Showing 27001 words to 30000 words out of 87436 words
Chapter 10 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt
ya yiwa su Kawu ba. A lokacin ya shigo tsakar gidan ya tsaya yana zagaye ransa a matuƙar ɓace zuciyar sawuya, fuskarsa tayi wani irin ga jijiyoyin kansa sun tashi. Abokin karawa kawai yake nema ya wuce a kansa.
"Assalamu alaikum, Didi na da......" Maganar Nayla ta maƙale saboda wanda suka haɗa ido dashi a cikin gidan. "A'uzubillahi minal shaiɗanir rajim!" Nayla ta faɗa a tsorace cikin gigicewa dan bata san ma ta yi ta'awizin ba. Omar ya sake wara ido a kan fuskarta cike da mamaki da fusata ya ce, "Shaiɗan!" Ya faɗa yana kallon Nayla tare da takowa zuwa inda take.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 08.*
Nayla baya take ja yana takowa inda take idanunta a waje ƙirjinta yana up and down saboda tsoro da tashin hankali. Shi kuma yana takawa inda take saboda ɓacin rai da zallar haushi da takaici a zuciyarsa. Sai da ta jingina da bango ya dakata da bin bayanta, jikinta na rawa kar kar kar bakinta na motsawa amma ta kasa magana.
"Ni ki ke yiwa korar shaiɗanu? Wacece ke! Waye ya turo ki gidan nan!?."
Tsawar da ya yi ya sake firgita Nayla ta runtse idanunta cikin fargaba da tashin hankalin da bata taɓa shiga irin ta ba. Numfashita ya kusa ɗaukewa ganin ƙaramar wuƙar da ya zaro daga ƙasan takalminsa ya ɗago ya ɗora wuƙar akan wuyanta yana sake wara idanunsa waje ya ce, "Wacece ke!?."
Nayla bata taɓa shiga tashin hankali kamar yadda take a ciki yanzu ba, ƙafafunta sai rawa suke yi saboda tashin hankali, zuciyar tacike da dana sanin abinda ya shigo da ita gidan. "Omar!" Didi ta faɗa da hanzari tana zuwa ta janye Omar daga kusa da Nayla da take zubar da hawaye. Sharaf Nayla ta faɗi a numfashi ta na sama da ƙasa saboda tashin hankali.
"Baka da hankali ne Omar? Kashe ta zaka yi?." A fusace ya kalle ta ya ce, "Wacece ita? Ban ce kar na sake ganinta a gidan nan ba?."
"Gidanka ne da sai wanda ka ke so ne zai shigo? Na ce gidanka ne!?."
"Ba gidana ba ne, amma ina da ikon hana duk wanda bana so shigowa cikinsa. Ban son sake ganin wannan yarinyar a gidan nan, bana son sake ganin ta!" Ya faɗa da ƙarfi yana nuna Nayla da take zaune a baya kamar sumammiya.
Didi ta fusata sosai ta ce, "baka isa ba, baka isa ka hana baƙina shigowa gidan nan Omar. Wai kai Meya ke damunka? Meye a cikin kanka? Meyasa baka aiki da hankali ne kai?." Idanu ya sake warawa waje yana kallon Didi jin kalamanta musamman na ƙarshe ta ce, "eh na faɗa, Meyasa baka aiki da hankali? Meyasa ko yaushe zuciya ce take sarrafa tunaninka ba ƙwaƙwalwarka ba?." Kai yake girgizawa Didi ta sake cewa, "wacce irin zuciya ka ke da ita ne kai? Meyasa baka mantuwa baka yafiya?."
"Eh bana yafiya, kuma bazan yafe ba. Iya yau kin cece shi ya sha, amma wata rana zamu haɗu a lokacin da babu ke ko?."
"Ƙanin mahaifinka ne, ko ka ƙi ko ka so dole ka kira shi da Kawu." Ƙasa ya yi da muryar da yana girgiza kai cikin ƙunar rai ya ce, "Har abada bani da dangin mahaifi, bani da dangin mahaifiya, kamar yadda na rasa iyayena suma ki ɗauka sun mutu. Ke kaɗai na sani dangina, bayan ke babu wata halitta a duniyar nan da ta rage da zan kalle ta matsayin dangi!" Ya ƙarashe maganar da ƙarfin gaske.
