Showing 21001 words to 24000 words out of 87436 words
Chapter 8 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt
falo, Abiy yana cin abinci Mama na gefensa ganin ya kammala cin abincin sai ta kalle shi ta ce, "ɗazu Nayla ta kira ni, na ce mutanen Kano ya Hajja." Abiy ya murmusa ya ce, "nima daga dawowa ta gidan nan zuwa yanzu sau biyar ta kira ni, Ai naga alama tana son zama wajan Hajja sosai."
Mama ta yi murmushi ta ce, "itama Hajjan tana matuƙar jin daɗin zama da Nayla ai, kasan Nayla ba dai hankali da iya magana ba." Abiy ya murmusa kawai bai ce komai ba kafin ta ce, "Kwana nawa ka bar ta yi ne?."
"Sati ɗaya."
"Haba Abiy, ina laifin ka barta tayi sati uku tunda dai ta kammala service ɗinta kuma baka samar mata aiki ba. Tahzif ɗin da ta shiga ma ta kammala tana gida a zaune. Hajja na son zaman ta a can, ita take ɗauke mata kewar mahaifiyar ta da ta rasa take kallon Nayla tamkar Bilkisu."
Abiy ya kalle ta ya ce, "Bana son zaman ta a Kano ne gabaɗaya, kar ki manta abinda ya so faruwa da ita a shekarun baya, ba dan Allah ya kiyaye ba da an cutar da ita. Tun daga nan zaman ta a Kano ya gama fita daga raina, da ina da iko ma ko kwana ɗaya baza tayi a can ba, to ban isa na rabata da dangin mahaifiyarta da suke can ba. Kuma suna tsananin son Nayla da ƙaunar ganinta, dole ne na barta ta je gare su."
"Na sani Abiy, Amma ai komai ya wuce kuma yanzu Nayla ai tana da hankali da wayon da abinda ya faru a baya bazai faru yanzu ba sai dai ƙaddara. Hajja tana sonta, tun farko ta nuna maka ka bar mata Nayla kawai dai ka ƙi ne. Kuma suma sun yi mana kara a kanta sosai."
Abiy ya ce, "har abada bazan iya barwa kowa Nayla ba, ke bama Nayla ba kaf ƴaƴana biyar har Nayla shida bana tunanin zan iya barin su su je wani wajan su zauna gaskiya. Sai dai aje ayi ziyara a dawo, ni ne na haife su haƙƙin riƙe su a hannuna yake."
"To ka ƙara mata lokaci kafin ta fara zuwa aiki ta zauna a Kano wajan Hajja."
Abiy ya sauke numfashi ya ce, "zan yi tunani a kan hakan na gani, amma a yanzu dai sati ɗaya na bari tayi, in naga zan ƙara mata sai na ƙara mata, In naga bazan iya ba ta dawo gidan mahaifinta." Mama tayi murmushi ta ce, "Hakan yayi, Allah ya kaimu." Ya amsa da amin kafin ya tashi ya shiga ɗaki ya bar Mama a zaune a wajan.
"Nayla hmmm! Ai wallahi sai na raba ku, yadda ta bar gidan nan a bana tunanin zata sake dawowa cikin sa, in ma ta dawo na ɗan lokaci ne kawai amma sai nayi amfani da wayo da dabarar da na nisanta ka da Nayla. Sai na san yadda na yi Nayla ta je gidan mijin da zai ci ubanta, ya hanata walwala ya kuma hanata jin daɗi. Burina Nayla ta rayu a gidan auren da zata sha wahala kamar ydda uwarta ta wahalar dani, Zan fashe wahalar da na sha akanta!." Girgiza kai Mama take yi tana hasaso lokacin da wannan buri na ta zai cika. Bata nufin Nayla da ko wanne irin sharri ko makirci, ta raini Nayla daidai da yadda ta raini ƴaƴanta, ta bata tarbiyya da rayuwa mai kyau. Ita babban burin ta Nayla ta yi aure a inda zata sha wahala kuma sai tabbatar da ta cika wannan buri na ta hankalin ta zai kwanta, ta yi ƙwafa ta miƙe zuwa daƙi.
Washe gari
Kano.
