Showing 9001 words to 12000 words out of 87436 words
Chapter 4 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt
shigar Omar wannan hali saboda yawan aibata yaran mutane da yake yi Allah ya ɗorawa na sa. Amma ta tabbatar da Allah ne ya rubuta faruwar hakan a gare su, tana kuma sake gode masa yadda aka so su wulaƙanta a duniya basu wulakanta ba sun samu rufin asiri daidai gwargwado.
Shi kansa Omar ɗin yadda aka so ya lalace bai kai haka ba, duk da ta san tasirin addu'arta ne da ta malaman islamiyyar da take zuwa su taimaka mata da addu'a kansa. Duk da ana kallon su a matsayin masu cin kuɗin haram amma ita ta san ba haram suke ci ba shiyasa maganar mutane akan wannan baya damun ta. Da wannan tunanin tayi alwala ta fito falon ta samu baya nan ta kashe kayan wuta na falon ta koma ciki.
Washe gari.
Kamar yadda Omar ya saba bai cika bacci bayan sallar asuba ba, gari yana haske ya fita motsa jiki bayan ya dawo yayi wanka ya shirya. A lokacin Didi ta fito tsakar gidan shima ya fito ya shirya cikin ƙananun kaya kamar ko yaushe. Riga ce fara a jikin sa sai ta sama da ya ɗora baƙa mai zip amma bai kulle zip ɗin ba ya zama ana ganin farar. Sai dogon baƙin jeans da ya saka, sai takalmi wanda ya rufe ƙafarsa gabaɗaya. Kallo ɗaya in kayi masa baza ka ce yana taɓa dabanci ba saboda gabaɗaya yanayinsa bai gwada hakan ba, wani lokacin kana kallonsa zaka tabbatar da tantiri ne, wani lokacin in ka kalle shi sai kaga kamar ba shi ba. Murmushi tayi tana kallon sa kafin ya ce, "Ina kwana Didi."
Sai da ta ƙaraso kusa dashi sannan ta ce, "Ka tashi lafiya?."
"Lafiya lau, na shirya zan wuce, a yau zan dawo ba kwana zan yi ba."
"Baza ka ci abinci ba?."
"Uhum bana jin yunwa." Ta girgiza kai ta ce, "To Allah ya dawo da kai lafiya."
"Amin. In akwai abinda ki ke so su Tk suna nan." Tayi murmushi ta ce, "To a dawo lafiya." Ya ɗaga kai kafin ya juya ya fita daga gidan.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t
*Book 1*
*P 03*
*ABUJA*
*11:00am.*
Senator Sagir Sani yana zaune a babban falo mai kyau da ƙayatarwa ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana ƙadawa. Su biyu ne shi da wani abokinsa mai kuɗi da mulki kamarsa. Yanayin yadda suke magana zai baka tabbacin sun saba sosai. Sen Sagir ya kalli abokin na sa ya ce, "Wallahi shine abin ya dame ni, bana son zuwan Narma Kano gabaɗaya, kai ka san abinda ya faru kwanaki."
Minister ya kalle shi ya ɗan dariya ya ce, "Haba Senator, yanzu meye abin damuwa a nan? Wancan lokacin ma ai akasi aka samu yanzu kuma baza a maimaita irin sa ba. Duk jam'ian tsaron da suke Kano sai hankalinka ya tashi dan Narma zata je can?."
"Kai baka san yadda na tara maƙiya bane shiyasa ka ke faɗar haka."
Minister ya sake yin dariya ya ce, "ko shekara zata yi a Kano babu abinda zai sameta, akwai fa masu tsarom lafiyar ta ka manta ne?. Akwai police da za a bata, in ta kama a bata sojoji ma duk normal ne ba abin damuwa bane." Sen ya kalle shi ya ce, "kuma fa haka ne. Ni na san da wanda zan haɗa ta."
"To ka gani, meye na damuwa?."
Wayar Senator ce tayi ƙara ya duba kafin ya saka a kunne ya ce, "Ya shigo mana." Sauke wayar ya yi ya kalli minister ya ce, "Yanzu mutumin zai shigo." Minister ya ce, "Waye kenan?."