"Ƙarya ka ke Omar, ƙarya ka ke. Kawu ƙanin mahaifinka ne duk da abinda ya aikata maka ba a canjawa tuwo suna. Baba Adamu Yayan mahaifiyarka ne, duk da abinda ya yi maka ba a canjawa tuwo suna. In dai har ka manta da dangin iyayenka to zaka manta da wanda suka haife ka Omar!."
Hannu ya saka ya daki kansa ya juya ya sake juyowa ya kalle ta ya ce, "iyayena sun rasu dan haka bani da wani a duniyar nan in ba ke ba."
"Nima ɗin baka ɗauke ni komai ba Omar, tunda baka yin abinda nake so." Sake kallon ta ya yi ya ce, "na rantse da Allah Didi, in na sake ganin ƙafar wani dangin Baba a gidan nan ranar bazai kwana lafiya ba. Zan iya ɗagawa dangin Mama ƙafa, amma bazan taɓa ɗagawa dangin mahaifina ƙafa ba. Ke kin san waye ni, kin kuma san abinda zan yi da wanda bazan yi ba."
Didi sai ta kasa magana dan baza ta iya da taurin kansa ba, tayi murmushin takaici kawai ta kalli Nayla da take zaune a wajan har lokacin kamar bata numfashi.
Da sauri ta ƙarasa inda take ta ɗago ta jikinta ta ce, "Nayla! Nayla buɗe idon ki don Allah." A hankali Nayla ta buɗe ido tana kallon Didi sai jikinta ya cigaba da rawa ta ƙanƙame Didi tana kuka sosai.
"Yi haƙuri Nayla, ki daina kuka don Allah ki yi haƙuri" ta faɗa tana shafa bayanta a hankali cikin tausayinta da mugun takaicin halin Omar.
Omar takaici kamar ya kashe shi haka yake ji, cikin tsananin ɓacin rai da takaici da tsawa ya ce, "in na sake ganin yarinyar nan a gidan nan bazan ƙyaleta ba." Cikin ɓacin rai da fusata Didi ta ce, "Sai ta shigo! Omar sai ta shigo in ka dama ka kasheta ka kaima ka ga in za a barka da rai. Na gaji da wannan shirmen na ka, kullum kana girma amma kana cin ƙasa, sam baka aiki da hankali balle ka san abinda zaka yi."
Runtse idanu yayi yana jin zafin kalamanta, Babban abin haushin ma a gaban yarinyar da ta taɓa yi masa faɗa kwanaki a gabanta, yau ma gashi an maimaita har tana cewa yana shirme baya aiki da hankali. To shi wanne gangancin ne ma zai bari ya bar yarinyar da lafiyarta? ai in bai taɓa lafiyar jikinta ba bazai ji daɗi ba. Bai taɓa jin haushin wata halitta kamar ita ba, saboda itace mace ta farko da aka yi masa faɗa a gabanta.
Zai sake magan ta dakatar dashi cikin fushi ta ce, "Dallah Malam fita ka bani waje kafin na tsinke ka da mari." Sak ya yi yana kallon ta jin wai zata mare shi, kallon ta yake yi cikin mamaki dan abinda ta faɗa bata taɓa furtawa shi ba sai a lokacin. Ganin kallon mamakin da yake mata sai ta ce, "ko kana ganin ban isa na mare ka ɗin ba ne? In kana ganin ban isa ba ka cigaba da tsaya min kai wallahi sai na mare ka."
Kai yake gigirzawa yana kallon Nayla da take kwance a jikin Didi tana sauke numfashi ya ce, "na gama haddace fuskarta, duk abinda ya faru tayi kuka da kanta" yana faɗar hakan ya fita daga gidan cikin baƙin ciki da ƙunar zuciya. Wai kamar shi Omar Tiger Didi take cewa zata mara a gaban wata yarinya, ƙarshe ma akan yarinyar take zancen zata ta dake shi.
