Showing 42001 words to 45000 words out of 87436 words

Chapter 15 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

yaji shauƙin son kasancewa da ita cikin yanayi na soyayya. Ya so hakan ya kasance tsakanin su amma taƙi ba da haɗin kai, da ya yi magana sai ta ce ya jira sai bayan auren su, shi kuma gani yake kamar bazai iya jurewa ba.

Ɗan hugging ɗinsa tayi daga gefen kafaɗarsa kana ta zauna a akan kujera ta ɗora ƙafa kan ɗaya tana cigaba da cin abincinta. Zama Shima ya yi yana kallon ta cikin yanayin da ya ke kasancewa da duk lokacin da suke tare, yanayin sa na sake yin gaba in ta yi hugging ɗinsa ko ta yi masa kiss sai ya ji kamar zai zauce. Ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce, "What wrong? Naga fuskarki da alamun damuwa."

Yatsine fuska tayi ta ce, "Wani banzan driver Dad ya haɗa ni dashi yake raina min hankali, wai ni yake ɗagawa murya har yana cewa in na sake magana sai na fitar masa a mota." Ashraf ya ce, "Like Seriouly? Ke ɗin yake faɗawa haka?." Bata amsa ba sai murmushin takaici da tayi tana girgiza kai.

"Waye shi haka?."
"Wani ɗan iskan mutum ne dan daba wai shi tiger, ni yake yiwa tsawa saboda Dad yana son ya dinga kai ni ko ina nake so."
"Kuma Dad ɗin ya san da haka?."
"Yes he knew, but today i won't inform him, i want to take action independently and how him my capabilities." Ashraf ya ce, "That's good my Love, you should teach him a lesson so he understands you deserve respect and won't tolerate any nonsense."

Kallon sa tayi taga yana kallonta ba, iya fuskarta yake kallo ba duka jikinta yake kallo sai tayi murmushi ta ce, "zan koya masa hankali."
"Nima zan taya ki." Murmushi tayi tana kallonsa  tace, "yaushe ka zo Kano?."
"Ɗazu." Kai ta girgiza ya ce, "yaushe zaki fara event ɗin Samra?."
"Lahh ka tuna min, gobe ne fa, ko makeup artist ban nema.

He looks into her eyes yana wani lumshe ido then he say, "My Narma event without makeup you looks magnificent." Tayi murmushi ta ce, "Duk da haka dai zan yi kwalliya." Ya bita da kallo ta ɗauki waya ta kira tana magana da turanci nan da nan ta yi booking makeup artist za a zo har gida ayi mata home service.

Ashraf ya jima suna hira kafin ya tafi dan shima a gajiye yake ya tafi ya huta da niyar in anjima zai dawo. Narma bayan ya tafi sama ta hau ta buɗe balcony gidan tana kallon ma'aikatan gidan ɗaya bayan ɗaya tana mamakin rashin ganin Omar, wato ko ya taimaye ta ya ji babu inda zata je shine yayi tafiyar sa kamar itace take aiki a ƙarƙashin sa. Wayarta duba taga number sa Dad ya turo mata kawai ta dubawa number ido kafin ta girgiza kai tare da yin tsaki ta koma cikin falon.

      Omar kuwa ko da suka bar wajan shi da Tk ba gida suka koma ba sai da suka je wani wajan bai koma gida ba sai bayan la'asar. Yana shiga kai tsaye wajan Didi ya shiga, ya same ta a zaune tana shan magani ya ƙarasa ya zauna ya ce, "Ya jikin?." Ta kalle shi ta ce, "Jiki da sauƙi sosai, na sha magani." Ya girgiza kai ya ce, "kin tabbatar babu abinda yake damın ki?." Ta ɗaga kaii alamun eh.

"AbdulHamid zai zo in anjima, ka zauna ku gaisa." Da to ya amsa mata a taƙaice kafin ya tashi ya fita daga falon. Ba jimawa AbdulHamid ya ce masa gashi ya zo ta ce ya shigo ya shigo da sallama ya samu ta ajjiye kujeru gıda biyu kamar wancan lokacin.

