Showing 33001 words to 36000 words out of 87436 words
Chapter 12 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt
a idanunta, tana mamaki daman idanunsa suna da haske haka ko kuma dan yau ransa ba a ɓace yake ba?.
Muryar Didi taji tana cewa, "itace fa ta dafa awarar da ka gama ci." Bai ce komai ba,
amma yana mamaki meyasa Didi take son saka shi a lamarin yarinyar nan ne? Dan tsabar neman waje irin na Didi wai Yaya Omar, shi kaf duniya babu wanda yake ce masa Yaya.
Wayarsa take ƙara ganin mai kiran sai ya tashi ya fita daga falon. Didi ta bishi da kallo sannan ta kalli Nayla da itama kallon sa take yi Didi ta ce, "Yau kin yi mamakin mutumin naki ko?." Nayla tayi murmushi kawai bata san meyasa ta kasa furta komai ba. Ji take kamar an ɗaure mata baki harshenta ya sarƙe ta saka cewa komai. Didi ta ce, "wallahi ɗazu ya gama yabon awarar ki wai kar na sake kaiwa inda ake yi na dinga yin irinta, yau tsokanarsa nake tayi shiyasa yake ta murmushi."
Nayla ta ce, "abin mamaki, ban ɗauka yana dariya ba." Didi tayi dariya ta ce, "dariya har da ta ƙeta in dai Omar ne, kawai bashi da saurin sabo ne kwata-kwata, amma da zaku saba ke kan ki da kinga canji daga halayensa. Yana da hira sosai in ya so, zaku zauna ku yi hira cikin raha da wasa da dariya. Inda zaku saba murmushinsa bazai miki wahalar gani ba, kafin a saba ɗin ne ana jimawa." Nayla ta girgiza kai kawai ta sake kallon inda ya tashi sai take ji a zuciyarta dama ya dawo ta sake gani yana murmushi.
Shi kuwa Omar ganin kiran Senator ya saka shi ya fita ya ɗauja da sallama, suka gaisa Senator kamar ko yaushe ya ce, "Tiger gobe Narma zata sauka a Kano, jirginta zai sauka bayana azahar in sha Allah. Akwai wanda na bashi number ka zai kira ka ya kai ka airport ɗin, in ya nuna maka ita sai ka karɓi motar ku wuce. Zan tura maka address ɗin gidan da zata sauka."
Omar ya ce, "Allah ya kaimu."
"Amin. Tiger please kar kayi wasa da wannan lamari, ka kula da Narma kar ka bar wani wanda baka yarda dashi ba a kusa ita. Akwai wanda basa son su ga Narma a Kano, na san baka da wasa shiyasa na zaɓe ka akan police."
"In sha Allah babu damuwa, sai dai in a samu damuwa daga wajanta."
"kar ka damu zan ja mata kunne sosai, in kaga abu ba daidai ba ka kira ni."
"In sha Allah" ya sake amsawa a taƙaice kafin su yi sallama ya kashe wayar.
"Zan wuce" yaji an faɗa daga bayansa muryata na rawa sosai alamun a tsorace take. Juyowa yayi ya kalle ta kanta yana ƙasa jikinta na ɗan rawa kamar wacce aka jonawa lantarki. Didi ya gano fito daga falo ta nufo inda Nayla take tsaye.
Bai ce komai ba kuma bai motsa ba har sai da Didi tazo wajan ta ce, "Omar ka bata hanya mana." Magana yake so yayi amma sai ya fasa ya shiga ɗaki Nayla ta fita a guje, Didi tana dariya ta bi bayan ta sai da ta ga ta shiga gidan Hajja sannan ta dawo.
Tana shiga ta dinga yiwa Salma masifa akan me ta san zasu fita bata faɗa mata ba, Salma ta ce, "Anty bala'i, na kira ki ban samu ba, kuma ba ga shi kin shiga gidan su mai baki tsoro ba?."