Didi ta kalli Nayla bayan ya fita ta ce, "Nayla yi haƙuri don Allah ki nutsu, ki dawo nutsuwarki ji." Tashi tayi da sauri ta ɗauko mata ruwa mai sanyi ta bata, ai kam Nayla ta sha ruwan nan sosai dan tana buƙatarsa. Hijjabin jikinta ta cire mata ta riƙeta ta ce, "taso mu shiga ciki." Daƙyar Didi ta iya ɗaga ta suka shiga falon Didi ta zaunar da ita akan kujera ta kunna mata fanka sannan ta zauna kusa da ita tana yi mata firfita.
Bata sake magana ba sai da taga Nayla ta ɗan nutsu hawayen da take yi ma ya tsaya sannan ta sake kawo mata ruwa ta ce, "karɓi ki sha Nayla." Nayla kallon ta tayi sai ta ɗan zabura Didi ta riƙe ta ta ce, "kar ki ji tsoro, babu abinda zai miki baya cikin gidan ma gabaɗaya. Yi haƙurk ki sha ruwa." Ba musu ya sake karɓat ruwa ta sha tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudu.
Didi ta kalle ta ganin ta dawo nutsuwarta sai ta dafata ta ce, "ki yi haƙuri Nayla, ban saka ki shigowa gidan nan dan ki shiga wannan yanayin ba, wallahi ban san zai dawo ba da ban ce ki zo ba. Ki yi haƙuri don girman Allah, da na san hakan zai faru da ban ce ki zo ba."
Nayla jin yadda take mata magiya cikin sanyim murya sai ta ce, "Haba Didi, don Allah ki daina yi min magiya haka babu komai Didi."
"Dole na roƙeki ki yafe min ai Nayla, da ban je har gida na taho dake ba da haka bai faru ba, tun farko kin nuna bakya so amma na takura miki. Gashi na saka ki a halin tsoro da fargaba wanda ya kusa sakawa ki suma ki fita daga hankalinki, ki yafe min kin ji? bazan sake takura miki akan zuwa gidan nan ba."
Nayla ta ce, "babu komai Didi, don Allah ki daina bani haƙuri." Didi ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "ransa ne a ɓace sosai kin tarar dashi akan gaɓa shiyasa, zaki ga ni kaina bai ƙyale ni ba saboda in ransa ya ɓaci ya kan rasa hankalinsa na wani lokaci sai daga baya yake fahimtar abinda ya faru. Bayan fitar ki baƙon da ya zo shine silar ɓacin ransa, na tabbatar ba dan haka ba da bazai kalle ki ba, saboda nayi masa magana ranar da ya yi miki wannan abun."
Nayla ta riƙe hannun Didi ta ce, "babu komai Didi ya wuce." Ta yi murmushi ta ce, "na gode. Amma ki rage tsoronsa har haka, ki koyi dakewa koda zaku haɗu a wani waje" tayi murmushi ta ce, "Dan na san baza ki sake shigowa gidan nan ba, Nayla ban ga laifinki ba Omar abin tsoro ne a wajan wanda bai san shi ba, amma in ka san shi normal mutum ne kamar kowa" ta faɗa tana ƴar dariya tana kallon Nayla da take yaƙe.
Didi ta ce, "ina jin aure zan masa wataƙila zafin kansa ya ragu." Nayla bata san san da murmushi ya subce mata ba, ta wara ido ta ce, "Aure! Kuma sai a samu wacce zata aure shi? Taɓɗi! amma sai dai mai taɓin hankali." Sai bayan tayi magana ta fahimci a bayyane tayi maganar. Didi tayi dariya sosai ganin ta saka Nayla murmushi ta ce, "Ni da nake cewa ƴar gida za a yi dake? Shikenan tuwo na mai na, Yayar amarya kuma Yayar ango."
Wani irin numfashi Nayla ta sauke mai nuni da ta rasa abinda zata ce. Didi tayi dariya ta ce, "wato kin kasa magana ma kenan?." Nayla tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Didi ta ce, "mu je na raka ki wajan Hajja in na soya awara sai na kawo miki." Ai kamar jira Nayla take ta miƙe tana neman hijjabinta.