Zama ya yi suka fara gaisawa cikin girmama juna ya faɗa mata duk yadda suka yi da Kawu da jiran sa da yake yi dan ya ce zai neme shi. Ta girgiza kai ta ce, "Kawu ya faɗa min komai, bayan ka bar wajansa ya kira ni a waya."
"Haka nake so naji. Amma Aisha na tambaye ki." Ta kalle shi ta ce, "ina ji."
"In Kawu ya baki dama kina ganin zaki iya aurena?." Murmushi ta yi ta ce, "Allah nake roƙa ko yaushe ya zaɓa min mafi alkhairi, sai gaka kazo, in dai har kai ba alkhairi bane Allah bazai bani ikon zaɓarka ba."

Ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya ne, Allah ya tabbatar mana da alkhairi baki ɗaya." Ta amsa da amin. Omar ne ya zo wajan ya ƙaraso yana kallon su ta kalli Omar ta kalli AbdulHamid da yake kallon sa ta ce, "AbdulHamid ga Omar ƙanina kuma Yayana." AbdulHamid ya miƙawa Omar hannu suka gaisa ya ce, "Omar ya aiki?."
"Alhamdu lillah" ya bashi amsa a taƙaice yana sake kallon sa dan haka kawai ya ji ya burge shi.

Didi ta ce, "Ina zuwa haka?." Ya girgiza kai ya ce, "akwai inda zan je." AbdulHamid cikin wasa ya ce, "ko wajan ƙanwarta mu zaka je?." Kallon sa ya yi ya ɗan saki fuska amma bai ce komai ba kuma bai yi murmushi ba.

Barin wajan Omar ya yi AbdulHamid ya kalli Didi ya ce, "ma sha Allah, babu wanda zai ce ƙanin ki ne, kallon farko in aka yi masa za a ace Yayan ki ne dan ya cancanci zama yayan naki. Yana da kwarjini sosai kana kallon sa kaga jarumi."

Didi tayi murmushi ta ce, "Omar kenan." Shima murmushin ya yi yana mamaki dan shi yadda ake bashi labarin Omar ɗin sam bai yi kama da haka ba, ba dan ya sani ba ma da bazai ce shine Omar tiger dake bashi labari ba.

AbdulHamid bayan sun yi sallama da Didi ya fito zai shiga mota sai ga wani babban mutum mai ƙaramin jiki ya ƙaraso inda yake, ya yiwa AbdulHamid sallama ya amsa da girmamawa. Mutumin ya kalle shi ya ce, "Bawan Allah don Allah wajan Aisha ka zo?." AbdulHamid ya ce, "Eh, wajan ta nazo."
"Neman aurenta ka ke yi kenan?."
"Haka ne." Ya girgiza kai ya ce, "kuma ka san duk abinda da suke faruwa a akan ta?."

Abdulhamid ya ce, "a'a, sai ka faɗa min." Sai kuwa ya gyara tsayuwa cikin son isar da gulma ya ce, "Ko da naji, da ganin ka yaro ne ɗan mutunci baza ka kawo kan ka gidan nan ba sai dai rashin sani. Wato Aisha da Omar da ka ke gani abinda suke aikatawa a gidan nan Allah ne kawai ya sani, ya hana kowa shiga gidan ko almajiri baya shiga ya yi bara, da shi sai ita kullum su kwana su tashi. Baligi mara aure da baligar mace a waje ɗaya ai dole a samu matsala, zan iya yi maka rantsuwa da Allah masha'ar su kawai suke aikatawa a cikin gidan. Shiyasa ba ya barin kowa ya shiga gidan, irin yaran nan ƴan mata na unguwa ko kallon ƙofar gidan basa yi saboda shi. Gashi tantirin ɗan iska ajin ƙarshe, kai da ka gashi ma ai ka ga zubin ƴan iska."

