Showing 51001 words to 54000 words out of 87436 words

Chapter 18 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

sane ya ce wace a nan dan yarinyar ta soma zuwar masa wuya.

Nayla ta ce, "ni ce, ina yini." Bai amsa ba ya ce, "Haka ake shiga gidan mutane babu sallama?." Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "nayi sallama."
"Mtsww! To me ya kawo ki?."
"Wajan Didi na zo."
"Tattara ƙafafunki ki bar gidan nan Didi bata nan." Jin abinda ya ce sai ta ɗago ta ga shima ita yake kallo fuskarsa a ɗaure sosai. A hankali ta tako ta zo ta wuce shi ya bita da harara ya koma ciki.

Haushin Didin ita kanta yake ji tun safe ta wani fita gidan biki, bikin ma kuma wai gidan Kawu tsabar lalacewa. Ga Nayla da ta ke neman tunzura zuciya sa, ta dame shi da shige da fice a cikin gidan su. A bayyane ya ce, "wannan yarinyar akwai nacin tsiya."

Nayla ba ƙarmain daɗin ganinsa taji ba ta dinga sauke ajiyar zuciya tana tafiya fuskarta da murmushi, ji take kamar an yi mata babbar kyauta mai matuƙar daɗi kasancewar ta ganshi har sun yi magana. A haka ta hau napep ta tafi gidan Mama Zaliha dan kar ta koma Hajja ta fahimci wani abun da baza ta je ba.

Omar shiryawa ya yi cikin manyan kaya na yadi baƙi mai gajeran hannu kansa babu hula, gidan ya kulle da makulli sannan ya tafi wajan Narma da niyar kai ta inda ya ce zasu je.

Narma tun shigarsa tana tsaye a balcony tana kallon sa, wara idanu tayi tana kallon sa cikin shigar manyan kaya dan ya yi mata kyau sosai. Bata taɓa ganin sa da manyan kaya ba, duk da ƙananun kayan suna karɓar sa kamar jarumin india, amma kyaun da yayi a manyan kaya ƙarshe ne.

Gani tayi kamar kwanakin da ɗauka bata ganshi ba ya sake yin kyau ga wani class na musamman da ya ƙaro, duk da fuskarsa babu annuri amma ya yi mata kyau sosai. Gazebo ya shiga ya zauna akan kujerun da suke cikin ta. Yadda ya zauna ya ɗora ɗafa kan ɗaya yafi komai tafiya da ita, bata san tayi murmushi ba a bayyane ta ce, "Tiger!."

Sakkowa tayi daga saman ta fito harabar gidan tana kallon inda yake, samun kanta tayi da nufar wajan da yake cikin salon tafiyar ta ƴan gayu. Har ta isa bai sani ba sai tsayuwarta ya gani da ƙhamshin turarenta. Ɗago ido ya yi ya kalle ta, ta yi kwalliya cikin straight gown, ta kawo mayafi mai kauri amma mara girma ta saka, tayi ɗauri da ta ja shi baya gaban gashin ta ya fito sai hakan ya ƙara mata kyau sosai.

"Ina yini" ta furta tana kallon sa shi kuma tuni ya janye idanunsa dan ya kasa gane abinda yake ji in yana kallon ta musamman in itama kallon sa take yi. Miƙewa ya yi ba tare da ya amsa ba, a shagwaɓe ta ce, "na gaishe ka kayi min shiru, kuma saboda kirkin da ka yi min ya saka na gaishe ka." Lumshe ido ya yi ya buɗe jin yadda maganarta ta tatsa har cikin zuciyarsa, wani irin sanyi yake ji a jikinsa yanayinsa na canjawa.

Sake haɗa ido suka yi ya janye ido bai ce komai ba. Narma ta ce, "baza ka amsa gaisuwar ba?." Ɗan ƙaramin tsaki ya yi ya ce, "lafiya." Daga haka ya yi gaba ta bishi da kallo duk sai taji haushin kanta da ta yi abinda ya dizaga ta.