"Masu bada ransu a kan mu mana, wanda nake faɗa maka ina da shi a Kano."
Minister zai yi magana Omar ya bayyana a falon da sallama cikin dakakkiyar muryarsa. A tare suka kalle shi suka amsa Senator yana kallonsa yana murmushi har ya ƙaraso ya zauna akan kujera kamar yadda suke akan kujera kana ya ce, "Barka da safiya Senator."
Murmushi ya yi sosai ya ce, "Tiger! Ka tashi lafiya?."
Omar ya ɗaga kai sannan ya ce, "lafiya lau" ya kalli Minister da yake kallonsa ya ce, "Barka da safiya." Minister yayi murmushi ya ce, "barka." Sen ya kalli minister ya ce, "minister wannan shine Tiger! Babban makami na a garin Kano, Tiger ga Minister" ya faɗa yana kallon Omar da burgewa.
Minister ya ƙare masa kallo ya ce, "wai shine Tiger ɗin da ka ke bani labari ko yaushe?." Sen ya amsa yana kallo Minister shi kuma ya zare glasess ɗin idon sa yana kallon sa ya ce, "Wow! He seems really nice, babu wanda zai kalle shi ya ce he's the one. Kalle shi fa kyakykyawa kamar balarabe." Sen yayi murmushi ya ce, "shiyasa ake masa laƙabi da damisa, komai cikin nutsuwa ake gabatar dashi babu hayaniya balle ɓata lokaci."
Minister ya sake kallon Tiger da yake kallon wani wajan daban kamar ba dashi suke magana ba, fuskar nan a cushe kamar ko yaushe. Minister ya ce, "Dan samari ka burge ni fa, gabaɗaya yanayin ka ya bani mamaki sosai." Kallon Miniter ya yi a kasalance ya ce, "na gode." Sen ya kalli Minister ya ce, "jiya baka ga ya saka an kama wani da ya ƙwacewa wani waya sannan ya kashe shi ba? Maganar da take trending kenan a media ai."
"Yeah...yeah..I saw it. Ya bani mamaki sosai Sentor." Yayi murmushi ya kalli Tiger ya ce, "Tiger!." Ya jiyo ya kalle shi ba tare da ya amsa ya ce, "Daman magana ce akan zaɓen chairman da za a gabatar da kano. Kai ka san na mu shine a DPD so bama buƙatar wata damuwa da zata haifar mana da matsala shiyasa na kira ka." Omar ya kalle shi ya ce, "kamar ko yaushe zan maimaita, babu abinda zai faru. Amma mun jima da daina tayar da hayaniya a wajan zaɓe, an daina jiwa kowa ciwo, amma na tabbatar da komai zai tafi yadda ake so."
Minister ganin yadda Tiger yake magana sai ya murmusa ya ce, "Tiger I like your confidence." Kallo minister yayi amma bai ce komai ba dan ba kasafai ya cika so ayi masa turanci ba, ba komai yake fahimta yadda ya kamata ba shiyasa baya so ma ayi. Senator ya sake kallon sa ya ce, "na san in kace babu matsala babu ɗin, shiyasa nake matuƙar jin daɗin aiki da kai."
"Na gode" ya furta a taƙaice ba tare da ya saki fuska ba balle murmushi.
Sen ya ce, "Magana ta gaba; Akwai daughter na da zata zo Kano biki next week,ina so duk inda zata je ka kasnace a kusa da ita saboda an taɓa attacking na kashe ta kwanaki baya. Nafi yarda da kai akan jami'an tsaro dan na san zaka fi bani abinda nake so. Kuma mutanen Kano duk sun sanka babu wanda zai kawo mata raini in tana tare da kai, Kana ganin kana da damar Hakan?." Tiger ya girgiza kai yana tunani, aiki da Sen yana matuƙar kawo kuɗi, shi kuma yana buƙatar su a yanzu. Zai karɓa ne kawai saboda kuɗi da yake so wanda ya ke adanawa saboda bikin Didi zai iya zuwa ko yaushe, kuma shine uba shine uwa a gareta, duk abinda ya kamata shi zai yi.