"Ke kin san halin da nake ciki da na dawo? Fitsari kamar ya kashe ni bani da zaɓin da wuce na shiga gidan." Salma tayi dariya tana bin ta da kallo ta ce, "ya ban ga fitsari yana bin jikinki ba? Dan na san gamuwar ku dole ki yi fitsarin wando."
Nayla ta ce, "kee abin mamaki, yau bai min komai ba, hasalima da na shiga suna hira da Didi murmushi bawan Allah nan yake yi. Wai daman yana murmushi?." Salma ta ce, "mai zai hana ya yi? Kawai ba kowa yake yiwa bane." Nayla ta ce, "naga alama" ta faɗa tana shiga ɗaki tana sake hango murmushinsa a idanunta.
Washe gari har rana ta fito Nayla ta kasa mantawa da fuskar Omar yana murmushi, da ta rufe ido shi take gani da lokacin da suka haɗa ido hasken idanunsa ya shiga cikin nata ido. Gabaɗaya ta kasa mantawa da abin ta kwana, tayi-tayi ta manta amma abin ya ci tura.
Omar kuwa lokacin da driver ya kira shi ko Didi bai sanarwa ba ya fita, ya same shi yana jiransa a mota ya shiga motar suka ɗauki hanyar airport. Mutumin yana ta jan Omar da hira shi kuwa ba amsawa yake ba yayi shiru abinsa.
A cikin airport suka ajjiye motar Omar ya fito ya jingina da motar shima driver ya fito yayi kamar yadda Omar ya yi. Kallon Omar ya yi ya ce, "Abokina sai kayi haƙuri da yarinyar nan bata ji, tana da rawar kai sosai sannan tana da gadara duk abinda yake so shi za a yi mata." Omar ya ɗago ido ya kalle shi mutumin ya ce, "Wallahi sai kayi haƙuri dan bata da kunya ko kaɗan, mulki take ji dashi da isa, hatta buɗe ƙofar mota zata ce kai zaka yi mata. Ga tsawa da kyara kamar waɗanda ta haifa."
Omar ya girgiza kai kawai mutumin ya sake cewa, "Ni ai naji daɗi da aka ce wannan karon ba ni zan dinga kai ta inda take so ba, wallahi sai sha biyu na dare zata yi min waya na baro gidana nazo na siyo mata pizza ko shawarma. Ta tara ƴan mata irinta ƴaƴan manya a gidan suna ihuu kamar ba dare ba."
Omar duk yana jinsa kawai bai san me zai ce masa ba ne, amma duk abinda yake faɗa baya tunanin ko babanta zai yi masa shi balle ita. Drivern ya ce, "Abokina gata nan ta fito, Hajiya Narma kenan shugabar masu shigar banza nigeria."
Omar ya ɗaga kai yana kallon inda yake kallo, Narma ya hango cikin atamfa fitted gown ta atamfa ta kama ta sosai ɗakyar take motsawa, mayafi ne siriri ta yafa shi a kafaɗa, hannun rigar gabaɗaya da net aka yi shi hakan ya bayyanar da farin dantsen hannunta, hatta pink colour ɗin bra ɗinta ana gani. Tahowa take fuskar ta ɗauke da baƙin glasess, gabaɗaya ilahirin jikinta a bayyane yake, daga wrist ɗinta zuwa hips ɗinta an kama shi ɗam, a kuma cike sosai. Duk yadda ka kai ga kushe sai ka yabi surar Narma, dan Narma akwai sura ma sha Allah, shiyasa take ɗaukar hankalin maza nan take.
Omar gani yayi wanda suke tsaye ya ƙarasa da sauri ya karɓi trolly bag ɗinta ya saka a bayan mota, sannan ya buɗe mata bayan motar ta shiga. Omar ya bawa key ɗin motar ya ce, "Allah ya fushsheka lafiya mutumina, ni daga nan zan wuce." Omar ya kalle shi ya ce, "na gode. Amma kazo mu je gidan tare ban gane kwatancen ba."
"To mu je" ya faɗa yana buɗe motar ya shiga shi kuma ya shiga gaba.
