Showing 1 words to 3000 words out of 88313 words

Chapter 1 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

              *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:* ✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad UmmuDahirah*👈

           *SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga mahaifiya ta Abar Alfahari na, uwata maganin kuka na, I Love You so Much Momma ❤️, Allah ya taimake ki da taimakon sa._ 😭

_Bismillahir rahmanir Rahim, in the Name of Allah the most Beneficient, the most marcerfull praise be to God Lord of the words.._

_My Follow Fans, I'm starting my New Book, I ask Allah subhanahu wata'ala to guide me through and make me it sussufull till End. Amin ya Allah._ 🤲🏽






*________________________________*

                  *PAGE* 1

*________* *ALH. HAYAT SUNUSI* da Matar sa *BARRISTER DEEBIZAH* _(Khadeejah Yunusa Ubale)_ kamar yanda kuka sani a Littafin *LABARIN DEEBIZAH,* mazaunan Kano ne, kuma har yanzu ɗin suna cikin Kano da zama, yanzu haka suna da yara biyar da suka haifa.


           *ABUL-KHAIRI* Shi ne ɗan su na farko, me sunan mahaifin Brr. Deebizah wato *YUNUSA,* lokacin da aka haife shi time ɗin Brr. Deebizah tana shirin shiga B.U.K ne, hakan yasa tun daga kansa suka jingirta da haihuwar har sai da ta kammala karatun ta, sannan ta sake ɗaukan wani cikin, lokacin ABUL KHAIRI na da shekaru 7 a duniya sannan aka haifi ƙanwar sa, yarinyan ta ci sunan Kakar Alh. Hayat ne (wato Gwaggo) Zainab, sai dai basu ɓoye mata sunan ba; da Zee suke kiran ta, a cewar Gwaggo gwara a kira Takwaran ta da sunan ta ya fi, Allah da ikon sa kuma an haifi Zee da watanni biyar Gwaggon ta rasu, sosai mutuwar ya girgiza ahalin su duk da kasancewar ta tsohuwa, sai dai Gwaggo mace ce me tsananin kirki da daɗin zama, musamman ma Alh. Hayat ya fi jin mutuwar ta fiye da kowa, sabida duk a cikin jikokin ta tafi ƙaunar sa, kuma sun fi shaƙuwa matuƙa.

Bayan Zee Brr. Deebizah da yanzu suke kiran ta Mamy, ta sake haihuwar ɗa na miji, sai dai be zo da rai ba tun sanda aka haife sa, daga shi kuma sai da Zee tayi shekaru uku da watanni kafin ta sake haihuwar Fatimah, suna kiran ta da Batool kasancewar sunan ƙanwar Mamy ne, kuma sunan kishiyar Mahaifiyar Alh. Hayat ne, Falmata.

Daga Batool kuma sai Sunusi me sunan Mahaifin Alh. Hayat, suna kiran sa Amir, sai kuma Auta Maryam, wacce taci sunan Maman Brr. Deebizah, suna ce mata Baby, sai dai kasancewar Brr. Deebizah (Mamy) tana ce mata Auta na, shiyasa gaba ɗaya gidan hakan suke kiran ta, ya fi kama bakin su a kan Baby ɗin.

Yanzu haka Zee tayi aure watanni Goma kenan, sai dai bata haihu ba, but tana da ciki yanzu haka.

Waɗannan su ne iyalan gidan Alh Hayat (Abba), ku bi Ni a sannu don jin Labarin rayuwan *ABUL-KHAIRI* da iyalan gidan su.


▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

               Lumsassun idanuwan sa da suke cike taf da barci ya ware su a kan ta

Tana kwance gefen sa, hannun ta ɗaya saman ƙirjin sa da babu riga, barci itama take shararawa wanda yayi wa cuty face ɗin ta kyau matuƙa.

