Showing 81001 words to 84000 words out of 87436 words

Chapter 28 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

tana tashi ta shiga ciki a guje. Dad yayi dariya suna tattauna yadda za'a tarbi siriki in yazo.

Narma na shiga ɗaki Omar ta kira bai ɗauka ba, ta sake kira bai ɗauka ba sai ta ƙyale shi dan baya son tana tara masa kira. Wajan mintina kaɗan da kiran ya kira ta ta ɗauka da sauri ta saka a kunne sai ta ce, "kashe na kira ka."

Daga can ɓangaren Omar ya ji abinda ta ce ya maimaita a zuciyarsa, me take nufi kenan? bashi da kuɗin da zai iya kiran ta kenan sai dai ita ta kira shi?. Kafin tayi magana ya yanke wayar, Narma ta kira sau adadi yaƙi ɗauka.

Narma ta tayar da hankalinta ganin yaƙi ɗauka, ta je WhatsApp ta tara masa message tayi masa text message shima ba reply. Tun tana kiran sa har ta gaji ta kuma kasa gane laifin da tayi wanda ya saka ya yanke mata waya ya kuma ƙi ɗauka.

Shi kuwa Omar yayi haka ne dan ya koya mata hankali nan gaba bazata sake cewa ya kashe ta kira shi ba. Yana ganin message ɗinta da kiran yayi banza ko kallo bai yi ba dan ya yi alqawari bazai ɗauka ba, kuma bazai kira ta ba, zata san waye Tiger.

Sunday ta wuce, Monday ta wuce Omar baya ɗaukar wayarta kuma baya kiranta. Narma hankalinta ya tashi sosai sai ƙarya ta yiwa Dad ta ce ya ce ranar Monday baya nan. Sai ranar talata da yamma ya ga kiran na zuwa bai ɗauka ba sai da ta katse sai ya kira ta da hanzari ta ɗauka, tana sakawa a kunne ta ce, "laifin me nayi maka haka? Me nayi ka ke hukunta ni da wannan hukuncin Faruk?."

"Gobe in na kira ki sai ki sake cewa na kashe ki kira ni. Banda kin raina ni saboda kinga ina surarenki har ke zaki ce min wai na kashe ki kira ni? Nuna min ki ke yi bani da kuɗin da zan kira ki?." Jin yadda yake maganar da tsawa sai Narma ta ce, "I'm sorry...." Cikin tsawa ya katse ta ya ce, "kin manta gargaɗin da nayi miki ko?." Narma ta ce, "yi haƙuri, na saba da yin English ne ko yaushe shiyasa, Amma zan dinga kiyayewa. Kayi haƙuri don Allah."

"Mtsw! Faɗi matsalarki" ya faɗa kai tsaye yana sauraren ta.
"Ka yi haƙuri, nayi kewarka, kuma Ina sonka, Ina ƙaunarka." Sai ya ɗan sassauta murya bayan ya ja tsaki ya ce, "Ina jin ki."

"Daman tun ranar asabar na faɗawa Dad maganar zuwan ka ya ce in kana dama kazo Monday...au litinin, shine na kira na sanar dakai a lokacin."
"Yanzu sai me?."
"In zaka iya zuwa gobe yana jiran zuwan ka."
Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "bazan zo gobe ba, amma zan zo ranar alhamis hakan ya yi?." Narma tayi murmushi ta ce, "Ya yi Faruk ɗina, na gode Allah ya barmu tare na haifa maka yara masu kama da kai." Samun kansa ya yi da murmushi mai sauti har taji murmushin nasa. Omar ya ce, "na faɗa miki ban shirya aure ba ko? Ban ma san yaushe zan yi ba."

Narma ta ce, "ai fata nayi mana ko?" Ta faɗa cikin shagwaɓa tana narkar da murya. Shagwaɓar da take yi yana ƙara masa karkasashi da yanayin da ya saba ji in suna waya. Jin ya yi shiru sai Narma ta ce, "baka ce amin ba, baka so na haifa maka yaran ne?." Murmushi ya sake yi har Narma tayi mamakinsa, dan ta san sai a gama waya dashi bai yi maganar kirki ba balle murmushi. Ya ce, "Ki jira lokaci."

