Showing 78001 words to 81000 words out of 87436 words

Chapter 27 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

kin fito dashi ya zama mutum shima kamar kowa. Kwanaki ya je kasuwa zai siya aka ce masa azurfa mai kyau daga ko dubu talatin ta fara, ya dawo na ce ya baka siyo ba wai ai ba hauka yake yi ba, ta sha zaman ta." Nayla tayi murmushi kamar yadda Didi take murmushin itama tana sake yiwa Nayla godiya.

Basu ji sallama ba kawai sun ganshi ya shigo falon, Didi ta kalle shi ta ce, "shigowa babu sallama Omar?." Kallon Didin ya yi kafin ya kalli wacce take zaune a kusa da ita yana aiyana wacce baƙuwa ce tazo musu gida. Nayla tunda taji an shigo an kuma ce Omar ta nutsu ta sunkuyar da kai ƙasa.

Sake kallon Didin ya yi ya ce, "Nayi sallama baki ji ba ne." Ajiyar zuciya Nayla tayi jin murya sa a kunnen ta, ido ya cikowa da ƙwallar kewarsa da take ji. Didi jin ajiyar zuciyar da tayi sai ta kalle ta a tausashe tace, "Nayla ki bar jin tsoron Omar don Allah, wannan ajiyar zuciya ta meye haka? Kar ki dinga cutar kanki fa." Nayla bata ce komai ba domin Didi baza ta gane ba, ita ba ajiyar zuciyar tsoron sa take yi ba, ta soyayyar da take yi masa ce.

Ta kalli Omar ta ce, "ga tsaraba Nayla ta kawo maka daga Saudia." Sarai ya gane Nayla ɗin ya haddace sunanta tsaf a wajan Didi, har mamakin haddace sunanta da yayi yake yi, da zarar ta ce Nayla fuskarta zata zo idonsa. Bai san me yasa hakan ba amma ya ɗauki hakan a yawan kiran sunanta da Didi take yi ne, da kuma faɗan da ta yi masa a gabanta. Basarwa yayi kamar bai gane ba ya ɗage gira sama ya ce, "Wace haka?."

Wani iri Nayla taji a zuciyarta, amma jin muryarsa na kore waccan damuwar. Didi ta Harare shi bata yi magana ba ta ce, "ga tsarabar sai kayi mata godiya, nima ta gwangwaje ni da doguwar riga. Kuma irin ta jikinta sak, ni sai yanzu ma na lura" ta faɗa tana nuna masa.

"Kin gode" ya faɗa yana niyar juyawa. Didi ta ce, "kai baka gode ba?." Ya kalli Didi ya kalli Nayla da take zaune kamar munafuka, shi fa wallahi haushi take bashi ba kamar in ya tuna faɗan da Didi tayi masa a gabanta, tayi masa faɗa tana wajan kuma ta hana shi ɗaukar mataki sannan ta shigaba da shigowa gidan su. Lokaci ɗaya yaji haushinta na sosa zuciyarsa. Ya ce, "ai ban roƙa ba ko?." Didi taji babu daɗi cikin takaici da jin kunya take kallon sa, in da ba a gabanta bane ba da sauƙi, amma a gaba idon mutum akwai cin fuska sosai.

Sai ya samu kansa da kallon Naylan da take zaune, baƙin gani ya yi domin kuwa murmushi take yi ga kuma hawaye yana sakkowa daga idanun ta. Ƙaramin tsaki ya yi dan haushi yaso ya bata, duk da yaga hawaye amma hawayen bai kama da na jin haushi ba. Ganin kallon da Didi take yi masa sai ya ce, "an gode" daga haka ya fita ta harari bayansa ta ce, "kaji dashi bahagon mutum kawai. Ni mamaki ma nake yi da Narma ta iya dakon soyayyarka zuwa yanzu, ko da wanne yanayi ka ke soyayyar oho."

Dam gaban Nayla ya buga bata san ta ɗago tana kallon Didi ba, ganin tana hawaye jikin Didi ya yi sanyi ta ce, "yi haƙuri kinji Nayla, don Allah ki yi haƙuri." Nayla bata ce komai ba dan labarin soyayyar tasa take so taji.