Idanu kawai ya zuba mata cike da takaicin ganin ta kusa dashi, sake ware idanuwan sa da suka sauya kala zuwa ja yayi, ya mayar dasu kan hannun ta dake ƙirjin sa, dogon tsaki yaja kafin ya saka hannayen sa biyu ya riƙo hannun nata ya sauke kan jikin sa ya yarfar dashi

Wanda hakan sai da yasa taji zafi sosai cikin barcin ta, babu shiri ta farka tana zare idanu ba tare da ta motsa ba

Shi kuwa tuni ya ma sauka a kan gadon, yana gyara rigan zuwa jikin sa, tare da ɓame bottles ɗin gaban rigan da suke a buɗe gaba ɗaya

Kallon sa kawai take yi tana karantan yanayin sa, sai da ta gama ƙare masa kallo har ya gama abinda yake yi, ya zari makulle zai fice ba tare da ya sake kallon ko inda take ba, ai kamar ƙiftawar ido ta dira daga kan gadon ta sha gaban sa da sauri, har da saka hannu tana kare sa alamun bazai wuce ba

Sauke idanun sa yayi a kan ta cikin ɓacin rai da ya nuna a face ɗin sa, sai dai be iya ce mata komi ba illa kallon ta da yake yi yana sake haɗe rai

Ita kuma yatsina kyakykyawar fuskar ta tayi, kafin ta kafa masa manyan idanuwan ta tace, "Wai ina zaka je ne ka bar Ni bayan kasan me ya kawo Ni wajen ka? Bie babu inda zaka je wlh sai mun tsayar da maganar mu, tunda ka ƙi ɗaukar waya ta to na biyo ka". Sai kuma taja numfashi tana ci gaba da faɗin, "Wlh idan har baka yarda da buƙata ta ba Bie, na rantse da Allah zan nemi mafita kamar yanda na faɗa maka, kasan kuma Ni ɗin ina da waɗanda suke jira na in Kai musu kain..."

"ZIYA.." Yafaɗa da ƙarfi cikin tsananin ɓacin rai da ya ninka wanda yake ciki, lokaci ɗaya farar fuskar sa ta sauya kala tayi jazur, haka ma jijiyoyin kansa sosai suka fito raɗau

Ƴar siririyan dariya ta saki tana kallon yanda gaba ɗaya ya sauya lokaci ɗaya, hakan kuma sosai ya faranta mata don ta fi son yayi zuciya yabi ra'ayin ta, cikin yatsina tace, "kar ka yimin tsawa Bie, kasan bazan ɗauka ba, kuma kabar tunanin bazan iya rabuwa da kai bane, wlh a kan haka sai mu raba hanya.."

Damtsen hannun ta da ya damƙe ƙam, shi ya hana ta ƙarisa maganar ta, domin sosai zafin ya shige ta

Matso da fuskar sa kusa da nata yayi yana huci, idanun sa sun sake yin jazur fiye dana da, cikin amon muryan sa me haɗe da fushi yace, "Wlh kinji na rantse miki idan har kika ba ma wani daman riƙe hannun ki; ba shiga jikin ki ba ma, wlh wlh sai kinyi dana-sanin sani na a rayuwan ki! bazan hana ki rabuwa dani ba, sannan bazan hana ki aika ta duk abinda kike so ba, fine ki aika ta kinji ko?" Ya ƙarike maganar da girgiza ta yana ware mata jajayen idanun sa, sai kuma ya janye ta daga gaban sa ya nufi ƙofa dasauri ya fice

Duk da ba wani jan ta yayi ba sai da ta faɗi ƙasa sabida rashin ƙwarin jiki, ƙofan tabi da kallo cike da tsoro a ranta, babu shakka ta san Kishin da yake mata zai iya aikata komi, idan tace komi tana nufin komi zai iya yi a kan ta, sai dai kuma ba ta tunanin zata nuna tsoro ko gajiyawa da buƙatan ta, domin baza ta zauna dashi ba ya biya mata buƙatan ta ba, sannan kuma ya hana ta zuwa inda za'a biya mata, tabbas zata ci gaba da tunzura sa don ganin ta cin ma burin ta

Itama miƙe wa tayi ta zura Takalman ta, sannan ta ɗau gyalen ta; ta rataya a kafaɗa ta fice da sauri.

                 ▪️▪️▪️

            Motan sa ya gangarar da ita gefen titi, babu abinda zuciyar sa ke yi sai suya, iska kawai yake faman fesar wa daga bakin sa yana riƙe da sitiyarin motan, ya rasa meke masa daɗi a lokacin, sabida kalaman ta daga jiya zuwa yau sai kai komo suke masa a rai

Hannu ya saka ya soma hargitsa gashin kansa cike da tsagwaron KISHI dake cin sa, sai kuma ya kwantar da kansa jikin kujeran yana lumshe kyawawan idanun sa, ya jima a haka be ɗago ba illa numfashi da yake sauke wa yana faman ci je leɓe, daga ƙarshe kuma yayi wa motan keey ya fige ta da gudu yayi gida.