Washe gari Alhamis Nayla da azumi ta tashi kasancewar ta mai ibadar azumin litinin da alhamis, ranta a jagule gabaɗaya bata da walwala saboda rashin chajin waya, daman gidan Daddy da suka je da daddare ne ya saka ta cikar wayarta kuma ta ƙarar gashi yanzu kuma babu wuta kuma ba a gyara solar Hajja ba.
Hajja na kula da ita tana zaune a falo tayi shiru masu yiwa Hajja aiki suna ta aikace-aikacen su kafin kammala su bar wajan. Hajja ta kalle ta tace, "Hauwa'u baki da lafiya ne? Ko ki karya azumin." Ta kalli Hajja ta ce, "Rashin chaji bala'i ne Hajja, duk shi ya saka ni a wannan yanayin."
Hajja ta ce, "ki kaiwa Aisha ta saka miki mana." Nayla ta dafe ƙirji ta ce, "har kin saka gabana ya faɗi, ni in sake shiga wannan gidan...? Ai har abada." Hajja ta ce, "To a ina zaki saka chajin?."
"Bara Salma ta tashi mu ji ya za a yi." Salma ce ta fito da kayan bacci ta kalli Nayla ta ce, "meye naji kina maganata?."
"Salma chaji nake so wallahi, Ke kin san bana son zama babu chaji."
"Ga power bank ɗina can ki saka, amma ba zai yi miki da yawa ba dan shima babu chajin."
Jin haka sai taji daɗi ta saka chajin amma duk da haka bai mata ba dan da gani chajinsa ya kusa ƙarewa. Sallama aka yi aka shigo falon duk suka kalli wanda ya shigo.
Ganin Daddy ya saka Nayla ta miƙe tana cewa, "Lah Daddy sannu da zuwa." Kallon ta yayi yana murmushi ganin fuskar ƙanwarsa Bilkisu a kan fuskar Nayla ya ce, "yauwa Hawwer, yanzu ma ki ka tashi kenan?" ya faɗa yana kallon Salma da ta fito daga kitchen da kofin shayi.
Hajja ta ce, "Yanzu kam suka tashi dan ko wanka ba su yi ba." Gaisawa suka yi da Hajja kafin suma su gaishe shi ya kalli Nayla ya ce, "Jiya kun je bamu haɗu ba, ya services ɗin naki?."
"Daddy ai na gama, yanzu aiki nake jira."
"Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya kawo miji na gari." Hajja ta amsa da amin kafin ta ce, "Duk sun girma sai aure, su huɗu ne gasu nan kan su ɗaya. Hauwa'u, Salma, Ummimi da Zainab." Daddy ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya ne wannan, Allah ya kawo namiji na gari."
Hajja ya ce, "Amin. Amma ga mazaje nan a gidajen ku meye amfanin su?. Zaratan samari nawa muke dasu?." Salma da Nayla suka kalli juna Daddy ma dariya ya yi ya ce, "basu da amfani kan Hajja, muna jira wani ya furta yana son ƴar uwarsa ne sai ayi."
"Har sai an jira? Lallai kace zan rarraba su ga duk wanda naso. Duk wanda na ce na bawa ɗaya a cikin su ai babu wanda zai musa ko?."
"Babu kam Hajja."
"Yauwa, to ku jira zan fara watandarsu tunda na ga ku kun yi sanyi." Dariya Daddy ya yi ya kalli Nayla ya ce, "Ya gidan babu wuta? Naga kina gumi ki kunna ac mana."
Nayla cikin shagwaɓa ta ce, "ba solar ta lalace ba har yanzu ba a gyara ba." Daddy ya ce, "Subahanallah! Har yanzu ba a gyara ba daman? Ke Salma meye amfaninki da baki faɗa min ba?" Ya faɗa yana ɗauko waya tare da kiran masu aikin solar suka tabbatar da zasu zo a lokacin. Nayla murna kamar tayi me saboda zata samu chaji yadda take so. Daddy sallama ya yi musu bayan ya basu kuɗi ita da Salma ya tafi.
