Showing 24001 words to 27000 words out of 87436 words

Chapter 9 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

abincin gidan nan har sai abinda ya kawo ya ƙare." Ta rausayar da kai ta ce, "Omar! Omar!! Wai wacce irin zuciya ce da kai ne don Allah?."

"Wacce Allah ya yi min Didi."
"Shikenan naji. Amma abinda na dafa yau ko abu ɗaya a cikin abinda ya kawo ban taɓa ba. Kazo kaci abincin ka." Ya kalle ta alamun bai yarda ba ta ce, "da gaske nake, ka san ai bazan maka ƙarya ba. Ka je ka ɗauko abincin, ka kira su Tukur su ci ga na su." Shiru yayi kamar zai ci ɗin sai kuma ya girgiza kai ya ce, "su dai zasu zo su karɓa, ni kam bazan ci ba."

Duk sai Didi ta damu a tausashe ta ce, "in baka ci ba me zaka ci?."
"Assalamu alaikum, Damisa na dawo." Jin muryar Bashir a cikin yaransa ya saka shi ya fita tsakar gidsa sai ga shi ya dawo da packs da alamun abinci aka siyo masa. Didi ta kalle Bashir ta ce, "Bashir ku zo ku ɗauki abinci." Bash ya ce, "An gama babbar Yaya, godiya mu ke Allah ya saka da alkhairi." Kitchen ɗin ta shiga ta ɗauko musu ta bashi shi kuma ya fita.

Lokacin da ta dawo ta tarar grill tilapia fish ne da chip a cikin pack ɗin irin mai sauce ɗin nan da ake siyarwa yana ci hankalin sa kwance. Daman ta san shi masoyin kifi ne sosai, bai damu da cin nama ba akan yadda yake son cin sa ba. Numfashi ta sauke ta kalle shi kamar zatayi magana sai ta fasa ta zauna akan kujera.

Wani pack ɗin taga ya miƙo mata sai tayi murmushi, daman ta san bazai taɓa siyan abu bai siya da ita ba, koda a waje ne in ya ci itama sai ya kawo mata. Ganin bata karɓa ba sai ya ajjiye mata ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ya maganar saurayinki?."

Dariya ya bata sosai, wai saurayinta a ganin ta ai sai dai ace bazawari ba saurayi ba, ita mantawa da take itama tana cikin sahun wanda za a kira da budurwa. Ganin tana dariya sai ya kalle ta ya ce, "me ya baki dariya?."
"Kaine ka bani dariya Omar, wai saurayina. Ina laifin ka ce mai neman aurena? Saurayi ai sai dai irin ku masu neman yara su aura."

Shima sai ya ɗan saki fuska yana kallon ta ya ce, "Yaushe zai zo ɗin?." Ta ce, "ba ka ce gobe ba? ya ce goben zai zo in sha Allah."
"Ya yi" ya faɗa yana ɗauko waya yana dannawa. Abinda ya faɗo ƙasa ta kalla garin ɗauko wayar ya faɗo daga aljihunsa. Ta kalle shi ta ce, "Omar me nake gani a kusa da ƙafarka?." Kallon wajan ya yi sannan ya kalle ta ta ce, "Omar baka daina shan sigari ba daman?."

"Na daina Didi, ɗazu ne da raina ya ɓaci shine...."
"Shine ka sha?."
"Uhum."
"Omar ba ka ce min ka daina ba?." Ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "Didi na daina wallahi, ɓacin rai ne kawai." Shiru tayi alamun ranta ya ɓaci, ya kalle ta ya ɗauke kai ya cigaba da abinda ya ke yi. Jin shirin na ta yayi yawa ya sake kallon ta ya ce, "Didi yau ne kawai, kuma daga yau har abada bazan sake ba."

Kawai sai ta fara kuka ta ce, "amma ka ce min ka daina ko? Ka san bana so. Yaushe ka fara yi min ƙarya? Ina yarda da duk abinda ka ce min saboda na san ƙarya ba ɗabi'arka ba ce, amma gashi ka fara Omar." Ya tausasa murya ya ce, "ai na faɗa miki dalilina Didi, kuma bazan sake ba faga yau nayi miki alƙawari, ki daina kuka." Ajiyar zuciya tayi ta kalle shi bata ce komai ba.