A hankali take takowa dan ɗakyar take motsawa saboda yadda ta kamata rigar, daga wajan guiwarta an kama rigar sosai ta tsuke. Baya ta juya tana yiwa mai gadi magana a nan ya hango doguwar tsagar bayan rigar wacce ta bayyana farara digadiginta, har abinda ya rab digaginta da cinyarta a bayyane yake. Ɗauke kai ya yi daga kanta yaja dogon tsaki ba tare da ya san dalili ba, ta buɗe motar ta shiga shi kuma ya ja motar suka fita.

Babu wanda yake magana a cikin su kamar ko yaushe, shi titi yake ita kuma danna waya amma lokaci zuwa lokaci tana ɗagowa ta kalle shi sai ta cigaba da abinda take yi. Shopping complex suka shiga kamar yadda ta ce, ya tsaya a harabar store ɗin ta buɗe ta fita bata ce masa komai ba.

Fitowa ya yi shima ya shiga dan akwai abinda yake so ya siya. Bata san ya shigo ba sai ganin sa tayi a ɓangaren turare ya ɗauki ɗaya na maza sannan ya ɗauki ɗaya na mata. Ƙarasowa wajan tayi ta kalle shi shima ya kalle ta amma bai ce mata komai kafin kuma tayi magana ya wuce. Wajan kayan shayi ya je ya ɗauki coffee sannnan ya ɗaukarwa Didi milo dan ya san ta akwai son Milo, haka kawai ma sha take yi.

Kafin Narma ta gama shi ya biya kuɗi ya koma mota ya zauna yana duba turaren da ya siya. Ba jimawa sai gata nan ta fito bayan ta da mai riƙe da ledar da ta yi siyayya. Yana daga zaune buɗe baya aka saka mata sannan ta shiga motar suka tafi. Jira yake yaji ta ce ga inda zasu je yaji tayi shiru shi kuma bazai tambaya ba.

Ta wani ƙaramin cafe suka zo wucewa Narma ta ce, "ɗan tsaya a nan zan siyi donut." Faka motar yayi ta shiga ciki bata jima sosai ba ta dawo ta shiga motar. Wani almajiri ne yazo wucewa yana bara Omar ya sauke glass ya miƙa masa kuɗi shi kuma yana addu'a, Omar ya ɗaga glass ɗin bai ko kalle ya ba. Donut ɗin ta buɗe sai ta kalle shi ta ce, "Ga donut" ta faɗa tana miƙa masa ledar. Kai ya girgiza mata kawai ya ja motar suka tafi.

Wayarsa ce tayi ƙara ya kalla yaga Goje ne yake masa waya sai ya ɗauka ya saka a kunne Goje ya ce, "Damisa babbar Yaya ce babu lafiya, yanzu ta dawo daga unguwa."
"Subahanallah! Me ya same ta?" Ya tambaya a gigice. Goje ya ce, "Bamu sani ba, kawai mun ga saukarta daga napep tana jiri kamar zata faɗi."
"Gani nan" ya faɗq yana yanke wayar tare da ƙara speed ɗin motar.

Kallon sa Narma take tana mamakin Wacece babu lafiya haka ya damu?. Sannan mamakin kanta take yi wai ita Narma itace driver yake amsa mata waya a mota bata ɗauki mataki ba, ita kanta ta san ta canja.

Gani tayi sun wuce hanyar su ta kalle shi ta ce, "gida fa zan je." Ai ko kula ta ma bai yi ba sai da ya ganshi a ƙofar gidan su ya fita a gigice ya shiga gidan. A kwance ya samu Didi kana ganin ta ka san bata da lafiya, ya tallafo ta jikinsa ya ce, "Sannu Didi, tashi mu je asibiti." Ta kalle shi ta ce, "A'a Omar, ba sai naje ba."
"Wallahi sai kin je, ki tashi mu je ko na ɗauke ki wallahi." Jin abinda ya ce sai tayi murmushi ta miƙe ya riƙe hannunta suka fito, gidan ma a buɗe ya barshi saboda su Bash suna nan.