Ganin Didi bata sake cewa komai a kai ba sai Nayla ta ce, "Didi yana da budurwa ne?." Didi ta ce, "yana da wahala dai, Omar Ina ga wata budurwa kema ban da abin ki. Ɗazu dai ya gama furta min da gaske yana son yarinyar kuma ya shirya aurenta ta ko wanne hali. Ko waye zai bashi auren ƴarsa oho."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Nayla ta faɗa a bayyane ba tare da ta sani ba.


*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

             ©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 23.*


Jin dogon salatin da Nayla tayi Didi ta kalle ta da mamaki, Nayla tayi saurin cewa, "Kuma itama tana sonsa? Taɓ bata san waye shi bane." Jin abinda ta ce sai Didi tayi dariya ta ce, "wallahi tana son Omar matuƙa Nayla, har nan tazo ta zube min akan na saka baki Omar ya saurareta. Amma tsabar wulaƙanci irin nasa a gaban idanunta yake cewa in ma yaudarar sa tazo yi yafi ƙarfinta. Shi da ita ya ce mata shi bazai yi soyayya da ita ba kar ta sake gangancin furtawa, kuma fa ƴar manya mutane ce wallahi, mahaifinta shine Senator Kano central a yanzu. Omar yana yiwa mahaifinta aikin siyasa, kin san ƴan siyasa suna son irin su Omar a tafiyar su. To shine fa da zata zo Kano ya ce Omar ne zai dinga kaita duk inda zata je saboda ya yaba dashi, daga nan dai sai ta fara sonsa."

Nayla tana ji amma bata fahimtar me take cewa, tayi tsitt zuciyarta na bugawa a guje, sai goge ido take yi bata so hawayen da ya taru a ciki ya zubo. Didi ta cigaba da faɗin, "A hankali dai shima ya fara sonta, sonta ya fara dai ko ba so bane shi ya sani. Ban da hauka irin na Omar ina shi ina wannan yarinyar? To baya jin magana, ya ce min tunda ya ɗauki hanya bazai karkace ba, ni wallahi tsoro nake ji kar a cutar dashi.."

Nayla bata iya magana ba tayi shiru zuciyarta na bugawa sosai har zazzaɓi take ji yana neman rufe ta. Jin tayi shiru sai Didi ta ce, "ki daina tsoron sa don Allah, abinda ya yi miki da yanzu bazai miki ba."

Nayla tayi murmushin yaƙe ta ce, "ba tsoron sa nake ji ba Didi, kawai na tafi tunani da mamakin sa ne. Daman zai iya son wata mace? Lallai tayi sa'a ko wacece."
"Mtsww! Meye abin sa'a dan Omar yana son wata? Rashin sa a ne ma ai wata ta fara sonsa ni a wajena. Meye abin so a Omar don Allah?. Farar fata ko kyaun fuska? Allah dai ya shirya kawai."

Nayla tayi murmushi bata ce komai ba dan kanta ya yi mata nauyi sosai kwanciya take da buƙatar yi. Miƙewa tsaye tayi ta ce, "Didi bara na koma wajan Hajja." Did ta ce, "To Nayla. Na gode Allah ya bar zumunci. Zan aiko miki da mutuminki shinkafa da wake shi nake dafawa." Nayla tayi murmushi ta ce, "to Didi" ta faɗa tana fita kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki.

Tana fitowa tsakar gidan taji muryarsa ya yi ƙaramin tsaki ya ce, "to ni ƙaramin yaro ne da wani abun zai same ni a hanya? Lafiya naje gida." Nayla tana takowa inda yake tana jin zuciyarta na cigaba da bugawa dan ta san da budurwarsa yake waya. Tana zuwa kusa dashi ta ji ya ce, "kar ki dame ni!" Sai ya yanke wayar fuskarsa ba yabo babu fallasa.