Omar kuwa a safiyar yana zaune a falon Didi yana cin indomie ita kuma ta kitchen tana wanke-wanke. Sallama akayi tare da shigowa falon ya ɗago yana kallon wanda ya shigo. Ɗiff yayi ganin wanda yake tsaye a bakin ƙofar shi bai shigo ba kuma bai koma ba. Omar bai amsa sallamar ba sai ma ɗauke kai da ya yi. Didi jin sallama kuma bai bada amsa ba ya saka ta fito falon tana kallon inda yake kallo.
Da Yayan Mahaifiyarsu ta haɗa ido Baba Adamu sai kuwa ta saki fara'a ta ce, "Lah Baba kai ne tafe? Sannu da zuwa." Ƙarasowa tayi shima ganin ta sai ya shigo yana murmushi ya ce, "Ni ne Aisha."
"Sannu da zuwa, Ka zauna mana Baba."
Ya zauna yana satar kallon Omar da yake cin indomie kamar bai san ma ya shigo ba. Gaisawa suka yi da Didi ya ce, "ya kike ya sana'ar taki? Fatan komai Lafiya."
"Lafiya lau Baba, ɗazu nake zancen gobe juma'a zan zo mu gaisa in sha Allah."
"Allah sarki, Allah ya baki ladan niya." Ta amsa da amin ya kalli Omar ya ce, "Omar ina kwana."
Wani iri Didi taji na rashin jin daɗi ganin babban mutum kamar Baba Adamu shine yake gaishe da Omar. A sanyaye ta kalli Omar da kamar bai ma ji abinda aka ce ba ta ce, "Omar magana ake maka, ka gaishe da Baba."
In bowl ɗin da yake hannunsa ya amsa shima ya amsa. Didi ta ce, "Omar!."
"Na'am" ya amsa ba tare da ya kalle ta ba.
"Baka ji abinda nace ba ne?."
"Naji mana."
"To ka gaishe shi." Ya kalle ta ya ce, "bazan ba."
Zata sake magana Baba Adamu ya girgiza mata kai alamun tayi shiru ya kalle shi ya ce, "Omar ina kwana." Nan ma ya sake yi masa banza Didi zata yi magana Omar ya ce, "Bana iya girmama wanda bai girmama mahaifiyata ba, bana iya girmama wanda bai tashi nuna min mu masa bane sai da haƙora talatin suka fito a bakin mu. Kar ki ɓata bakinki Didi, kema kin san bazan yi ba."
Baba Adamu ya ce, "Omar kayi haƙuri, kuskure ne an yi shi a baya kuma na nemu afuwar ku."
"Ita wacce ƙasa ta rufe idonta fa, itama ka nemi afuwarta ne?"Omar ya faɗa yana kallonsa da rikitattun idanunsa. Baba Adamu ya ce, "Ina yi mata addua'ar samun gafara a wajan mahaliccinta." Omar ya ce, "yadda bakwa son mu wallahi nima bana son ku, yadda ku ka wulaƙanta mahaifiyar mu dan kawai tana auren mahaifin mu babu wanda zan iya ganin darajarsa wallahi, kum...."
"Omar!" Didi ta katse shi da ƙarfi tana kallon sa.
Kallon ta yayi sai ya fasa faɗar abinda zai ce kuma bai tashi daga inda yake ba, dan bai isa yazo ya same shi ya tashi ya bar masa wajan ba. Baba Adamu ya ce, "ƙyale shi Aisha. Daman magana ce nazo da ita akan sabon company na da na buɗe, in Omar ɗin yana so sai yazo mu fara aiki gabaɗaya." Kallon ƙasan ido ya yiwa Baba Adamu kamar zai yi magan sai ya fasa ya cize bakinsa cikin ƙunar zuci.
Didi ta washe baki ta ce, "Lah yaushe aka buɗe Baba?."
"Satin da ya wuce."
"Allah ya sanya alkhairi ya sa albarka, Me zai hana ya zo? Zai ma yi aikin...."
"Gwara na koma bara akan titi da dai nayi aiki a ƙarƙashinsu wallahi" Omar ya katse a yana ɗaga mata hannu.
