Showing 63001 words to 66000 words out of 87436 words
Chapter 22 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt
Jalil autan, Yaya Jawad wanda Nayla ke kira da Ya J. Hirar Kano kawai ake yi suna dariya kafin Abiy ya kalle ta ya ce, "Kin dai je Kano hankali ya kwanta." Nayla tayi murmushi ta ce, "Gidan Hajja akwai daɗi Abiy."
"Ai dole ya yi miki daɗi Nayla. Yaushe zaki fara aiki ne? Ko school ki ke so ki koma?" Sai ya kalle ta sosai ya ce, "Ko kuma aure?."
Gabanta ya faɗi, a da in an yi zancen aure bata jin faɗuwar gaba, amma yanzu ta rasa dalilin faɗuwar gaban da take ji ko yaushe. Nayla ta kalli Abiy ta ce, "duk wanda Allah ya zaɓar min Abiy? Amma nafi so na fara aiki tukunna."
Abiy ya ce, "Alright, zaki fara a cikin kwanakin nan in sha Allah." Nayla ta yi murmushi sannan ta kalli Yaya Jawad ta ce, "Yaya J aiki da wahala ko?." Dariya ya yi ya ce, "ɗauka ki ke sauƙi ne dashi? Hmm zaki gani yarinya." Abiy ya ce, "ƙyale shi tsorata ki yake yi." Tayi dariya tana cin abinci amma zuciyarta tana Kano musamman gidan Didi, a gidan Didin ma Omar take tunani.
Abiy ya ce, "Amma maganar aure ma ya kamata ayi ta Mamana, bayan tafiyar ki ina ta samun masu neman aurenki, harda Abbas cousin ɗinki." Gabanta ya faɗi sosai ta wara ido ta ce, "Abiy Ya Abbas yazo nan?."
"Yazo. Ya tabbatar min da yana neman auren ki ko ke bai sanarwar da yana sonki ba. Hakan da ya yi ya min daɗi sosai, duk da ɗan uwanki ne amma bai nemi soyayyar ki kai tsaye ba ya biyo ta wajena."
Nayla tayi shiru gabanta yana faɗuwa sosai ta ji Abiy ya ce, "yana da kyau ki yi tunani, zan basu damar magana dake dan mutane uku kenan har Abbas. Kin ce a ajjiye batun Sadiq ko? To an ajjiye, bayan shi akwai uku har Abbas yayan ki. Bana son yawan tara samari kema kin sani, ya kamata ki san abinda zaki yi. Abinda ya jawo rabuwarki da Jidda kenan, dan haka kema yazo kan ki, ki nutsu ki yi addu'a."
Nayla jikita yayi sanyi ta kalli Abiy ta ce, "to Abiy, ka taya ni addu'a."
"Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi Mamana." Suka amsa da amin kafin ya ce, "ina jin next week sai muje umra ko kwana goma mu yi sai mu dawo." Ihu suka yi cikin murna, Abiy ya yi murmushi ya tashi ya hau sama. Yana jin daɗi in yaga iyalansa suna farin ciki, hakan yana ƙara masa jin daɗi a zuciyarsa.
*Bayan Kwana biyu.*
Omar ya yi ƙoƙari ya yakice tunanin Narma ya koma sabgoginsa, baya bari tunaninta ya hana shi wani abun dan tun bayan tafiyarta basu sake koda waya ba, hakan kuma ya yi masa daɗi dan baya son abinda zai hana zuciyarsa sukuni.
Ɓangaren Narma duk yadda tayi ta jure share Omar ta kasa, tayi-tayi amma abin ya girmi tunaninta. Har ta kai ta kawo ta fara ware kanta a gida da wajan aiki, saboda gabaɗaya bata son magana sai aikin tunaninsa da ganin fuskar Omar a idonta. Ta rasa meyasa take jin abinda take ji a kansa, gabaɗaya ta kasa sarrafa kanta akan tunanin Omar.