Ya ɗago ido suka haɗa ido daidai lokacin da hawaye ya sakko daga idanun ta. Kallon ta yake yi da mamakin abinda ya saka ta kuka tunda yaga tana hawaye a wajan Didi, kusan ko yaushe in zai ganta kuka take yi bai sani ba ko kukan ne yake mata daɗi. Da sauri tazo zata wuce doguwar rigar jikinta harɗe ta zata faɗi tayi saurin dafa bango bata faɗi ba, yana tsaye shi dai yana kallon ikon Allah dan kallon ta yake yi. Da sauri ta fice shi kuma ya yi tsaki ya ce, "tunda ba a nutse ki ke ba ai dole ki nemi faɗuwa, yarinyar ta cika rawar kai" ya faɗa yana shiga ɗaki.

Nayla a guje ta shiga falon Hajja ko kula Hajja da Salma bata yi ba ta wuce ɗaki a guje ta faɗa akan gado tana sakin kuka mai sauti. Hajja da Salma suna jiyo sautin kukan nata Hajja ta kalli Salma ta ce, "Salma wai me yake damun ƙawar ki ne?." Salma ta ce, "Wallahi Hajja ban sani ba, amma tun waccan tafiyar ta na lura tana cikin damuwa, dana tambaya sai ta ce babu komai."

Hajja ta ce, "ki duba har rama tayi fa, gaskiya tana cikin damuwa ya kamata ki tambayeta ki ji abinda yake damunta. Ko ki yiwa takwararta magana tunda ku biyu ne ƙawayen ta." Salma cikin damuwa ta ce, "to Hajja. Amma tabbas tana da damuwa, ki duba da farin ciki ta fita amma ta dawo a wannan yanayi. Gaskiya akwai abinda yake damunta sosai." Hajja ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba amma tana tunanin abinda ya damun jikar ta ta.

Nayla kuwa kuka take yi kamar ranta zai fita, in ta tuna Omar yana son wata mace sai taji sabon kuka da hawaye yana ambaliya daga idonta. Zuciyarta fara harbawa take yi kanta na juyawa, kanta ya yi nauyi haka ƙirjinta ma ya yi mata nauyi sosai.

Shikenan ita a haka zata gama rayuwa da dakon sonsa, tunda gashi yana da wacce yake so kuma har yana cewa zai je ya samu mahaifinta. Shikenan ta ta ta ƙare, sai dai ta mutu da sonsa ba tare da ya sani ba. Kalaman Didi take tunowa ta fara girgiza kai ta ce, "Ko da zan mutu ni bazan ce ina sonsa ba, bazan faɗawa Didi Ina sonsa ba, bazan faɗa ba" ta faɗa tana kuka sosai tana kwanciya a kan gadon jiki na rawa.

Sai da tayi kuka mai isarta sannan ta iya yin shiru ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta zauna tayi shiru tana salati. Wayarta ta ɗauko ta kira Baba Salisu da ya kawo ta ta shaida masa gobe yazo ya ɗauke ta fasa kaiwa ranar Sunday.

Salma ce ta shigo bayan ta gama wayar ta zauna kusa da ita ta ce, "Nayla a duniya a baki da ƙawaye masu baki shawara kamar ni da Twiny, ana kallon ki an san kina cikin damuwa, ki faɗa min abinda yake damunki."

Kallon Salma tayi jin ta ce Twiny sai ta ce, "Sayyadi...Driver Hajja, yana nan ya kai ku gidan Twiny?." Salma ta ce,"yana nan." Nayla ta miƙe ta yafa mayafin doguwar rigar ta ce, "na fasa kaiwa jibi a garin nan gobe zan koma Kaduna, muje ya kaimu ko zuwa anjima ne ma dawo." Tare suka fito suka faɗawa Hajja inda zasu je tayi musu a dawo lafoya suka fita.

Jidda tayi murnar ganin Nayla a gidan ta suka baje a falo dan sun saba da Salma sosai. Salma ta kalli Jidda ta ce, "Jidda wani abun da yana damun Twiny ki wallahi, nayi-nayi ta faɗa min taƙi faɗa. Tsabar damuwa wai Nayla ce take cewa ta fasa yin kwana biyu a Kano gobe zata koma Kaduna. Kowa ya ji wannan magana sai ya yi mamaki sai kuma ya tambaya meyasa." Twiny ta kalli Salma ta ce, "tun a Saudia muka yi maganar nan da ita, amma abin yawa yake sake yi yana bani mamaki" ta kalli Nayla ta ce, "Nayla don ki faɗa min waye wannan da ki ke so."