Didi ta bita da kallo dan ƙananun kaya ne a jikinta ta ɗora dogon hijjabi ta fito ta ce, "Irin wannan kyau haka Nayla? gaskiya ina yiwa ƙanina kamu." Taɓe fuska Nayla tayi ta kalle ta tace, "Didi wallahi kina saka zuciyata cikin fargaba, don Allah ki daina faɗar haka bana so." Didi tayi dariya tana cewa, "na daina faɗa, yi haƙuri." Nayla ta saka hijjabin ta, itama Didi ta saka suka fito.
Ganin tana dafe kai ya saka Didi ta ce, "ciwon kai ko?." Ta ɗaga mata kai alamun eh, Didi ta ce, "sannu, Allah ya ye." Ta amsa da amin suka fita ƙofar gidan. Nayla ganin Didi bata rufe gidan ba sai ta ce, "baki kulle ƙofar ba." Didi tayi murmushi ta ce, "a tunanin ki za a shiga ayi mana sata ne? Gidan su Omar Damisa ne fa, gidan nan ko almajiri baya shiga yayi bara balle ɓarayi." Nayla ta ce, "Ya ci suna Tiger ɗin ai, ba shi da sabo." Didi ta yi murmushi Nayla ta girgiza kai bata kuma cewa komai ba amma zuciyar ta tana jinjina girman baƙin halin sa.
A zaune suka samu su Hajja ita da Salma suna cin abinci. Didi ta ce, "Hajja ga Nayla na dawo da ita na kuma yi mata laifi, a taya ni roƙon ta tayi haƙuri." Hajja ta ce, "me ya faru ke da ƙanwarki?." Didi ta ce, "ita da Omar suka gamu wallahi, gamuwar bata yi daɗi ba sam kuma duk ni ce sila. Ni nazo har goda muka tafi, da ban mata dole ba da baza ta je ba, yanzu haka kanta ciwo yake yi."
Salma ta yi dariya ta ce, "Shiyasa ni da gidanki sai kallo daga nesa." Didi ta zaunar da Nayla ta ce, "ki yi haƙuri Nayla." Nayla ta ce, "Haba Didi, tun a can ki ke bani haƙuri, don Allah ki bari."
"Na bari, Na gode sosai Allah ya baki miji na gari. Zan koma gida yanzu amma zan shigo anjima." Nayla ta ce, "to Didi." Didi ta fita zuciyar taduk babu daɗi akan abinda Omar ya yi mata.
Ai Didi tana fita Nayla ta zare hijjabinta ta cillar ta ɗaga wuya sama ta kalli Salma ta ce, "Salma duba wuya na ki ga babu yanka da wuƙa." Salma ta kalli wuyan ta ce, "babu komai, Meye ya faru?." Nayla ta ce, "wannan mutumin an yi ɗan tijara kuma ɗan bala'i. Ina shiga ban ma kula dashi ba fa, ina ganinsa sai nayi ta'awizi ashe yaji haushi, wai korar shaiɗan nayi masa, to meye marabarsa da shaiɗan ɗin?."
Salma ta ce, "shine ya shaƙe ki?."
"Ke faɗar tashin hankalin da na shiga ai ɓata baki ne, ba na jin ma abinda yake cewa saboda tsoro da fargaba. Kawai naga ya ɗora min wuƙa a wuya daga nan ƙwaƙwalwata taje hutun rabin lokaci, dan numfashi na kaɗan ya rage bai ɗauke ba."
Salma ta ce, "to shi wai bashi da hankali ne ko ne? Faɗa masa aka yi in yayi miki wani abun ƙyale shi za a yi?." Nayla ta ce, "shima ya san wasa yake yi ai, babban abin mamakin ma wallahi har ita Didin bai bari ba, kin ji yadda yake zazzaga bala'i kamar ba ita yayarsa ba?. Sai magana yake akan shi bashi da dangi da sauran su."
Salma ta ce, "wannn mutum dai ya zama annoba a unguwar nan, almajiri fa baya shiga gidan saboda tsoro." Nayla ta ce, "haka Didi take faɗa min yanzu, ke ni naga bala'i ai. Ruwa kuwa ina jin na sha yafi leda uku." Hajja da take jin ta tayi dariya ta ce, "kin cika tsoro ne kawai Hauwa'u."