Yau ta kama Sunday bata je aiki ba tana kwance a ɗaki sai ga Mum ta shigo, ta kalle ta cikin nutsuwa ta ce, "Narma tashi zaune." Ba musu ta tashi ta kalle ta ta ce, "me yake damunki? Tunda kika dawo daga Kano baki da walwala, me ya faru?." Narma ta ce, "babu komai Mum, kawai bana jin daɗi ne."
"Kin je asibiti ne?." Ta girgiza kai alamun a'a, Mum ta ce, "meyasa baki je ba?."
"Zan je Mum." Mum ta ce, "good. Yanzu ki zo ga Ashraf nan a falo yana jiranki" Mum tana faɗa mata haka ta fita. Haushi taji ya tokare mata zuciya jin wai Ashraf ne yazo. Yanzu ta rasa meyasa yake ɓata mata rai, haushi yake bata yanzu, kwata-kwata bata son magana dashi. Ɗankwali kawai ta ɗaura ta fito falon cikin shigar ta kullum ta same shi a zaune, yana ganin fitowar ta ya miƙe tsaye har ta ƙaraso ya ce, "Why Narma? Bakya picking calls ɗina, bakya responding messages ɗina. Me yake faruwa?."
Narma ta ɗan yi ajiyar zuciya ta ce, "babu komai."
"akwai komai, ki faɗa min abinda yake faruwa. Gabaɗaya kin canja, ko a Kano ba haka ki ke ba."
"Na faɗa maka babu komai, kawai bana jin daɗi ne, yanzu Mum tace naje naga Dr." Ashraf ya bita da kallo ganin yadda take yi masa in yazo gidan yanzu ta canja, yadda take welcoming ɗinsa gabaɗaya ta canja.
Ya ce, "Amma kin canja Narma, da ba haka ki ke ba yi min gabaɗaya. Yadda ki ke welcoming ɗina in na zo gidan nan yanzu kin daina. Nayi miki laifi ne?." Narma ta ce, "baka yi mun laifin komai ba, kawai bana son yawan magana ne." Ashraf ya nuna kansa ya ce, "Har ni bakya son magana dani?."
"Ba haka nake nufi ba."
Ya ce, "Okay, zan barki ki huta zuwa kwana biyu zan dawo mu yi magana." Narma ta ce, "thank you" ta faɗa tana komawa ɗaki ya bita da kallon mamaki.
Tana shiga ta cire ɗankwalin kanta cillar ta ce, "Aikin banza kawai, Bana son magana dashi gabaɗaya." Ajiyar zuciya take yi kafin ta ɗauki wayar ta tana kallon number Omar. Kira tayi ba tare da tunanin komai ba tana jira a amsa.
A lokacin Omar yana zaune a ɗakinsa ya ga waya na shigowa, bai manta number ba yana gani ya gane ta kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka ya saka a kunne. Narma ta yi ajiyar zuciya jin ya ɗauka sannan ta ce, "Hello Faruk."
Omar ya yi ɗiff jin muryarta har cikin jininsa, wani irin yanayi yake ji yana ratsa gangar jikinsa. Kafin ya yi magana ta sake cewa, "Ka manta dani ko? Tunda na tafi ko waya baka yi min ba."
Nan ma Omar ya yi shiru bai amsa ba, ta kwantar da murya ta ce, "Faruk na san kana ji na, kawai baka son magana da ni ne." Omar ya rasa abinda zai ce mata, bai saba waya da mace ba balle ya san abinda zai ce mata sai kawai ya ce, "kin je lafiya?." Da shagwaɓe ta ce, "yau kwana na nawa da dawowa sai yanzu zaka tambaya?."
"Uhum!" Shine abinda ya ce kawai bai yi magana ba. Narma ta ce, "ina nan na kasa mantawa da tunaninka, bana iya komai a ko yaushe sai tunaninka, na kasa gane me yake damuna."
Omar ya yi shiru yana jinta yana mamakin kenan itama tana tunaninsa, to akan me?. Narma ta yi ajiyar zuciya ta ce, "ka manta dani ko? Ni ban manta da kai ba." Nan ma bai yi magana ba kuma bai bata wata alama da zata fahimci ya ji ba. Narma ta ce, "baza ka yi min magana ba?."
