Showing 72001 words to 75000 words out of 87436 words

Chapter 25 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

tayi murmushi tana girgiza kai ta ce, "Zaka amince da akwai soyayya Omar, zaka tabbatar da soyayya gaskiya ce a lokacin da ka fara son wacce ka ke so, daga wannan lokacin zaka tabbatar da soyayya ba film bace ko wucewar iska. Yanzu babu abinda ka sani sai ni, soyayyar Yaya da ɗan uwanta kaɗai ka sani, baka san ko wanne irin so ba sai ita, baka san son ko wacce mace ba sai ni, baka jin ko wacce mace a zuciyarka sai ni ɗin. A yanzu baza ka gane ba, sai zuciyarka ta fara son wata mace sannan zaka tabbatar. Yanzu meye mafita akan Narma?."

"Mafita kamar ya?."
"Ya zaka yi da ita?. Misali ace da gaske tana son naka, ya zaka yi mata?."
"Haƙuri zata yi Didi, me zan yi mata?." Didi ta ce, "Haka nake so naji ka ce, domin Narma ba kalar wacce zaka yi gangancin fara so bace, in ka bari zuciyarka ta yaudare ka ka fara sonta wallahi kaine a ruwa domin kaine zaka sha wahala. Mallakar Narma abu ne mai wahala a wajan namiji irinka, in kuma kaga hakan ya faru to sai dai tsananin rabo."

Omar ya murmusa kaɗan ya ce, "ban san meyasa kike faɗar wannan maganar ba, ni ban cancanci a soni ko a aure ni bane?." Didi ta girgiza kai ta ce, "ka cancanta mana, ka cancanta a wajan wanda ka cancani kaso a soka. A wajan Narma, ko a wajan masu matsayin na ƙasa da ita wallahi baka cancanta ba Omar. Ba maganar hasken fata ake yi ba, ba maganar kyau ko sajen fuska da ƙirar jiki ake ba Omar. Magana ake ta karatu da kuma kuɗi, magana ake ta asali mai kyau, in ma asali na kuɗi ko na sarauta. Omar duka wannan baka dashi, kaga kenan a wajan ta baka cancanta ba, ba ita kaɗai ba har masu biye mata."

Ransa yaji ya ɗan sosu akan maganar Didi, ya zuba mata ido yana kallon ta kafin ya ce, "Shi mutumin da bashi da karatu ko bashi da kuɗi ba mutum ba ne?." Didi ta ce, "Mutum ne mana Omar, amma a gidan Senator Kano central ba mutum bane wallahi."

Kallon Didi yake yi kawai bai ce komai ba, kamar zai yi magana sai ya fasa bai ce komai ba ya kawar da kai gefe. Didi ta tausasa ta ce, "Ka bata haƙuri Omar, in mahaifinta yaji tana sonka ma wani babban tashin hankalin ne, kar kaga kuna waya dashi ko kana zuwa inda yake yana yi maka dariya. Wallahi dariyar nan ta manufa ce Omar, ba tsakani da Allah yake sonka ba amfani yake yi da kai. Da zarar ya ji ƴarsa na sonka duk wannan zai gushe, saboda ba matsayin ku ɗaya ba."

A fusace Omar ya ce, "Saboda ita muslma ce ni kafiri shiyasa ki ke kiran ba matsayin mu ɗaya ba?." Mamaki ya bawa Didi ganin yaji haushin abinda tace, har ya kasa ɓoyewa ya nuna mata hakan. Didi ta ce, "a wajan su gwara kasancewar ka kafiri akan kaje a yadda ka ke kace kana sonta Omar."

Didi ta ta sake tausasa murya ta ce, "Ni don Allah ka rufa min asiri kar ka bari wannan kalaman nata ya yi tasiri a kanka, yadda na sanka baka bawa kowa ƙofa a rayuwarka itama kar ka bata, ka ɗauka komai ba komai bane ka manta da ita, ka toshe duk hanyar da zata bi wajan neman ka."