"Alhamdu lillah! Faruk yana son ya auri Narma har ya haɗa jini da ita. Wannan abin farin ciki ne." Nan ma murmushi ya sake yi amma bai ce mata komai ba, tana ta yi masa zance shi kam baya tanka mata sai ya ga dama, sai da ya gaji ya ce, "Zamu yi magana anjima" daga haka ya yanke wayar yana shafa gajin fuskarsa yana murmushi. Ajiyar zuciya ya yi ya miƙe ya shiga wajan Didi da niyar faɗa mata zai je gidan sirikai.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️


*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 24.*


A zaune ya samu Didi tana waya ya zauna a kujerar da ya saba zama ya harɗe ƙafa yana kallon ta tana cewa, "Ya jikin na ki?." Shiru tayi ana bata amsa sannan ta ce, "Allah ya ƙara lafiya Nayla, a gaishe da su Mama." Ta Amsa daga nan ta yanke wayar. Ambatar Nayla da tayi ya saka shi ya tuna fuskar ta a lokacin da take hawaye, sai ya samu kansa da jin wani iri a zuciyarsa ba tare da ya san dalilin haka. "Omar ya aka yi?." Maganarta ta katse shi ya kalle ta ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ranar alhamis zan je Abuja wajan mahaifin Narma."

Didi ta kalle shi ta kasa cewa komai sai kallo, ta zuba masa ido bayan ta tallafi haɓarta da hannayenta. Ta ce, "Omar!." Jin yadda ta kira shi ya saka ya kalle ta sai ta ce, "Ka shirya aure ne? Yanzu in aka ce an baka aurenta kana da abinda zaka aure ta?."

Ajiyar zuciya ya yi ya sauke ƙafasa daga kan ɗaya, ya sarƙe hannayensa waje guda ya kalle ta ya ce, "ni ai na faɗa mata ban shirya aure ba, tana so iyayenta su san da ni ne kawai." Zuba masa ido tayi tana kallonsa, a tausashe ta ce, "Omar anya baka yi ganganci da rayuwarka ba? Anya baka saka zuciyarka a tsaka mai wuya ba?. Sai nake ji kamar akwai wani shiri da yarinyar ta shirya maka Omar."

"Didi babu wani shiri sannan babu abinda zai faru, Ina sonta kuma zan je wajan iyayenta matsayin mai sonta."
"Omar kenan, ta ya iyayenta zasu karɓe ka a matsayin mai son ƴar su?. Tausayi ka ke bani wallahi, domin wanna hasashe naka ba mai yuwa bane Omar." Kallon ta ya yi ya ce, "Didi bana so kina ce min haka, wai ita wacece da zaki dinga cewa tausayi nake baki a kanta?."

"Ita ba tsarar ka bace ba Omar, ita ba daidai da kai ba ce ba Omar." Kallon Didin ya ke yi na wani lokacin kafin ya ce, "Didi!."
"Omar."
"Bakya son abinda nake so ne?."
"Omar Ina so mana."
"Meyasa ki ke faɗar abinda ki ke faɗa indai haka ne."
"Hmmm!" Didi ta faɗa a taƙaice bata ce komai ba. Omar ya ce, "kawai ki ta ya ni da addu'a." Didi ta ce, "Omar addu'a ko yaushe Ina yi maka ita ai, Allah ya baka abinda ka ke so in alkhairi ce."

Shiru ya yi Disi ta ce, "kuma kaima ka dinga addu'a, kana da ƙoƙarin ibada na sani, amma ka ƙara daga yadda ka ke Omar. Ka cigaba da yaƙi da shaiɗan kana tashi cikin dare, wani lokacin shaiɗan yana galaba a kanka. Ni shiyasa nake son ka samu mace nutsatstsiya mai ilimi wacce zata cigaba da taimaka maka wajan bunƙasa ibadar ka."