"Ina jinki" ya faɗa dan shi bai san me zai ce mata ba wallahi. Narma ta ce, "zan zo Kano ina so na haɗu da kai."
"To" shine abinda ya furta kawai sai yaji ta yanke wayar, ya bi wayar da kallo yana mamakin son ganin sa da take yi da kuma dalilin kiransa.
Narma kuwa ta kashe wayar ne saboda jin an buɗe ƙofa an shigo Mum ta bita da kallo ta ce, "wai me yake damunki? Me Ashraf ya yi miki ne?." Narma zata yi magana Mum ta ce, "ki zo." Ko ɗankwalin bata ɗaura ba ta biyo Mum ta samu Dad falon sama yana kallo tahowar su. Zama tayi Dad ya kalle ta ya ce, "me yake damunki Narma me Ashraf ya yi miki?." Narma ta ce, "ni bai yi min komai ba."
"Amma meyasa ki ke treating reletionship ɗinku like that? Kin san yana sonki ai kema kina sonsa. Shine future husband ɗinki, meyasa ki ke masa haka ne?." Narma ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Dad!." Dad ya kalle ta ya ce, "ina jinki." Narma ta ce, "Ni yanzu gabaɗaya bana son Ashraf, bana tunanin zan iya aurensa! In fact akwai wanda nake so zan aura ba shi ba" ta faɗa kai tsaye tana kallon Dad da yake kallon ta.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 19.*
Dad ya bita da kallon mamaki ya kalli Mum da take kallon sa itama kafin ta sake kallon Narma ya ce, "Bakya sonsa yanzu?." Ta ɗaga kai alamun eh kamar zata yi kuka. Dad ya ce, "meyasa? Ya yi miki laifi ne?." Narma ta ce, "bai yi min komai ba Dad, kawai zuciyata bata sonsa yanzu."
Mum ta ce, "to wa ki ke so?." Narma ta kalle ta ta ce, "Wani ne Mum, zan faɗa miki in muka gama daidaita kan mu." Dad ya ce, "Waye shi?."
"Dad zan faɗa maka, but not now" she said it from the bottom of her heart, and her voice trembled with emotion.
Dad ya ce, "to shi Ashraf ya zaki yi dashi? Kin san yana sonki ko?." Narma ta ce, "to Dad saboda yana sona sai na cutar da kaina?."
"Amma bazai ji daɗi ba dai ko?."
"Amma Dad rayuwata ce."
"Is okay. Shi wanda ki ke so ɗin a Kano ku ka haɗu?" Dad ya tambaya da kulawa yana kallon ta.
Narma tayi murmushi ta ce, "Yes Dad." Ya kalli Mum yana murmushi kafin ya sake kallon ta ya ce, "Alright, ki je ki huta in ya so daga zamu sake yin magana." Narma in a trembling voice ta ce, "Dad zaka amince min na aure shi?." Dad ya yi murmushi ba tare da damuwa ba ya ce, "why not my baby? Tunda kina sonsa ai shikenan. Ki je ki huta."
Da sauri Narma ta miƙe ta shiga ciki cikin farin ciki. Dad yana dariya ya kalli Mum ya ce, "ashe wannan ne dalilin da ya saka Narma bata son dawowa daga Kano, she's in love." Mum ta yi dariya ta ce, "nayi mamaki fa, ka duba yadda take da Ashraf amma tunda ta ce bata so bata son ɗin ne. Ka san ita free and open ce, bata ɓoye abinda yake damunta ko kaɗan. Gaskiya zan so naga waye wannan da ya kama zuciyar Narma very cheap haka."
Dad ya ce, "Oh love! Kin manta a ranar da na fara ganinki na fara sonki? Uhum kin manta?" Ya faɗa yana kallon Mum da murmushi. Mum tayi dariya ta ce, "I will never forget that time, shi ake kira da love at first sight." Dad ya yi murmushi ya ce, "indai Narma zata yi farin ciki hakan ya yi min dadi." Hira suka cigaba da yi cikin farin ciki da son samawar da ƴarsu abinda take so.
