Showing 60001 words to 63000 words out of 87436 words

Chapter 21 - KIRAN RABO BOOK1 COMPLET BY NANA HALEEMA.txt

yana kallon glass ɗin gaban motar. Ganin kallon ya yi yawa ya juyo fuska a ɗaure ya ce, “Kina bina bashi ne? Kin ishe ni da kallo.”

Murmushi ta yi bata ce komai ba kuma bata daina kallo sa ba. Ƙaramin tsaki ya yi jin hakan sai ta ce, “Faruq!.” Wani irin bugawa zuciyarsa tayi ya kalle ta da manyan idanunsa da suke da haske a wannan lokacin. Itace mutum na farko da ta taɓa kiransa da wannan suna, kowa ya san Faruk sunan sa ne amma babu wanda ya ke faɗa masa sai dai Omar ko sunayen da aka san shi da shi.

Ganin yana kallon ta sai ta ce, “Zan tafi, amma na kasa gane yanayina haka kawai bana so na tafi.” Bai amsa mata ba ta sake cewa, “Amma zan dawo, naji daɗin kwanakin da nayi a Kano tare da kai. Da farko nayi maka wata fahimta daban please ka yafe ni, abinda nayi maka ya wuce.”

Shi wallahi mamaki take bashi yana tunanin anya ba ƙwaya ta fara sha ba, to in ba aikin ƙwaya ba ina ita ina bashi haƙuri? Laifin me tayi masa da take bashi haƙuri? A matsayin sa nawa da zata bashi haƙuri?. Daga yin kwana takwas tare dashi har tayi masa laifin da zata bashi haƙuri?. Katse shirun ta yi ta ce, “Faruk say something..”

Kallon ta ya yi ya ce, “zaki rasa jirgi.” Ta kalli agogo ta ga saura mintina ashirin jirgi ya tashi ta kalle shi ta ce, “in na rasa zan iya neman wani.” Ganin bazai magana ba sai ta buɗe motar ta fito, ga mamakinsa da kanta ta ɗauko jakarta a bayan mota ta riƙe handbag ɗinta ta dawo kusa dashi ta ce, “thank you for being always by my side, thank you for your helpful.”


Ya fahimci abinda take nufi rass, ya gane abinda ta ce kawai shi sam baya so ayi masa turanci ne. Inda ace zasu cigaba da zama a Kano tare sai ya karta mata warning akan yi masa turanci, baya ra’ayi ya fi son ayi magana da yaren da ya iya.

Kallon ta ya yi ya ga abaya ta saka, a karo na farko da ya ganta da abaya amma duk da haka an yi shaping abayar ta zauna daidai da jikinta ko wanne lungu na jikin ta ya shiga cikin abayar ya zauna dasss kamar a jikinta aka ɗinka.

“Allah ya kiyaye hanya.” Narma ta ce, “Amin. Can you do me a favor please?.” Kallon ta ya yi da mamaki da kuma takaici, shi ba ya son turanci amma ita ya ga alama in bata yi ba bata jin daɗi gabaɗaya. Narma ta ce, “Smile please.” Ko kallon ta ma bai yi ba balle ya yi murmushi, sai ma sake haɗe gira da ya yi ya ɗauke kai.

Murmushin ita take yi dan iya wannan ɗauke kan ya biya ta ta ce, “I like your acting Faruk. Anyway, na tafi ka bawa Yahya key ɗin motar sai na sake dawowa a karo na biyu.” Kai ya ɗaga mata ta fara tura jakarta gaba tana tafiya ya samu kansa da binta da kallo.

Juyowa tayi ta kalle shi ganin yana kallon ta sai ta yi murmushi ta ɗaga masa hannu alamun bye, bai ko motsa ba sai ma buɗe motar da ya yi ya shiga ya tafi ita kuma ta girgiza kai tana tafiya. Wannan ɗabi’ar ta sa ta ko in kula tana matuƙar burgeta. A haka ta ƙarasa ciki ta tana jin wani abu mai kama da kewa na shiga jikinta.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

             ©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 18.*

Omar tuƙi yake yana tuna murmushin Narma tayi da ta juyo tana ɗaga masa hannu, bai san ya yi murmushi ba sai da ya kalli inda ta zauna har lokacin ƙhamshin turarenta bai daina tashi daga motar ba. Haka yake tafiya har ya koma gidan ya tarar Yahya yana nan ya bashi key ɗin motar ya fito zuwa gida. Da ya koma bai shiga wajan Didi ba ɗakinsa ya shiga ya kira Sen a waya domin ya sanar dashi aikin da ya saka shi ya kammala lafiya.