Drivern ya kalle ta ya ce, "Hajiya barka da zuwa." Danna waya take yi ta ce, "barka." Bata sake magana ba shima bai sake ba ya kunna motar suka bar cikin airport ɗin. Tafiya suke babu wanda yake magana a ciki su, ƙhamshin turarenta ya gama mamaye motar gabaɗaya.
Wayar Omar ce tayi ƙara ya duba yaga Didi ce ya ɗauka yana cewa, "Na fita zan dawo anjima." Abinda ya ce kenan ya cire wayar daga kunnesa, hakan ya saka ta ɗago kai tana kallon inda Omar ɗin yake.
"kai meye ma sunan ka?." Driver ya ce, "Yahya Hajiya,"
"Waye wannan muna tafiya yana amsa min waya?." Yahya ya ce, "baƙo ne Hajiya, bai san dokokin ki ba."
"Ka sanar dashi" ta faɗa tana cigaba da danna wayarta. Omar bai ma kalle shi ba ya cigaba da danna waya a haka suka isa katafaran gidan da yake cikin nasarawa gra, mai gadi ya buɗe masu ƙofa suka shiga.
Yahya ya fito da sauri ya buɗe mata ƙofa ta fito ya ɗauki jakar ta yabi bayan ta a guje. Omar ya bushi da kallon mamaki dan shi bai ga abu ɗaya da zai iya yi mata ba, daga buɗe ƙofar da ɗaukar jakar. Yana nan tsaye Yahya ya dawo ya kalle shi ya ce, "Abokina wannan matar bata da kunya na faɗa maka, gwara ka ja girmanka, in ba haka ba zata yi maka abinda bazai maka daɗi ba. Ba a waya a mota in tana ciki, ka kiyaye."
Omar ya girgiza kai ya ce, "wai abinda ka ke yi mata nima shi zan yi?."
"Fiye da haka ma."
"Ba a haifi yarinyar da zan yiwa wannan abun ba." Yahya yayi dariya ya ce, "Tunda har ka karɓi aiki da Hajiya Narma sai kayi haƙuri kawai, duk abinda ka ke faɗa yanzu a baki ne, amma zaka tabbatar da magana ta gaskiya ce." Kallon idon Yahya ya yi ya ce, "nayi maka kama da wanda yake wasa?."
Kwarjini ya yiwa Yahya sosai sai ya girgiza kai ya ce, "A'a, amma ina baka shawara." Omar ya ɗauke kai suka yi sallama da Yahya ya tafi.
Fanfo ya gani daga can gefen compound ɗin kuma yana fa buƙatar yin sallah, ya ƙarasa yayi alwala, ya juya yana kallon gidan a nan ya ga wani ƙaramin masallaci da mai gadin da ya buɗe musu ƙofa a ciki, Omar ya nufi wajan kai tsaye da niyar yin sallah. Narma ce ta fito ta canja shiga zuwa riga mai jikin roba ta kama, sannan daga sama wuyan a buɗe yake ana iya hango saman ƙirjinta. Narma ta ce, "kai!." Bai ko kalle ta ba balle ya saka ran dashi ta ke, ta sake cewa, "da kai nake."
Nan ma Omar bai kalle ta ba sai ma cigaba da tafiya da yayi, mai gadin da yake zaune a cikin masallacin ya taso da sauri ya tari Omar ya ce, "Abokina magana Hajiya take maka." Omar ya kalle shi ya ce, "magana?."
"Eh, gata can tana magana."
"Ba da ni take ba." Muryar Narma ya ji a bayansa ta cewa, "Waye kai ina yi maka magana baza ka amsa ba?." Nan ma bai motsa ba balle ya kalle ta.
Shan gabansa tayi tana kallonsa daga sama har ƙasa ta ce, "ba kai ne Tiger ba? Kana ji ina yi maka magana zaka yi min banza waye kai?." Ganin yayi shiru bai amsa ba ya dai zuba mata ido har hakan ya saka ta janye idanunta ta ce, "charger zaka je ka siyo min yanzun nan, ka bar shiga masallacin ka je ka siyo min."