Hakan ya saka ya ce, "Akwai dama, amma bana kwana a wani wajan in ba gida ba. Zan iya zama tare da ita daga safe har dare amma a gida zan kwana."
"No problem, buƙata ta daman ka kasance da ita din a duk inda zata je, If possible ka zama mai kai ta ko ina."
"Ka ɗauka an gama" ya faɗa yana kallon sa.
Sen ya yi murmushi ya ce, "Dakyau Damisa!." Ɗan sakin fuska yayi kaɗan ya juya suka haɗa ido da Minister da tun ɗazu kallon sa yake yi dan shi mamaki yake bashi sosai, maganarsa da yanayin komai ya yi masa.
"Hello Dad, how are you?" Narma ta faɗa tana shigowa falon amma sai ta tsaya cak ganin mutane biyu a zaune. Minister ya kalleta ya yi murmushi ya ce, "Our Barrister." Tayi murmushi ta ce, "Daddy good morning."
"Morning my dear, how's your day going?."
"Been good Dad. Ina ilham?."
"Ilham tana Canada, tayi miki wayo ta tafi phd."
"Oh Dad! I'm so tired from studying, I really need some rest" ta faɗa tana ɗan sauke numfashi kaɗa tare da juya ido alamun gajiya.
Minister ya yi murmushi ya ce, "As your wish." Kallon Tiger tayi da yake zaune kamar bai san ma ta shigo ba amma a zuciyarsa yana so ya tuna inda ya san maganarta, dan tunda tayi sallama ya ɗau murya amma ya kasa gane a ina yana santa.
Ita kuma Narma ta ɗauka tare suke da Minister hakan ya saka ta ce, "Hiiii" ta faɗa tana kallon Tiger wanda ya ɗago idanunsa ya watsa shi a cikin nata. Da sauri ta kawar da kai jin idanunsa a idonta kamar jan wutar lantarki, mamaki take yi waye wannan haka da idanunsa suke da ban tsoro a kallo ɗaya haka?. Shima ya ɗauke kansa ba tare da ya amsa ba dan lokaci ɗaya ya gane itace wacce suka gani da Didi jiya a tv.
Sen ya kalle ta ya ce, "Narma ina aikin?." Cikin shagwaɓa ya ce, "Dad I need to talk to you about something ."
"Alright, ki koma gida zan shigo in na gama."
"Dad ka yi sauri."
"Okay Daughter." Yana faɗa ta fita da sauri.
Kallon Tiger ya yi sannan ya ce, "She's my second daughter Narma, Itace wacce nake maka magana a kai. Itace wacce na amince da kai na baka ragamar kula da ita." Omar ya kalle shi ya ce, "babu damuwa." Ya girgiza kai cikin gamsuwa dan ya gama amincewa da aikin Omar.
Sen ya ce, "Akwai inda zaka je in ka bar nan?." Omar ya ɗaga kai alamun eh ba tare da ya yi magana ba.
"Okay I think it's okay, zaka iya tafiya. In yaso in lokacin tafiyar na ta yazo zan sanar da kai. Zan tura maka kuɗin mota."
Minister ya kalli Omar kafin yayi magana ya ce, "Tiger ya kamata ace ni na biya kuɗin motar zuwa garin nan, zan iya samun account number ɗina ka?." Omar ya kalle shi kai tsaye ya ce, "Me zai hana?." Ya karanto masa account number shi kuma ya saka masa kuɗi. Omar da ya ji ƙarar shigowar saƙo wayar sa ya ce, "na gode."
Minister ya ce, "you deserve it, kar ka damu. Yadda ka ke yin komai a nutse ya burge ni sosai, Nima zan so na shiga cikin wanda za a dinga taimakawa." Omar bai ce komai ba ya kalli Sen da yake kallon sa sai ya ce, "Zamu yi magana Tiger, na san in kana nan babu matsala."
