Showing 84001 words to 87000 words out of 87436 words

Chapter 29 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

ya sake gyarawa sannan suka nufi gidan su Narma.

Lokacin da su Omar suka je ƙofar gidan Narma ya kira a waya ya ce mata gasu sun zo. Mai gadi ta kira a waya ta bashi umarnin buɗe musu su shigo. Mai gadi ya kalli su Omar bayan sun gama waya da Narma ya ce, "Hajiya ta ce ku shiga." Ya faɗa yana bisu da kallon mamaki.

Yadda ake ta zuzuta su, tun safe aka ce musu za a yi baƙi ya ɗauka zai ga motoci sun cika estate ɗin sai ya gansu taxi. Buɗe musu ya yi suka shiga gate ɗin farko suka shiga na biyu. Narma ya gani a tsaye da alama jiran su ta ke yi,da sassarafa ta ƙaraso inda suke dan takalmin ƙafarta ma silifa ne, tana zuwa ta kalle shi da murmushi ta ce, "Barka da zuwa Faruk."

Su Bash dai sunan tsaye suka yi, basu ɗauka inda Ogan nasu ya kawo kansa ya kai haka ba. Duk da sun san gidan, suna zuwa tare dashi wani lokaci. Kenan a gidan Sanata yake neman aure? Kuma wannan kyakykyawar budurwar ita yake so?. Gaskiya sun jinjina ƙarfin guiwa irin ta Omar, gashi babu damar magana balle su tanka, sun san halinsa. Narma ta ce, "mu je falon." Bayan ta suka bi tana tafiya tana yiwa ma'aikatan gidan faɗa, su kuma sai gaishe su suke yi suna ana bata haƙuri.

A babban falon ta kalli Omar ta ce, "Dad sun je masallaci, tun ɗazu suna jiran zuwan ka baka zo ba, yanzu zasu dawo." Omar ya girgiza kai ya zauna ko ɗar a zuciyarsa baya ji. Yadda ya zauna ya harɗe ƙafa sai ka ɗauka Sen ɗin ne da kansa, su Bashir kallon ikon Allah kawai suke yi, basu ɗauka lamarin ogan nasu ya kai haka ba.

Nan take aka cika gaban su Omar da abin sha da abin motsa baki. Narma ta fita ta koma cikin gida dan ta sanar da Mum zuwan su. Bash ya kasa haƙuri bayan ta fita ya ce, "Sai da kai Tiger, wallahi Madugu ƙwarin guiwar ka yana burge ni sosai. Allah ya bani ikon koyi da kai, Allah ya zamanin Jan wuya na mu." Omar bai ko kalle shi ba kaɗa ƙafa kawai yake yi, babu abinda suka taɓa abinda aka kawo musu. Su Bashir suna son cin koda Apples ɗin da aka ajjiye ne, amma waye ya isa ya taɓa bayan ga Boss a gefe bai taɓa komai ba? Sai dai kallon.

Dariyar Dad suka jiyo suna shigowa falon shi da minister. Turus suka yi ganin su Omar a zaune a kan kujera suna kallon masu shigowa. Kallo ɗaya Sen ya gane Omar ya kalle shi da mamaki ya ce, "A'a Tiger, saukar yaushe? Zuwa babu notice?" Ya faɗa yana ƙarasowa fuskarsa ba yabo babu fallasa.........

Senator ya haɗu da In law😂😂🫸🏼

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
wa.me/701 809 8175
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️


*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*_Godiya ta musamman ga waɗannan mutane masu karamci, kirki, daraja da kuma alkhairi._*

1-Halimahz
2-Oum Nabil
3-Jamila Umar Janafty
4-Oum Mumtaz
5-Maryam Kitty
6-Aisha Muhammad Alto
7-Autar Manya
8-Mai Dambu
9-Maryam Jumare
10-Maryam Hadeja
11-Zainab Kano
12-Aunty Nice
13-Gureenjoh.

_Ina miƙa godiyata a gare ku, Allah ya saka muku da alkhairi, Allah ya bar zumunci ya cikawa kowa burinsa na alkhairi amin._❤️❤️

*Book 1*
*P 25.*


Omar bai tashi tsaye ba kuma bai ce komai ba, su ma su Bashir ganin Boss bai tashi tsaye ba sai suka gyara zama. Sen ya ƙaraso yana bin su da kallo, ransa ya ɓaci ganin su a zaune akan kujera kamar wasu baki masu mahimmaci.

