Showing 48001 words to 51000 words out of 87436 words

Chapter 17 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

rigar zuwa guiwarsa hannun, farin hannunsa da gashin da yake a kwance a hannun ya bayyana sosai, hakan da yayi sai ya ƙara masa kyau sosai. Nayla kallon sa take yi kawai cikin burgewa, daga sama yana da faɗi duk da ba faɗi sosai ba, amma daga ƙasa ɗan ƙarami dashi kuma a tsuke kana ganin sa kaga halittar cikakken namiji jarumi.

"Ina zuwa haka Alhaji Omar?." Didi ta tamabaya tana kallon sa da murmushi. Ya kalle ta bayan ya ɗage gira ya ce, "Yaushe ki ka fara sanin inda zan je?." Tayi dariya ta ce, "abin ne da mamaki, naga ƙarfe sha biyu ma bata yi ba ka shirya. Ko wajan yarinyar nan zaka je?." Agogo ya kalla ya ce, "A'a sai anjima."

"To ina zuwa ko abinci baka ci ba?."
"Bana son cin komai, zan je wani waje wataƙila bazan dawo ba sai dare." Didi ta girgiza kai ta ce, "Allah ya kiyaye Alhaji Omar Faruk." Murmushi ya yi yace, "Amin."

Murmushin da ya yi shine ya saka narkar da Nayla a kogin kallonsa har bata san ta tallafi haɓar ta tana kallonsa ba, ya gama tafiya da ita daga shigarsa, da maganarsa, uwa uba murmushin da yake sakawar Didi.

Sai da ya fita sannan ya kalli Didi taga tana neman wayarta sannan ta miƙe ta ce, "Didi bara na koma." Didi ta ce, "da wuri haka? Na ɗauka sai anjima." Nayla ta ce, "zan dawo anjima in sha Allah, ai yanzu na rage tsoronsa." Didi tayi dariya ta sake yi mata godiya ta raka ta har waje sannan ta dawo.

Nayla sai da ta tsaya a gate ɗin gidan Hajja ta dinga sauke ajiyar zuciya. Namiji mai murɗaɗɗen jiki irin na sa sam basa burgeta, hasalima itace mai kushe duk wani namiji mai irin wannan jikin, bata ƙaunar su tafi son namiji mai normal jiki ba wannan murɗewar ba. Wannan halitta tana daga cikin dalilin da ya saka bata so ace Abbas yana sonta, dan ta san baza ta so shi ba saboda jikinsa dan shi ya fi Omar murɗewa. Amma yau Omar ya burgeta, ya tafi da imaninta fiye da tunanin ta har mamaki abin yake bata. Har hango kanta take yi ta kwanta a ƙirjinsa tana hasahen wanne irin yanayi zata ji a wannan lokacin.

Da ta rufe ido murmushinsa take gani, sau biyu kenan taga yana murmushi, hakan ya shiga cikin tarihin ta dan tun daga murmushin farko da ta gani ya yi komai ya canja, faɗuwar gaban da take ji akansa ta canja salo zuwa harbawar zuciya a duk sanda tayi araba dashi. A haka ta shiga gidan zuciyarta na bugawa sossi.

Shi kuwa Omar yazo zai fita sai kiran Sen ya shigo wayarsa ya ɗauka yana shiga ɗakin sayana amsawa. Gaisawa suka yi Sen ya ce, "Tiger Narma ta faɗa min duk abinda ya faru jiya, gaskiya i'm so proud of you, naji daɗin taimakon da ka yiwa Narma sosai." Omar ya ce, "babu komai. Amma ka ja mata kunne Kano ba Abuja bane, akwai masu ƙwace sosai wanda za su yi mata illa ma kafin su ƙwace ɗin. Ta kula in zata fita ta daina kaiwa dare, in ta kai dare ma kar ta sake ta tsaya a ko ina. Allah ne ya taimaka da har motar zasu ƙwace musamman in suka lura da bata san gari ba."