Zata yi magana ya ce, "Didi! Ke kin san waye ni, babu ɓoye-ɓoye, babu kare, wallahil azim bazan yi ba. Wato nayi aiki a ƙarƙashin su a samu damar wulaƙanta ni a zage ni ko? Kema kin san bazai yu ba, ai ko rahama ake rabawa a company na amince ta wuce ni na samu a wani wajan daban. Hanyar samun ta ai yawa ne dashi."
Baba Adamu ya ce, "babu laifi Omar. Amma duk lokacin ka ji kana da ra'ayi ƙofa buɗe take, Kuma har abada baza ka taɓa goge mu a rayuwarka ba, mu ɗin dai mu ne gatanka saboda mu ne jinin mahaifiyarka."
Omar ya taɓe baki ko kaɗan baya jin nauyi da girman Baba Adamu duk da ya girma sosai. Ya ce, "Allah ne gatan mu gaba da baya, babu wata halitta da zata zama gatan mu a duniya in ba Allah ba." Murmushi Baba Adamu yayi dan ya san shine ya jawo kuma ya san halin Omar da shegen riƙo da taurin kai, shekara sama da goma sha ana abu ɗaya amma har yanzu yaƙi sakin jikinsa.
Baba Adamu ya ce, "Aisha zan tafi, akwai abinda ki ke buƙata ne?." Didi cikin sanyin jiki ta ce, "Babu komai Baba, in akwai zan sanar da kai a waya."
"To akwai kayan abinci da nazo miki dashi, zo mu je yara sai su shigo dasu" ya faɗa yana miƙa mata rafar ƴan dubu-dubu guda biyu ta saka hannu biyu ta karɓa ta ajjiye. Omar ya kalle shi ya ce, "duk wanda ya ganni ya ganta ya san ba ma tare da yunwa." Babu wanda ya kula shi Didi ta kalle shi sannan ta bi bayan sa tana hararar Omar saboda kallon da ta ga yana yi mata.
Ba jimawa aka shigo da madara da milo da sugar da butter, kwai, taliya, doya, dankali, platain, da sauran abubuwa. A guje yaran suke ajjiyewa suna fita saboda Omar da yake kallon su daga falon.
Tana shigowa gidan yana fitowa daga parlon ya ce, "babu abinda za a ci a cikin kayan nan, ko ki mayar masa da tsiyarsa ko kuma na kwasa na zubar wallahi." Ta Harare shi ta ce, "wallahi bazan mayar ba, kuma baza a zubar ba Omar ba. Yayan mahaifiyata ne ya bani ba wani bare ba."
Da mamaki yake kallon ta ya ce, "ba gwara ace wani baren ne ya bayar akan ace shine ya bayar? Didi kar mu yi haka dake, ba za a ci abubuwan nan a gidan nan ba."
"Wallahi sai an ci!" Ta bashi amsa a kausashe tana kallonsa. Idanunsa sun yi ja saboda ɓacin rai ya kalle ta ya ce, "Akwai abinda babu a gidan nan ne? Faɗa masa aka yi yunwa tana tare damu ne da zai kawo mana wannan tarkacen?."
"Omar wai meye ya sa baka yafiya ne kai?." Ta kalle shi ganin sai wuci yake kamar zaki, idanun nan nasa sun yi ja haka jijiyar kansa ta miƙe kana kallon sa kasan ran masa ya ɓaci. "Tambayarka nake, meyasa baka yafiya ne?."
Bai iya yi mata magana ba sai wuce zai fita tayi saurin riƙo hannunsa ta ce, "Yayan mahaifiyarka ne in ka saka aka yi masa wani abun tamkar Mama ka yiwa, sannan ka tuna Mama baza ta taɓa alfahari da kai a yadda ka ke ba Omar. Zata yi alfahari da kai in ka kasance na gari, amma a haka baza taɓa alfaharin haihuwarka ba." Runtse ido yayi cikin ƙunar zuci ya zame hannunsa daga riƙon da tayi masa ya bar gidan da sauri.