Motar da taga ya buɗe mata gaba ne ya bata mamaki, duk da tana cikin ciwo bayan ya shigo sai sa ta ce, "Omar motar waye wannan?." Narma da take baya ta maimaita Omar a zuciyarta tana cewa, _Dama sunan sa Omar? Suna mai daɗi. Shiyasa yake da fushi mana da yawa masu suna Omar haka suke._ bai bata  Didi amsa ba ya ja motar ta ce, "wai yaushe ma ka iya mota Omar?."

Kallon ta ya yi ya ce, "Don Allah ki yi shiru baki da lafiya" ya faɗa yana taɓa goshinta yaji zafi sosai. Narma da take baya ta ce, "Sannu, ya jiki?."
Didi kanta ciwo yake ɗakyarta iya waiwayowa bata ma iya gane wacece sosai ba, ta ɗaga kai kawai daga nan tayi shiru. Narma dai mamaki take yi ko wacece wannan? Ya ruɗe tunda aka ce bata da lafiya, gata kuma har yana haɗa ta da Allah akan tayi shiru cikin rarrashi, lallai ko wacece tana da mahimmaci a gare shi.

Asibitin da suka je aka yiwa Narma dressing nan suka je ya fito da kansa ya riƙe Didi suka shiga asibitin. Narma ganin yadda jikin Didi yake rawa sai ta bata tausayi sosai daman ita akwai tausayin mara lafiya hakan ya saka ta fito itama ta bi bayan su. Kwantar da Didi aka yi akan gado aka yi mata allura kafin a ɗauki jininta a gwada a dawo a fara yi mata treatment ɗin malaria.

Ɗakin gado biyu ne a ciki amma Didi ce kawai a kwance, Narma tana jingine da bango tana kallon Didi da aka gama saka mata ruwa bacci ya ɗauke ta. Hannun Didi ya riƙe wanda aka sakawa ruwan ganin zai faɗi ya ajjiye a gefen ta ya zare mata hijjabin jikinta ya sake taɓa wuyanta. Ƙaramin tsaki ya yi jin har lokacin da zazzaɓin ya ce, "Sai da nace mata kar ta fita amma taƙi ji."

Narma ita dai kallon sa take yi domin mamaki yake bata sosai, gabaɗaya ya sauya mata ya yi sanyi damuwar rashin lafiyar wacce bata san alaƙar su ba ta canja shi. Kana jin yadda yake magana kasan ko wacece wannan ya damu da ita sosai. Kallon gefen ta ya yi yaga tana kallonsa sai a lokacin ma shi ya tuna da ita dan wallahi tunda yaga yadda Didi take ya manta da wata Narma a bayan mota. Sai Narma tayi murmushi ta ce, "Zata samu sauƙi in sha Allah." Kai ya girgiza bai ce komai ba, amma yaji ta burge shi sosai.

Awa ɗaya suka kwashe a asibitin dan shi bazai iya tafiya ya bar Didi ba, ita kuma Narma duk ta gaji sosai. Bai ma lura da yanayin ta ba, abinda ya sani ko babanta ne zai zo bazai bar Didi ya tafi wani waje ba. Ya kalle ta ya ce, "zan kira waya azo a mayar dake gida yanzu." Narma ta ce, "A'a, ka bari ta farka sai mu tafi gabaɗaua, jikinta bai yi worst ɗin da za'a yi addminting nata ba." Shiru kawai ya yi bai sake cewa komai ba. Fita ya yi ya yi sallar magriba ya dawo a lokacin Didi ta buɗe ido. Bayan ya dawo ya ƙaraso inda take ya riƙe hannunta ya zaunar da ita akan gadon ya ce, "ya jikin?."

Didi ta ce, "na ji sauƙi sosai, ciwon kai ya rage sai rashin ƙarfin jiki da babu."
"Shima zaki daina ji in sha Allah." Ba sake magana ba ya fita jim kaɗan ya dawo ya kalle ta ya ce, "zamu tafi gida, ga magani da allurai an bayar, ai kin ce jikar Hajja ta iya allura ko?." Didi ta ɗaga masa kai, ya riƙota ta tashi tsaye ya saka mata hijjabi da kansa ya riƙe hannunta ya ce, "Mu je gida." Kallon Narma tayi ta ce, "Ka bar baƙuwar ta ka."
"Wacce baƙuwa?" Ya furta yana kallon Narma dan wallahi ya sake mantawa da ita.