Omar ya zuba mata idanunsa yana zagawa dasu a fuskarta ya ce, "Yanzu kika gama faɗa min baka sanin lokacin da soyayya take shiga zuciyarka, nima in soyayyarta zata shiga zuciyata zan hana ne?."

Gaban Didi ya faɗi jin kalamansa, tsoron ta ɗaya kar taje ya fara son Narma ta shiga uku. Didi ta ce, "Addu'a zaka yi Allah kar ya baka ikon fara sonta." Baice komai ba ya fita yana mamakin wannan kalamai na Didi masu kama da rainin hankali. 

Didi da kallo ta bishi a bayyane ta ce, "Wai Narma ke son Omar...Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ya Allah ka kiyaye min ƙanina daga faɗawa tarkon soyayyarta, gwara ce itace take sonsa da ce shine yake sonta, gangancin fara son Narma kamar ganganci da rayuwarsa ne. Ya Allah kar ka bashi ikon fara son wannan yarinya" ta faɗa kamar zata yi kuka.


••••••
       Narma da zazzaɓi mai zafi ta sauka a Abuja, ta kira Najwa ta ce tazo ta ɗauke ta, ba jimawa sai gata ganin yanayin da take ciki sai ya bata tsoro ganin da gaske bata da lafiya kawai ta wuce asibiti. Sai bayan sun je asibitin an bata taimakon gaggawa sannan ta kira Mum ta sanar da ita.

Awa biyu tayi a asibitin suka koma gida an samu  zazzaɓin ya sauka. Bacci tayi sosai bayan sun koma dan har da maganin bacci aka bata, ta jima sosai tana bacci har dare sannan ta farka, da yake ta san ba sallah zata yi bata yi ƙoƙarin yin sallah ba tana kwance tana tuna kalaman Omar masu kama da sukar mashi a zuciyarta.

Tashi tayi ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta, wai itace take son namiji kamar Omar, ɗan daba wanda bashi da komai bai san komai ba sai riƙe wuƙa. Ita Barr Narma, manager director ta kamfanin mahaifinta, ita Narma da take juya kuɗin mahaifinta da suka haura billions wai itace take son wani da bashi da komai har yake mata wulaƙanci. Turarukan da suka kan madubin ta watsar, ta jawo madubin ya faɗi kasa ya tartwase a wajan, ta faɗa kan gado tana fashewa da kuka.

A guje Mum, Dad, Najwa da Nabil suka shigo  daƙin. Dawowar Dad kenan sun rako shi sama wajan ta suka ji sautin fashe-fashe daga ɗakin. Ganin yanayin da take ciki ya saka su ƙarasowa da gudu kowa yana tambayarta abinda yake faruwa. Bata iya magana ba sai kuka da take yi a jikin mahaifinta mai tsuma zuciya. Duk sun yi shiru suna surarem kukan da take yi, sai da tayi mai yawa sannan ta tsagaita sai ajiyar zuciya da take yi.

Najwa ta kawo mata ruwa Dad ya bata tasha yana kallon ta a nutse. Sai da yaga ta nutsu sosai sannan ya ce, "Me yake damun ki Daughter? Me ya faru kika shiga wannan yanayin?."

Narma murya a shaƙe ta ce, "I'm in love Dad." Dad ya kallo Mum ya sake kallon Narma ya ce, "kina nufin ki ce duk wannan damuwar da kike ciki saboda soyayya ne? You're in love, that's why you looks like this?." Bata yi magana ba sai lumshe ido ta tayi a jikin Dad bata ce komai ba.

Dad ya yi shiru bai ce komai ba Mum ta kalle ta tace, "Narma taso mu je ki ci abinci." Bata samu damar magana ba ta miƙar da ita tsaye suka fito falo ta zaunar da ita. Tea ta zuba mata ta miƙa mata ta ce,"Oya take it." Narma a sanyaye ta ce, "I want to brush my teeth first."
"Okay, Najwa kai ta bathroom." Najwa ta riƙeta ta miƙe tsaye, Dad ya ce, "take her to my bathroom, sai an gyara ɗakin ta, ki buɗe drawer akwai sabon brush." Da to ta amsa suka wuce zuwa ɗakin Dad.