Sen kamar gaske ya yaba sosai kafin su yi sallama ya kashe wayar yana jin wani abu mai nauyi a zuciyarsa. Gajiya yayi da zaman kasancewar rana ta yi ga yunwa da yake ji dan bai karya ba. Yana fitowa daga ɗakin Nayla tana shigowa gidan, kai tsaye idanunsa ya faɗa cikin nata da mamaki. Saurin janye ido tayi saboda abinda taji yana sukar zuciyarta, bata iya jure kallonsa ko ya ya yake.

"Ina yini" ta furta cikin sanyi tana niyar gifta shi. Ga mamakin ta sai ta ji ya amsa hakan ya saka ta juyo tana kallon sa shi kuma yana kallon waya, ji ya yi ana kallon sa hakan ya saka ya kalle ta sai ya ga tayi murmushi ta ɗauke ido ta shiga wajan Didi.

Didi ganin ta ya saka ta murna suka zauna suna hira kafin Nayla ta ce, "Didi gobe zan koma Kaduna in Allah ya kaimu, sallama na shigo nayi miki." Didi tayi sak cikin rashin jin daɗi ta ce, "da wuri haka?." Nayla ta ce, "wallahi, naso Abiy ya barni na ƙara kwanaki amma ya ce a'a na dawo."
"Wallahi na ɗauka zaki kai gab da ramadan a garin nan tunda naga azumi ya kusa. Allah ban ji daɗin tafiyar nan da zaki yi ba Nayla." Nayla ta ce, "ni kaina ban taɓa jin bana son tafiyar ba kamar wannan lokacin, sosai nake jin bana so na bar Kano."

Didi ta ce, "in kin tafi sai yaushe?." Nayla ta ce, "Wallahi ban sani ba Didi." Didi ta ce, "Allah ya kiyaye hanya ya kai ki lafiya." Ta amsa da amin Didi ta tashi ta shiga ɗaki sai gata da turaren da Omar ya siyo mata ta kawo mata ta ce, "Na rasa me zan baki Nayla, ga turare sabo ne mutuminki ne ya siyo min shi shekaran jiya." Nayla ta karɓa ta ce, "na gode sosai Didi."
"Haba tsakanin mu babu godiya Nayla. Wallahi duk ji nake yi bana so ki tafi."

Nayla kam murmushi take yi ko babu komai ta samu abinda ya fito daga hannun Omar. Shigowa falon ya yi fuskar nan a tamke matuƙa kamar zai yiwa Didi magana sai ya fasa ya juya zai koma. Didi ta ce, "Omar Nayla ce zata tafi gida gobe." Tsayawa ya yi ya kalli Didi bayan ya ɗora yatsunsa a goshi ya ɗan murza kaɗan ya ce, "Wace haka?." Wani irin yarr Nayla taji a jikinta, haka nan idanunta suka taru da hawaye, kenan yana nufi bai ma san sunan ta ba.

Didi ta nuna Nayla ta ce, "gata a zaune." Omar ya tsaya kawai yana kallon Didi cike da takaici. To ina ruwan sa da tafiyar da zata yi banda abin Didi da take son saka shi a sabgar yarinyar, shi kuma tunda tayi masa faɗa a gabanta wallahi yake jin haushinta, ya tabbatar ba zai daina jin haushin ta ba har abada.

Bai ce komai ba ya fita Didi ta kalli Nayla ganin tayi shiru ta sunkuyar da kai sai ta ce, "Yi haƙuri Nayla, Omar ne sai addu'a. Ta bakin Hajja ta ce carbin ƙwai ne, jan sa sai mai nutsuwa." Murmushin yaƙe tayi kaɗan tayi mata sallama ta fito zuwa ƙofar gidan. Yana zaune a ƙofar gidan da yaran sa suna magana, Nayla ta wuce da sauri sai da taje gate ɗin gidan Hajja sannan ta tsaya tana sake kallon sa.