"Hajja tsoro halak ne, dan naji tsoronsa ai ban yi laifi ba, da tuni an kawo miki ni ya yanka min wuya."
"Haba dai, shima ai bazai fara ba, tsorataki yake yi kawai."
Salma ta ce, "amma abin yayi yawa wuƙa fa? Wai bashi da dangi ne?." Hajja ta ce, "kin taɓa ganin wanda bashi da dangi?." Salma ta ce, "to suna ina? Ai ko dan wannan jagaliyancin da yake yi ya ci ace na gaba dashi sun tsawatar masa." Hajja ta yi murmushi ta ce, "wai ba gidan babar ku Sa'adatu zaku je ba?." Nayla ta miƙe ta ce, "bara na canja kaya mu tafi" ta faɗa tana shiga ciki dan ta canja kaya su tafi.
***** Didi haka ta koma gidan gabaɗaya zuciyarta da jikinta babu ƙarfi, haka ta soya awarar da suka gama ta rage wata ta saka a fridge dan ta ga da yawa sosai, ta zuba wata a food flakas ta zuba sauce ɗin ta fita da kanta ta kaiwa Hajja, Hajja take sanar da ita su Nayla sun fita itama ta koma gida.
Kamar yadda baƙon ta ya ce zai zo bayan la'asar hakan ce ta kasance, ita ta manta da zuwan na sa sai da yayi mata waya ya ce gashi nan ya tawo ta tuna. Dole ta miƙe tayi wanka tana fatan Allah ya sa shine na ƙarshen masu zuwa neman aurenta. Ba jimawa ta gama shiryawa ya zo ta sauke shi a harabar gidan dan bata shiga da baƙo ciki saboda bakin mutane.
Sun jima suna tattaunawa kuma ta yaba da kalamansa da nutsuwarsa da alama da gaske yake, ya kuma faɗa mata duk abinda ake faɗa a kanta shi kuma bai damu ba ya amince da auren ta a haka. A nan ya yi masa kwantancen gidan Kawu da lambar wayarsa dan yaje su tattauna inda dai gaske yake, bai jima sosai ba ya yi mata sallama ya tafi da alqawarin zuwa gidan kawu.
Haka kawai ta ke jin kanta da farin ciki fiye da sauran masu zuwa neman aurenta, zuciyarta lokaci ɗaya taji tayi na'am da shi sosai ta kuma ji daɗi da har ya tafi Omar bai shigo ba, duk da ya san labarin Omar ɗin da komai amma a yanayin da Omar ɗin ya ke a ranar tsaf zai kwafsa.
Bata da uwa kuma ta da abokin shawara a kusa sai Hajja, Hajja ce maƙociya, kaka, uwa a gareta. Hakan ya saka ta gama abinda take yi ta rufe gidan ta shiga wajan Hajja. Hajjan kawai ta samu a zaune tana jan carbi tana kallon tashar madina.
Didi ta ce, "Hajja ƴan matan basu dawo ba?."
"Ba su dawo ba Aisha, amma na san suna hanya tunda magriba ta taho."
Didi ta ce, "Hajja yau ma wani yazo da batun aure, abinda ban taɓa yi ba yau nayi, domin na tura shi wajan Kawu su yi magan." Hajja fara'ar ta ta ƙaru ta ce, "Alhamdu lillah! Aisha ai abinda ki ka yi daidai ne, shi kansa zai yaba da hankaliki da kika tura shi wajan na gama dake."
Didi ta ce, "Hajja ban taɓa jin na gamsu da duk masu zuwa neman aure na wani lokaci ɗaya ba sai shi." Hajja cikin farin ciki ta ce, "lokacin aurenki ne yazo Aisha shiyasa. Duk masu baki da kunu da suke ta magana a kai in yanzu Allah ya rubuta shine lokacin ki sai yanzun zaki yi aure."
Didi ta ce, "sunan saAbdulhamid kuma bashi da mata, ya sanar dani sun rabu matar da yara biyu kuma suna hannunta.