Ɗauke wacce ta faɗi ƙasa tayi ta miƙe ta ce, "Zan shiga na kwanta." Ya miƙe shima yana kallonta ya ce, "ki daina kuka to, bazan sake ba in sha Allah." Ya share mata hawayen da kansa ta kalle shi tace, "na daina Omar." Da hannu yayi mata alamun tayi murmushi sai tayi murmushin shima yayi murmushi ya fita ya barta a wajan. Ajiyar zuciya tayi ta shiga ɗaki bayan ta kashe hasken falon.

Washe gari.

Kasancewar Juma'a ce da wuri ta tashi dan tana yin abincin sadaka duk ranar, nan da nan ta haɗa shinkafa da wake da dafaffan kwai ta zuba a disposable packs kamar yadda take yi in an idar da sallah ta fita da kanta ta rabawa yara. Lokacin da ya shigo ta gama tana zubawa a packs ɗin ya kalle ta ya ƙaraso ya ce, "Didi wai ba za a samu mai taya ki aikin nan ba?" Ya faɗa yana karɓa tare cigaba da yin abinda yake yi.

"To Omar ko wacce mace tsoron shigowa gidan nan yake yi saboda kai, kai kanka in kaga baƙuwa ka dinga faɗa kenan taya zan samu mai ta ya ni aiki?."

"Gabaɗaya mutanen unguwar nan munafukai ne, musamman ma matan." Jin abinda ya ce sai tayi murmushi ta bar masa ya cigaba da abinda yake yi dan tasan bazai barta ta cigaba ba. Sai da ya gama sannan ta kalle shi ta ce, "Amma dai ba da ƙananun kaya zaka je masallaci ba?." Zai yi magana ta ce, "Don Allah ka saka manyan kaya, don Allah na don ni ba." Hannu ya wanke bai ce komai ba ya shiga ɗakinsa.

Sai gab da lokacin sallah sannan ya fito yana fitowa ta fito itama daga falo ta bishi da kallo tana murmushi. Ya yi mata kyau cikin yadi milk colour, abin ka da namiji mai kyau, duk da bai saka hula ba amma yayi kyau sosai. Murmushi tayi ta ƙaraso inda ya ke ya ce, "ƙanina mai kyau ne wallahi, Allah ya sa kayi budurwa yau." Taɓe baki yayi bai ce komai ba kuma bai yi murmushi ba.

Ta kalli gashin kansa ta ce, "ya kamata ka ɗan rage gashin nan na kanka, kalli fuskar ka ma, gashin yayi yawa kamar wani buzu."
"Shi ne" Abinda ya ce kenan yana juyawa ya fita ta bishi da kallo tana murmushi.

Hijjabi ta saka ta fita bayan ta rufe ƙofar gidan ko makulli bata saka ba dan ta san babu wata halitta da zata iya shiga gidan da sunan sata. Kai tsaye gidan Hajja ta shiga a lokacin Nayla tana zaune kusa da Hajja sun saka ta a gaba ita da Salma sai wai ta basu labarin lokacin haihuwar Salma.

Sallamar Didi ya saka suka amsa Nayla ta ce, "Didi." Didi ta harare ta ta ce, "daman kin ce min baza ki sake zuwa ba gashi kin tabbatar." Nayla tayi dariya sosai, Didi ta kalli Hajja ta ce, "Hajja ki shaida mun yi faɗa da Nayla." Hajja ta ce, "ko ɗazu sai da tayi zancenki, amma wai baza ta shiga ba saboda Omar. Na ce Omar ya raba Yaya da ƙanwarta."

Didi tayi dariya suka gaisa da Hajja suma duk suka gaishe ta amsa da murmushi ta ce, "Hajja mutuminki shine yake firgitata, na faɗa mata kuma ta daina jin tsorosa babu abinda zai mata amma ta kasa. Kuma da zata zauna a garin nan na wani lokaci suna sabawa shikenan. Wahalar sabo ne dashi kawai." Salma ta ce, "Didi ko iya wannan idanun na sa ma ai ya isa ka ji tsoro balle ya buɗe baki."

