Showing 54001 words to 57000 words out of 87436 words
Chapter 19 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt
kalle ta ya ce, "me ki ke yi a wajansa?." Narma ta ce, "mu je ciki" ta faɗa tana wucewa shima ya bi bayan ta.
A falo ta zauna shima ya zauna yana kallon ta ya ce, "Ina tambayarki, me ki ke yi a wajansa har kina yi masa murmushi haka?." Narma ta kalle shi ta ce, "ba na faɗa maka abinda ya faru ba akan ƙwacen waya? Tun daga nan na gane yana da kirki shine mu ke gaisawa. Kuma jiya ne da ya kaini shopping complex ya yi mantuwa a mota shine na bashi."
"Kawai dan ya taimake ki sai ki fara sakıin jiki dashi? To daman taimakon ki a dolensa ne ko baya so, saboda aikinsa ne, biyansa aka yi dan ya kula dake. Ki san matsayinki Beb, ke fa ba gama garin mutane bace you have to know that."
"Na sani, kuma ni ba wani abun ne ya kaini wajansa ba."
"Gaskiya ya kamata ki koma gida, zaman Kanon ya isa haka tunda dai an gama bikin da ya kawo ki. Ta ya zaki dinga tsayawa kusa dashi kina yi masa murmushi kamar wani mate ɗinki?. He's just your driver, driver ɗin ma ɗan daba shashasha, mara ilimi, ƙazami, jahili ne wanda bai san komai ba sai...."
Narma bata san ta katse shi ba ta ce, "Ashraf stop please! na faɗa maka dalilina na zuwa wajan sa why are you insulting him like that?."
Da mamaki yake kallon Narma ya kafa mata ido ya kasa koda motsa idon yana kallonta, sai a sannan ta fahimci abinda ta ce cikin mamakin kanta ta kalle shi itama kafin tayi magana ya ce, "just because i insulted him that's why you are upset?." Jin a yadda ya yi tambayar cikin jin haushi sai ta ce, "Ba haka bane, kawai bana so ka dinga yi min faɗa ne akan abinda na faɗa maka dalili. Ka san wacece ni ai, na san abinda zan yi."
Shi dai mamakin ta yake yi sosai dan Narma tana neman canjawa daga yadda ya santa, amma sai bai nuna ba ya ce, "Well, is okay" ya faɗa cike da jin haushi yana ƙoƙarin miƙewa. Riƙe hannunsa ta yi ta ce, "Are you upset?." Miƙewa tsaye ya yi itama ta miƙe tana riƙe da hannun sa ya ce, "kin nuna min driver ya fi ni a wajan ki Narma." Ta buɗe idanu ta ce, "haba Beb, what are you saying? Ni ban haka nake nufi ba."
"No! driver ki ya yafi ni, you show me my limit. Saboda na zage shi ki ke yi min shouting ko?."
"Sorry beb, ba haka bane" ta faɗa da shagwaɓe tana kallonsa.
Lumshe ido ya yi kafin ya buɗe ta kwanta a jikinsa ta ce, "kar ka ji haushi, i'm sorry." Hugging ɗinta back ya yi na wasu seconds kafin ta janye jikinta tace, "Smile." Murmushi ya yi yana kallon ta ya ce, "I love you." Itama murmushi tayi ta ce, "I love you too." Waya ya ɗauka ya yi musu selfie suka yi kyau kuwa kafin ya kalle ta ya ce, "ina zaki je yau?."
"Babu ko ina, na gaji kaina na ciwo so bana son fita."
"Okay yanzu zan je wani aike da Abba ya yi min, so in na dawo zan dawo." Murmushi ta yi ta ce, "okay sai ka dawo." Har bakin mota ta raka shi ya shiga ya fita ita kuma ta koma ciki.
Omar lokacin da ya koma Didi tana a falo zaune ya shiga shima ya zauna ya ce, "ya jiki?." Ta kalle shi ta ce, "da sauƙi Omar." Ledar hannunsa ya miƙa mata ta karɓa ya ce, "jiya na kai yarinyar can wani kanti sai na siyo miki, na san ki da son turare da kuma son milo."