AbdulHmaid kallon sa kawai yake yi cikin tsananin mamaki ya ce, "Baba ba ƙaninta ba ne? Aka ce uwa ɗaya uba ɗaya suke."
"Hmm ƙaninta ne mana, amma zama suke yi kamar mata da miji. Kuma bayan shi ma ta kan kawo wasu cikin gidan shiyasa take samun kuɗi tana siyan abinda take so. To in ba mazan banza ne suke bata kuɗi ba wannan sana'arta ta ta siyar da abincin order wata riba ce da ita da zata dinga wannan kashe-kashe kuɗi? Ai kana gani ka san da walalin giro a miya, ba a haka kawai ta kai wannan shekarun bata yi aure ba. Akwai mai biya mata buƙatarta daga gefe."

AbdulHamid ya sake kallon sa ya ce, "to Baba yanzu me ka nufi da labarin nan da ka bani?."
"Ina nufin ka rabu da Aisha kaje ka samu yarinya ƴar mutunci ka aura, gabaɗaya unguwar nan babu wanda ya sana salin su, kwatsam suka tare a cikin ta kuma wayi gari dasu. Ba a ganin dangin uwar su dana uban su balle a saka ran suna da dangi. Kaga a haife na haife ka, kamar ɗana ka ke bazan ga abinda zai cutar da kai na bari ba, kayi gaggawar daina zuwa wajan Aisha kafin girman ka da mutuncin ka ya zube a idanun mutane."

Yayi murmushi ya kalli gefensa kawai idanunsa ya faɗa cikin na Omar da alama duk yaji abinda suke tattaunawa. Sai kuwa ya ce, "Yauwa Omar ƙaraso ga Baba yana bani bayani akan ku." Mutumin yana ji an ce Omar ya kalli wajan da sauri ya ganshi kuwa a tsaye yana kallon sa ya Kalli AbdulHamid murya na rawa ya ce, "Aisha ai mutuniyar kirki ce, ga sanin ya kamata, ga girmama na gaba da ita. Don Allah ba abinda nake faɗa maka kenan ba?."

Ba AbdulHamid kaɗai ba Omar ɗin kansa sai da yayi murmushi jim abinda Baba ya ce, bai nuna ba haka ya tako cikin ƙasaita yana zuwa ya kalli mutumin ya ce, "Waye kai a layin nan?." Jikinsa ya soma rawa kar kar kar saboda tsoro. Omar ya kalli gefe yana girgiza kansa kafin ya sake kallon sa fuska babu walwala ya ce, "nace maka waye kai a layin nan?." Murya tana rawa ya ce, "Malam Salihu."

"Mai kiran sallah?" Omar ya tambaya yana kallonsa. Jiki na rawa ya amsa AbdulHamid ya ce, "Yanzu Baba kana da matsayin mai kiran sallah ma a unguwar nan amma ka ke faɗar irin wannan maganar akan yaran wasu? Ko baka da yara matsayinka na babba wannan ba girman ka bane balle na tabbatar kana da yara kaima da ka ke burin aurar dasu. Ko da da gaske abinda ka faɗa gaskiya ne ka taɓa gani da idon ka?."

Shi dai yayi shiru sai hannunsa da yake rawa sosai. Omar ya kalle shi ya ma rasa abinda zai yi masa, baya son yiwa manya wani abun ko ya yi niya sai ya kasa amma babu abinda zai saka ya ƙyale Malam Salihu, sau biyu kenan yana kama shi da irin wannan munafurcin a kan su.

Malam Salihu ya ce, "Ni fa wasa nake maka yaro, so nake naga ko maƙaryatan unguwar nan sun faɗa maka haka, dan Aisha mutuniyar kirki ce." Omar ya ce, "Zaka tabbatar da mutuniyar kirki ce in nayi maka illa yanzun nan."

Malam Salihu ya ce, "Ka bashi haƙuri don Allah" ya faɗa yana kallon Abdulhamid. Shima ya kalle shi ya ce, "Baba ai ko ya yafe nima bazan yafe ba, matar da zan aura ka ke yiwa ƙazafi a gaban idanuna. Ko shi ya ƙyake ka ni sai hukuma ta raba mu da kai."

