Showing 12001 words to 15000 words out of 87436 words

Chapter 5 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

jin tsoronsa haka ake jin tsoronsa a duk inda ya je, Ganin sa kawai a kusa dake babu wanda zai iya yi miki magana. Kuma ba maganar school, dan bana tunanin ya yi secondry school."
Mum ta wara idanu ta ce, "da jahili zaka haɗa min yarinya? Gaskiya ban amince ba."

Dad ya ce, "haba dear, ki yarda dani mana na san abinda nake yi fa." Narma ta ce, "amma Dad sai ayi min dariya in aka gan mu tare."
"Kar ki damu kowa ya san aiki yake miki a ƙasan ki yake." Narma ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "well, a wanne Guest house ɗin zan zauna? Kasan akwai friends ɗina da zamu zauna tare."

Sen ya ce, "bana tunanin zan bar ki ki zauna a guests house, Ina tunanin ki tafi hotel kawai."
Narma ta ce, "okay Dad, yadda ka ce" ta tashi tana hawa sana dan ta ɗauko jaka ta tafi aiki.

Mum ta kalli Sen ta ce, "amma my dear meyasa zaka haɗa ta da wani ɗan daba for god sake? Meye haɗin ta dashi? Iya wannan bad smell ɗin ma da suka yi ai sai ya saka tayi ciwo, gaskiya hakan bai yi min ba."

Sen ya ce, "wannan ɗan daban ba irin wanda ki ka sani yake ba, kuma aiki ne na lokaci kaɗan da ya ƙare shikenan ba sake ganin ta zai yi ba. Ni nasan matsayinsa bai kai ace yana jan Narma a mota ba, kawai zamu jure ne saboda lafiyar ta. Zai iya bada ransa akan kula da Narma, ko da kashe shi aka yi a maimakon Narma an fa kashe banza."

Mum ta ce, "in ba dan aikin ba ina shi ina haɗuwa da Narma? Ai sai dai a tv." Sen to yayi dariya ya ce, "na san abinda nake yi kar ki damu." Ya faɗa yana tashi ya hau sama bayan ya saka waya a kunnen sa.

*******

Nayla tana zaune tana shan tea tana danna waya Abiy ya fito falon yana kallon ta yana murmushi. Itama murmshin ta yi ta ce, "Abiy har ka fito?." Abiy ya ce, "To Mamana ta gama shirin tafiya Kano ba dole na fito ba."

Nayla ta wara idanu da mamaki ta ce, "Abiy kai zaka kai ni?." Yayi murmushi ya ce, "Mun yi magana da Salisu jiya bazai samu damar kai ki ba, sannan Yayan ki Jawad baya nan balle ya miƙa k, Kin san ni bana barin sauran direbobin gidan nan su kai ku waje mai nisa dole ni zan kai ki." Mama ta shigo yana falon tana faɗin, "Abiy ban da dai kana so ka wahala ga direbobi a gidan nan sai kaje da kanka?." Nayla ta ce, "Abinda na gani kenan Mama."

Ya girgiza kai ya ce, "kin san bana son driver ya kai ta Kano in ba Baba Salisu ba, nafi yarda ta tuƙinsa akan kowa. Jawad yana wajan aiki balle ya kai ta, Ahmad ma baya nan balle ya kai ta."

Mama ta girgiza kai fuska da murmushi amma zuciyarta cike da baƙin cikin abinda ya ce. Abiy ya kalli Nayla ya ce, "ta so mu je, so nake ta je lafiya ta kuma dawo lafiya, ni badan ta matsa ba ai babu inda zata je saboda bana so tayi nisa da gida." Nayla tayi murmushi ta ce, "Abiy ai bazan jima sosai ba zan dawo."
"Shikenan Mamana yadda ki ke so." Ta ajjiye mug ɗin hannunta ta shiga ɗaki sai gata ta fito da jaka ta tafiya ta kalli Mama ta ce, "Mama zan tafi" ta kalli Jalila ƙanwarta da Jalil ɗan autan su da suke fito tace, "zan tafi."

