Showing 75001 words to 78000 words out of 87436 words

Chapter 26 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

nan bai ƙara koda kalma ɗaya ba. Narma ta dinga murna tana farin ciki, shi kansa farin ciki yake yi, duk da wani lokacin sai ya ji kamar soyayyarta ta bar zuciyarsa, bayan kwana biyu sai ta dawo.

Duk da basa haɗuwa amma babu laifi sun saba a waya, da yake ba aikin yi ne dashi ba in dai zata kira shi zata same shi, shine dai bai cika kiran ta sosai ba.

Yau ta kama ranar juma'a kamar ko wanne sati Didi ta kammala abincin sadaka ta rabawa yara ta koma tana hutawa ya shigo bayan an sakko daga masallaci. Da kallo take binsa ya zauna ta ce, "har an sakko?." Gira kawai ya ɗaga alamun eh kafin ya kalle ta sosai ya ce, "Didi." Ta kalle shi  ba tare da ta amsa ba, ya ce, "ta ya zan iya gane Ina son wata?."

Da kallon rashin fahimta ta bi shi ta ce, "ban gane ba, me ka ke nufi?."
"Ina nufin in na fara son wata ta ya zan fahimci hakan?. A taƙaice ya ake gane soyayya?."

Didi da kallo take bin sa cikin faɗuwar gaba, babban tashin hankalin ta bai wuce kar ya ce yana son Narma ba, amma tunda ya tambaya zata faɗa masa dan tafi kowa sanin bai san soyayya ba. Didi ta ce, "To nima Omar ba wani sani nayi ba ai."

"Amma baza ki kasa yi min bayani yadda zan gane ba ai ko?" Ya faɗa yana tsare ta da ido. Didi ta ce, "Zuciyarka zata dinga bugawa a yayin da ka ganta, zaka dinga ɓata lokacin ka wajan saurarenta, zaka dinga jin shauƙi sosai koda sautin muryarta ka ji, zaka dinga jin zaka iya yin komai dan ka mallaketa. Sannan....." dakatar da ita ya yi ya ce, "iya wannan da ki ka faɗa ma ya isa."

Kallon fuskar ta yayi, cikin rashin tsoro ya ce, "Hakan yana nufin ina son Narma, daman na tambaye ki ne dan na tabbatar kuma na tabbatar ɗin."

Cikin tashin hankali Didi ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Omar ka san abinda ka ke faɗa kuwa?. Kana son Narma ka ce fa? Don Allah ka faɗa min wasa ka ke yi." Da mamaki ya ke kallon ta jin tayi dogon salati ya ce, "wannan salati haka Didi na meye? Bata cancanci na sota ɗin ba ne?."
"Omar kai ne baka cancanci ka sota ba, Omar ita ba ajinka bace, don girman Allah ka rufa min asiri ka bar maganar nan, Ina kai ina soyayya da ƴar gidan sanata Omar?."
"Kin zo a makare Didi, domin kuwa wannan asirin naki bazai rufu ba. Ina sonta kuma zan je har gaban sanatan na faɗa masa."

Didi numfashi ta ja kawai tayi shiru bata ce komai ba, dan babu amfanin maganr, ta san kuma wallahi sai ya aikata tunda ya faɗa. Hawaye yaga tana yi ya tausasa murya ya ce, "don Ina sonta shine ki ke kuka?."

Didi ta ce, "Omar bana so wani abun ya same ka, Ina ji a jikina soyayyarta bazata zama alkhairi a gare ka ba."
"Kin san gaibu ne Didi?." Jin tambayar da ya yi mata ya saka take kallon sa da mamaki, kenan dai da gaske son Narma yake yi tunda gashi yana yi mata wata bahaguwar tambaya.

"Ban san gaibu ba Omar, amma auren ka da ita da kamar wuya." Omar ya murmusa ya jingina da kujera ya ɗora ƙafa kan ɗaya ya ce, "ki taya ni addu'a kawai, amma kin san tunda na ɗauki hanya bazan karkace ba. Zan je har gidan su har gaban sanata na nemi auren ta, kin san bana jin tsoro komai kuma bana tsoron kowa. Ki kwantar da hankali ki daina kuka, babu abinda zai same ni sai alkhairi."

Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "ai shikenan" ta faɗa cikin rashin mafita dan ta san bazai bari ɗin ba kamar yadda yace. Ganin ta a yanayin damuwa sai ya yi ƙoƙarin kawar mata da tunani ya ce, "Ya zancen AbdulHamid? Kwana biyu bana ganinsa." Didi a sanyaye ta ce, "Ta ya zaka ganshi kullum kana ɗaki kana soyayya?."
"Hmm! Saura wata nawa bikin?."
"Ban sani ba" ta bashi amsa a taƙaice tana miƙewa ta shiga ɗaki ta bar masa falon.

Murmushi ya yi dan ya san haushinsa take ji, shi kam tunda ya ɗaura ɗammaara bazai kwance ba. Kiran Narma ne ya shigo wayarsa ya ɗauka ya ji ya ce, "Faruk na shigo Kano, Ina so mu yi magana da gaggawa, kuma zuwa dare zan koma Abuja. Na karo Mum gaisuwar rasuwa ne." Daƙyar ya ce, "maganar meye?."
"Ni dai Ina so mu haɗu, zaka zo ko nazo gidan ku?." Numfashi ya sauke kana ya ce, "kina ina?." Narma ta ce, "Ina guest house, amma ba wanda ka sani ba. Ina zaka zo zan baka address ɗin, ko kuma naje wancan da ka sani sai mu haɗu."

Shiru yayi yana nazari akan zuwan kamar bazai ce komai ba, ta san halinsa akan wannan shirun yanzu sai ya ɓata mata lokaci har lokacin tafiyar su ya yi. Ta ce, "please na faɗa maka da wuri zamu bar Kano."
"Zan zo" ya bata amsa taƙaice kafin ya kashe wayar. Ba jimawa yaji ƙarar messege ya miƙe ya fita daga falon.

        Da kayan jikinsa ya tafi tunda Didi ta laqaba masa saka mayan kaya ranar juma'a. Bashir ne ya kai shi a machine ya kuma saka shi ya tsaya ya jira shi ya fito su tafi. Kafin ya zo Narma ta sanar da zuwan da hakan ya saka kai tsaye aka masa iso zuwa harabar gidan. Kiran ta ya yi a waya ya ce, "ki fito." Narma a sanyaye ta ce, "don soyayyar ka da annabi Muhammad S.A.W ka shigo, ba don halina ba" ta faɗa dan ta san zai ce bazai ce bazai shiga ba.

Jin magiya da tayi masa sai ya kashe wayar bashi da zaɓin da ya wuce shiga inda nuna masa matsayin nan ne hanya. Tafkeken falo ne mai kyau da tsari, babu haukan ado a cikin sa amma ya tsaru irin sa ake kira da luxury parlour. Tana tsaye a falon cikin riga da siket na atamfa ta yi mata matuƙar kyau. Kasancewar atamfar baƙa ce sai ta haska farar fatarta sosai.

Ta ɗame kamar ko yaushe, daƙyar take iya motsawa a cikin siket din. Rigar kuwa tsabar kamata da tayi gabaɗaya ana ganin saman ƙirjinta, gashi bata da tsaho in ta ɗaga hannu ana hango cibiyarta. Kallon farko in kayi mata zaka ga shigar ta ƙara mata kyau, amma in ka nutsu zaka fahimci fidda tsaraici ƙarara a tare da ita.

Bai san yana kallon ta sai da yaji ta a jikinsa ta rungume shi da sunan welcome hug. Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, shi bai yi hugging nata ba kuma bai ƙoƙarin cire ta a jikinsa ba. "Nayi kewar ka" ta faɗa tana kwance a jikisa tana jin farin ciki da nutsuwa na shiga jikin ta. Maganar da ta faɗa ne ya saka shi janye ta daga jikinsa yana binta da shegiyar harara. Da yatsa ya nuna ta ya ce, "gargaɗi na karshe zan miki, kar ki sake aikata haka, kar ki sake cewa zaki riƙe ni, kar hakan ya sake faruwa in ba haka baza ki sake ganina a inda ki ke ba!."

