja gabaɗaya, ya rasa meyasa take masa irin wannan abubuwan kamar wacce take tare da wani mijinta.
“Bazan je ba” ya faɗa kai tsaye. Narma taji babu daɗi a zuciyarta, ta buɗe ta fita ya bita da kallo dan iya tafiyarta ma abar ɗaukar hankali ce.
Ba jimawa sai gata da wani waiter a bayan ta da ledoji, ta shiga motar sannan ta karɓa ta kalle shi ta ce, “mu je.” Fita suka yi ta sake kallon shi ta ce, “Zaka kai ni zoo park? Amma mu shiga tare kaji!” Yadda tayi maganar kaɗan ya rage bai saki motar ba, amma kasancewar sa akwai dakiya da basarwa bai nuna ba ya ce, “ni bazan shiga ba.”
“Don Allah Omar!.” Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba ya ɗauki hanyar Zoo park.
Ba ya cewa komai yana ji tana kallonsa ya rasa meyasa take son kallon sa haka kawai. Narma kuwa tunani take yi, ko shima yana jin irin abinda yake ji akan sa oho. A haka suka ƙaraso bakin zoo park, ta kalle shi ta ce, “mu je don Allah.” Yana kallon gabansa ba tare da ya kalle ta ba ya ce, “babu inda zan je.”
“Don Allah” ta faɗa tana kallonsa.
“Bazan je ba!.”
“Ba don ni ba, don Allah, don Annabi.” Numfashi ya sauke ya kalle ta, baya son magiya ko kaɗan, magiya tana daga cikin abinda Didi take masa ta cuce shi ya yi abinda ba ya so. Ba tare da ya kalle ta ba ya buɗe motar ya fito ta biyo bayan sa tana murmushi.
Shi ya biya kuɗin ticket suka shiga ciki. Tafiya suke yi tana gaba yana baya, sam yaƙi yarda su jera su tafi tare, da tazo kusa dashi zai ɗan tsaya har sai ta wuce sannan zai biyo ta. A haka ta suke ta tafiya, suna zuwa waje-waje baya cewa komai dan shi kam ya gaji. Mamaki yake yi ma da ya amince ya biyo ta, mamakin kansa yake yi kamar ba shi ba wani abun yana niyar canja shi. Da aka zo wajan tiger sai Narma ta yi murmushi ta kalle shi sai ta ga ba wajan ma yake kallo ba.
Ta yi murmushi ta ce, “Tiger i like your acting” daga haka tayi gaba. Bai yi tunanin me ta ce ya wuce shima.
Waya ya tsaya yana amsawa hakan ya saka ta tsaya tana kallon sa cikin annushuwa mai yawa, ko tare da Ashraf take bata jin wannan abinda take ji a kansa, shiyasa ta kasa fassara shi har yanzu. Basu jima ba suka fita suka mota tare da ɗaukar hanya. Har lokacin bai ce mata komai ba itace dai take kallon sa kamar ta cinye shi. Lokacin sallah ne yayi hakan ya saka yake gudu har suka ƙarasa gidan ya tsayar motar.
“Na gode.” Kai ya ɗaga kawai bai ce komai ba. Ta yi gyaran murya ta ce, “Gobe zan koma Abuja.” Kallon ta ya yi ta ɗaga masa kai ta ce, “Daddy ya ce na koma ni kuma ban gaji da Kano ba.” Maimakon ya amsa mata abinda ta ce sai ya ce, “Allah ya kaimu.”
“Amin ya rabbi. Ƙarfe sha biyu jirgina zai tashi, zaka zo ka kaini airport?.” Yadda take maganar a shaƙe ya saka shi ya kalle ta, sai ta marairaice ta ce, “please!.”
“Allah ya kaimu” ya sake faɗa a taƙaice. Ta amsa da amin ta ajjiye masa abinda ta siyo ta ce, “ga naka nan, in baka so ka kaiwa Sister. Sai gobe” ta faɗa tana buɗe motar ta fita. Kafin ta shiga gidan ya fito ya ce, “Makullin.”
Tsayawa tayi tare da dawowa, ta karɓi key ɗin tana kallon sa bata ce komai ba ta wuce ciki zuciyar tahar zillo take yi daga ƙirjin ta saboda bugawar da take yi. Bai bar gidan ba sai da yayi sallar la’asar sannan ya fita daga gidan ya nufi gidan Didi.
Narma tana kallon sa har ya fita ta jingina da bango idanunta a lumshe ta ce, “Wayyo Allah, ne nake ji haka akan wannan mutumin? Meyesa bana so ya yi nisa dani? Meyasa nake so naji yayi magana? Ina haushinsa da nake ji a baya ya tafi?.” Babu mai bata amsa ta buɗe idanunta a bayyane ta ce, “me hakan yake nufi?.” Gate ɗin gidan take kallo kamar shi take kalla kafin ta ja baya ta ta koma ciki.
Omar da ya koma ya bawa Didi kayan gabaɗaya, Didi ta karɓa tana godiya dan shi kam ta san ba ci zai yi ba. Didi tana ta yabon Narma shi dai bai ce komai ba ya yi shiru yana kallon wani waje daban yana mamakin yanayin da yake ji a kanta da abubuwan da take yi masa ita kanta Narma. Bai bari tunanin ya yi tasiri a kansa ba ya tashi ya fita daga gidan domin samu ya manta da maganar.
Washe gari.
_Tiger don’t forget my flight is at 12pm._ abinda ya gani kenan a wayar ɗsa, ya sake maimaitawa karantawa ya fahimci abinda take nufi. Sake karantawa ya yi a karo na uku sai ya ja tsaki ya cillar da waya ya ce, “iyayi, baza a yi magana da hausa ba sai da turanci, sai ka ce an faɗa mata na iya oho.”
Wanka ya yi ya saka manyan kaya daman ya sanar da Didi zai mayar da ita bai shiga wajan ta ba kai tsaye ya tafi. Ta sama ta hango zuwan sa ta ƙare masa kallo tun kafin ya shigo tana murmushi. A haka ta sakko ta same shi, ta ƙarasa tana sallama da masu aikin a yatsine kamar bata so. Mai gadi ya saka mata jakar ta booth ta shiga motar. Kamar jira yake yi ya shiga shima suka tafi.
Bai ce mata komai ba daman ta san bazai ce ba ita kuma hakan da yake yi ba ƙaramin burge ta yake yi ba. Murmushi tayi bai kalle ta ba abinda yake gabansa kawai yake yi.
Wayarta ce tayi ƙara ta duba taga sunan Dad ta ɗauka ta saka a kunne kafin ya ji ta ce, “Yes Dad, gani nan zuwa.” Shiru yaji ta sake yi kafin ya ce, “shine.” Daga nan bai sake ji ta ce komai ba ta yanke wayar. Shigar su Airpot ba jimawa ya ƙarasa ɓangaren domestic kamar yadda suka ɗauko ta a wancan lokacin.
Tsayar da motar ya yi ta zuba masa ido tana kallo. Kamar bai san kallonsa take yi ba ya share