••••••••
Omar bayan ta kashe wayar gabaɗaya kashe masa jiki tayi, ya rasa abinda abinda yake yi masa daɗi. Tana faɗa masa tayi kewarsa, to wai me hakan yake nufi ne? Sannan bata manta dashi ba? Shi ya ɗauka a kwanakin da ya wuce ta manta da shi kamar yadda yake ƙoƙarin mantawa da ita. Ajiyar zuciya ya yi a bayyane ya ce, "ko meyasa ta ce tayi kewa ta oho."
Wajan Didi ya shiga ya samu tana amsa waya, daga yadda take mayar da amsa ya tabbatar da Yayan mahaifiyar su ne. Kamar bazai zauna ba sai kuma ya zauna, ta gama wayar ta kalle shi ta ce, "Baba Adamu ne, yana magana ne akan kayan ɗakin bikina." Ya kalle ta a kaikaice ya ce, "Haka aka ce masa bani da kuɗin da zan miki kayan ɗaki?. Didi ya kamata ki ja musu kunne fa su daina shiga lamarina da naki, Ina ruwan su ne wai?." Didi ta ce, "da ruwan su mana Omar, iyayen mu ne."
"Iyayen ki dai, ni kam babu ni. Kuma babu abinda za a karɓa daga wajan su komai ni zan yi in sha Allah. In kuma ki ka ce sai kin karɓa wallahi na bar garin nan baza ki sake ganina ba, sai ki zauna dasu ki cigaba da rayuwa tunda su ki ka zaɓa.
Tayi murmushi tana kallon sa a ranta tana ayyana bai san hidimar aure bane, in ba dan haka ba bazai furta komai shi siya yi ba, shida ba sana'a yake yi ba an ina zai samu kuɗi?. Ita har mamaki take yi da bata ji yana zancen bashi da kuɗi dan ta san dai ba abinda yake yi balle tace kuɗi na shigo masa. Sannan tana mamaki in ya siyo mata kaya ya kawo mata, kayan sakawa ko na abinci haka yake siyowa ya kawo mata. In ta tambaya ya ce ta san ba satar mutane yake yi ba.
Tana ji yana ta yi mata mita tayi masa shiru bata ce komai ba dan bazata tanka masa ba indai akan dangin su ne baya gane gaskiya, ko me zata ce bazai amince ba gwara ma tayi shiru. Haka ya dinga faɗa lokacin da aka kai kuɗin aurenta gidan Kawu kamar shine babba itace ƙarama, wai meyasa ba a kawo masa ba ai ya isa ya aurar da ita. Ita dai bata tanka ba tayi masa banza dan tana tankawa zai hargitse ya tashi garin Kano. Ajiyar zuciya tayi tana ayyana rigimar Omar yawa ce da ita.
"Kai ma sha Allah, Allah ya kaimu garin madina. Allah ka sa ina da rabon zuwa wannan gari, Allah ya sa ko a radio na ci wata gasar da za a kaini Madina. Omar kalli yarinyar nan ka gane ta?" Ta faɗa tana nuna amsa wayarta. Bai yi musu ba ya kalla ya ga yarinyar sanye da baƙar abaya tayi rolling kanta fuskarta ɗauke da murmushi. Ɗauke kai ya yi ya ce, "a'a." Ta harare shi ta ce, "Nayla ce fa, jikar Hajja." Tsaki ya yi ya ce, "itama dai ban san ta ba."
"Yarinyar da ka dinga bawa tsoro a gidan nan? Kai Omar har yaushe ta bar Kano da zaka ce ka manta ta?. Yarinyar da ka ceta lokaci......" katse ta ya yi ta hanyar faɗin, "to wacece ɗina da zan kasa mantawa da ita? Mun haɗa dangi ko kuma akwai wani abu tsakanina da ita?."
Didi ta yi dariya ta ce, "babu komai. Amma na san baka manta ta ba, kawai halin wulaƙancin naka ne ya motsa." Ɗauke kai ya yi yana mai jin haushin Nayla a ransa, ita kanta Didi haushinta yake ji, haka kawai ta dinga nuna masa yarinyar kuma ta ce lallai sai ya game ta kamar wata ƙanwarsa. Fushi ya yi ya tashi ya bar mata falon bata ma wawaye shi ba ta cigaba da harkokinta dan in ta saka lamarin sa a zuciyarta ciwo zata yi.