_Tashin hankali, haka za a yi da yarinyar nan?, ni zata tsayarta ce zata aika? Ni take yiwa tsawa? Lallai kafin na gama aiki da ita sai dai a kai gawar ta Abuja._ Abinda yake aiyanawa kenan yana ƙare mata kallo cikin ɓacin da ya baya bayyana akan fuskarsa.
Ta buɗe baki zata yi magana ya ce, "in kika sake yi min magana sai na yi ball dake a wajan nan, sa'anki ne ni ko yaron ki ne..? bani waje!?" Ya faɗa da tsawa idanunsa na waje yana kallon ta.
Narma bata san ta daka tsalle ta koma gefe ba sai sautin tsakinsa ta ji ya shiga masallaci yana ayyana dole ma ya kira baban yarinyar nan bazai juri wannan shirmen nata ba, ko ya ajjiye aikin da ya karɓa ko a wayi gari yayi mata illa.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 10.*
Narma suman tsaye tayi ta bishi da kallo cikin faɗuwar gaba, ba a taɓa yi mata tsawa ba sai yau, tsawar ta ratsata sosai shiyasa bata san ta koma gefe ba. Sai da ta dawo hankalinta ta kalli ma'aikatan gidan ta ga kowa kallon ta yake yi rai a ɓace ta wuce cikin gidan a guje. Tana shiga babban falon gidan ta ɗauki waya hannu na rawa ta kira mahaifinta.
Yana ɗauka kafin ya yi magana ta ce, "Dad waye wannan ka haɗa ni dashi? Dad tsawa fa yake yi min ina yi masa magana yayi min banza. Kuma tun airport ko sannu da zuwa bai yi min ba, kamar ma bai san ya ɗauko ni a mota ba. Gaskiya Dad bazan jure zama da wannan mutumin ba na gaji."
Senator da yake sauraren ta sai da ta gama ya ce, "ƙyale ni dashi zan kira shi yanzu a waya, kin sauka lafiya?." Da shagwaɓe ta ce, "lafiya lau Dad. Charger na ce ya siyo min na bar tawa a gida kaga yadda ya yi min tsawa kamar ni ce nake aiki a ƙasansa? Babban abin ɓacin ran a gaban maids ɗin gidan nan. Gaskiya Dad i can't toleret this kind of nonsense." Dad ya ce, "don't worry my dear, zan kira shi yanzu."
"And let him come and say sorry to me Dad." Senator ya yi murmushi ya ce, "hold on, i'm coming." Kashe wayar tayi ta nemi waje zauna tana lissafa kalar wulaƙancin da zata yi masa.
Omar kuwa tun yana sallah yake jin kiran waya na shigowa wayarsa, bai katse sallar ba sai da ya idar sannan ya duba wayar ganin mai kiran sai yayi ƙaramin tsaki ya taso ya fito daga masallacin. Car park ya ƙarasa, daga gefe akwai madaidaiciyar gazebo ta shan iska da kujeru a ciki nan ya shiga ya zauna, yana zama wayarsa ta ɗauki ƙara ya ɗauka ya saka a kunne.
Daga can ɓangaren Sen ya ce, "Tiger." Omar ya amsa suka gaisa kafin ya ce, "Tiger Narma ta kira ni ta ce kayi mata tsawa dan ta ce a siyo mata charger." Omar ya ce, "ba ɗan aiken ta bane ba ni, haka zalika ni ba yaron ta bane. Saboda kai na karɓi aikin nan, kai ta wajan da take so shine abinda ka ce zan yi, amma ba wai dan ta saka ni a gaba tana yi min ihu ba. In a haka za a tafi gaskiya zan ajjiye aikin nan sai a samo wani, ni bazan jure ba."