Wayar ta ta ɗauko ta yi zooming ɗinsa sosai tayi masa hoto ba tare da ta san dalilin aikata hakan da tayi ba. Wajan Hajja ta shiga ta nuna mata turaren da Didi ta bata kafin su shirya tafiya gidan su Salma dan tayi musu sallama.

Har suka je suka dawo Nayla bata da walwala, Salma tayi-tayi ta faɗa mata abinda yake damunta tace babu komai. A haka suka dawo wajan Hajja Salma tana ta ciwon bakin taƙi faɗa mata damuwarta, Hajja tace bata son komawa Kaduna ne ta ƙyale ta kawai.

Ɗakin da Nayla take kwana Salma ta shiga ta ɗauki wayar Nayla da take gefe ta ce, "bara na tura hotuna." Nayla bata ce komai ba Salma ta fara duba wayar. Ɗagowa ta yi ta kalli Nayla kafin ta ce, "Wannan ba hoton Tiger ba ne?." Jin hakan sai gaban Nayla ya faɗi, ta kalli Salma dan bata da mafita ta riga ta gani. Cikin borin kunya Nayla ta ce, "Hotonsa kuma?."

Salma ta haska mata fuskar wayar ta ce, "gashi nan." Nayla ta ce, "oho ban ma san na ɗauka ba." Salma ta bita da kallon rashin yarda ta ce, "gashi har zooming ɗinsa akayi ki ce baki san kin ɗauka ba?." Nayla tayi shiru bata ce komai ba.

Salma ta ce, "me ki ke nufi da ɗaukar hotonsa Nayla?." Tayi shiru bata ce komai ba Salma zata sake magana ta ce, "Don Allah Salma ki yi shiru, ki bar ni naji da abinda yake damuna don Allah. Na ce miki ban sani ba ai, ga wayar nan a hannunki ki goge mana." Salma ta ce, "ai ko baki ce ba sai na goge" ta faɗa tana goge hoton ta ajjiye mata wayar ta fita bata sake magana ba.

Washe gari ƙarfe sha ɗaya na safe Abiy ya iko da driver. Nayla na shan tea taga kiran drivern gidan su sai da gabanta ya faɗi, ta ɗauka nan yake sanar da ita yana waje ta kashe wayar. Kallon Hajja ta yi da salma ta ce, "Hajja ya zo zamu tafi" ta faɗa a sanyaye tana ajjiye kofin shayin hannunta.


Hajja ta bita da kallo ta ce, "Zo Hauwa'u." Ba musu ta ƙarasa kusa da ita ta zauna, Hajja ta riƙe hannunta tace, "faɗa min damuwarki." Sai kawai ta rungume Hajja ta ce, "bana son tafiya Hajja, bana son tafiyar nan, wani iri nake ji a zuciyata Hajja. Bana so na tafi wallahi."

Hajja ita kanta zuciyarta sai tayi rauni, tana matuƙar ƙaunar Nayla saboda kasancewar ta marainiya, kuma a cikin ƴaƴanta mahaifiyar Nayla ce kawai ta rasu, tana kallon Nayla kamar ƴarta da ta rasa. Hajja cikin shigar rarrashi ta ce, "ki yi haƙuri, ki daina kuka, kin ga bakya koma gida masa kina yi masa kuka ba, bazai ji daɗi ba. Ki yi haƙuri ai zaki sake dawowa nan gaba in sha Allah." Nayla ta ce, "Bazai bar ni na kusa ba Hajja, Abiy baya so nayi nisa dashi" ta faɗa tana kuka sosai wanda ya bawa Salma mamaki kawai ta zuba mata ido.

Hajj ta ce, "kewar mahaifiyarki yake yi shiyasa baya so ki yi nisa dashi, gani yake kamar zai rasa ki kamar yadda ya rasa ta. Ki daina ku ka kin ji?." Ta goge ido ta ce, "To hajja." Hajja ta ce, "Akwai saƙo a kitchen ki kaiwa Abban naki, sannan akwai wani ma a bokiti ki bawa Maman taki kin ji?." Nayla ta ɗaga kai tana tashi ta ɗauko ta ajjiye a kusa da ita. Ta ƙarasa jikin socket ta zare chargerta, ta shiga ɗaki ta ɗauko trolly bag ɗinta da handbag ta fito bayan ta saka mayafi.