Minister ya kalli Omar ya kalli Sen ya ce, "Ina baƙin da aka ce mana sun zo?." Sen ya ce, "to nima dai ban ga kowa ba, nayi tunanin zan ga Bakuwar mota a car park amma ban gani ba."

Kallon su Omar ya yi ya ce, "ku jira ni daga waje zan gana da baƙi yanzu. Bana son irin wannan zuwan babu notice, ni ban san ma ya akayi aka bar ku kuka shigo ba wallahi. Mtsww..." Sai kuma ya ɗaga murya ya ce, "Auwal!." Da sauri wanda aka kira da Auwal ya shigo, Sen ya kalli su Omar ya ce, "kai su BQ, in na gama ganawa da baƙi sai su zo. A taƙaica waye ya bar su suka shigo? Irin waɗanan baƙin ba ni nake faɗa muku zuwan su ba?. Waye ya shigo da su?."

"Hajiya Narma ce" ya bashi amsa da girmamawa.
"Narma!" Ya maimaita cikin mamaki.
"Itace.." Sen ya tafi tunani, ya kalli Omar ya sake kallon Auwal ya kuma maimaita sunan Narma. Omar da ya ke jinsa yake kuma kallon reaction ɗinsa ya murmusa ya ce, "babu wasu baƙi da zasu zo Sen, mu ɗin nan dai mu ne baƙin." Da sauri Sen ya juya yana kallon Omar ya ce, "ban gane ba."

"Ba kana jiran zuwan sirikan ka bane?" Omar ya faɗa yana kallonsa kamar yadda shima shi yake kallo. Kasa magana Sen ya yi sai kallon Omar da yake yi cikin mamaki. Omar ya ce, "to ai ni ne." Sen ya yi ƙaramin tsaki tare da tamke fuska ya ce, "kai kar ka ga Ina wasa dakai, Ina baka damar zuwa gidan nan ko yaushe ka raini ya shigo tsakaninmu, ka tsaya matsayin da na baka. Ku tashi ku bar min falo!."

Narma ce ta shigo falon ta ce, "Dad!." Kallon ta ya yi cikin fusata ya ce, "Ina baƙin naki suke? Sannan kece kika buɗewa waɗanan falon nan suka shigo?." Narma cikin shagwaɓata ce, "ni ce mana. Kuma Dad ai sune baƙin nawa, Tiger shine Faruk ɗina, your inlaw."
"What!!" Sen ya faɗa da ƙarfin gaske yana kallon Narma da take kallon sa, ya kalli Omar da yake zaune har lokacin kamar falon babansa, ya kuma kalli minister da yake tsaye ya rasa ma abinda zai ce.

Kallon Narma ya sake yi cikin wani irin yanayi ya ce, "kin san abinda ki ke faɗa kuwa? Are you out of your senses Narma?."
"Dad da gaske nake, he's your son in-law." Sen ya nuna Omar da ya miƙe tsaye a lokacin bakinsa har rawa yake yi ya ce, "Wai wannan?." Narma ta ce, "yes Dad, I love....."
Ai bata ƙarasa ba ya tsinke ta da marin da sai da ta koma ta daki bango.

"Narma!!" Ya faɗa da ƙarfin gaske yana riƙe kafaɗunta ya jijjigata cikin fusata ya ce, "kalle ni, ki dawo hankalinki, ki kalli waɗanda suke gabanki ki daina furta min shirme. Narma ki dawo hankalinki!" Ya faɗa yana sake jijjigata da ƙarfi. Narma da ta dafe kunci tana kallon mahaifin nata cikin gigicewa, bai taɓa dukanta ba a rayuwarta ba sai a wannan lokaci. Omar da yake tsaye ya gaji da wannan surutun ya ce, "tana cikin hankalinta, da gaske take ni ɗin sirikin ka ne."