Sen ya ce, "ai ganganci ne irin nata, na faɗa mata duk inda zata je ta kira ka amma bata ji." Omar ya ce, "tafiyar mu baza ta zama ɗaya ba, ni bana son ɓata lokaci ko kaɗan, kuma dai yanayinta bai yi daidai da nawa ba." Sen ya ce, "kar ka damu yanzu ta fahimci abinda nake nufi." Omar ya ce, "babu komai."
"Yau zata je biki zata kira ka."
"Allah ya kaimu."
"Amin. Akwai saƙonka na kyautatawar da ka yi mata jiya, naji daɗi sosai."
"Na gode" ya bashi amsa a taƙaice kafin Sen ya kashe wayar.


Ɓangaren Narma a daren sai da tayi mafarkin Omar, da ta farka sai kawai ta ɗauka taimakon ta da ya yi ne ya saka haka. A haka ta tashi ta shirya dan a ranar zasu fara bikin Samra. Ƙawayenta guda uku ne suka zo gidan, ganin hannunta a ɗaure suka dinga yi mata sannu kafin ta sake a fara hira.

Da wuri mai kwalliya tazo aka fara yi musu kwalliya, sai da aka yiwa duk ƙawayenta sannan aka yi mata a lokacin an idar da magriba. Narma tayi kyau cikin ankon kamu dukkan su dogayen riguma suka yi marasa kama jiki, amma Narma fitted gown tayi wacce ta kama ta matuƙa, sannan saman rigar gabaɗaya net ne a jiki ana ganin jikinta.

Ganin yadda tayi kyau duk suka ruɗe suna zugata ita kuma tana jin daɗi tana fari da idanu. A lokacin Ashraf ya zo gidan haɗa ido da ya yi da Narma ji ya yi kasala ta saukar masa lokaci ɗaya, ya haɗɗiye yawu ya bita da kallo ya ce, "Beb ke ce?." Gira ta ɗaga masa ya ce, "you look so magnificent." Mursmushi tayi ya matso aka fara yi musu hotuna masu kyau.

Ashraf ya ce, "Amma dai ni zan kai ki ko?." Narma ta ce, "Dad ya ce Tiger ne zai kai ni."
"Tiger again?."
"Yes, sai dai mu haɗu a can." Ya girgiza kai ya ce, "Okay normal, sai mun haɗi din." Daga nan suka yi sallama ya fita su kuma suka fara sallar i'sha. Narma dai sai da ta cire rigar gabaɗaya sannan ta iya sallah bayan ta idar ta mayar.

A cikin ƙawayen ta wacce suke kira da Safna itace babbar ƙawar Narma, ta kalle ta taɓe baki ta ce, "Narma ya kamata ki daina wannan ɗinkin fa, yanzu an daina wannan matsewar musamman ke da kike da halitta irin wannan."

Narma ta ce, "kina da matsala Safna, to in ban nuna halittar da Allah ya yi min ba meye amfanin ta?."
"Ki adana sai ki yi kwalliya a gidan mijinki."
"Ke baki ga yadda Ashraf ɗin ya ruɗe da ya ganni haka ba? Da iya surata nake sake kama zuciyarsa. Kuma in bai ga abinda nake dashi ba ta ya ya zai yi mararin aurena?."

Safna ta ce, "amma hakan ba daidai bane, wannan shigar zata iya jawo miki abinda ba kiyi tunani ba Narma. Ina yawan faɗa miki wannan maganar amma bakya ji, su Nasreen su daina zugaki, wallahi cutar ki suke yi. Da wannan shigarta ki babu lallai ki samu wanda zai aure ki saboda Allah."

Gabaɗaya suka yiwa Safna can akan abinda ce ita dai tayi musu banza suka ƙaraci surutun su. Ɗaya daga cikin su da ta fita ta shigo yana cewa, "Nass yanzu da bouncers ki ka dawo yawo?." Narma ta ce, "a ina?."
"Gashi nan" ta faɗa tana nuna musu Omar ta window wanda ya ke tsaye yana amsa waya.

Narma ta kalle su ta ce, "shine Tiger fa, na san kin san sunan na sa ko?."
"Ni kuwa na san sunan, ban dai san fuskarsa ba amma na san sunansa ko ɗazu media akan maganarsa ta yamutse."
"Yes shine. Ai na baku labarin abinda ya faru jiya, shiyasa Dad yake so ya dinga kai ni duk inda nake so."