Narma ta shagwaɓe ta ce, "I'm sorry, I just missed you ne shiyasa." Ƙaramin tsaki ya ja sai ta ce, "i'm apologize fa, smile please." Sake bashi haushi tayi dan shi baya son magana da turanci, duk abinda ta ce yaji amma baya ra'ayin ayi masa magana yaren. Murmushi tayi ganin ya sake tamke fuska, ita hakan ma yana matuƙar burge ta wallahi, sake ƙara mata ƙaunarsa yanayin sa yake yi a zuciyarta.

"Have a seat" ta faɗa tana nuna masa wajan zama. Kallon ta yayi da birkitattun idanunsa, yana ayyana dole ya taka mata burki akan turancin nan kafin hakan ya saka ya tsane ta. Bai musu ba ya zauna ta zauna nesa dashi kaɗan ta ce, "kayi kyau Faruk! Sai naga kamar ana ƙara maka kyau ne sosai." Kallon ta ya yi jin wata magana mai kama da zagi dan ya wuce zolaya, shi bai ce tayi kyau ba sai ita zata faɗa? Ina kyaun a wajansa.

Daman ta gama shirya center table ta kalle shi bata damu da rashin bashi amsa ba ta ce, "bismillah." Kallon abinda ta nuna ya yi ya kalle ta ya ce, "ki faɗa min dalilin ki na kira nan." Ta langwaɓar da kai ta ce, "Amma ka sha ko ruwa ne ko? Ni wallahi kamar baka yi kewata ba sai ɗaure fuska ka ke, don Allah kayi murmushi."

Kallon ta ya yi suka faɗa ido ya ce, "zuwan da nayi bai nuna miki abinda kike tunani ba?." Sai ta yi murmushi cikin zallar shagwaɓar da take sake canja masa yanayi ta ce, "haka ne my Faruk. Da kace zaka zo naji matuƙar farin ciki, domin kuwa na san tabbas na babban samu matsayi a wajan ka."

"To Ina jinki." Narma ta gyara zama ta ce, "Yaushe za ka zo Abuja ku haɗu da Dad ɗina? Ba a matsayin Tiger ba, a matsayin Faruk inlwa ɗinsa. Yaushe zaka zo?." Bata ji ya amsa ba hakan ya saka ta ce, "Ina so kaje don ya san da zaman soyayyar mu Faruk, bana son yin aure da wuri, amma tunda na fara sonka nake ji a zuciyata ina son yin aure da gaggawa."

Omar ya kalle ta yana wani tunani, ya rasa meyasa in ta yi zancen aure wani lokacin zuciyarsa bata karɓa, sai ya dinga ji kamar shi bazai aureta ba, sai ya dinga ji shi kamar ba aurenta yake son yi ba akwai abinda yake zuciyarsa ba aure ba. Ya kawar da tunanin ya ce, "na faɗa miki na shirya yin aure ne yanzu? Kuma shi ne ya ce nazo?."

"A'a, ni nake so kazo saboda ya san da kai ayi maganar aure a wuce wajan kawai." Kai ya girgiza ya ce, "baza ki samu matsala ba?."
"Babu wata matsala."
"To zan duba na gani, in na samu lokaci zan sanar dake sai ki faɗa masa." Narma tayi murmushin jin daɗi ta ce, "thank you my Husband to be. I can't wait to be your wife, I feel like na jawo lokacin da zaka kasance miji a gare ni. Ranar da aka ce na zama matar ka bazan iya bacci ba."

Gyara zama y yi ya ce, "Narma!." In ya faɗi sunan nan kamar ya soka mata abu a zuciya haka take ji, bata taɓa jin wanda yake faɗar sunan ta daidai kamar sa ba. Ta narke tana kallon sa ya ce, "kar ki sake yi min wani yare in ba hausa ba in muna tare kin gane?." Jin yadda ya faɗa a kausashe sai ta nutsu sosai ta ce, "in sha Allah bazan sake ba. I'm sorry..." hararar da ya yi mata ya saka ta tsorata sosai ta ce, "ka yi haƙuri" ta faɗa a sanyaye. Bata taɓa zaton soyayya zata saka ta tsoron wata halitta irin Omar ba, tsoronsa take ji matuƙa bata son abinda zai ɓata masa rai ko kaɗan. Shiyasa take kiyaye dokikinsa dan a zauna lafiya.