Da wata irin fusace Sen ya juya ya nuna da yatsa Omar ya ce, "kar ka sake saka min baki, da ƴata nake magana" ya jiyo ga Narma ya ce, "faɗa min prank ki ke yi ko? Ko kuma April fools joke ne?."
Narma in her trembling voice ta ce, "Dad it's not a pranks, da gaske nake maka ni na gayyato shi. Shine wanda ku ke zaman jiran zuwansa. He's my Faruk!."

Muryar Mum Narma taji ta ce, "Narma what are you saying?." Ta kalli Mum da take tsaye tashin hankali ya gama bayyana a tare da ita, Narma ta ce, "Mum da gaske nake, shine Faruk ɗina, kuma shi nake so. Sannan....." Ai bata ƙarasa ba Sen ya sake tsinke ta da marin da sai tayi ƙara saboda shigarsa jikintq. Minister ne ya riƙe shi ya ce, "easy mana, control yourself. A kan wannan zaka dinga dukan Narma? Haba kamar ba kai ba" ya faɗa yana nuna Omar shima ransa a ɓace.

Kallon Omar ya yi da yake tsaye ƙyam yana kallon su one by one. Sen ya girgiza yana nuna Omar ya ce, "meye ma sunanka?." Omar ya bishi da kallo cikin ko in kula ya ce, "ka fini sani." Sen ya kalle shi ya ce, "shaye-shayen da ka ke yi ya taɓa maka ƙwaƙwalwa ko?. Dan in ba mara hankali ba babu wanda zai yi abinda ka yi. Har kana da zarrar ɗauko ƙazaman ƙafafunka kazo gidana da sunan neman aure?. Na jima Ina jin ana cewa kawai mahaukatan da haukan su ya wuce ace musu mahaukata sai dai dadbobi, ban yarda ba sai yanzu. Look at you..." Sai kuma ya dafe kai ya rasa ma abinda zai ce.

Narma da take kuka ta ce, "Dad ni ce na gayyato shi, kuma ni sonsa nake yi...." Maganar ta maƙale saboda zaburar da Sen ya yi zai yi kanta Minster ya riƙe shi, Sen ya kalle shi ya ce, "kana jin abinda take faɗa? Kana jin abinda take cewa?."

Minster ya ce, "ba itace mai laifi ba ai, ga mai laifi nan a tsaye a gaban ka. Ita meye nata da zaka dinga dukanta? Shi zaka daka ai ba ita ba" ya faɗa yana nuna masa Omar da yake tsaye yana kallon su. Minister ya sake cewa, "Akwai abinda ya shirya shiyasa ya yi amfani da asiri wajan mayar da Narma haka, don't judge her Sen, bata san tana faɗa ba, it's the spell he cast on her that's working."

Narma ta ce, "Ni bai yi min ko wanne asiri ba, ni ce na fara sonsa kuma har yanzu ina sonsa. Babu wani abu da ya shirya a kaina, yana sona kamar yadda nake sonsa" ta faɗa da ƙarfi tana daga inda take.

Sen ya rasa abinda zai yi ya kalli Omar da yake tsaye yana kallon sa ya ce, "kai kuma ka san ƴata ce ka amince har ka ke sonta?."
"Ga zahiri kana gani" Omar ya faɗa yana kallon sa kamar yadda yake kallon sa. Kasa magana Sen ya yi na wani lokaci kafin ya ce, "ƴar tawa ka zo nan da ka ce min kana so. Ƴata zaka yiwa asiri? Saboda na haɗa ka zama da ita a waje ɗaya shine ka samu damar yi mata tsafi?."

Omar ya ce, "ƴarka zaka tambaya, in asiri nayi mata ma ta sani."
"Shut up! Ina magana kana magana dan ka raina ni?."
"Kaine ka haife ni?" Omar ya bashi amsa kai tsaye yana kallon sa kamar yadda yake kallon sa.

"Ko a matsayin diver Narma baka isa ka zo ba, haɗa numfashin ka da na ta babban zunubi ne saboda tazarar ku kamar sama da ƙasa ne. Na baka ita ne saboda wani buri nawa har ka dinga yawo da ita a mota na wani lokaci, amma ba dan haka ba ko a mai aikin gidan nan baka isa kazo ba. Bana ɗauka mutum aiki sai yana da matakin diploma a karatu, kai kuwa fa?." Omar ya kalle shi ya ɗora yatsun sa biyu akan goshin sa kamar ko yaushe ya ce, "ban zo a mai aiki ka ba, amma nazo a sirikinka."