Didi tayi dariya ta ce, "yanzu saboda shi sai ku daina zuwa wajan Yayarku?." Salma ta ce, "ai Didi lamarin na sa ne akwai ban tsoro." Nayla ta ce, "Ke da bai taɓa tarfa ki kamar yadda ya yi min bama kenan, ina jin in ke ya yiwa abinda ya yi min suma zaki yi." Didi ta ce, "ai na faɗa miki shi zan saka yazo ya ɗauko min ke in baki koma ba, zaki gani kuma."

Hajja ta ce, "wai! ranar sai Hauwa ta suma." Suka yi dariya gabaɗaya kafin Didi ta ce, "Hajja dahuwar awara zaki koya min, wacce nake kaiwa ana yi min bata yiwa Omar daɗi." Hajja ta ce, "shikenan kin kama Hauwa har wuya. Ja hannunta ki je ta dafa miki, ta iya dafa awara nesa ba kusa ba. Itama irin Omar ɗin ce, tsabar son cin ta da take yi sai da ta iya dafawa." Didi ta kalli Nayla ta ce, "Alhamdu lillah, ki ce shiga gida ya kama ki."

Nayla ta wara ido ta ce, "ai gwara ki aiko min da kayan nayi miki a nan sai na aiko miki da ita, kuma ban iya mai yawa ba ƴar kaɗan na iya dafawa." Didi ta ce, "ai wallahi gida zamu je ki yi min nima na koya, babu wani na aiko miki dashi baki isa ba."
"Allah Didi tsoronsa nake ji, in na ganshi hantar cikina kaɗawa take yi." Suka yi dariya gabaɗaya Didi ta ce, "Tsoron nake so na cire miki, ki saba dashi shima yayanki ne kamar yadda nake yayar ki."

Hajja ta ce, "ai na faɗa mata in da amana ai ruwa bazai dafa kifi ba, Ita da ya saɓo ta a kafaɗa ko riga babu itace mai faɗar haka a kansa." Nayla ta dafe kai cikin takaicin kalaman Hajja ta ce, "Wai Hajja don Allah meye haka?." Didi ta yi dariya ta ce, "Hajja kina bata kunya."
"Kunyar ƙarya ce, ai ba ƙarya nayi ba a kafaɗar ya ɗauko ta ko? Kuma ai gaskiya ne rigarsa ya saka mata."

Didi ta ce, "Gaskiya Hajja ki daina tuna mana maganar nan kunya mu ke ji." Hajja tayi dariya ganin Nayla sai ɓata rai take yi, ita kuma tana sane take faɗa saboda ta tunzura Nayla ɗin. Didi ta miƙe tana dariya ta ce, "Nayla ina jiranki." Nayla ta ɗaga kai dan babu yadda zata yi ne amma bata son haɗuwa da Omar.

Bayan Didi ta fita Nayla ta kalli Hajja ta ce, "Haba Hajja! Meyasa zaki ce mata na iya don Allah? Kin san tsoronsa nake ji." Hajja ta ce, "ke ni fa saboda kyautatawarsa akan ki ne ce ki je, sannan Didi jikata ce kamar ki, tana sona tana son ku gabaɗaya." Nayla ta kalli Salma ta ce, "Salma zamu je?." Salma ta wara ido ta ce, "ai na rantse da Allah baza ni ba, Ke dai ki je." Nayla ta zauna kamar zata yi kuka zuciyarta cike da fargaba.

Didi na rabon abinci a ƙofar gida ta hango Nayla tana tahowa a nutse sai tayi murmushi tana kallonta, ita dai Nayla na matuƙar burge ta sosai, bata sani ba ko dan tana kyau ne ya saka haka oho. Babban abinda yake burge ta game da Nayla shine shigarta, bata taɓa yin shigar banza. Kayanta ta basa wuce doguwar riga, riga doguwa har guiwa da siket, butterfly da sauran kayan mutunci na zamani. Wannan dalili ya saka take sonta sosai, gata kirki.

Tare suka ƙarasa rabon abincin da Nayla suka shiga cikin gidan Nayla sai ɗari-ɗari take yi. Didi ta kalle ta tace, "kwantar da hankalinki baya nan, ya kai yamma bai dawo ba."