Narma ta ɗan saki fuska kaɗan ta biyo bayan su. Yanzun ma Didi ya buɗewa gaba ta shiga, Narma ta shiga baya suka sake komawa gidan Didi. Narma tana mamaki kenan itace bazai buɗewa ƙofa ba tunda gashi yana buɗewa wacce bata sani ba. Suna tsayawa Narma ta ce, "Allah ya ƙara sauƙi."
Didi ta kalle ta ta ce, "Amin. na gode Barr Nass." Narma bata yi mamaki yadda ta santa ba tayi mata murmushi ta fita.

Bayan sun shiga Didi ta ce, "ka bar ni kaje ka mayar da ita gida, tayi ƙoƙari sosai wallahi." Ya kalli Didi ya ce, "zan kai ta, so nake na tabbatar kin samu lafiya."
"Na samu lafiya Omar, ka je ka mayar da ita ba kowa ne zai yarda da irin haka ba." Bai ce komai ba ya fita ya shiga motar bai ce mata komai ba har suka je gidan.

Fitowa yayi daga motar bayan ta fito ta kalle shi ta ce, "Allah ya ƙara lafiya, a gaishe ta." Dan kawai kallon sa take yi ne ya saka taga bakin sa ya amsa da amin, amma maganar ko kan harshensa bata zo ba balle laɓɓansa. Ya miƙa mata key ta girgiza kai ta ce, "kaje da motar saboda kana da mara lafiya, kaje da ita kawai." Kai ya girgiza ya ce, "bana buƙata" ya faɗa yana sake miƙa mata key ɗin.


"Ka je dashi." Ya girgiza kai ya ce, "bani da buƙata, na gode."

Murmushi tayi jin yana yi mata godiya ta karɓi key ɗin har ya juya ta ce, "Omar!." Wani iri ya ji a jikinsa, ya waiwayo ya kalle ta ta ce, "Ranar da aka yanke ni a hannu kaine ka biya kuɗin asibiti, na manta ban biya ka ba. Please ka bani account number ɗin ka na tura maka."

Kamar zai yi magana sai ya fasa ya ɗaga kai kawai yana juyawa ya fita, ta bishi da kallo tana murmushin da bata san dalili ba. Mai gadi ta kira ta bashi key ɗin motar ta ce ya kwaso mata kaya ya shigar mata dasu ita kuma ta shiga ciki.

        Omar kuwa haka ya koma gida sunansa da ta kira yake ji har cikin zuciyarsa bai san lokacin ba, ya yi murmushi Didi ta kalle shi ta ce, "murmushin me ka ke yi?." Ya ƙarasa shiga yana kallon ta ya ce, "ya jikin naki? Na ɗauka ma kin yi bacci kin huta."
"Ban yi bacci ba."
"Abinci fa?."
"Na ɗan ci, Hajja ce ta ta aiko min da abinci yanzu." Ya girgiza kai yana kallon ta ya ce, "To yanzu ki ki kwanta ki huta. Sai da nace miki kar ki je gidan bikin nan kika ƙi ji, wataƙila wani abun suka yi miki dan ki yi rashin lafiya daman ba son ki suke yi ba."

Tayi ƴar dariya ta ce, "naji, ko ma meye dai ƴan uwana ne." Ya taɓe baki bai yi magana ba. Tana  so tayi masa maganar Narma da inda ya koyi mota amma bata jin ƙarfin jiki hakan ya saka ta tashi taje ta kwanta shi ma ya fita zuciyarsa cike da tunani kala-kala.

Washe gari bai fita ba har yamma sannan ya je gidan dan yaga kiran Narma bai ɗauka bane. Lokacin da ya je gidan shiru babu komai duk bai ga masu aikin ba bai damu ba ya yi zamansa a inda ya saba zama. Ihu ya dinga ji daga cikin gida, da farko ya ɗauka kunnensa ne amma sai yaji abun ya yi yawa ihu ake sosai ana neman taimako.