Salma tana tsaye tana kallon ta tace, "Nayla wallahi mamaki ki ke bani, kamar yau kika taɓa zuwa wajan Hajja zaki koma ki ke wannan kuka?." Hajja ta kalli Salma ta ce, "Ki kaiwa Salisun abin kari ya karya kafin su wuce." Salma ta wuce zuwa kitchen ta haɗa masa ta fita ta kai masa.

Nayla bata ce komai ba amma ta san ita kanta wannan kukan ba wai na rabuwa da Hajja bane kawai, tabbas akwai manufarsa a ƙasan zuciyarta, amma ta kasa gane meye shi. Sai da aka bashi lokaci ya gama, ya shigo da kayan da kansa ya gaisa da Hajja sannan ya fita.

Hajja har bakin gate ta rako Nayla, Salma ta ɗaukar mata jaka suka fita ta saka a cikin booth ɗin motar, Nayla ta kalli Hajja ta ɗaga mata hannu kafin Hajja ta koma.

Kallon gidan Didi tayi sai ta hango Didin na ƙarasowa inda take, murmushi Nayla tayi tana kallon ta Didi cike da tsokana ta ce, "Kukan tafiya daga Kano ki ke yi Nayla? Ko da yake ai dole, ɗan ƙauyen Kaduna ai dole ya yi kuka in zai bar birni." Dariya Salma da Nayla suka yi Didi ta ce, "na ɗauka zaki sake shigowa mu yi sallama." Nayla ta ce, "kar na tsayar dashi ne shiyasa."
"Allah ya kiyaye hanya Nayla, ko Kano zata yi kewarki balle mu da muke cikin ta." Murmushi tayi ta amsa da amin tana ji ina ma tana da zarrar tambayar Omar da ta ce ina yake.

Tana shirin shiga mota ta hange shi ya fito daga gidan yana kalle-kalle da alama Didi yake nema, hannu Didi ta ɗaga masa sai ya ɗaga kai alamun ya ganta ya juya bai sake kallon kowa. Nayla ita hakan ma ya yi mata, ko babu komai ta ganshi kafin tafiyarta Kaduna. Bayan motar ta buɗe ta shiga tana yi musu sallama suna yi mata addu'a ya ja motar suka bar cikin unguwar zuciyarta sam babu daɗi.


•••••••••

"Dad zaman Kano ya yi min daɗi sosai, I feel like na sake komawa cikin kwanakin nan" ta faɗa tana cin Apple. Mum ta kalla kafin ta ce, "Mum wai ya ba ku je Paris ɗin ba?." Mum ta ce, "mun fasa."

Sen ya kalli Narma ya ce, "Tunda kin dawo lafiya haka nake so. Tiger ya kira ni tun jiya yana shaida min kin taho babu abinda ya same ki." Narma sai ta saki murmushi jin an ambace shi ta ce, "Classy boy kenan!." Da Sauri Mum ta kalle ta jin abinda ta ce taga murmushi ma take yi. Mum ta ce, "I hope bai cutar dake ba?."
"Babu abinda ya yi min, ya kula dani sosai fa Mum." Mum ta sake kallon ta tace, "amma da farko ai ya raina ki, yana ganin kanku ɗaya dan kuna haɗa numfashi dashi a mota, yanzu a ina zai ganki ma balle ku zauna mota ɗaya?."

Dad ya ce, "bai isa ba wallahi, ita dashi ai sai dai taimako shima ba daga hannunta ba, sai dai daga hannun personal assistant ɗinta." Mum ta ce, "Yana da jin kai yaron kamar wani ɗan sarauta, yana talaka, illirate, useless and dirty ya dinga irin wannan abun. I so much hate him wallahi, just imagine nonsense like him sayiing he won't open the car for her. Oh God! har yanzu na kasa mantawa da abin nan. Shi ba abin alfaharinsa bane ace ya buɗe mata mota? Talaka bashi da hankali sam, talakan ma irin sa jahili da bai san komai ba."