Da kallo ta bishi bayan ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ya Allah ka shirya min ƙanina Omar, Allah ka yaye masa wannan baƙar zuciyar da yake fama da ita, Allah ka bashi ikon manta abinda ya riga ya wuce ya kama abinda yake gabansa, Amin." Kayan take ɗauka a hankali tana shiga dasu dan ta san in zasu shekara a wajan bazai taɓa ba, gabaɗaya jikinta ya gama yin sanyi itama, abubuwan da suka faru a baya suna yi mata yawo a zuciyarta.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t
*Book 1*
*P 07.*
*Abuja.*
Zaune suke a babban falo na alfarma su biyar suna cin abinci cikin yanga da iyayi, kai da ka gansu ka san kuɗi da ilimi ya gama zama a jikin dukkan su. Duba da irin shigar da take jikin Narma zaka tabbatar da wayayyun ƴan boko ne.
Dad ya kalli Nabil ya ce, "Nabil ka san lokacin lissafi a store ya kusa ko?." Nabil ya kalli mahaifin na su ya ce, "Yes Dad, na sani."
"Ya kamata a dakata da karɓat kaya sai mun kammala lissafi."
"Okay Dad za a yi." Ya kalli Najwa ya ce, "Najwa yaushe zaki koma London?."
Najwa ya kalle shi ta ce, "Sai nan da three weeks Dad." Kafin ya bada amsa Mum ta ce, "My Dear tunda dai sun samu hutu lokaci ya yi da zamu je Paris. Akwai birthday party ɗin friend ɗina, za a yi surprising ɗin ta a can, so ina so nayi attending."
Narma ta kalli Mum tana turo baki ta ce, "Mum ni babu inda zan je gaskiya, beside ni Kano zan je." Najwa ta ce, "Yaya Narma wai me zaki yi a Kano ne?."
"Samra's wedding."
"Friend ɗinki sai aure suke yi amma ke kin tsaya wasa." Narma tayi murmushi ta ce, "na kusa."
Mum ta ce, "to ke ki tafiyar ki Kano ni da Najwa zamu je Paris." Najwa ta ɗan ɓata rai ta ce, "Paris Mum?."
"In baza ki je ba kin huta, ai ba hanya ce ban sani ba." Najwa tayi dariya ta ce, "dole na ma." Mum ta kalli Nabil ta ce, "Nabil ka faɗawa Zuhra sai mu je tare, I hope Asim sun samu hutun school?."
"Yes Mum, sun yi hutu."
"Okay" ta furta tana cigaba da cin abincin ta.
Dad ya kalle Narma ya ce, "Yaushe zaki je Kano din?." Narma ta kalle shi ta ce, "Ranar Sunday zan tafi." Dad ya kalle ta ya ce, "Ranar yaushe zaku fara events ɗin?."
"Wednesday."
"Okay. Narma ban da yawo ke kaɗai ba, kin yanayin Kano ba wani security ne dashi ba. Dan ma kin takura ne da babu abinda zai saka na bar ki ki je." Narma tayi shiru bata ce komai na dan kar ma tayi magana a hana ta zuwa.
*Kano.*
Didi share Omar tayi dan ta san yinin ranar a ɓacin rai zai yi shi in tace zata biye masa itama ranta ne zai ɓaci. Aikace-aikacenta ta cigaba da yi gabaɗaya abubuwan da suka wuce suna yi mata yawo a kanta, duk yadda ta so ta kawar itama ta kasa hakan ya sanya idanunta zubar hawaye tunawa da iyayen su da suka rasa a shekarun da suka wuce.
Bata sake tunanin Omar ba dan ta san bazai dawo ba ransa a ɓace yake da ita sosai ta fi kowa sanin hakan. Ta kuma san in ba dan ita ɗin babu babu halittar da yake ɗagawa ƙafa, shi bai san kara ba, bai kuma son alfarma ba. Haka ranar ta yini sukuku bai dawo ba har yamma, ko da ya shigo bai ce mata komai ba daman ta san bazai ce ba ɗakinsa ya shiga bai jima ba ya fito ya sake fita.
Sai bayan sallar magriba kamar yadda ya saba shigowa ko yaushe sannan ya shigo kamar baza ta yi masa magana ba ganin ya haɗe rai sai kuma ta ce, "Baza ka ci abinci ba ne?." Kallon ta yayi yana shan ruwa ya ce, "Na daina cin