Kamar kar ya shiga sai kuma ya miƙe ya shiga falon gidan dan bai san abinda ya faru a ciki ba, a daidai lokacin Narma ta sakko a guje daga ita sai towel ƙarami wanda ko cinyar ta bai gama ɓoyewa ba, kanta babu ɗankwali tana ihu kamar wacce aka biyo.

Ganinsa a tsaye sai kawai ta yo inda yake ya yi saurin yin baya dan yaga ƙoƙarin rungume shi take yi.

"Geckos a toilet ɗina, ka taimaka min ka kashe shi tsoronsa nake ji." Takaicin da Omar ya ji ji yayi kamar ya tsinke ta da mari ya tsaya kawai yana kallon ta cike da takaici. Wai tsaka take yiwa wannan ihum, da farko ya ɗauka wasu ne suka shigo gidan da niyar cutarwa take kukan neman ceto.

"Ka taimake ni ka je ka kashe ta don Allah" Ta faɗa tana niyar yin kuka. Kallon inda ta sakko ya yi dan shi kam dai bazai hau saman ba. Mai aikin ta mace ce ta shigo tana cewa, "Hajiya lafiya?."
"Geckos zaki kashe, maza jeki toilet ɗina." Da sauri ta hau saman shi kuma ya fita bai sake kallon ta ba.

Zama ya yi yana amma gabaɗaya ita yake gani a idanun sa ɗaure da towel ta nufo shi a guje, runtse ido ya yi ya buɗe ya tashi zaune sosai ya tuna lokacin da ta riƙe shi da aka ƙwace mata waya, ya sauke numfashi yana jin sabon yanayi a tare dashi mai wahalar fasaarawa.

Bai jima sosai sai ga mai aikin ta ta ƙaraso ta ce, "Wai kazo." Ya kalle ta ya ce, "na zo?."
"Eh, haka Hajiya Narma ta ce." Kai ya ɗaga  mata kawai ta tafi shi kuma ya sake gyara zama dan bazai shiga ba. Bata isa ta aiko a kira shi ba kuma ya je, dan ta ga yana sake mata bata isa ta raina shi ba.

Ga mamakinsa sai gata ta fito cikin riga roba mai bin jiki ko ina na jikinta yana rawa. "Wannan yarinya bata da hankali!" Ya furta yana yana rufe idonsa. Ƙarasowa tayi ta ce, "Tiger daman tambayarka zan yi ya jikin mara lafiya shiyasa na kira ka ɗazu, da baka ɗauka ba shiyasa kayi tunanin akwai inda zan je." Omar ya miƙe tsaye jin tana tambayar lafiyar rabin ransa ya ce, "ta ji sauƙi."
"Allah ya ƙara lafiya, ka gaishe ta."
"Zata ji."
"Baka tura min account details ɗin ba." Ya kalle ta suka haɗa ido ya ce, "zan tura."

Miƙa masa ledar jiya tayi ta ce, "ka barta a mota jiya, da na ce kwaso min kaya sai aka haɗa min har ita. Nace wannan ai saƙon Tiger ne ba nawa ba." Kallon ledar ya yi dan shi wallahi ya manta da ita gabaɗaya, karɓa yayi bai yi magana ba. Narma ta ce, "Zaka iya tafiya babu inda zan je."

Nan ma bai yi mata magana ba yana mamaki a ransa lallai ma ta samu sake, har zaka iya tafiya take ce masa wato ga yaronta. Ƙwafa ya yi kaɗan zai wuce ta ce, "Meyasa baka son yi min magana? Jiya naji kana ta magana amma ni baka yi min." Bai jiyo ba balle ya tanka ba ya wuce, a nan ya ga Ashraf a tsaye yana kallon su da alama ya jima da zuwa gidan. Bai ko kula shi ba ya fita daga gidan.


*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

             ©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

Masu nema daga farko ga WhatsApp link nan.
https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t

*Book 1*
*P 16.*


Narma wajan Ashraf ta ƙaraso da yake kallon ta har tazo inda yake ya kalli Omar da ya fita ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login