"Allah ya kiyaye" suka faɗa a tare. Jalil ya ce, "Ya Nalya kar ki daɗe, in bakya na gidan nan babu daɗi." Murmushi ta yi ta shafa kansa tace, "an gama auta. Me zan taho maka dashi?."
"Wannan donut ɗin da muka taɓa ci...." Ya faɗa yana jan sunan dan ta tuna. Ta yi dariya ta ce, "kar ka damu auta in sha Allah."

Jalila ta ce, "Ya Nayla ni dai kunun Hajja nake so." Nayla ta yi dariya ta ce, "tun daga Kano zan yi dakon kunu...? Lallai sannun ki Jalila."
"Allah ba don school ba sai na biki."
"Wani lokacin sai mu je tare."

Mama ta ce, "Nayla har na fara kewarki." Nayla ta ce, "Nima haka Mama" ta faɗa tana Rungumeta. Abiy da yake kallon su cikin murmushin haɗin kan ƴaƴan na sa ya ce, "to mu je." Nayla ta saki Mama tana cewa, "Abiy motata fa?."
"A Kano zan bar ki ki ja mota? Gaskiya Nayla da sauran ki baki san ina ne Kano ba." Tayi dariya suka fito har harabar gidan ta shiga mota tana ɗagawa Mama hannu suka fita.

Mama ta girgiza kai tana kallon bayan motar har suka fice ta ce, "Nayla lokaci dai, ki jira ki sha mamaki dan wallahi! wallahi! sai ma farraƙa wannan soyayyar da yake miki. Ki je ki dawo, sai na tabbatar da kin je gidan auren da zaki sha wahala, So nake ki ƙare a wahala har abada, bana so ki san daɗin aure ko kaɗan. Ina nan ina jiran ki!."

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t

*Book 1*
*P 04*

Nayla da Abiy tafiya suke a mota a hankali kafin ya kalle ta ya ce, "Ummina." Ta kalle shi ta ce, "Na'am Abiyna."
"In kin je Kano ban da yawo kin ji?." Ta ɗaga kai sannan ta ce, "in sha Allah Abiy."
"Kin ga abinda ya taɓa faruwa dake a shekarun baya shiyasa na tsani zuwan ki kano, ki kula ba ko yaushe zaki gida fita ba."

Nayla ta ce, "zan kiyaye in sha Allah Abiy."
"Yauwa. Allah ya yi miki albarka ya jiƙan Ummanki." Ta amsa da amin kafin ya kalle ta ya ce, "zan saka miki kuɗi a account ɗinki duk abinda ki ke so sai ki siya." Tayi murmushi ta ce, "Thank you Abiy." Shima murmushin ya yi kana ya ce, "Ya batun Sadiq ne? Ban ji kin ce komai ba." Ta turo baki tace, "Abiy ya cika takura, kuma shi wai in na aure shi bazan yi aiki ba ni kuma gaskiya a'a" ta faɗa da shagwaɓa tana juyar da fuska gefe tana ƙifta idanu.

Murmushi ya yi cikin ƙaunar ɗiyar ta sa ya ce, "Gaskiya bazai yu ba, ya kamata ki turo min shi mu tattauna." Ta sake ƙifta idanu wanda hakan ya zama ɗabi’arta tace, "A'a Abiy, ka ƙyale shi kawai."
"To na ƙyale shi. Sai waye kuma?." Tayi dariya ta rufe fuskar ta alamun kunya ya sake yin murmushi suka cigaba da tafiya.

Awa biyu da mintina ne suka kawo su Kano, har ƙofar gidan Hajja ya faka motar ya kalli Nayla bayan ya tsaya ya ce, "Ki shiga ki sanar da Hajja zan shigo mu gaisa." Nayla ta amsa ta fito ta ɗauki jaka ta shiga gidan dan ta sanar da Hajja zuwan Abiy ɗin.

Da sallama ta shiga cikin muryar ta mai zaƙin gaske, Hajja da take alwalar sallar azahar ta amsa yana kallon wacce ta shigo. Nan da nan fuskar Hajja ta washe Nayla ta tafi a guje ta faɗa jikinta ta ce, "Hajja ta."

Hajja tayi dariya tace, "Hauwa'u ke ce da ranar nan? Sannu da zuwa mutanen zazzau. To ɗaga ni kar ki karya ni." Nayla tayi dariya ta ce, "Abiy yana waje zai shigo ku gaisa." Hajja ta tashi daga inda take ta ce, "maza jeki ki ce ya shigo, ai ban san shi ya kawo ki ba." Nayla ta juya ta fita ba jimawa suka shigo tare da Abiy.