Basu jima ba suka dawo, Narma ta zauna tana shan tea ɗin kaɗan-kaɗanan tana tunanin yadda suka yi da Omar. Sai da shanye tea ɗin tass suna ta yi mata sannu. Sai da ta gama ta nutsu sannan Dad ya ce, "akwai abinda ki ke so?."

Ta girgiza kai alamun babu ya ce, "okay, tell me your problems. Who is the guy you are in love with?." Ta yi shiru bata amsa ba, Mum ta ce, "Narma Dr ya tabbatar mana da kina cikin damuwa shine ya haifar miki da zazzaɓi ɗazu, yanayin muka same ki a ɗaki ya tabbatar min da maganar Dr gaskiya ne. Waye wanda ki ke so haka?."

Shiru tayi bata ce komai ba, Nabil yayanta ya ce, "Narma feel free ki faɗi abinda yake ranki, kar ki damu zamu yi supporting ɗinki hudrend percent." Narma tayi ajiyar zuciya ta ce, "Dad ku taya ni da addu'a saboda kamar bazai karɓi ni ba." Mum ta ce, "what! Kina nufin daman ke kike sonsa ba shi yake sonki ba?." Narma ta ɗaga kai alamun eh. Mum cikin wani yanayi ta ce, "damn it! Ta ya hakan ya faru Narma?."
"I don't know" ta faɗa kamar zatayi kuka.

Dad cikin rarrashi ya ce, "ɗan waye? Ɗan sarkin Dubai ne?" Ya faɗa yana kallon ta, dan a ganinsa duk wanda Narma zata so har haka kuma bai san tana yi ba, bai ma karɓeta ba, a ganinsa sai dai ɗan sarkin Dubai. In ba haka ba to waye zata iya wannan son da ya saka mata zazzaɓim damuwa? A ganinsa ko ɗan president albarka.

Narma ta katse shi ta ce, "Not at all. Dad...!" Ta faɗa tana jan sunan tare da kallon sa. Ta ce, "promise me you will allow me to marry him at any cost." Dad ya riƙe hannunta ya ce, "I promise you zaki aure shi indai yana sonki, abinda bazan amince ba shine in baya sonki bazan yarda ki aura shi ba." Ta yi murmushi ta ce, "Dad I'm Barr Nass don't forget, i will attract his attention."

Dad ya yi murmushi ya ce, "anything for you my daughter. Kema ki yi min alƙawarin damuwarsa baza ta sake baki damuwa har ki yi ciwo ba." Narma ta girgiza kai ta ce, "in sha Allah." Rarrashinta suka dinga yi suna bata baki har ta ware ana hira da dariya da ita.

Bayan Kwana biyu.

Narma ta tabbatarwa da kanta Omar shine farin cikin ta dole ta san ya zatayi kafin ta rasa ranta, duk da tayi ƙoƙarin ajjiye damuwar ta kamar yadda ta yiwa mahaifinta alƙawari amma soyayyar tana nan a tare da ita. Ta daure bata nemi Omar a kwanakin ba tana so taga zai kira ta ko bazai kira ta ba.

Abin mamakin bai kira ba kuma bai yi mata koda text ba, sai ta tabbatar da gaske bai ɗauki maganar ta da mahimmaci ba tunda gashi ya share ta bai kira ya ji ya take ba.

Shi kuwa Omar shi kansa ya san ya damu da lamarin Narma, daurewa kawai yake yi yana nuna bai damu ba amma a zuciyarsa ya damu da ita sosai ma kuwa. Bai san dalilin da ya saka ya damu ɗin ba, shi ba sanin so ya yi ba balle ya ce sonta yake yi. Bai taɓa ƙoƙarin kiranta ba,
dan shi kansa ya san bazai iya neman ta ba ko meye zai faru, dalilin da ya saka ya jure rashin jinta ya share ya bar tunaninta.