Kallon Didi ya ke yi har ta gama magana kafin ya ce, "oh kina nufin dai ban cikin masu ibada? Kina so ki ce mace ce zata saka na yi ko ta hana?."
"Ni ban ce baka yi, in na ce baka ibada ai ƙarya nake yi. Ko a unguwar nan an shaida sallah bata wuce ka a masallaci, sannan ni shaida ce, tunda ni nake rayuwa da kai. Ko a gaban Allah zanyi shaidar kana da ibada daidai gwargwado. Ina so ka ƙara ne kawai Omar, amma batun mace zata saka ka yi ko ka bari wannan zai faru." Taɓe baki ya yi bai ce komai ba ya yi shiru, ya lura adawa take yi da Narma shiyasa bai tanka ba.

Didi ta ce, "To a yadda ka ke ɗin nan Omar in ba dan kana ibadar ba ai da ban san ya zaka zama, Allah sai ya dubi maraicina ya taimake ni ya saka maka son ibadar a zuciyar. Malam Salahudden kuma shine sila, shi ya ɗora ka a kan hanya gashi yanzu baya duniya ka ɗore akan abinda ya ɗora ka a kai. Inda ace ibadar ma bata dame ka ba ai da yanzu ka kashe ni da raina." Ƙala bai ce ba, ya share ta yana kallon wani waje daban kamar ba da shi take maganar ba.

•••••••

Nayla lokacin da Didi ta yanke wayar taji sallamar Omar hakan ya saka ta yin shiru tana sauke numfashi a hankali. Dawowar ta daga office kenan ta samu kiran wayar Didi. Tashi ta yi ta shiga banɗaki tayi wanka lokacin har anyi magrib, ta fito ta yi sallah sannan ta fito falo. Tana fitowa Auta ya tare ta ya ce, "Anty Nayla ki zo in ji Mama."

Da to ta amsa tabi bayan sa zuwa ɗakin Mama ta shiga da sallama. Amsawa tayi tana kallon ta har ta shiga kafin ta ce, "Abiy ya ce a sanar dake kina da baƙo in anyi sallar i'sha." Nayla ta ce, "To" ta faɗa a sanyaye tana juyawa zata fita, Mama ta ce, "Nayla bakya son faɗa min damuwarki ko?." Nayla ta kulle ido ta buɗe ta juyo a hankali ta ce, "Mama ki yi haƙuri, ba na ƙi faɗa miki bane, kawai babu damuwar ne shiyasa."  Mama ta ce, "Shikenan jeki."

Nayla ta fito zuwa falo ta zuba abinci tana ta jagalgala shi amma ta kasa ci. Daƙyar ta iya cin kaɗan kafin ta tashi ta shiga ɗaki ta zauna kawai babu abinda take yi. Cikin wannan tunani har aka yi sallar i'sha ta tashi tayi sallah bayan ta idar hijjabi ta saka kawai akan kayan jikin ta dan na shan iska ne ba canja kaya zata yi ba.

Sallama akayi a ɗakin nata ta juyo taga Yaya da kansa ya kalle ta ya ce, "Nayla ga baƙon ki can a babban falo, ki yi sauri yana jiran ki."

Kai ta ɗaga kawai bata ce komai ba. Ya kalle ta sosai ya ce, "Nayla wai me yake damunki ne?." Murmushin ta ƙaƙalo ta ce, "Yaya na gaji ne kawai, zaman office ko wahala." Dariya ya yi ya ce, "Yanzu kika fara aiki ai Nayla, maza ki zo yana jiran ki." A hankali take takowa zuwa babban falon gaban ta yana faɗuwa sosai.

Da sallama ta shiga kanta ta na ƙasa ya amsa har ta ƙaraso ciki ta zauna. Kanta yana ƙasa ƙafarsa kawai ta iya gani ta haka ta fahimci a inda yake zaune. Nayla ta ce, "ina yini." Murmushi ya yi ya ce, "kin yini lafiya Nayla?."
"Lafiya lau" ta amsa a taƙaice.
"Ya aiki?."
"Alhamdu lillah" ta sake bashi amsa tana wasa da hannun ta. "Ma sha Allah. Sunana Omar ...." Bata bari ya ƙarasa ba ta ɗago da sauri suka haɗa ido dashi. Saurin ɗagowar da tayi ne ya saka shi ya dakata daga maganar da yake yi yana kallon ta. Ajiyar zuciya tayi ta sauke ido ƙasa ganin ba wancan Omar ɗin bane suna ne yazo ɗaya.