Ajiyar zuciya tayi Didi tayi dariya suka fara haɗa awara kamar yadda ta ce. Didi tana gefe tana kallon ta har suka markaɗa a blender aka tace aka fara dafawa. Didi ta ce, "bara na gyara kayan miyar nan mai sauce nake so nayi." Nayla ta ce, "ashe kina son awara, nifa saboda son da nake mata ne ya da na iya dafawa, dan tunda na taɓa ganin gashin kai a cikin wacce ake yi min a gida na daina bari masu aiki su yi min." Didi ta ce, "ni bata dame ni sosai ba, mutuminki ne masoyin awara, bai damu da nama ba kamar yadda ya damu da awara. Zai iya ci miki awara da safe da rana da daddare, Sam shi nama bai dame shi ba, da rayuwar nama da babu duk ɗaya, har gwara kifi ma."

_Shiyasa yake gabjeje mana ashe soya beans yake afakawa cikinsa_ Nayla ta faɗa a zuciyarta. Didi ta ce, "kuma kar ki ɗauka da yawa yake ci, kin san ɗan iyayi ne, ƴar kaɗan in ya ci zata ishe shi kawai  sonta yake yi. Da ita da jollof rice mai kifi, da noodles, da pasta and stew. Inda safe ne kuma doya da ƙwai in ta huce ya ci ta da ketcup ko yaji, har mamakin inda ya iya cin ketcup yake yi. Noodles ma sai ya ci ta tun safe har dare kamar yaro. Wani lokacin kuma baya cin ahinci sai dai ya shafa coffee ko ya yini yana cin apple da kankana." Nayla ta yi murmushi kawai tana mamakin ko ita ina ruwanta da abinda yake so.

Didi ta ce, "yau so nake yaci har ya barta, bara na haɗa sauce ɗin." Nayla ta ce, "bar shi nayi miki kafin awarar tayi, tunda kin gyara kayan miyar bara ayi blending, ni gyara su ne bana so." Didi ta ce, "yau Omar zai ci abincin ki kenan." Tayi dariya kawai ta fara haɗa sauce ɗin tana yi suna hira.

Nan da nan suka gama Nayla ta tace awarar ta kalli Didi ta ce, "Zamu bar ta haɗa jikinta sai mu soya. Ita kuma sauce ɗin in kina da mayonnaise ki zuba mata, ko in kin zo serving ki zuba ni dai tana min daɗi." Didi ta ce, "ai kam na gode sosai Nayla, Kin ga nima na koya saboda gaba, ashe ma babu wahala." Tayi murmushi ta ce, "bara naje gidan Hajja."
"To ki dawo mu ƙarasa don Allah."
"Zan dawo yanzu Didi" ta faɗa tana fita da sauri.

Didi sallama ta jiyo daga tsakar gidan hakan ya saka ta kashe gas ta fito tana amsawa. Gabanta sai da ya faɗi ganin wanda ya yake tsaye a tsakar gidan ta daure tayi murmushi ta ce, "Kawu kai ne tafe? Sannu da zuwa." Wanda ta kira da Kawu ya yi murmushi ya ce, "Yauwa Aisha, ke kaɗai ce a gidan?."
"Eh ni kaɗai ce Kawu, Omar bai dawo daga masallaci ba. Shigo kawu."

Kawu ya yi ajiyar zuciya dan yana daga cikin masu tsoron Omar ya shiga falon da sallama. Didi ta amsa ya zauna suka gaisa ta ce, "Ya Mutanen gidan?."
"Lafiya lau Aysha. Daga masallaci nake na biyo mu gaisa na kawo miki kafin bikin ƙanwarki" ya faɗa yana miƙa mata katin.

Didi da murmushi ta ce, "bikin wa za a yi Kawu?." Kawu ya ce, "Bikin Ramla." Jin sunan Ramla sai da gabanta ya faɗi itama sai tayi murmushi ta ce, "Kai ma sha Allah! Allah ya nuna mana lokacin."
"Amin ya Allah, Amma zaki zo ko?."
"Zuwa kai Kawu, in ban zo ba waye zai zo?." Yayi murmushi ya ce, "gaskiya ne, ku ne yayyen amarya."