Ai Sen ji ya yi kamar ya zuba masa ruwan zafi, jikinsa har rawa ya ke yi, ya zare ido ya ce, "me ka ke dashi? Waye kai a duniya?. Ko matsayin mai gadin gidan nan baka dashi, mai aikin gidan nan dukkan su graduates ne, meye matakin karatun ka? Faɗa min me ka ke dashi a duniya?.." Omar ya ɗan yi murmushi kalle shi ya ce, "abinda nake dashi ka ke so ka ji?" Ya kalli Narma da take wajen tana kuka ya sake kallon Sen ya ce, "zuciyar ƴarka, ita nake dashi."

Fusata Sen matuƙa ya yi ya kai hannu kamar zai mare shi amma sai ya fasa yana jin zuciyarsa kamar ana zuba masa ruwan zafi saboda ɓacin rai. Minster ne ya ƙaraso yana kallon Omar ya ce, "Dan kaji last time na yabe ka sai aka ce maka ka kai matsayin da zaka zo gidan nan neman aure?. Kana da hankali kuwa?."

Omar shima shi ya ke kallo ido cikin ido ya ce, "babu tabbacin kowa yana da hankali tunda ba ganin hankali sa ake yi ba." Sen ya zabura ya yi kan Omar Minster ya riƙe shi Sen yana cewa, "ka barni nayi maganin wannan mahaukacin, bar ni na kashe shi kuma na kashe banza wallahi. Ni zai dinga yiwa hauka a cikin gida? Kalle shi fa?." Minister ya ce, "ba class ɗin ka bane."

Ya kalli Omar cikin ƙunar rai ya ce, "baka da maraba da dabba a idona, amfanin ka a gare ni na biya ka kaje ka sadaukar da rayuwarka domin cigabana da na ƴaƴana. Saboda wannan kawai nake nuna maka so a baki dan bai kai zuciyata ba, in ba dan haka ba baka ka kai ka ce kana son mai aikin cikin gidan nan ba. Jahili ne kai baka da ilimin komai, babu inda zaka je a rayuwa a haka zaka ƙare rayuwarka a gagari akan titi. Ko riƙe gidan ku baka iya yi, Yayarka itace take ciyar da kai ba kaine ka ke citar da ita ba. A haka ka samu zarar ratso cikin gidan nan ka ce kana son Narma!? Ka san wacece Narma?."

Omar ransa ya ɓaci sosai, tunda aka fara maganar sai yanzu ransa ya ɓaci hakan ya saka shi zubawa Sen ido bai ce komai ba. Ganin ya yi shiru Sen ya ce, "Ni Senator ne, Mahaifiyar Narma tsohuwar ƴar majalisa ce. Narma lawyer ce, ta kai matakin masters a karatu, tana kuma riƙe da company guda a ƙarƙashinta. Tana juya biliyoyin kuɗaɗe wanda sai ta saka hannu kuɗin zasu fita. Tana aiki da babban kotun Nigeria, tana da ikon da zata yi ko wacce irin shari'a a faɗin ƙasar nan. Faɗa min kai waye?. Ɗan daba ne, mai garari akan titi, ɗan shaye-shaye, jahili, wanda bashi da ilimi balle a saka ran zai kai wani mataki a nan gaba?. Ko kana so kace ban san labarin uwarka hiv ce ta kashe ta ba...." Ai bai ƙarasa ba Omar ya damƙi wuyan Sen jikin sa na rawa.

Narma da take gefe ta yi tsalle ta zo wajan, Nabil da Minster suke ƙoƙarin cire hannun Omar daga wuyan Sen amma sun kasa. Wani irin wuci Omar yake yi, ransa bai taɓi ɓaci a duniya kamar yau ba, bai taɓa jin tsanar abu lokaci ɗaya kamar tsanar Sen ba, bai taɓa ji zai iya aikata komai ba kamar yadda yake ji zai iya shaƙe Sen har sai ya daina numfashi.