Murmushi tayi ta buɗe turarenta ga kuɗin sa a jiki naira dubu talatin da uku ta ce, "Omar wannan turare mai tsada haka?."
"Eh, ki dinga fesawa in sirikina zai zo." Dariya tayi ta ce, "Ka raina ni." Shima murmushi ya yi kafin ya ce, "Ya maganarsa kuwa?."
"Sun gama magana da Kawu to rashin lafiyar nan tawa ban sammu mun tattauna sosai ba, ko mai yake faruwa zan faɗa maka." Kai ya girgiza kafin ta kalle shi ta ce, "Omar yaushe ka iya mota?." Murmushi ya yi ɗan daman ya san sai ta tambaya, ya gama sanin halinta ko wanne motsi in ta yi zai fahimci me take nufi kamar yadda ta sa nasa. Ya kalle ta yaga shi yake kallo, kafin yayi magana ta ce, "Omar kana bani tsoro fa, a ina ka san Sen har ya baka ƴarsa kana yawo da ita?."
"Didi" ya faɗa yana gyara zama ya kalle ta sosai ya ce, "na san abinda nake yi fa, kar ki damu kanki." Ta ce, "nima ban ce baka sani ba Omar, amma abubuwan ne suke bani mamaki sosai."
"Kar ki damu, babu komai sai alkhairi."
"Allah ya sa hakan" ta furta tana buɗe turaren dan ya yi mata ƙhamshi sosai. Bai sake magana ba ya tashi ya fita itama bata sake cewa komai ba saboda kanta ya fara yi mata ciwo.
Da daddare Hajja ta shigo ita da Nayla da Salma dan su duba Didi, kamar ko yaushe yana zaune a falon shi da ita duk da ba hira suke ba ita tana abinda yake gabanta shi kuma yana ta danna waya.
Sallamar su ya saka suka kalli masu shigowa Didi da fara'a ta ce, "Hajja kece da kan ki?." Hajja ta ce, "Aisha an ce baki da lafiya harda su kwnaciya a asibiti ai dole nazo."
"Sannu da zuwa" ta faɗa da fara'a tana kallon Hajja. Hajja ta zauna suka gaisa da Didi kafin ta kalli Omar suka haɗa ido ta ce, "Omar Faruku mazan fama, ja daku ba dai rago ba. Wannan hakimcewa da ka yi a falo sai ka sa a ɗauka mai gidan ne ai."
Samun kansa ya yi da sakin murmushi mai sauti haka kawai yake jin farin ciki a zuciyarsa ba tare da ya san dalili ba, ya kalli Hajja ya ce, "Ina yini."
"Lafiya lau Ummaru, Na ɗauka ai baka ganni ba da naga ka ɗauke kai." Bai ce komai ba kuma fuskarsa bata bar murmushin ba.
Nayla suman zaune tayi ganin yana murmushi a karo na uku da ta ga yana yi, sai taji ƙirjinta yana sama da ƙasa wani irin abu yana fizgar ta zuwa gare shi kamar ta saka igiya ta jawo shi haka take ji. Daƙyar ta iya ɗauke ido daga kansa suka gaisa da Didi kafin ta kalle shi ta ce, "ina yini." Jin ta gaishe shi sai Salma ma ta gaishe shi ya ɗago ido ya kalli Nayla da take kallon sa kamar zai amsa sai ya yi shiru.
Hajja ta ce, "Kana ji ana gaishe ka fa."
"Ni bana son gasuwa ni kam, Lallai sai an gaishe ni?" Ya faɗa yana kallon Hajja kafin ya kalli Didi. Hajja ta kalli Nayla ta ce, "to kin ji sai ki daina gaishe shi. Daman ai dodon ki ne ko yaushe cikin tsorataki yake." Didi ta ce, "Omar meye haka? Gimamawa ce zata saka a gaishe ka, kai wanne irin mutum ne da komai baka so?."