Senator ya ce, "bata san waye kai bane shiyasa, Amma zan mata magana za a samu mai yi mata aike da siyo mata abinda take so, kai dai kai nake so ka dinga kai ta inda zata je." Omar ya ce, "bazan dinga zama a nan ba gaskiya, zan dinga tafiya in zata fita sai ta sanar dani nazo na kaita." Senator ya ce, "Daman ni abinda nake so shine ka kaita ka kula da lamarinta a duk inda take." Omar ya yi shiru Sen ya ce, "ina zuwa" ya faɗa yana yanke wayar.
Omar yana nan zaune bai san me ya faru ba sai yaga Yahya wanda suka rabu ya dawo ya shiga gidan ba jimawa ya dawo ya hau mota ya fita. Taɓe baki yayi dan a kaf duniya bai ga macen da zata aike shi ba in dai ba Didi ba. Tsabar raini shi zata dinga yiwa tsawa ta ɗauka shi yaron ta ne?. Bai jima sosai a zaune a wajan ba kawai ya tashi bayan ya bawa Yahya key ɗin motar da ya bashi ya fita daga gidan.
A can Abuja kuwa Dad yana yanke wayar Mum ta kalle shi a fusace ta ce, "ni fa tun asali ban so ka haɗa riƙaƙƙen ɗan daba da ƴata ba, ta ya ya za a ce kaf jami'an tsaron da suke Kano ka rasa da wanda zaka haɗa ta sai da ɗan daba?. Waye shi da zai mata tsawa har yake ganin yafi ƙarfin ta aike shi? Ba a ƙarƙashin ka yake ba?."
Nabil da yake zaune shima rai a ɓace ya ce, "abinda zan ce kenan Mum. Ta ya zai mata tsawa har kuma Dad ka biye masa ka ce wai in zata yi aike ta aiki Yahya? Kenan shi ya fi ƙarfin ta aike shi ko me?. Gaskiya Dad wannan ba wanda za a zauna dashi bane, ina bayan Mum ka salleme shi kawai a tura mata wani ya dinga kaita duk inda yake so. Wani ƙazami dashi har yana da bakin da zai ce wai baza ta aike shi ba? Waye shi?."
Mum ta kuma ɗora da cewa, "ba kowa bane face ɗan iska gari na banza da wofi, matsayin numfashi su ma ba ɗaya bane amma Dear ya saka tana shaƙar gurɓataccen numfashinsa a mota ɗaya. Tsakanin ta dashi shine mahaifinta ya biya shi ya ne ya tayar da hayaniya a wajan zaɓe da sauran su, amma matsayin ya haɗa mota ɗaya da Narma sam-sam bai tashi ba."
Dad yayi murmushi yana kallon su ya ce, "na fi ku tsanar kusancin da ya samu da Narma saboda bashi da wannan matsayin kuma bazai taɓa samun sa ba har abada. Tsakanin Narma dashi kamar tazarar sama da ƙasa, turaren da Narma take sakawa sai ya siyi danginsa kaf balle kuma agogon da take ɗaurawa a hannunta. Ban haɗa shi da Narma dan ya yiwa Narma wani abun ba, na haɗa ta dashi ne na ɗan lokaci saboda lafiyar ta da zaman ta lafiya a Kano. Ke kin san wancan lokacin abinda ya faru da ita, tare musu hanya aka yi ana ƙoƙarin saceta in ba dan Allah ya tsare ba da yanzu wataƙila bata gidan nan. Shi kuwa kaf kano a san shi, in baka san shi ba ka san sunan shi, ana faɗar sunansa shikenan duk iskancin da ka ke ki dashi ka ajjiye. Saboda haka kawai na bashi Narma ya dinga kai ta duk inda zata je, in ba dan haka ba haɗa ido ma bai kai matsayin da Narma zata yi dashi ba."
Nabil ya ce, "Amma Dad akwai police a Kano da zaka ɗauka a haɗa ta dasu ta je duk inda take so, suna da bindiga shi kuwa bashi da ita, sun san aikin su shi kuwa me ya sani ban da wasa da wuƙa?. Gaskiya Dad ban ji daɗi ba, wani ƙazamin bagidaje dashi har yana da zarrar da kana yi masa