A falo suka same ta Abiy ya zube a kan carpet ya gaishe ta. Hajja ta amsa da fara'a suka ta ce, "ya yara?."
"Lafiya lau Hajja."
"To ma sha Allah, Allah ya taimaka ya tsare." Ya amsa da amin kafin Hajja ta kalli Nayla ta tace, "Hauwa'u maza kawo masa ruwa a fridge, Yau Salma bata nan ta shiga kasuwa sai zuwa anjima zata dawo." Nayla ta ce, "Hajja ni fa shiyasa bana son zuwa wani lokacin, Na faɗa miki ki daina ƙara u ɗin nan a gaban sunana bana so." Hajja bata kula ta ba saboda sirikinta da yake wajan.

Abiy ne ya yi murmushi ita kuma ta tashi ta ƙarasa wajan fridge ta kawowa Abiy ruwan roba harda lemo. Ya ɗauki ruwan ya riƙe a hannun sa. Hajja ta ce, "Na gode fa Abdullahi da ka kawo min ƴar rigimata." Abiy yayi murmushi cikin girmamawa ya ce, "Babu komai Hajja, Allah ya ƙara lafiya."
"Amin ya Allah, Allah ya gafartawa Bilkisu."

Da Abiy da Nayla suka amsa da amin kafin Abiy ya ce, "To Hajja zan wuce, ina so na shiga Kaduna kafin duhu ya yi." Hajja ta ce, "Da wuri haka? Na ɗauka sai anjima har zan yi waya a kawo maka gurasar Kano ka kaiwa yara." Yayi murmushi ya ce, "Babu komai Hajja, a kan hanya nake daman ita kawai na sauke zan koma." Hajja ta ce, "ikon Allah, daga zuwa har zaka koma kamar ba waje mai nisa zaka koma ba? Baza ka zauna ka ci abinci ba?." Murmushi ya sake yi ya ce, "Hajja kamar wani baƙo? Babu komai wallahi" ya faɗa yana saka hannu a aljihu ya ajjiyewa Hajja kuɗi sannan ya fita Nayla ta bi bayan sa.

Yana jin godiyar da Hajja take yi yana murmushi har ya fita. Nayla da take bayansa ta tsaya kusa da shi ta ce, "Abiy Allah ya kiyaye hanya, Allah ya sauke ka Lafiya."
"Amin Mamana, ki kula kin ji? Banda yawo. Kin ga yadda gari yake babu tsoro ƙwacen waya yayi yawa, duk inda zaki je kar ki yi dare kuma ki sanar dani. Ki kuma tabbatar driver Hajja ne ya kai ki ban yarda da hawa keke ba kin ji?."
"İn sha Allah Abiy, Kuma daman Hajja bata barin fita da daddare."
"Yauwa."
"Allah ya kiyaye a gaishe da Mama" ya amsa yana shiga mota ya tafi.

        Wajan Hajja ta koma tana cewa, "Hajja me ki ke dashi a gidan nan? yunwa nake ji wallahi." Hajja ta ce, "Sarkin ci, shiyasa ki ke ƙiba ai. Duba Salma tayi abinci kafin ta shiga kasuwa." Falon Hajjan ta shiga dan a ciki kitchen yake dan gidan Hajja gidan ƴan gayu ne. Hajja ta biyo bayanta sai ta same ta ta shiga da kayan ta ɗakin da take sauka in tazo sannan ta fito.

Hajja ta kalle ta tace, "Baki zuba abincin ba?."
"Sallah zan fara yi tukunna, wai Hajja ya gidan yau babu wuta ne?."
"Wata waya ce ta solar ta katse har yanzu dai ba a zo an gyara ba." Nayla ta wara idanu ta ce, "wai kina nufin babu wuta a gidan nan?."