"Yaushe zaka saba dani ne Faruk? Ka kasa sakin jiki dani har yanzu. Ina sonka, da kai kaɗai nake so na rayu. Don Allah kar ka dinga amfani da rauni na akan sonka kana cutar dani." Kallon ta ya yi bai san lokacin da ya yi murmushi ba, kamar shashasha itama sai tayi murmushi ta ce, "na gode da wannan kyauta Faruk."

Miƙewa tsaye ya yi alamun zai tafi ta ce, "Zaka tafi ko ruwa baka sha ba."
"Zan sha wani lokaci" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba, dan in yana kallon ta wani ne yake shiga jiki sa take sai yanayinsa ya canja.

Miƙewa itama ta yi ta kalli window ta kalle shi ta ce, "Ga irin wajan zaman ka can a wancan gidan, naga kana son zama a gazebo, dole gidan auren mu kasance da gazebo saboda ka shiga ka huta" ta faɗa cikin son burgewa. Kallon ta ya yi kafin ya ɗauke kai ya ce, "kina tunanin samunta a aurena?."

Narma jin ya bata amsa sai ta sake karya murya cikin iyayi ta ce, "ko ba yanzu ba ko nan gaba. Kuma gidana da nake ginawa akwai."
"Gidan ki!" ya maimaita yana yi mata kallon bakin da hankali kafin ya sake cewa, "kina tunanin in Allah ya ƙaddara na aure ki ni Omar zan zauna a gidan da yake naki? Hmmm baki san Omar ba har yanzu, ki yi gaggawar canja tunaninki a kan hakan" ya sake cewa, "In har da gaske kina son auren Omar ki san irin tunanin da zaki yi" ya faɗa dan ya tuna mata, dan shi ba irin mazan da suke zama a gidan mata bane, gwara ya yi mata gargaɗi da babbar murya.


Narma a sanyaye ta ce, "Ina yi mana fata a rayuwar auren mu mu samar da ita."
"Dakyau!" ya furta yana fita ta biyo bayan sa tana ta yi masa shagwaɓa yana sharewa kamar bai gani ba ko kamar baya jin shagwaɓarta a jikinsa, yana ji kawai bazai nuna bane, dan in ya nuna mata shine a ruwa. A haka suka yi sallama ya fita ya samu Bashir na jiran sa suka koma gidan Didi.


         Bayan fitar Omar Didi tana zaune rana ta buɗe sosai tana shan iskar fankar solar taji anyi sallama. Amsawa tayi tana jiran mai shigowa sai kawai suka haɗa ido da Nayla. Didi ta wara ido ta ce, "Nayla!." Nayla tayi dariya ta ƙaraso kusa da Didi ta zauna ta ce, "Na'am Didi." Didi da farin ciki ta ce, "Saukar yaushe? Wannan bazata haka."
"Saukar ɗazu. Ina yini." Didi ta amsa da fara'a tana tambayar ya mutanen gida ta tabbatar mata da kowa lafiyar sa lau.

Didi ta ce, "wallahi nayi kewar ki Nayla, haka kawai nake ji bana so ki bar Kano." Nayla tayi dariya ta ce, "wallahi nima bana son barin Kano Didi, amma ya zama dole dan yanzu na fara aiki ma a can."
"Ma sha Allah, amma na taya ki murna Nayla. Allah ya sanya alkhairi ya kaɗe fitina."
"Amin ya rabbi. Na gode sosai Didi."
"Amma kwanaki zaki mana ko?." Nayla tayi dariya ta ce, "Ranar Sunday da safe zan tafi, kin manta na ce Ina aiki?." Didi ta ce, "kai! Wallahi ban ji daɗi ba. Amma babu komai in sha Allah ɗan Kano zaki aura, kin ga sai dawo Kano gabaɗaya mu dinga ganin ki."