Tayi murmushi ya miƙe tsaye ta ce, "Kawu ko ruwa baka sha ba ka miƙe." Kawu ya ce, "sauri nake yi, babu komai ba sai na sha ruwa ba. Na ce Omar bai shirya aure bane?." Ta kalle shi ta ce, "Gaskiya bai shirya ba."
"In ya shirya akwai ƙannensa zai iya zuwa ya nema." Jin abinda Kawu yace sai tayi murmushi tana murna da Omar baya nan da an shiga uku da wannan furuci na Kawu.

"Didi!" Omar ya faɗa yana shigo falon. Ganin wanda yake parlon sai ya tsaya cak yana kallonsa kafin ya girgiza kai ya kalli Didi da ita kanta bata so ya shigo ba, Kawu kuwa ya gamq tsurewa saboda tsoro.

Karaf Didi tayi ta ce, "Omar ga Kawu, ya biyo mu gaisa ya kawo katin biki ƙanwarka Ramla." Idanu ya waro waje ya ce, "ni bani da wani Kawu a duniya, kuma bani da ƙanwa, bani da ƙanwa a duniyar nan kar ki sake cewa ƙanwata!."

Kawu yayi tsitt bai ce komai ba zuciyarsa rawa kawai take yi saboda tsoro. Kallon Kawu ya yi ya ce, "Baka san baƙi ba sa zuwar mana gıda ba?." Kawu ya ce, "Omar ni ne fa."
"Kaine wa? Na ce kai ne?" Ya faɗa a zabure yana fito da idanunsa waje cikin fusata.

Didi ta kalle shi ta ce, "Omar meye haka?."
"Didi wai meyasa ki ke min haka ne? Su waye waɗannan da ki ke bari suna shigo mana gıda?. Waye shi? waye na mu?" Ya faɗa yana ɗaukar iv da aka kawo ya watsar dasu a tsakiyar falon.
"Omar Kawu ne fa."
"Ke ki ka san wani Kawu ni ban san shi ba, bani da wani Kawu a duniya" ya faɗa idanunsa a waje yana karkaɗa yatsansa. Kallon Kawu ya yi ya ce, "ka manta abinda na yi maka wancan lokacin ko? Baka ji ba ka sake zuwa gidan nan ko?. Shikenan zan maka tabon da baza ka sake marmarin zuwa ba."

Kawu ya tsorata sosai ya ce, "ka yi haƙuri Oma...."
"Kar ka sake faɗar sunana, haƙuri kuma ban san shi ba!" Ya faɗa da ƙarfi yana kallonsa. Didi ta kalli Kawu ta ce, "Kawu yi haƙuri, ka tafi kawai Kawu." Ganin Omar zai fita ta ce, "Omar kar ka fita daga falon nan, Kawu mu je na rakaka." Omar jikinsa rawa yake saboda ɓacin rai ya fita daga falon. "Omar! Omar ka dawo!" Ta faɗa da ƙarfi amma ina ya fita daga gidan.

Kawu ya ce, "Aisha tsoro nake ji kar ya saka ayi min wani abun, haka kwanaki ya saka aka kusa hallaka ni." Ganin Kawu ya tsorata sosai sai ta ce, "babu abinda zai maka Kawu, tunda nace babu abinda zai yi babu ɗin, Kayi haƙuri."
"Ni zan bada haƙuri da na zo tunda na san baya so, ki yi haƙuri duk laifina ne ni na jawo wannan tsanar da yake mana." Didi ta ce, "Mu je kawu." Har ƙofar gida ta raka shi, ta ka ga su Bash kuwa suna jiran fitowarsa.

Kallon su tayi ta ce, "Kar wanda ya yiwa Kawu komai, in kuma wani abun ya same shi duk sai ranku ya ɓaci, ku faɗawa Damisar na ku ni nace a ƙyale shi. Kawu shiga motarka." Kawu jiki na rawa ya ce, "A'a Aisha."
"Kar ka damu Kawu babu komai." Kawu dai tsoro ne ya saka shi shiga motar ya bar unguwar a guje.

Didi gidan ta shiga cikin ɓacin rai ta shiga falo tana mamakin baƙar zuciya irin ta Omar da baya mantawa. Bai bar dangin uwa ba, haka ma dangin uban bai bar su ba. Har gwara ma na uwa tsanar da ya yi musu bata kai wacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login