         "Eh yanzu dai kam babu, Wataƙila sai gobe ko jibi." Nayla ta ce, "Innalillahi! Wallahi da na sani bazan zo ba sai an gyara, Ga wayata babu chaji ina zan saka?." Ta faɗa ido na cikowa da hawaye cikin shagwaɓa. Hajja ta harare ta tace, "Sarkin shagwaɓar tsiya, gabaɗaya Abiy ya shagwaɓaki. Ki yi sallah tukkuna sai a san abinda za a yi." Nayla ta ce, "wallahi Hajja gabaɗaya raina ya ɓaci, bana son zama babu chaji" ta faɗa tana komawa cikin ɗakin tana mita ta yi alwala ta fito tayi sallar azahar sannan ta ci abinci.

       Kallon Hajja tayi da take kallon ta itama ta ce,"babu masu chaji a unguwar nan na kai?." Hajja ta ce, "a sace miki wayar ai." Nayla ta ce, "ni fa shiyasa ban cika son zuwa Kano ba wallahi, da na san babu wuta ai da na taho da power bank ɗina. Yanzu tsakani da Allah ta ya zan iya rayuwa babu chaji?."

Hajja ta ce, "In kin huta zuwa la'asar sai ki shiga wajan Aisha ki saka chaji." Nayla ta ce, "wace haka?." Hajja ta kalle ta tace, "Didi." Nayla ta wara ido ta ce, "wannan mutumin yana nan zan shiga gidan? A'a rufa min asiri kar ya naushe ni, Itama Didin in ta shigo gaiahe ki ma gaisa." Hajja tayi dariya ta ce, "babu abinda zai yi miki, ki huta sai ki shiga."

Nayla ta ce, "ni tsoronsa nake ji Hajja, Zuwana na ƙarshe harara ta ya dinga yi dan kawai ina hira da Didi. Didin ta fishi kirki shi bashi da mutunci, daman gashi da zubin abin tsoro." Hajja ta ce, "ke dai baza ki ce bashi da kirki ba, dan ya taimake ki taimakon da babu wanda ya taɓa yi miki shi a rayuwa." Ta turo baki ta ce, "ni wallahi ban so kuna tuna min wannan maganar" ta faɗa tana tashi ta shiga ɗaki. Hajja tayi dariya zuciyarta cike da farin cikin ganin jikarta ta.

          Didi kuwa cikin lokaci kaɗan ta kammala sana'ar abincin da mutane suka saka order, mai delivery ya tafi kaiwa kowa tayi wanka ta gyara gidan kamar ba ita ce tai aikin ba. Sana'arta karɓe ta, tun tana yi da kaɗan-kaɗan har ta kai ta kawo wata ran sai ta yi abinci pack ɗari da hamsin ko ɗari biyu. Sosai ta ke samun alkhairi tana kashe matsalolin gabanta, babu abinda zata cewa Allah sai godiya. Shiyasa kullum in ka ganta fes da ita, daman ga ta ƴar gayu in ta yi kwalliyya sai ka kalle ta ka sake kallo saboda babu abinda ya fi ƙarfinta.

Tana zaune bayan ta idar da sallar la'asar tana ta zullumin rashin kiranta da Omar bai yi ba tunda ya tafi Abuja, ta kuma san hakan ba halin sa bane ba. Sallama aka yi ta amsa tana jiran a shigo. Nayla ta shiga falon bayan ta sake yin sallama Didi ta amsa tana murmushi kafin ta ce, "kaii Nayla! Saukar yaushe?."

Nayla tayi murmushi ta ƙarasa ta zauna ta ce, "ɗazu da azahar nazo Didi, Ina yini."
"Lafiya lau Nayla, ya hanya?."
"Alhamdu lillah."
"Ma sha Allah, sannu da zuwa. Tunda kika koma Wancan lokacin baki sake dawowa ba, na cewa Hajja Nayla tayi mana yaji kenan."

Nayla tayi murmushi ta ce, "Wallahi Abiy ne sam baya son zama na a Kano, kuma ga makaranta shiyasa dole ina can. A cikin kwanakin nan na kammala tahfiz ɗin da na shiga shiyasa." Didi tayi dariya ta ce, "baya so ki yi nisa dashi ne." Nayla murmushi ta yi kafin ta ce, "Didi don Allah zan saka chaji." Didi ta ce, "Kamar wata baƙuwa Nayla? Jeki ki saka mana." Nayla ta tashi ta saka chaji ta dawo ta zauna.