Dad ya murmusa ya ce, "saboda ƴan iska irinsa na garin Kano ya saka na haɗa ta dashi, gashi kuma ta dawo lafiya." Mum tace, "kana ganin scar mark ɗin hannunta kana cewa ta dawo lafiya? Ta dawo dai babu laifi amma ba lafiya ba."

Narma gabaɗaya bata jin daɗin zagin nan da suke yi masa ko kaɗan. Dad ya kalle ta ya ce, "block his number then delete it, Matsayinsa bai kai ya samu number ki ba kin gane?." Narma gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ta ɗauki wayar ta miƙe tsaye ta ce, "Okay Dad" abinda tace kenan ta hau sama zuciyarta a cushe cikin jin abinda iyayen ta suke faɗa akansa.

••••••••

Nayla basu shiga ba sai la'asar, a gajiye take tana shiga Jalil da suke kira aura ya ɗafe ta yana muryar ganinta. Dariya take yi ya riƙe jakarta ya shiga da ita. Drivern ya kai mata kayan zuwa cikin falon. Abiy ta samu a zaune yana kallonta da murmushi sai ta saki fara'a ta ƙarasa wajan sa ta zauna akan carpet ta ce, "Abiy na." Yayi murmushi ya bata hannu suka gaisa ya ce, "Ummina kin dawo?."

"Na dawo Abiy. Barka da yamma."
"Barka dai Mamana, ya hanya?."
"Lafiya lau Abiy. Na same ku lafiya?."
"Lafiya lau. Ya ki ka bar Hajja?."
"Hajja tana nan lafiya, tana gaishe ku." Mama da take kallon ta ta ce, "Nayla sannu da zuwa." Kallon Mama tayi ta ce, "Mama nayi kewar ku wallahi." Mama ta ce, "ai gashi kin dawo."

Baban Yayan su ne ya shigo da suke kira da Yaya ganin Nayla sai ya ce, "A'a mutanen Kano, saukar yaushe?." Ta kalle shi ta ce, "yanzu na dawo Yaya. Ina yini."
"lafiya lau Nayla, ya Hajja?."
"Tana gaishe ku." Nayla ta ɗauko saƙon Abiy ta bashi, bawa Mama nata saƙon. Abiy yana ta murmushi ganin gurar kano mai kyau kana gani ka san sabuwa ce ta saka yi masa. Ga Dambun nama a cikin wani ƙaramin bokiti. Yana ta murmushi yana sake girmama matsayin Hajja a wajan sa.

Mama ta buɗe nata kayan ta ga girki ne su kuka da kuɓewa da daddawa. Mama ta yi godiya tana ta murmushi. "Twiny." Nayla jin abinda akace ya saka ta kalli wacce take shigowa ta ga Jidda ta ce.

Nayla ta ce, "Twiny yaushe ki ka zo?." Ƙarasowa tayi ta zauna kusa da ita ta ce, "Jiya nazo. Kuma guess what? Kano zamu koma da zama." Wara idanu Nayla tayi ta ce, "da gaske?."
"Wallahi da gaske, Ke dai ki je ki huta zan shigo mu sha labari." Nayla ta kalle ta tana cewa, "gaskiya bana so ki bar Kaduna, in kika koma Kano ya zanyi?." Jidda ta riƙe hannunta suka yi ciki suna hira. Murmushi Abiy ya yi yana jin daɗin zumuncin da yake tsakanin ƴaƴansa, duk da Nayla ce kaɗai ba uwa ɗaya suke da sauran ba amma in ba sani ka yi ba bazaka banbance ba uwa ɗaya ce ta haife su ba.

Kowa ya san Jidda da Nayla tasu tafi zuwa ɗaya saboda sa'anni ne kuma masu suna iri ɗaya. Kwana goma sha huɗu Jidda ta bawa Nayla, tare suka tashi komai tare. Komai tare suke yi Aure ne Jidda ta riga Nayla shine abinda ya raba su.

Da daddare suna zaune akan dining da Abiy da Mama da Nayla, Jidda, Jalila,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login