Murmushi ya yi ya ce, "me ya baki mamaki?." Kai ya girgiza alamun babu komai ya ce, "Sunana Omar Mansur Garkuwa, ni ɗan garin Kaduna ne iyaye da kowa nawa yana cikin garin nan. Amma Ina aiki da NCC a Abuja a can make da zama." Nayla jin sa take ba fahimta take yi ba, shi kam yana ta magana yana gabatar mata da kansa amma ba ji take yi ba saboda hankalin ta baya tare da ita.

"Nayla!." Jin ya kira sunanta ta ɗago suka haɗa ido ya ce, "Ina sonki, auren ki nake da burin yi shiyasa na samu mahaifin ki da maganar ya ce nazo na same ki yau. Ina fata zaki amince dani."

Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Allah ya zaɓa mana abinda yafi alkhairi." Murmushi ya yi ya amsa da amin ya ce, "ki saka min number wayarki" ya faɗa yana miƙa mata wayar. Karɓa tayi ta saka number ta miƙa masa wayar. Ya ƙarba ya ce, "na gode sosai Nayla, na gode da damar da kika bani." Murmushi tayi kaɗan kafin ya bata kuɗi ta ƙi karɓa tace ta gode. Babu yadda bai yi ba amma ta ce bazai karɓa ba dole ya haƙura ya ƙyaleta suka yi sallama ta koma cikin gida.

A falon cikin gida ta tarar da Abiy ana zaune kamar ko yaushe shida Yaya da Yaya Jawad da Auta da kuma Jalila da Mama. Abiy ya kalle ta ya ce, "baƙon naki ya tafi?."
"Eh Abiy, ya tafi." Abiy ya kalli Yaya ya ce, "A NCC yake aiki kuma bazai wuce sa'an ka ba, na san mahaifinsa a nan Kaduna suke gabaɗayan su. Familyn Mansur Garkuwa ne. Yaron babu laifi gaskiya, yana da hankali ana ta yabonsa sosai."

Yaya yace, "Family Garkuwa Abiy? Lallai manyan mutane."
"Sosai kam. Amma ni yadda ake yabon kirkin yaron ne ya burge ni ba familyn sa ba."
"Ita samarin ma har sun yi mata yawa Abiy. Wannan shine na huɗu kenan fa, ga cousin ɗinta Abbas."

Abiy ya murmusa ya ce, "bari kawai Babana, ka san bana son wannan yazo wannan ya tafi. Abinda ya jawowa Jidda aure ba tare da Nayla ba kenan" ya kalli Nayla ya ce, "Nayla bana son tara samari, bana son wannan saurayi yazo wannan saurayi ya tafi kema kin sani, kamar yadda na bawa wannan Omar ɗin dama zan bawa sauran dama a ciki ki zaɓi wanda ki ke so ki yi auren ki. In kuma Yayanki Abbas ki ke so shikenan."

Nayla ido ya ciko da hawaye ta turo baki ta ce, "To Abiy." Yaya J ya ce, "ke dallah meye na wani hawaye?." Ta goge ido tana kallon sa, Abiy yana dariya ya ce, "Nayla ce fa. Tunda kin fara aiki Nayla aure zaki yi, in Abuja kika tafi sai a nemi transfer ki koma can, in Kano ne sai ki koma can, in a nan ne dai duk ɗaya." Kanta na ƙasa sai ajiyar zuciya da tayi, ta miƙe Jalila na ta tsokanarta, Nayla ta harare ta ta miƙe ta shiga ɗaki.