Daƙyar suka cire hannun Omar daga wuyan Sen. Sen yana fitar da numfashi daƙyar Omar ya nuna shi da yatsa ya ce, "ka san irin kalaman da zaka faɗa a kaina, in ba haka zaka fara dana sanin sanin Omar a rayuwarka." Minister mamakin ƙarfin halin Omar yake yi ganin ko tsoro ma shi baya ji. Har gidan Sen yazo ya shaƙe masa wuya kuma yana faɗar magana mara daɗi.

Sen da ya kammala dawowa hankalinsa ya nuna ya ce, "kaine zaka yi dana sanin sani waye ni a duniya, zan nuna maka banbancin dake tsakanin aya da tsaƙuwa, zan nuna maka banbancin da yake tsakanin sama da ƙasa. A yau zaka tabbatar da ka tafka babban kuskure a cikin rayuwarka, zan shafe danginka kaf da kai kanka."

Waya Sen ya ɗauko yana dannawa hannunsa har rawa yake yi saboda ɓacin rai. Narma ta riƙe hannu Omar tana ja cikin fitar hayyaci ta ce, "Faruk ka zo mu tafi, ka zo mu tafi kawai ni zan bika duk inda zaka kaini. Ni Ina sonka har yanzu kuma zan aure ka. Ka zo mu tafi, na zaɓi na zauna da kai akan zama a gidan nan."

Marin ta Nabil ya yi, ya janye ta gefe tana kuka ya riƙeta gam yadda baza ta iya ƙwacewa ba. Omar ya kalli Sen muryarsa ta koma can ƙasa saboda ɓacin rai ya ce, "ka ce babu inda zan iya zuwa ko?" Sai ya girgiza kai ya ce, "zan tabbatar maka da zan iya kaiwa irin matakin da ka ke kai a yanzu, zan iya zuwa inda kai baka isa ka je. Abinda nake so da kai ka kasance a raye."


"Har abada! Kai da zuwa irin matsayin da na taka a rayuwa har Allah ya tashi duniya. Ko da ace  a lahira ana mulki baka isa kayi irin abinda na yi ba, a lahirar ma baka isa ka zo inda nake ba. Aljanna ma akwai irin ta mu, akwai irin ta ku. In ka ci sa'a ka shiga aljanna ko a cikin ta baza ka hangi inda nake ba, na yi maka nisa mai tsahon gaske a lahira balle kuma a duniya. Kana jahili wanda ko jss bai kammala ba wanne mataki zaka je? A haka rayuwarka zata ƙare, daman domin ku yi mana amfani Allah ya halicce ku, kuma kun yi mana amfani rayuwar mu ta yi kyau. Sai kaje ka cigaba da zaman chamber ana shan wiwi."

Kallon sa yake yi shima kallon sa yake yi, kowa ransa a ɓace yake ba kamar Omar da yake yi kamar ya murƙushe Senator.

Sen ya ce, "Narma ba daidai dakai take ba, kar kayi mafarkin mallakarta a cikin rayuwarka domin daga yau zaman duniya bazai sake yi maka daɗi ba, zaka koma rayuwa irin ta gidan yari har ƙarshen rayuwarka. Zan iya kashe ka kuma na kashe banza wallahi, bana son aikata hakan ba dan ina tausayin ɗaukar ranka ba, sai dan nafi so wahala ta yi ƙasa-ƙasa da ƙasusuwan jikinka. Wahala da baƙin ciki nake so su ga bayanka ba bindiga ko wuƙa ba. Sai ka yi dana sanin wannan rana a rayuwarka, sai kayi dana sanin sanin waye Senator Sagir a cikin rayuwarka."

Omar ya yi murmushi yana kallonsa ya ce, "wahala bata kisa, babu wahalar da zaka bani wacce zata kashe ni Sagir!. Babu inda zan je, zan kasance da raina, zan cigaba da rayuwa fiye da yadda na yi a baya. Zan kuma kai matakin da kai baka kai shi ba a rayuwarka, abinda nake so da kai kawai ka kasance a raye Sagir!" Ya faɗa yana girgiza kai yana kallonsa.


A lokacin ƴan sanda suka shigo Sen ya kalle su ya ce, "yayi attacking ɗin kashe ni, sannan ya yi ƙoƙarin sace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login