Salma ta ce, "wai zaman akan soyayya ne? Da yake bata faɗa min ba ta ce kawai mu zo nan." Jidda ta kalle ta ta ce, "akan soyayya ne Salma, wani take so shi bai ma san tana sonsa ba."

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Lallai Nayla tana cikin azaba mai tsanani." Jidda ta ce, "tayi addu'a a Saudia amma ta ce soyayyar bata raguwa sai ma sake sonsa da take yi, nace ta nemi zaɓin Allah in shine alkhairi Allah ya kawo silar da zai fara sonta shima. Amma sai tayi murmushi ta ce ko da yana sonta auren sa da ita da wahala ya yu."

Suka kalli Nayla a tare da take hawaye Salma a raunane ta ce, "Nayla waye wannan?." Nayla ta goge ido ta ce, "Sanin waye bashi da amfani, ku taya ni addu'a kawai Allah ya kawo min mafita. Twiny bani paracetamol kaina ciwo yake yi."

Ba musu ta tashi ta kawo mata haɗi da ruwa ta sha kafin Jidda ta ce, "amma faɗa mana zai iya sakawa ki ji sauƙi a zuciyarki, kin san babu wanda zai ji labarin daga bakin mu." Nayla tayi murmushi ta ce, "qaunar da zaku nuna min shine ku yi min addu'a."

Ganin ta dage taƙi faɗar waye sai suka ƙyaleta suna ta hira har ita, dan ta ɗan sake amma da ta tuna sai hawaye. Sai tara na dare suka baro gidan Twiny zuwa gidan Hajja. A nan Hajja take faɗa mata ga abinci Didi ta kawo mata kaɗam ta iya ci ta ajjiye ta kalli Hajja ta ce, "Hajja gobe zan koma Kano, na kira driver Abiy zai mayar dani gida."

Hajja ta kalle ta tace, "Hauwa'u an fasa kaiwa jibin?." Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Na fasa Hajja. Na tuna akwai abinda zan yi a gidan, kuma ranar ranar litinin Ina da aiki." Hajja ta ce, "To Hauwa'u Allah ya kiyaye hanya ya nuna mana goben, Allah ya yi miki maganin damuwarki." Ta amsa da amin daga nan bata sake cewa komai ba, Salma tana kallon Labarina ita kuma ta miƙe ta shiga cikin ɗaki.

Kamar yadda ta fada washe gari da ƙarfe goma na safe driver ya zo daga Kaduna, sai da ta bari ya huta ya ci abinci a wajan Hajja bayan sallar azahar suka ɗauki hanyar Kaduna.

Ko a can kasancewar babu wanda ya san da dawowata, da yake ta asabar ce Abiy yana gida shi da Yaya Ahmad tayi sallama a falon ta shiga. Yaya ya ce, "A'a, mutanen Kano." Murmushi tayi ta ƙaraso ta zube akan carpet ta ce, "Abiy ina yini."
"Lafiya lau Mamana, ya kika baro Hajja?."
"Lafiya lau, tana gaishe ka. Ga saƙo ta ce a baka." Ya karɓa yana cewa, "Hajja bata gajiya da hidima in dai aka je sai ta bayar? Na kuwa gobe sosai. Zan yi mata waya na yi godiya."

Da Yaya suka gaisa kafin ya ce, "mutanen kano, ba sai gobe zaki dawo ba daman?." Ta yatsine fuska ta ce, "Gajiya nayi kawai na kira Baba Salisu na ce ya zo ya taho dani yau." Ya yi dariya ya ce, "ikon Allah, zaman Kanon ne kuma ya ishe ki?." Tayi dariya kaɗan Abiy ya ce, "nima nayi mamaki, bata faɗa min ma zata taho ba, sai Salisu ne yake cemin ita zai ɗauko tayi amsa waya jiya, na ce to sai ka dawo. Gaskiya zan faɗawa Hajja taci tarar ki kin gudo kin barta."