Salma ta taɓe baki cikin jin haushi, daman in banda karanbani irin na Nayla ina ita ina gaishe shi? Gabaɗaya haushin kanta take ji da ta biye mata itama ta gaishe shi, ita kuma tayi haka ne saboda kar Hajja tayi mata faɗa tace bata gaishe shi ba.
Hajja ta ce, "ƙyale shi, wataƙila in ya amsa ɗin ma tsoro zai bawa Hauwa'u." Nayla ta sauke ido ƙasa zuciyarta babu daɗi akan abinda ya yi mata, amma bata gajiya za kallon sa daƙyar ta iya sauke idon ta ƙasa.
Nayla ido na ƙasa ta ce, "daman in an gaishe shi baya amsawa."
Kallon wacce Hajja ta nuna da Hauwa'u ya yi yaga Nayla ce ta sunkuyar da kai sai yaji wani iri a ransa kamar bai kyauta ba, ɗauke kai ya yi daga kallon ta ya kalli Didi da take kallon sa ya ce, "Lafiya lau, shikenan na amsa ko? To ki daina hararata" ya faɗa yana miƙewa ya fita daga falon.
Hajja tayi dariya ta ce, "ja'irin yaro, zan ga matar da zaka aura ai, sai na fara yi mata huɗuba na zama da kai kafin ta shigo, dan Omar jarbin ƙwai ne jansa sai me nutsuwa." Didi ta ce, "Ai Hajja dodo da donanniya zamu haɗa kawai" ta faɗa tana kallon Nayla cikin wasa tana dariya.
Hajja ta ce, "shikenan ba, ayi maganin tsoro da rashin son gaisuwa." Suka yi dariya gabaɗaya yanzu har Nayla. A baya in aka yi irin wannan maganar haushi take ji, amma yau sai taji daɗi a zuciyarta har tana murmushi zuciyarta na taya ta murmusawa. Basu jima sosai ba suka yi mata sallama suka tafi bayan Salma tayi mata allura.
Basu jima da fita ba aka yi sallama tare da shigowa falon. Da mamaki Didi take kallon wacce ta shigo ta ce, "wa idona yake gani kamar Barr Nass?." Narma tayi murmushi ta ƙaraso ta ce, "ni ce." Didi ta ce, "ki zauna mana."
Narma ta zauna tana kallon Didi itama ita take kallo ta ce, "Sannu da zuwa."
"Yauwa, ya jiki?."
"Jiki da sauƙi na samu lafiya, Bara na kawo miki ruwa."
"Ki barshi kawai, daman cewa nayi bara nazo na gaishe ki na barki babu lafiya." Didi taji daɗi sosai a ranta tace, "kai amma na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci." Ta amsa da amin.
Didi ta ce, "yanzun nan kuma ya tashi amma na tabbatar yanzu zai dawo." Kafin Narma tayi magana suka ji sautin murya sa yana magana dasu Bash tare da shigowa falon. Haɗa ido suka yi da Narma tayi masa alamun hiii da hannu, ya kalli Didi da take murmushi ta ce, "yanzun nan yazo, ta ce ta zo gaishe ni."
Narma kallon sa take yi shi kuma bai yi magana ba kuma bai zauna ba, kuma koma inda ya fito ba. Narma kallon sa take yi kafin ta ce, "Yayan ki ne?." Didi tayi dariya kaɗan ta ce, "kusan hakan, tunda ya fini tsaho da suffar manya, Yayana ne." Narma ta kalle shi a lokacin ya kalli Didi ya ce, "ina abincin su?." Didi ta san su wa yake nufi sai ta ce, "yana nan, ka jira na sallami baƙuwa sai na ɗauko maka ko?" Ta faɗa tana harararsa ganin ko kula ta bai yi.
Komawa ya yi ya bar falon bai ce komai ba, to me zai ce? Shi sam bai iya magana da baƙi ba, kuma ga gidan na su ba baƙi ake yi ba ko yaushe shiru babu mai zuwa, shi kuma damn ya son baƙi, shiyasa bai iya magana da baƙo a cikin gidan ba.