Safna ta kalle shi ta ce, "amma kin cuce shi, a ina ya yi kama da bouncers don Allah? Ki ga mutum ɗan daidai dashi ki haɗa shi da waɗanan jibga-jibgan halittar?." Suka yi dariya gabaɗaya Nasreen ta ce, "Gaskiya dai ta cuce shi, wannan ai ko rabin bouncers bai kai ba, yanayin jikinsa ma sha Allah."

Safna ta ce, "kuma gashi bai yi kama da yadda ake faɗarsa ba. Kalle shi fa fari kyakykawa mai zubin buzaye." Nass ta ce, "ni kaina mamaki nake yi anya kuwa ɗan daba ne kamar yadda ake faɗa?. Amma jiya na gani da idona." Narma ta sake cewa, "mu je mu tafi, ɗan rainin hankali ne yanzu sai na neme shi na rasa." Ɗaya daga cikin su tace, "Dan ya raina miki hankali?." Nasreen ta ce, "baki yi maganinsa bane." A haka suka fito harabar gidan ko wacce ta sha makeup kuma duk sun yi kyau.

Dukkan su da mota suka zo, ko wacce ta shiga motarta suka fita ita kuma ta shiga bayan motar. Bai ce komai ba ya buɗe mazaunin gaba ya shiga ƙhamshin turarenta ya sake kai amsa ziyara a hancinsa. Kamar zatayi masa magana sai ta kasa shi kuma yana so yaji inda zasu je.

Narma da ta fahimta sai ta faɗi sunan event center ɗin da location ɗin, bai ce mata komai ba ya kunna motar suka fita. Kallon gefen fuskarsa ta samu kanta da yi yana kallon gabansa hankali kwance fuskar sa babu fara'a ko kaɗan.
"Na gode" taji bakinta ya furta ba tare data sani ba. Kamar bai ji ta ba haka ya yi, ya cigaba da tafiya har suka zo inda ta ce kafin a buɗa masa gate ya shiga ta fito daga motar.

Har zata wuce taji ya ce, "zaki gama yaushe?." Kallonsa tayi suka haɗa ido ta ga fuskarsa babu alamun wasa ta ce, "nan da two hours." Bai sake cewa komai ba ta tsaya tana kallonsa ganin hakan sai ya kalle ta sai ta wuce shi ta shiga ciki. Samun kansa ya yi da kallon ta tana tafiya, ya yi saurin janye idanunsa jin baƙon yanayi ya na kawo masa ziyara.

Bai zauna a wajan ba fita ya yi ya koma gida a yadda ya lissafa ƙarfe goma kenan zasu gama. Ƙarfe goma da wani abun kuwa ya dawo ya samu ƴan mata suna ta fitowa ƴaƴan manya kai da ka ga yaran ka san yaran masu kuɗi ne manya ba ƙananu ba. Hango ta ya yi tana tahowa tana dariya gefen ta Ashraf ne shima dariyar yake yi.

Dauke kai ya yi ya kawar da fuska daga kallon ta ya lumshe ido, ido ya sake buɗewa a lokacin ta zo wajan, kallon motar tayi ta gane ta sai ta ce,  "Ka je kawai zamu tafi da Beb." Kallon baki da hankali Omar ya yi mata ya kalli Ashraf da shima shi yake kallo yana mamakin daman wannan ne tiger ɗin.

Narma ta sake cewa, "ka je kawai." Wani irin kallo yake mata alamun bazai ma yi magana ba ganin hakan Ashraf ya ce, "kai ba Drivern ta bane? To ta ce kaje zan kaita ka tafi mana." Kallon Ashraf ya yi bai ce komai ba dan bashi da lokacin sa. Narma ta ce, "ƙyale shi Beb, mu je ka kai ni na gaji....." bata ƙarasa ba maganar ta maƙale jin ya ce, "Ko ki zo ki shiga ko na ɗauko ki."