Nayla tayi murmushi amma a zuciyar tana aiyana in sha Allah ƙaninki zan aura Didi, amma a bayyane sai bata ce komai ba. Didi ta kalle ta tace, "an sha saudia. Ina fatan kin roƙawa mutumin ki shiriya a wajan Allah kamar yadda na ce, kin yi min?."

Wani iri taji a zuciyarta, domin kuwa babu ranar da zata fito ta koma bata ambaci sunan Omar a addu'arta ba, ba wai tana cewa Allah ya bata shi bane, tana roƙon Allah ya shirya shi ya cire masa dukkan abinda yake yi ya dawo mutum kamar kowa. Ita kanta bata san sau dubu nawa tayi masa addu'a ba. Har ɗawafi ta yi akan Allah ya canja Omar, ta yi ɗawafi bama sau ɗaya ba.

A bayyane ta ce, "Nayi masa sosai Didi, ba ma shi kaɗai ba har da ke. A jikina nake jin Allah zai amsa da gaggawa." Didi ta ɗaga hannu ta ce, "Allah Amin" ta kalli Nayla ta ce, "na gode Nayla, Allah ya bar zumunci." Nayla tayi murmushi ta amsa da amin. Didi ta kalle ta tana murmushi ta ce, "wallahi Nayla haka nan Allah ya saka min ƙaunarki, Ina jinki kamar ƙanwata." Nayla ta murmusa ta ce, "nima Ina jinki kamar yayata Didi."

Didi tayi murmushi ta ce, "Amma Nayla naga kin rame, kin yi rashin lafiya ne?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "haka ake cewa na rame amma ni bana gani, lafiya ta lau kawai kiɓar nake so na rage." Didi tayi dariya ta ce, "ai baki da kiɓa Nayla, gaki nan ƴar chubby dake in kika rame ai baza ki yi kyau ba. Gaskiya ki daina." Nayla tayi dariya kawai bata ce komai ba sai ledar da ta shigo da ita ta miƙawa Didi ta ce, "ga tsabar ki."

Didi ta karɓa ta ce, "Nayla harda tsaraba? Ai ni iya addu'ar da kika yi min itace babbar tsaraba a wajena." Didi ta buɗe ta ga doguwar riga irin mai babban mayafin nan da ake yayi, original ƴar Saudia dan a yanayin jikinta ma zaka tabbatar da ba fa irin ƴan Nigeria ba ce. Sai zamzam da chocolate da kuma cross shoe. Didi ta fara godiya Nayla ta ce, "Didi yanzu ki ka ce ni ƙanwarki ce ko? Don Allah ki bari."

Didi bata daina ba ta cigaba da addu'a tana yi mata godiya. Nayla ta sake bata leda ta ce, "Ga na...." Sai ta rasa wanne suna zata kira shi, Omar zata ce ko Tiger? Didi kallon ta take yi tana so ta ji na waye, Nayla ta ce, "Na Yaya Omar."

Didi tayi dariyar tsokana ta ce, "A'a, harda su kaza a cin danƙoo? Kuma yaushe Omar ɗin ya zama Yaya Omar?." Nayla tayi murmushi ganin tana tsokanarta, ta karɓa ta buɗe taga doguwar riga irin ta maza mai dogon hannu, ga wata cover ƙarama mai kyau a ciki, ta ɗauko ta buɗe idon ta ya faɗa kan lafiyayyar azurfa mai bala'in kyau.

Didi ta kalle ta a sanyaye ta ce, "Nayla duk wannan na Omar ne? Azurfa da take da tsada a nan ƙasar ma balle a Saudia?. Bayan azurfa ma harda doguwar riga ga wani abu ma a ciki ina ji" ta faɗa tana fito da ƴar ƙaramar kwalba ta oil perfume ta ce, "ga turare. Nayla hidimar bata yi yawa ba?."

Nayla ta ce, "Haba Didi wallahi babu komai, an zama ɗaya kar ki damu." Didi tayi ta ce, "To Nayla, mun gode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci, Allah ya baki miji na gari." Nayla ta amsa da amin kafin Didi ta ce, "Su Omar an samu azurfa, daman hannun nasa babu komai kamar ba saurayi ba, kin taimaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login