Miƙewa Omar ya yi ya ce, "A duk inda nake matsala bata zama, koda tana wajan da naje zata kama gaban ta.Kamar yadda ruwa da wuta basa haɗuwa waje ɗaya haka ni da matsala bama zama waje ɗaya." Sen yayi murmushi cikin jin daɗi ya ce, "ni na san da wannan."
"Na bar ku lafiya" ya faɗa yana fita da hanzari cikin takunsa na isa da ƙasata.
Minister ya kalli Sen bayan ya fita ya ce, "Amma wannan yaron sam bai yi kama da ƴan daba irin na mu ba, Anya kayi bincike akansa sosai?. Ka duba fuskarsa fa, irin kyawawan mazan nan ne masu kwarjinin tsiya." Sen yayi dariya ya ce, "kai ka san bazan fara mu'amala dashi ba in ban san shi ba, na san shi tun da jimawa na kuma san komai akansa. A kaf kano tsoron yaron nan ake ji in dai a ɓangaren daba ne, har ta kai ta kawo ƴan sanda su kan neme taimakonsa a ɓangaren kama wani ko wani abun. Duk yadda ka kai ga jin kai jan wuya ne da yazo waje ya kalle ka ya ce ta shi ka bi wannan ɗan sandan sai ya je. Dabarsa mai tsafta ce duk da a sanin da nayi masa a baya yafi haka jagaliyanci. Jikinsa mai matuƙar tsafta ne, baza ka taɗa ganinsa ka ce ɗan daba bane, amma kallo ɗaya zaka yi masa gabanka ya faɗi."
Minister ya ce, "Amazing! Ya burge ni sosai fa, especially yadda yake magana da izza kamar shi ne senator ɗin."
"Bai yarda da wulaƙanci ba, tun farkon haɗuwa ta da shi ya faɗa min wannan. Kai baka ganin akan kujera nake akan kujera yake baka yi mamaki ba?."
"Nayi mamaki sosai, na saba ganin thugs suna warin wiwi da sun ganka su zube a ƙasa suna magana mara kan gado, But he's different gaskiya."
"That's why I choose him, kar ka yi mamaki in nace maka bai jima da fitowa daga prison ba."
Minster ya ce, "a yadda ka ke bani labarinsa prison a wajan irin su ai is just normal, kamar a shiga gida ne a fito."
"Ya yi hidima a lokacin zaɓe, yana daga cikin wanda suka bani kujerar da nake kai. Sannan ka san shi baya kisa a lamarinsa, in ya zauna a ake zaɓen ma ganin sa zawo yake saka maza balle ya ɗauko wuƙa. In kaga ya zubarwa da mutum jini shi ya so, Minister, totally Tiger is different"
Minister ya yi murmushi ya ce, "I see. But yana da karatu?."
"Bashi da ilimi, bana tunanin ya yi SSCE."
"Ya aka yi ka ke mu'amala dashi kai da baka zama inuwa ɗaya da wanda bashi da karatu?."
Sen ya yi dariya ya ce, "shi ai daban da sauran mutane. Shi rayuwarsa ya ke sadaukar min, dan in aka kashe shi akan aikin da yake yi min an kashe banza da wofi, kuma ina amfani dashi ne daga lokacin ya wuce shikenan. In ba dan haka ba shi da ganina sai dai in a waya." Dariya suka yi gabaɗaya minister ya ce, "Yaran ba su da hankali, muna gina rayuwar mu suna ɓata ta su."
"Rashin ilimin kenan."
"Kaga in ka haɗa Narma dashi babu sauran damuwa."
Sen yayi dariya suka tafa kafin Minsiter ya ce, "Yaushe zamu yi bikin Narma ne?." Sen ya ce, "tana da damuwa, taƙi mayar da hankali a kai. Akwai ɗam Sarkin Gombe yana sonta amma wai Gombe tayi mata nisa, Ina jin dai da Asharfa ɗan gidan gwaman Katsina za a yi."
Minister ya ce, "wow! yaron yana da hankali sosai."
"Sosai ma kuwa, Maganar baza tayi nisa ba ina so ta nutsu sosai ne."
"Hakan yana da kyau, a barta ta zaɓi abinda ta ke so." Daga nan suka cigaba da tattauna abinda ya shafe su kafin Dad ya shiga ciki minister ya fita.