Kamar ko yaushe yana zaune cikin ƴan uwan sa ƴan daba ana meeting akan ƴan wata unguwa suna faɗa kuma ana cewa ƴan unguwar su ne. Yana zaune yaji kiran waya amma bai duba ba har suka gama meeting ɗin da bai ce komai ba, hankalin sa baya tare dashi shiyasa bai ce komai ba. Ana gamawa ya tashi ya nufi gida. Yana shiga ɗaki wayarsa sake yin ƙara ya ɗauko tare da zubawa number ido, har lokacin bai yi saving ba dan baya so ba, kawai baya so ya bada wata ƙofa da wani abun zai shiga ransa.

Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka tayi shiru bata ce komai ba shima bai ce komai ba. Nunfashinta kawai yake ji yana sauka a hankali, saukar numfashinta sai ya saukar masa da kasala sosai ya yi shiru bai ce komai ba.
"Da ban kira ka baza ka kira ni ba ko? Ka san damuwar da na shiga a kanka kuwa? Ka san har asibiti na kwanta saboda kai?. Saboda Ina sonka ka ke min haka ko Faruk? Shikenan na gode" ta faɗa a sanyaye.

Lumshe ido ya yi zuciyarsa na bugawa sosai, in ya ce bai ji daɗin maganarta ba ƙarya yake yi, in ya ce bai ji maganar ta na shiga zuciyarsa ba ƙarya yake yi, in ya ce bai ji rauni ya mamaye zuciyarsa ba ƙarya yake yi. Buɗe ido ya yi har lokacin bata sake magana ba yana dai jin nunfashin ta kamar ɗazu.

Shiru ya rasta tsakani har mintina biyu sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "shikenan ka gaishe da Didi."
"Ya hanya?" Ya tsinci muryarsa ya faɗa ba tare da ya shirya ba. Narma jin maganar sai tayi ajiyar zuciya mai nauyi ta ce, "hanya ba lafiya ba, ni kaina ba lafiya nake ba Faruk."
"Ayya Allah ya bada lafiya" ya faɗa a hankali.

Narma ta ce, "Amin,Thank you." Nan ma ya sake yin shiru bai ce komai ba, Narma ta ce, "Okay byee" ta faɗa tana yanke wayar da sauri. Shiru yayi yana kallon wayar yana mamakin kansa da ya tambaye ta hanya, to Ina ruwansa?. Numfashi ya sauke, ya saka a ransa tausayinta yake ji shiyasa haka da wannan tunanin ya share wancan.

•••••••

        Mutanen Saudia sun dawo Kaduna, Nayla har lokacin bata dawo daidai ba domin abinda take ji yafi ƙarfin zuciyarta. Nauyi take ji kamar dutse aka ɗora mata a ƙirjinta, wani lokacin numfashi wahala yake mata saboda nauyin da zuciyarta tayi mata. Washe garin da suka dawo Twiny ta juya Kano saboda mijinta ya gama komai na gida. Sai ta sake zama shiru-shiru bata da abokin shawara, gashi tana son zuwa Kano amma tana tsoron Abiy kasancewar bata jima da dawowa ba.

Kamar yadda ta zaɓarwa kanta kullum tana ɗaki a zaune sai ga autan su ya shigo ya ce Abiy yana kiran ta. Sai da ta daidaita nutsuwarta sannan ta fito ta same shi a falon da shi kaɗai yana kallon tv. Da sallama ta shiga ya amsa yana bita da kallo tare da tattara nutsuwar sa gabaɗaua a kanta.

Sai da ta zauna sannan ya ce, "Mamana dawo kusa dani" ya faɗa yana nuna amsa kan kujerar da yake. Ba musu ta tashi dawo kusa dashi ya fuskance ta ya ce, "Mamana baki da lafiya ne?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "bana son body language, ki yi min magana."
"Lafiyata lau Abiy." Abiy ya ce, "ƙarya ki ke yi, tun a Saudia kika canja gabaɗaya. A wancan lokacin na karɓi dalilinki ne kawai saboda kar na takura ki, amma ba dan na amince da abinda ki ka ce ba. Me yake damun ki kika koma haka? har rama naga kin yi, me ya faru?."