Bayan ya fita Didi ta ce, "in baƙi sun zo sam baya sakewa, sai ya yi ya abu kamar yaro." Narma tayi murmushi kawai bata ce komai ba dan taji haushin ƙin kula ta ɗin da ya yi. Ai ko babu komai tunda har ta tako har gidan su ta zo ya kamata ko hello ya ce mata.
Didi ta ce, "na jima ina bibiyarki a instagram, ko yaushe cikin fegin ki nake har Omar ya gane ya kan ce ke dai kina son yarinyar nan. Yadda ki ke tsayawa ƙananun yara musamman akan fyaɗe yana min daɗi sosai." Narma ta ce, "na gode" ta faɗa tana murmushi kaɗan.
Miƙewa tayi ta kalli Didi ta ce, "zan koma, dama nazo na duba ki ne." Didi ma ta miƙe tana yi mata godiya har bakin mota ta rako ta. Narma ta yiwa motar key ta buɗe mazaunin driver ta shiga tana sake kallon gidan ko zata ganshi, babu shi babu alamunsa duk sai taji babu daɗi ita ba haka taso ya faru ba.
Ajiyar zuciya tayi ta kunna motar amma taƙi tashi tana neman yi mata yadda tayi mata har aka ƙwace mata waya. Tsaki tayi ta fito daga motar a lokacin ta hango shi sai ya ƙaraso ta bashi hanya ya shiga gaban motar, yana shiga ya kunna sai ta tashi ya zauna bai fito ba. Zagayawa tayi ta buɗe gaban motar ta shiga tare da saka seat belt shi kuma ya ja motar yana mamakin dalilin shigar ta gaba maimakon baya mazaunin ta.
Tafiya suke bai bari ya kalle ta ba dan kallon ta yana yi masa illa a jikinsa, sanye take da kayan bacci riga da wando masu santsi rigar tana da tsaho tazo har guiwa amma ƙaramin hannu ne da ita. Sai wandon da yake dogo har ƙasa ta yafa mayafi ƙarami a kanta.
Har suka je gidan bai ce mata komai ba sai da ya tsaya sannan ya ce, "mun gode." Cikin shagwaɓa ta ce, "Sai yanzu zaka ce? bayan har gidan ku naje ko ka kula ni? Ina tausayin mara lafiya kuma sister ka ce shiyasa naje gaishe ta amma kayi min banza kamar baka sanni ba. Da na sani ban je." Yadda take maganar sai da ta saka shi yin ajiyar zuciya, ya kalle ta yaga shi take kallo ya ce, "mun gode" ya sake faɗa yana janye ido daga kanta.
"Amma sai yanzu ka ce, ko magana fa baka yi min ba." Shiru ya yi dan bai san me zai ce mata ba kuma, ita kuma ta kafe shi da ido tana mamakin abinda take aikatawa amma umarnin zuciyar ta kawai take bi.
Shiru ya ratsa motar kafin ya kashe motar ya ce, "zan koma" ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe ƙofar.
"Baza ka bani haƙuri ba?" Ta faɗa tana kallon sa da narkakkun idanunta. Kallon ta ya yi zuciyarsa na bugawa sosai, ya tsaya cak da buɗe ƙofar kamar an hana shi ya sauke ajiyar zuciya yana dana sanin biyo ta ma da ya yi.
"Sai da safe" abinda ya ce kenan ya buɗe motar ya fita dan ya ga so take ya tarwatsa masa tunani.
Narma ta bishi da kallo ta kwanta a kujerar motar tana sauke ajiyar zuciya cikin sabon yanayin da bata san daga ina yake zuwa ba. Haka kawai taji tana son ganin sa shiyasa ta tashi zuwa gidan su, ganin na sa da tayi sai taji kamar wani sabon yanayin wanda yafi na ɗazu tsayawa a rai da shauƙi a ranta. Ta kwashe mitina goma a haka kafin ta buɗe ƙofar ta fito bayan ta zare ɗin ta shiga cikin gida.
Kiran Dad take gani yana zuwa video call ta zauna a falon ta ɗauka tana kallon sa ta ce, "Hii Dad."
"Hiii Baby, how was your night."
"It was fine.."