Mama ta bita da kallo ba tare da ta tanka ba. Familyn Garkuwa kawai take maimaitawa a zuciyarta, ta ya zata bar Nayla ta auri ɗan Familyn Garkuwa?. Kaf wanda aka lissafa a cikin masu neman aurenta wallahi baza ta bari ta aure su ba, har cousin ɗinta Abbas bazata bar auren ya yu ba. In ma ta bari ta aure su taje ta huta kenan taji daɗin zaman aure, ai wallahi yadda bata ji daɗin zaman aure ba Nayla ma baza ta ji daɗin zaman aure ba, duk yadda zata yi zata yi don ganin Nayla ta sha wahala a gidan aure, baza ta bari a kai Nayla inda zata ji daɗi ba wallahi. In ta bar hakan ya faru mahaifiyar Nayla ta ci bulus kenan, ita ta wahalar da ita a gidan aurenta kuma sai ta bar ƴar cikinta ta ji daɗi...? Wannan ai ba abu ne da zai yu ba wallahi. Kai ta girgiza tana cize baki tana tunanin abinda ya kamata ace ta yi.


•••••••
Thursday
10:00am

      Didi kallon Omar take yi ganin ya sha kwallaiya cikin manyan kaya riga da wando da hula, ya yi matuƙar kyau kamar ba Omar ɗinta ba. Omar ya kalle ta ya ce, "Didi mun shirya sai Abuja." Didi jikinta gabaɗaya a sanyaye ya ke ta ce, "to Omar, Allah ya kiyaye hanya."
"Amin. Don Allah ki daina sanyin jikin nan bana so."
"Omar ji nake kamar akwai abinda zai faru wallahi, bana so ka tafi Omar."

Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Babu abinda zai same ni, kar ki damu." Kai ta girgiza ta ce, "kai da wa zaku je? Kana da abokan da zasu raka ka?."
"Ni ina da abokai ne? Sai dai yara su Bash."
"Dasu Bashir ɗin zaku je?" Ta tambaya da mamaki tana kallon sa. Gira kawai ya ɗaga mata sai gasu sun shigo kowa ya ci manyan kaya, Bashir da Goje ne, daman sune na hannun damansa, ba kamar Bashir.

Da kallo take bin su sai suka bata dariya ganin yadda suka yi wani iri dasu harda kwalli suka ranbaɗa su a lallai za a je gidan sirikai. Ganin Didi na dariya sai suna suka yi dariya dan sun fahimci canjin da suka yi take yiwa dariya.

Didi ta ce, "lallai su Bashir an ci kwalliya. To ina Tukur?
"Babbar Yaya ai baza a barki ke kaɗai ba."
"Shi zai yi gadina kenan. To a mota zaku tafi?." Omar ya ce, "eh a mota zamu je."
"Allah ya kiyaye" ta faɗa tana kallon su kafin su fita ita dai gani take wani abun zai faru dasu dukkan su.

*Abuja.*

Ana ta shirye shiryen tarbar in-law, Dad ko fita bai yi ba yana gida saboda tunda ya ga Narma tana matuƙar sonsa ya san ba ƙaramin mutum ta ɗauko ba. Ya gayyato Minister don tarbar sa suna zaune a falo suna hira. Narma ta ci kwalliya sai murmushi take yi, bata kawo matsala a zuciyarta ko kusa, a ganin ta tunda tana son Omar dan yazo gidan sunba abin damuwa bane ba.

Narma ta sakko daga sama Mum ta bita da kallo tana murmushi ta ce, "my daughter, kin yi kyau." Tayi murmushi ta ce, "thank you Mum. Yau rana ce mai mahimmaci a wajena shiyasa nayi kwalliya."  Mum ta ce, "dukkan mu rana ce mai mahimmaci, ko haɗuwarki da Asharaf baki wannan farin cikin da ki ke yi yanzu ba."

Jin Mum ta ambaci Ashraf sai ta murmusa kawai tana tuna yadda suka ƙare dashi jiya, yana jajjada mata wallahi sai ya aureta babu wanda ya isa ya aure ta in ba shi ba. Dad ne ya shigo yana kallon Narma ya ce, "Daughter bai zo bane?." Narma ta kalli Dad ta ce, "bai ƙaraso ba Dad."
"Okay zamu yi sallah." Ta amsa Dad ya fita don su yi sallah.

Su Omar basu suka shiga Abuja ba sai ƙarfe uku na rana, duk sun jigata saboda zama mota, kai tsaye hotel suka je suka kama ɗaki a nan suka huta zuwa la'asar suka yi sallah kowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login