•••••••
Nayla kuwa kamar yadda Abiy ya faɗa kaf ɗinsu suka tafi Umra, suna garin Madina suna ibada kafin su tafi makka. Nayla gabaɗaya bata da karsashi zaman, saboda zuwa lokacin ta tabbatar da son Omar take yi, so ba wai na wasa ba na gaske wanda ake kira so. In ta tuna waye Omar da halayensa, ta tuna waye Abiy sai gabanta ya faɗi tsoro ya mamaye mata zuciya ta kasa sukuni gabaɗaya.
Ta saka tunanin Omar a ranta ta hakan ya saka ta rame, bata ma zaman hotel ko yaushe tana masallaci tana kaiwa Allah kukan ta amma abin babu sauƙi sai sake gaba da yake yi. Duk ƴan uwanta sun fuskanci canji a lamarinta, in suka tambaya sai ta ce babu komai. A wannan yanayin suka shiga makka suka yi umra Abiy bai ji Nayla tana zancen zata je Makka mall ba, dan ya san indai suka zo sai Nayla taje Makka mall ta yi siyayya ta dawo.
Suna zaune a falon hotel ɗin su gabaɗayan su Abiy ya kalle ta ya ce, "Mamana zo nan." Ba musu ta ƙarasa inda yake ta zauna, ya kalle ta ya ce, "ban ji kina zancen zaki je Makka mall ba, lafiya ki ke?."
Nayla ta ce, "bana son zuwa ne, duk abinda zan siya zan siya a nan ba sai naje can ba." Yadda take magana a sanyaye ya saka ya kalle ta da kulawa ya ce, "Mamana me yake damunki? Na lura da rashin walwalarki, kina ware kanki ke kaɗai bakya son zama cikin mu, sannan baki da ƙwarin jiki, sannan kuma kin rame. Me yake damunki?. Duk lokacin da muka zo ƙasar nan har neman ki mu ke yi muna rasawa saboda yawo, amma gabaɗaya yanzu ki canja. Me ya faru?."
Zuciyar Nayla harbawa take yi sosai, idonta ya kawo ruwa kafin ta farga har hawayen ya sakko. Abiy ya damu ganin tana kuka ya ce, "Sanar dani damuwarki Mamana." Nayla ta goge ido ta ce, "Babu abinda yake damuna Abiy."
"Yaushe ki ka fara yi min ƙarya Mamana?." Ta sunkuyar da kai ya kalli ƴan uwanta ya ce, "in kuma kina so su bamu waje sannan ki faɗa min sai su bamu waje."
Nayla ta kalli Abiy ta ce, "A'a Abiy, babu abinda yake damuna." Abiy ya murmusa ya ce, "Mamana kina da damuwa, damuwar ma ba ƴar kaɗan ba. Ki faɗa min abinda yake ranki."
Nayla ta sunkuyar da kai ta rasa abinda zata ce, saboda ko giyar wake ta sha bazata faɗawa Abiy abinda yake damunta ba, da ta faɗa masa gwara abinda take ji ya kashe ta. Dabara ce tazo mata sai ta ce, "Ummana, mafarkinta nake yi a kwanakin nan Abiy" ta faɗa tana fashewa da kuka.
Duk sai kowa jikinsa ya yi sanyi ba kamar Abiy da take kusa dashi, fuskarta ya riƙe ganin yadda take kuka sai baice komai ba ya kwantar da kanta a kafaɗarsa ya bata dama tayi kukan. Ita kuwa Nayla kukan rashin mafita da tausayin kanta kawai take yi, sai da tayi mai isar ya sannan ta tsagaita kukan ya ɗago ta daga jikinsa ya ce, "Kina yi mata addu'a?." Nayla ta ɗaga kai alamun eh ya ce, "To ki yi haƙuri, addu'a itace kawai soyayyar da zaki nuna mata kin ji?." Ta ɗaga kai alamun to ya share mata hawaye