Tk da goje Omar ya hango da ido yayi musu alama su riƙe Malam Salihu, caraf Tk ya kamo shi daman haushinsa yake ji shekaran jiya ya yi masa munafurci hakan ya saka ya ce, "Malam Salihu yau ka zo hannu, ƙarshen munafurcin ka ya ƙare."

AbdulHamid ya kalli Omar ya ce, "Omar ka ƙyale shi kawai kar ka yi masa komai, ka bar shi da halin sa." Omar kallon sa ya yi jin yana bashi umarni kamar wani wanda ya haifa. Omar ya ce, "ai ba a dakatar dani in nayi niyar abu sai nayi." Ya yi murmushi ya ce, "kar ka manta kamar yayan ka nake tunda yayar ka zan aura."
"Ko ita bata faɗa maka bana bari ba?." Ya yi murmushi ya ce, "a yi min wannan alfarmar." Kallon sa ya yi zai sake magana sai kawai ya fasa ya kalli su Tk da suke tsorata Malam Salihu ya masa alama da su ƙyale shi ya juya ya shiga gida, shi kuma ya hau mota ya tafi yana mamakin munafurci irin na mutane.

       Omar yana shiga gida wayarsa ta fara ƙara ya duba ya ga number ce ya ɗauka, ana fara magana ya gane Yahya ne ya sanar dashi Narma zata fita in anjima. Bai amsa ba ya yanke wayar dan ransa a ɓace yake sosai ko wajan Didin bai koma ba.

Sai bayan sallar i'sha yaje gidan ya tarar da Narman ma ta hau mota ta tafi wai ta gaji da zaman jira ita ba baiwarsa bace ba. Tsaki ya yi da ya san hakan mai zai fito dashi daga gida yanzu. Gabaɗaya zuciyar saa cushe take akan kalaman Malam Salihu, duk da ba haka aka saba ba amma ya ji zafi sosai. Ɓacin ran da yake ji ya saka shi takowa a hankali yana tafiya ya saka pcap wacce ta rufe fuskar sa.

Narma kuwa a ƙasan gadar ƙofar nasara motar da take ciki ta mutu, tayi-tayi ta kunna ta kasa kunnawa gashi bata da number kowa balle ta kira azo a tafi da ita gıda. Tsaki tayi ta fito daga motar tana kallon hanya, wajan babu mutane sai mota da take wucewa kuma babu haske sosai hakan ya bata tsoro. Napep take so ta tare ta hau ta tafi amma bata san ma ya ake tare mai napep ba dan ba taɓa hawa tayi ba, bisa kuskure ko tsautsayi bata taɓa hawa napep ba. Shiyasa take kallon su ɗaya bayan ɗaya suna wucewa ta rasa me zata yi.

Abu taji an saka mata a bayanta kamar wuƙa zata juya aka ce, "kina juyawa wallahi sai na farɗe miki bayanki, kawo wayar hannunki." Narma jiki ya fara rawa hannu na karkarwa ta kuma kasa miƙar wayar.
"Baza ki bayar ba sai na kashe ki?." Hannunta rawa yake yi garin ta miƙa masa wayar garin ya yanke ya da wuƙar a hannuta. Narma tayi ƙara tana kallon hannunta, shi kuma ya yi cikin duhu a guje bai sake waiwayen ta.

Hannunta jini yake yi tana kuka ga tsoron tashin hankali, sai rawa jikinta yake yi dan bata taɓa tsintar kanta a irin wanna tashin hankalin ba sai a lokacin.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

             ©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 13.*


Omar tun daga nesa ya gane motar ya kuma ganta a tsaye a wajan, a hankali ya ƙaraso kamar zai gifta sai yaji tana kuka tana cewa, "a taimake ni don Allah, a taimaka min jinina zai ƙare."

Ɗaga pcap ɗin ya yi ya kalle ta suka haɗa ido ganinsa ta matso kusa dashi a gigice da fitar hankali sosai ta ce, "Tiger sun ƙwace min waya, sun yanke ki a hannu, jinina zai ɗare ka taimaka min zasu kashe ni." Ya kula gabaɗaya a gigice take har tana riƙe shi bata san ma tayi hakan ba saboda tsoro.