Mamaki suka juya suma kallon sa ganin kamar ba shi ya yi maganar ba, ya ɗago ido yana kallonta ta ƙasan ido ya ce, "bana son ɓata lokaci, ki zo ki shiga ina da abinda zan yi. Ni ba ɗan aikin ki bane da zaki ajjiye ni ina yi miki magana kina yin banza ba!." Yadda ya yi maganar a kausashe ya saka Narma ta ɗan ji tsoro amma ganin Ashraf na wajan sai ta danne ta ce, "ba fa zan shiga ba, a motar mijin da zan aura zan tafi."

Ashraf ya ce, "malam ka tafi daman ai aikin ka kenan ko? To Narma tace bata so ba sai ka ƙyale ta ba?." Kallon Narma ya yi yana cize baki ya sake kallon Ashraf ya ce, "in na sake magana ka saka min baki sai kayi dana sani. Wallahi sai na saka ka haɗɗiye haƙorinka."
"Me zaka yi?." Omar bai bashi amsa ba dan yadda yake jin zuciyarsa zai iya karya shi wallahi.

Fitowa ya yi daga motar ya matso kusa dasu ya ce, "ka sake yin maganar zaka ga abinda zan yi. Ke kuma kafin na irga uku ki shiga mota in ba haka ba wallahi sai na mare ki!" ya faɗa yana nuna ta da yatsa idanunsa a waje. Tsoro ya bayyana a tare da ita bata san ta buɗe motar ta shiga ba ya bar Ashraf a wajan ya shiga motar suka fita.

"Wai kai meye haka ne? Ina ruwanka da ni, bani nace ka bari ya kai ni ba?. Biyan ka ake yi, ina da ikon da zan ce bana son abu kuma dole ka yi min. Haba duk kabi takura min, ni wallahi na gaji." Tsayawa ya yi ya jiyo yana kallon ta kafin ya duƙa ƙasa ya ɗauko wata wuƙa mai madaidaicin girma, ya buɗe motar ya fito ya buɗe bayan motar inda take ya saka mata wuƙar a wuya kamar yadda ya yiwa Nayla ya ce, "in kika sake yi min magana wallahi sai na yi miki illa. Ni zaki dinga yiwa ihu? Sa'an ki ne ni?."

Ɗiff Narma tayi tana tuna yankan jiya ma taji azaba balle ya yanke ta a wuya. Kallon idonsa take yi yana kallon nata ya sake cewa, "in kika sake magana wallahi da ƙafa zaki koma, In na yi rantsuwa bana karyawa, ki kiyaye ni duk lokacin da na ce wallahi!."

Shiru tayi bata ce komai ba yaja tsaki ya ce, "stupid girl" ya faɗa yana barin wajan ya sake komawa motar ya ja motar suka tafi. Har suka je gıda Narma bata ce komai ba a tsorace take dashi ko motsin kirki ta kasa, ya buɗe motar ya fita ya barta a cikin motar bai sake kallon inda take ba ya fita daga gidan.

Narma haka ta koma gidan jikinta duk a sanyaye a daren ta kira Dad ta faɗa masa abinda ya yiwa Ashraf sannan ta kwanta amma zuciyarta cike yake da tunaninsa, wai wanne irin ƙarfin guiwa yake da ita haka?. Da wannan tunanin bacci ya ɗauke ta.

Shi kuwa Omar yana komawa text ya rubutawa Sen dan wallahi ya cigaba da zama inda Narma take bai dan adadin abinda zai aikata mata ba, gwara kawai su nemi wani shi kam ya gaji.

Sen yana ganin text ɗin sa ya kira shi ya faɗa maaa abinda ya faru shi kuma ya nuna jin daɗin sa akan hakan, dama amfanin kula da ita ɗin kenan, kuma shi Omar bai san Ashraf ba dole a samu damuwa in ya gansu tare. Daga nan suka yi sallama ya kashe wayar ya kwanta yana tunani, fuskar Narman yake gani a idonsa ya ja tsaki mai tsaho ya kulle ido da ƙarfin gaske.