Nayla tayi dariya ta miƙe ta shiga wajan Mama. Itama tayi mamakin ganin ta suka gaisa daga nan ta koma ɗakinta tana sauke ajiyar zuciya. Zaman Kano ai ba nata bane, indai tana son kanta da zaman lafiya dole ta bar shi.

Da daddare Mama ta shiga wajan Nayla ta same ta ta yi shiru ita kaɗai. Zama tayi kusa da ita ta ce, "Nayla." Nayla ta kalle ta ta ce, "Na'am Mama."
"Tunanin me ki ke yi haka?."
"Babu komai Mama."
"Haba Nayla, kowa ya ganki ya san kina cikin damuwa mai yawa. Meyasa baza ki faɗa min ba? Ko dan bani na haife ki ba?."

Nayla ta girgiza kai ta ce, "A'a Mama ba haka bane, babu damuwar ne shiyasa." Mama ta zo kusa da ita ta riƙe hannunta ta ce, "uwa nake a wajanki, na haife ki na yi jika dake Nayla. In baza ki iya faɗa min damuwar kiba wa zaki faɗawa? In baki furta min abinda yake damunki ba wa zaki fadawa?. Uwa ce fa ni, ko bani da maganin damuwarki in nayi miki addu'a Allah zai amsa." Nayla kalaman Mama suka karya mata zuciya ta fara share hawaye. Mama ta sake nutsuwa ta ce, "faɗa min Ina jinki."

Nayla ta ce, "Mama babu komai, in akwai zan fada miki bazan ɓoye ba." Mama tayi murmushi ta ce, "shikenan Nayla. Allah ya yi albarka, ki fito ki ci abinci" daga haka ta tashi ta fita tana tabbatarwa da kanta ƙarya Nayla tayi mata, amma zata tambayi Jidda dan ta san ita ta san dalilin damuwar Nayla.

••••••••

Washe gari Didi ta shiga gaishe da Hajja ta kuma yiwa Nayla sallama dan fita zata yi kar ta shiga bata nan tarar da Nayla ta tafi, tayi mamaki sosai Hajja ta bata labarin a yadda ta shigo gidan da yadda ta ce ita ta fasa zama. Didi ta ce, "Allah ya sa ba Omar ne ya tsorata ta ba, dan ke baki ji ajiyar zuciyar da tayi da ta ganshi ba. Ni wallahi tsoron nasa da take ji ya fara bani tsoro." Hajja ta dinga dariya tana faɗin ba wani tsoro kawai akwai abinda yake damunta ne.

*Abuja*

Kamar ko yaushe suna zaune gabaɗaya suna hira Narma ta kalli Dad ta ce, "Dad." Ya kalle ta ya ce, "Narma." Narma ta ce, "mun gama magana da Faruk ya ce zai zo ku gaisa." Sai kuwa Najwa ta ce, "Awwnn! Ki ce shima dai yanzu da gaske yana yi ko Sis?."

Aka yi dariya Dad da fara'a ya ce, "da gaske ki ke?." Ta ɗaga kai alamun da gaske kafin ta ce, "yana so ka bashi date da time ɗin da zai zo." Dad ya ce, "wow! wannan abin farin ciki ne sosai. Inda zai iya zuwa ranar Monday zan so hakan, zan kira minister mu zauna tare domin mu tarbe shi" sai kuma ya kalle ta ya ce, "Ko kuma ranar Monday da aiki?."

Narma ta ce, "Dad ko yaushe ne zai zo indai a kaina ne. Zan faɗa masa in ya amince ranar monday ɗin zai zo." Mum da take dariya ta ce, "oh my god! Narma....." Narma tayi dariya ta ce, "Mum I love him so much, my feelings for him are impossible to hide" ta faɗa tana murmushin sannan ta ce, "then he loves me too." Nabil yayan ta ya ce, "Ma sha Allah, muna taya ki murnar samun wanda ki ke so." Tayi murmushi ta ce, "thank you bro, let me go and call him" ta faɗa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login