Dad yana shiga falon Narma ya kalla ya ce, "Daughter waye ya baki izinin yiwa Tiger magana a falo? Waye shi ɗinki da zaki kalle shi ki ce masa hiii? Shi bai miki magana ya girmama ki ba sai ke zaki yi masa magana?. What kind of nonsense is the?." Narma ta turo baki gaba ta ce, "Dad who's Tiger? I don't know him."
"Guest ɗin da kika zo kika samu tare dashi a falo."
"Ohh Dad! daman shine tiger din? But ba kace ɗan daba bane ba?."
"Yes he's."
"But dad, he looks so handsome and decent."
Yayi tsaki ya ce, "look Narma! Ya kamata ki san matsayin da ki ke dashi, dan bai yi kama da ɗan daba ba ba haka yana nufin in kin ganshi ke zaki yi masa magana ba. Babu ruwan ki dashi, aiki yake yiwa babanki ya biya shi, bana son magana ta sake haɗa ki dashi kin ji ko?." Narma ta ce, "Okay Dad, Ka san halina, ni mutane ma ba isa ta kallo suka yi ba balle shi da ba mutum ba, Na dauƙa tare da Daddy suke tha's why na yi magana. But ba shine jiya ya saka aka kama wani a Kano ba?."
Hararar ta yayi sai ta yi ziping bakinta ta ce, "Sorry Dad." Ya sake kallon ta ya ce, "what is your problem?."
"Dad I need money."
"Shine dalilin da ya saka ki ka bini falo?."
"Yes. Zan yi order ashobi na bikin Samra." Yayi tsaki ya ce, "okay zan tura miki." Tayi murmushi ta ce, "thank you dad."
"Ya maganar saurayinki Ashraf?." Narma tayi dariya ta ce, "yau zai zo." Sen ya ce, "zuwa yanzu ya kamata ayi magana ayi bikin ku ko?." Tayi farrr da ido ta ce, "okay dad." Da mamaki yake kallon ta jin ta amsa abinda bata taɓa amsawa ba ya ce, "are you ready?."
"Sure" ta amsa tana kifta ido cikin murmushi.
Sen ya kalli Mum ta da take shigowa falon ya ce, "My dear your daughter she's ready to get married." Mum ta yi dariya tace, "ya kamata daman ai" ta faɗa tana zama akan kujera.
Narma tayi dariya ta ce, "Dad ya maganar zuwa kano?." Sen ya ce, "Yauwa maganar zan yi miki daman, Kin ga tiger ba?."
"Yes dad."
"To da shi zan haɗa ku a Kano ya zama escort ɗinki kuma driver, duk inda kika shiga yana tare dake na tabbatar bazai bari wani abu ya same ki ba."
Mum ta ce, "Tiger! Kana so kace da ɗan daba zaka haɗa min yarinya?." Sen ya ce, "Nafi yarda dashi akan police, zai kula da ita bazai bari wani abu ya same ta ba." Mum ta ce, "this is bad idea Sen, Ta ya zaka haɗa ɗan daba da daughter suna shaƙar numfashi ɗaya? Matsayinsu ai ba ɗaya bane. Ta ya zai shiga motar da Narma take ciki? Hakan ai babban abin kunya ne kuma is so disgusting" ta faɗa tana yatsina.
"Na sani, na kuma sam abinda nake yi. Kuma daman su aikin su su yi a biya su, in ba dan zai kula da ita ba ai ko kusa da ita bai isa yazo ba balle har ya samu damar yi mata magana. To na yarda da aikinsa hundrent percent, in nace kar ya bari wani ya kalle ta ma zai iya shiyasa na zaɓe shi. Kar ki damu wannan ba komai bane aiki ne kawai."
Narma ta ce, "Dad ni tsoronsa ma nake ji, kuma ta ya za ka haɗa ni dashi bayan bana tunanin ya taɓa zuwa school?." Dad yayi dariya ya ce, "Daman ai ya kamata ki ji tsoronsa, yadda ki ke