"Good. Yaushe zaki dawo ne?." Narma ta ɗin yi jim kafin ta ce, "maybe next week." Dad ya ce, "no, kin shirya ki taho Monday."
Cikin shagwaɓa ta ce, "Dad ina son zaman Kano sosai."
"Dole ki dawo akwai aiki a company da yake jiranki kin manta ne?." Shiru tayi tana tura baki gaba kafin ya ce, "kin fita ne?."
"Yes Dad, naje gidan su Tiger sister shi babu lafiya na gaishe ta."
Dad ya wara ido ya ce, "What? Kin je gidan su Tiger?." Narma ta ce, "Yeah, yanzu ya dawo dani."
"Kina cikin hankalin ki kuwa?." Shiru tayi bata ce komai ba Dad ya fara faɗa ya ce, "meye haɗinki dashi da zaki je gidan su gaishe da sister shi? Waye na ki? He's just your driver not your friend. Wai what is your problem ne Narma? Ina hankalinki ya tafi ne?."
Ganin yadda Dad ya ke faɗa sosai sai ta ce, "I'm sorry Dad, kawai naje ne saboda bata da lafiya sosai, sannan...." Dad ya katae ta ya ce, "Then what? Narma Tiger is not your mate, na faɗa miki reasons ɗina na barin ki tare dashi ba wai dan ya kai matsayin ya zauna ɗin bane. Aikin sa ya kula da lafiyarki na biya shi, ba dan ki ji gidan su im wani babu lafiya ba. Ke ko mutuwa ya yi matsayin kin wuce ki je gaisuwa kin gane?."
Narma ta ce, "Dad ka san ina tausayin mara lafiya shiyasa."
"Na sani, na san halin ki na tausayi mara lafiya amma ba irin famliyn Tiger ba. Wanda yake daidai dake ko ya fiki matsayi shi zaki tausayawa ba shi ƙasƙantacce ba. Aikin driving ɗin ma da ya samu daga gare ni ina da dalilina, ke kin san da ko mai gadin gidan da ki ke bai isa ya zama ba."
"Is okay, I'm sorry."
"Sorry for yourself. Dan haka ranar Monday ki siyo ticket ki dawo gida. Ki zo ayi maganar auren ki kawai, akwai mutane da yawa suke so su aure ki." Narma ta ce, "Okay."
"Ki je ki ci abinci sannan ki kwanta." Ta sake amsawa sannan ta kashe wayar tana turo baki ta hau sama. Shirin kwnaciya tayi amma babu bacci a idanun ta hakan ya saka ta tsaya a varander tana kallon motoci zuciyarta cike da tunanin Omar.
Omar a irin yanayin Narma ya ke tafiya, zuciyarsa gabaɗaya ta cushe babu abinda yake gani sai ita, kuma ta burge shi sosai zuwan ta gidan su ba ƙaramin girma ya bata a idanunsa ba, duk wanda ya san da Didi bata da lafiya har yazo ya duba ta ai abin ka girmama shi ne balle ita ga yadda matsayinta yake, ga kuma yadda ake faɗar rashin kırkinta. Kuma batu ake na Didi rabin ransa aka zo akazo dubawa, dole ya ji daɗi. Gaskiya in ya ce bai ji daɗin zuwanta gidan su ba ya yi ƙarya, har zuciyarsa ya ji daɗi haka ya samar mata da matsayin sosai a wajan sa. A karo na farko a rayuwarsa wata mace ba Didi ba ta burge shi, a karo na farko ya ji yana ganin girman wata mace ba Didi ba a zuciyarsa.
Koda ya shiga gida Didi ma zancen ta take yi, tana aikin faɗar ashe tana da kirki har haka ake mata kallon mara kirki, shi dai bai ce mata komai ba dan shi kaɗai ya san abinda yake ji a jikinsa a haka ya tafi ya kwanta, sai dai babu bacci babu alamun sa saboda tunani.
Nayla ma a irin yanayinsa take, gabaɗaya murmushinsa take gani a idanun ta zuciyarta na bugawa sosai, ajiyar zuciya tayi a bayyyane ta ce, "wannan