Kwana biyu bai je ba saboda Sen ya ce ya bari Ashraf ɗin ya dinga kai ta dan haka kwana biyu babu inda yake sai dai ya fita ya dawo kawai. Ita kuwa Narma biki suke sha Ashraf yana kai ta duk inda take so amma ta kasa daina tunanin Omar ko kaɗam, da ta rufe ido shi take gani musamman lokacin da yake kallon idanunta.

Ranar asabar Ashraf ya koma Omar bai sani ba yana zaune a ɗaki ya ga baƙuwar number tana kiran sa, ɗauka ya yi ya saka a kunne bai yi magana ba Narma ta ce, "Hello Tiger, Narma ce." Jin hakan sai ya gane ta ya ce, "ina ji."
"Ashraf baya anjima zan je biki."
"Okay" ya furta mata kafin ta sake magana ya yanke wayar.

Saurin katse da wayar ya yi jin zuciyarsa na wani irin harbawa lokacin da Narma ta fara yi masa magana, magana take cikin yanga da iyayi hakan ya saka yaji wani iri har bai san ya yi hanzarin kashewa ba. Shin wai me yake Shirin faruwa dashi ne?. Meyasa ya kasa daina tunanin ta? Meyasa yake jin wani iri da ta kira shi yanzu? Lallai dole ya san dalilin hakan kafin abun ya yi nisa.

Ɓangaren Narma murmushi ta samu kanta da yi bayan ya kashe wayar a bayyane ta ce, "muryarsa mai daɗi, zan so naga yana murmushi." Sai kuma tayi tsaki ta ce, "Ko Ina ruwana ma oho, da ya yi murmushi da kar ya yi shi ya sani. Ni so nake na manta dashi amma na kasa, ko meyasa na kasa mantawa dashi oho min" ta faɗa a bayyane tana tashi ta shiga ɗaki har lokacin muryarsa take ji a kunnen ta.


Tofa, Omar da Narma, ga kuma Nayla a gefe.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️


*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

https://www.tiktok.com/@nanahaleemawriter?_t=ZS-8zaZqblsrGp&_r=1

*Book 1*
*P 15.*       


Nayla kuwa yanayin da take ji akan Omar ya fara damunta domin ko yaushe a cikin tunaninsa take, ko yaushe a cikin ganin murmushinsa take da zarar ta kulle. Ga faɗuwar gaba da take addaba mata, ko ya taji an kira wani mai irin sunansa sai ƙirjinta ya buga. Ɗakyar ta jure kwanaki uku bata ganshi ba, a safiyar ranar bayan tayi wanka ta shirya cikin riga da siket, rigar har guiwa ta saka mayafi ƙarami a kanta ta fito falon.

Salma ta kalle ta tace, "Sai ina?." Ta kalli Salma ta ce, "Zan je gidan Mama Zaliha." Hajja ta kalle ta ce, "Sai kin dawo, amma dai kar ki yi dare." Nayla ta ɗaga kai alamun to, Salma ta ce, "Amma da kin faɗa min da na raka ki."
"Na ji jiya kina cewa bakya jin daɗi shiyasa, ni kuma tun jiya ta kira ni ta ce nazo." Salma ta ce, "Da motar Hajja zaki je?."

Nayla ta ce, "A'a, napep zan hau." Hajja ta ce, "ke bana son shirme, kin san babanki baya son kina hawa abin hawa na haya ko? Meyasa baza ki bari a kira Sayyadi ya kai ki ba?." Nayla ta ce, "Hajja ai ba jima zan yi ba, yanzu zan dawo" ta faɗa tana fita da sauri dan kar Hajja ta hanata.

Nayla tana fita daga gidan kallon ƙofar gidan Didi ta ta yi gabanta ya faɗi sosai, a hankali ta fara takawa zuwa ƙofar gidan faɗuwar gabanta na tsannanta, wani irin yanayi baƙo a gare ta yana ratsa ilahirin jikinta. Ƙofar ɗakinsa a buɗe take tayi sallama ta shiga gidan amma shiru babu alamun motsi.

Tana gab da shiga falon ta ji an ce, "wace a nan!?." Da sauri ta jiyo suka haɗa ido, Sarai ya gane itace tun wucewarta ya ganta, yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login