Didi ta kalle ta ganin sai murmushi ta yi sai tayi murmushi itama ta ce, "kwanaki na ga kun sha biki sai rawa ki ke, na ce Nayla akwai son rawa." Nayla ta kulle fuskar ta tana dariya ta ce, "Didi ashe kin ga status ɗin."
"Na gani tunda gashi na faɗa miki." Nayla ta sake yin dariya amma bata ce komai ba.

Didi ta ce, "yanzu kuma na gama aikin abincin order bara na duba miki abinci." Nayla ta ce, "Na ƙoshi Didi, ina zuwa gidan Hajja na ci abinci." Didi ta ce, "Daman ke ai bakya cin abincina, baki taɓa ci ba, kullum kin ƙoshi ki ke cewa."
"Ba haka bane ba wallahi, ina zuwa na ci abinci bana jin yunwa."
"Amma dai zaki mana shekara ko?." Nayla ta wara ido ta ce, "taɓ! Ai ko sati biyu bana tunanin zan yi a nan." Didi tayi dariya ta ce, "Abiy yafi so ya dinga ganin ki kullum, da gaskiyarsa."

Nayla ta murmusa tana jin daɗin zama da Didi, saboda mace ce mai fara'a da wasa ga saurin sabo. Ta zama tamkar jikar Hajja itama, tana matuƙar girmama Hajja sosai, ko me yake damunta Hajja take iya faɗawa ta bata shawara. Shiyasa duk wani mai zuwa gidan Hajja ya san Didi saboda gidan zuwan ta ne, ko biki ake a ɓangaren Hajja Didi na zuwa kuma an santa sosai. Didi ta miƙe ta shiga ɗaki tunawa akwai abinda zata yi tabar Nayla a zaune tana ƙarewa falon kallo.

         “Wacece ke!?.”

Abinda taji an faɗa kenan cikin kakkausar murya. A hankali ta juyo a firgice suka haɗa ido nan take gabanta ya yanke ya faɗi. Kafin ta tattaro abinda zata ce ya ware murya cikin tsawa ya ce, "Nace Wacece ke!? Me kika yi a zaune a na wajan?." Nayla tsabar tsoro bata san ta miƙe tsaye ba, jikinta na rawa nan da nan ido ya cika da hawaye abin ka da ƴar shagwaɓa.

"Goje!, Tk!, Bash! kuna Ina!" Ya faɗa da ƙarfi yana kallon ƙofa, sai gasu sun shigo falon da hanzari. Nayla ya nuna musu ya ce, "ya akayi wannan ta shigo gidan nan? Wacece ita? Kenan in bana nan barin kowa ku ke yi ya shigo!?." Goje ya kalli Nayla da har lokacin jikinta yake rawa cikin tsawa ya ce, "Ke daga ina ki ke!? Waye ya baki izinin shigowa gidan nan?."

Numfashi take ja daƙyar hawaye na sakkowa daga idonta, ta saka magana balle ta iya cewa wani abun. "Ba magana ake miki!?."
"Cha....ji....na....ka...wo..." a fusace Omar ya ce, "Nan gidan kawo chaji ne? Ku fitar min da yarinyar nan yanzu."

Didi da take banɗaki take jiyo amon maganarsa da hanzari ta fito dan da tasan zai shigo baza ta bar Nayla ita kaɗai ba, ta san sai an yi haka. Tana fitowa falon ta ce, "Kar wanda ya taɓata."

Cak suka tsaya da ƙarasowa inda Nayla take ta jawo hannunta zuwa kusa da ita sai kawai ta fashe da kuka ta kwanta a jikin Didi. Didi ta shafa kanta ta ce, "yi haƙuri Nayla, da na san zai dawo yanzu da ban barki ke kaɗai ba, Zauna" ta faɗa tana zaunar da ita akan kujera.

Omar ta kalla fuska babu walwala ta ce, "kai wai meyasa ka ke haka ne? kenan bazan yi baƙi ba sai wanda ka sani?. Haka kawai daga dawowarka kazo ka fara yiwa ƴar mutane ihu ba tare da ka santa ba? Kenan bazan yi baƙuwa ba lallai sai ka santa? Meye haka ne?."

Kallon Didi yayi amma bai ce komai ba ta kalli su Goje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login