Kallon hanyar ya yi ya sake kallon ta yaga yadda take hawaye shaɓe-shaɓe tana riƙe da hannu kamar wacce aka guntulewa hannu, kallon ɗan yankan da yake hannun ta ya yi tare da yin tsaki a bayyane har lokacin bata saki rigarsa.

"Take me to hospital please, ka kaini ayi min TT kar na samu ciwo." Kamar ba zai yi mata ba magana ba sai yaji ta ce, "Don Allah ka ɗauke ni daga nan, tsoro nake ji, ka taimaka min don Allah." Yadda take kuka tana ƙoƙarin shege masa jiki ne ya saka ya riƙe hannunta ya janye ta ya buɗe gaban motar ya ce, "shiga." Ba musu ta shiga jikin ta na shaking sosai ya buɗe mazaunin driver yana kunna motar ta tashi ya ja motar ya nufi asibiti mafi kusa.

Wani private hospital suka ƙarasa ya ajjiye motar ya kalle ta yaga sai kuka take yi ta riƙe hannunta, shi wallahi mamaki take bashi, ɗan wannan yankan take yiwa kuka kamar wacce aka yanka sosai. Ya kalle ta ya ce, "Fita ki je." Ta buɗe murfin motar ta kalle shi ce, "nayi bleeding sosai in na tashi jiri zan yi."
"Ko" ya furta a bayyane yana kallon ta.

Fita ya yi daga motar ya ce, "Fito" ya furta a kausashe dan ya ga tana neman mayar dashi ɗan aikinta, jin yadda tayi magana ya saka ta sakko amma tana fitowa tayi kamar zata faɗi, da hanzari kuwa ta riƙe shi tana cewa, "na ce maka i'm dizzy bazan iya tafiya ba." Ɗan tsaki ya yi ya janye ta a jikinsa ya kalli bayan sa yaga ma'aikatan asibitin nan ya yi musu magana suka riƙe ta suka shiga da ita.

Bai shiga ba ya tsaya a jikin motar sai ga wacce ta shiga da ita tazo tayi masa magana dole ya shiga. Yana shiga ya ganta sai kuka take yi an ɗaure hannun da bandage, likitan da ya gama yi mata dressing wound ɗin ya kalle shi ya ce, "Oga ka taya mu rarrashinta taƙi yin shiru."

Kallon ta ya yi suka haɗa ido sai wani juya ido take yi kamar mage. Ƙaramin tsaki ya yi Narma ta kalle shi ta ce, "kayi clearing bill ɗin, wayata da atm ɗina duk sun ƙwace." Sai a sannan ya tuna ma da batun wayar ta bai ce komai ba ya yi musu transfer a take suka fito tare da ledar magani a hannun nurse ɗin wai baza ta iya riƙewa.

Sai tafiya take kamar mara jini ita a lallai an yanke ta, gabaɗaya haushi take bashi yadda take langwaɓewa kamar wacce aka jiwa ciwon kirki. Suna zuwa gaban motar ta shiga bayan motar shi kuma ya shiga gaba ya ja motar da gudun gaske.

Da yake kwanciya tayi bata san inda suka nufa ba sai da taji ya tsaya yana niyar fita, ta miƙe ta gansu a wani waje mai duhu ta ce, "ina zaka je?." Kallon ta ya yi jin yadda tayi maganar a firgice bai amsa ba, "don Allah ka je dani bazan iya zama ni kaɗai ba, wallahi i'm scared." Nan da nan jikinta ya fara shaking cikin tsananin tsoro tana ganin kamar abinda ya faru zai sake faruwa.

Narma ganin ya yi mata banza yana niyar fita sai itama ta fito da sauri ta ce, "bazan iya zama ba, don Allah ka je dani tsoro nake ji."
"Inda zan je ba wajan zuwan ki bane" ya faɗa without looking her.
"Ni dai zan je, don Allah ka je dani." Kallon ta ya yi sai kawai ya yi gaba ta bishi a baya, kanta har sarawa yake yi saboda ciwon da ya fara yi mata.

Wani waje taga sun shiga sai gasu a gaban dandazon ƴan daba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login