Nayla tayi shiru bata ce komai ba Abiy ya ce, "ban kai na ji damuwarki ba?." Da sauri ta ce, "A'a Abiy."
"To faɗa min."
"Babu ne shiyasa."
"Kar ki yi min ƙarya Mamana, ƙarya ba halin ki bane. Ki faɗa min gaskiya kafin na gano da kaina." Nayla ta ce, "da gaske nake Abiy, babu abinda yake damuna."

Abiy ya yi shiru yana kallon ta cikin nazari, bai yarda da abinda ta ce ba, ya san kawai bazata faɗa bane amma zai san yadda zai yi mata. Ya sauke numfashi ya ce, "shikenan. Ga offer ki" ya faɗa yana miƙa mata takarda.

Nayla murmushi tayi cikin farin ciki ta karɓa Abiy ya ce, "Federal inland revenue service ne. Ranar Monday zaki je ki gama duk abinda ya kamata." Nayla cikin farin ciki ta ce, "Abiy na gode, Allah ya saka da alkhairi ya biya ka da aljanna." Murmushi ya yi ya ce, "Amin Nayla. Sai zancen shagon ku keda Twinyn ki, za a ƙara muku jari ku cigaba da juya kuɗin, Kwana biyu ma ke bakya zuwa."

Nayla farin cikin samun aiki duk ya cika mata zuciyata, burinta a rayuwa kawai ta yi aiki shiyasa Abiy ya samar mata. Ta ce, "Abiy ni na rasa me zance saboda murna." Murmushi ya yi kawai yana kallon ta ya ce, "Nayla kenan. Akwai abinda ki ke so bayan wannan?."

Nayla tana murmushi ta ce, "babu komai Abiy. Kawai Ina so na kaiwa Hajja tsarabarta ne." Murmushi ya yi ya ce, "Nayla sarkin zuwa Kano, Ke dai kina son shiga Kano." Tayi dariya ta ce, "Kano da daɗi Abiy."
"Shikenan, in kin shirya sai ki je gobe ki yi kwana biyu ki dawo."

Farin cikin da Nayla taji ko da ya miƙo mata offer bata ji ba, hakan ya bayyana a kan fuskarta sosai da murya ta ce, "Na gode Abiy, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan mahaifa, Allah ya jikan Ummana." Murmushi ya yi ya ce, "Amin. Bani offer ɗin kinje ki shirya." A guje ta miƙe ta shiga ɗaki tana murna.

Cikin murna ta yi ajiyar zuciya ta zabura ta buɗe trolly bag ta fara zuba tsarabar Hajja da ta Salma har da Didi ma. Wata maroccon jallabiya ta maza ta ɗauko kalar baƙa mai kyau da santsi ta kalla ta ce, "zata yi masa kyau sosai." Murmushi take kamar shashasha, tana hango in Omar ya saka rigar ya zai koma. Da haka ta gama zuba kayan a jakar tafiya Kano.

Wayarta taji tana ƙara da ta duba sai ta ga Abiy ne, tana ɗauka ya ce, "Mamana ki bar zuwa Kano gobe a gama settling aikin nan da kika samu, in aka gama kafin ki fara aiki sai ki je ki dawo. Yanzu ake sanar dani gobe ake so ki je." Sai jikinta ya yi sanyi ta ce, "to Abiy" daga haka ya yanke wayar ita kuma ta zauna gabaɗaya murna ta koma ciki.

Nayla Anya kuwa🤔


*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 22.*

Kwance tashi babu wahala a wajan Allah, a hankali zuciyar Narma ta fara rinjayar zuciyar Omar, tun tana kira yana ƙin ɗauka har ta kai in bata kira shi bama baya jin daɗi. Gashi da shegiyar izza shi bazai iya kiranta ba, in ta kira kanta ta yiwa, in bata kira ba bazai kira ba.

Tun yana ƙaryata kansa akan yana sonrta har ya amince da gaske yana sonta, kuma shima ya shirya auren ta kamar yadda ta shirya aurensa. Ranar da ya bayyana mata kamar zata yi hauka saboda murna, duk da bai yi wasu dogayen kalamai ba, kawai ya ce mata shima zai iya aurenta daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login