Gate man na buɗe masa Gate ɗin gidan ya kutsa motan ciki, a parcking space yaja birki yana kashe motan, sai dai be yi yunƙurin fitowa ba illa ma gyara zaman sa da yayi yana dafe kansa.




▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

                Eyeglasess ɗin fuskarta ta sake gyara masa zama a kan cikakkiyar kamilalliyar farar fuskar ta, murmushi yalwace a fuskar ta take kallon su tana magana, "Ba na son ku je ku zauna a can har in kira waya, idan kuwa kuka bari na aikata hakan, to Ni da ku ne, don kun san bazan sake barin ku zuwa ba".

Da sauri Batool ta dafa gwiwowin ta, har da ranƙwafo da kanta tana faɗin, "Wlh Mamy baza mu daɗe ba, idan muka je ma muna gaishe ta da jiki zamu dawo".

Jinjina kanta Mamy tayi kafin ta maida idanun ta kan Maimuna tace, "je ki kira min Aƙilun zan ba sa saƙo ne".

Da sauri Maimuna ta tashi ta fice daga ɗakin Mamyn, da gudu ta nufi hanyan parlour, ta buɗe ƙofan fita tana shirin saka kai waje taji tayi karo da mutum, kafin ta tabbatar da wanda suka ci karon, sai ji tayi an janye ta da ƙarfi an yi wurgi da ita gefe, ai babu shiri ta saki siririyan ƙara jin ta faɗa a saman hannun ta, da sauri ta ɗago kanta tana bin sa da kallo idanuwan ta cike fal da hawaye

Shi kuwa be ma bi ta kanta ba, ya taka ya shige fuskar sa a ɗaure tamau kamar be taɓa dariya ba

Bata dena kallon sa ba har ya shige ɗakin Mamy, sai taja majina tana matse idanunta hawayen ciki suka samu daman zubo wa, jiki babu ƙwari ta tashi ta fice don kiran Aƙilu drever'n su.

            Tura ƙofan yayi da sallama ciki-ciki

Mamy da Batool suka amsa mishi duk kan su suna juya wa ga ƙofan, da sauri Batool ta miƙe ta nufi ƙofan tana mishi sannu da zuwa

Be amsa ta ba, ita kuma ta fice abun ta

Tako wa yayi ya zauna a kan kujeran dake cikin ɗakin, hakan yasa yake fuskantan Mamy dake zaune gefen gadon ta tana kallon sa

"Baba na lafiya kuwa?" Ta tambaye shi cike da kulawa sabida sauyawan da ta gani a tattare dashi

Sakin faukar sa yayi sosai yana ƙoƙarin dai-dai ta kansa, cikin ƙwaƙulo murmushi yace da ita, "Mamy lafiya ƙalau me kika gani?"

Hakan yasa ta saki murmushi wanda ya zame mata ɗabi'a, koda yaushe fuskar ta a sake yake cike da annurin fara'a, sake tsare sa da idanu tayi tace, "Baba na kana son ɓoye min halin da kake ciki ko? Jiya haka ka wuni da ɓacin rai, yanzu ma ga shi ka dawo a yanayin, but kana son ɓoye min, Why?"

Sosa Kansa yayi cike da basarwa yace, "Mamy babu komi fa, ki yarda dani, idan da akwai ke ce ta farko da zan sanar ma wa".

Mamy ta murmusa cike da ƙaunar ɗan nata, shi dai daban yake cikin ƴaƴan ta, koda yaushe a zurfin ciki yake, idan har abu ba yayi tsamari bane, ba ya iya fitowa fili ya sanar musu su da suke iyayen sa, ya dinga ƙunbiya-ƙunbiya dashi kenan a ransa, sai dai wuni yana cikin ƙunci da ɓacin rai, wanda hakan ya jawo ba kasafai zaka ga yana shiga cikin jama'a yana walwala ba..

"Mamy har yanzu Abba be dawo bane?" Maganar sa ta katse mata guntun tunanin ta

"Be dawo ba, lafiya dai ko? In ce dai ba wani abun ka samo zaka ba shi Ni ka hana Ni ba?". Tayi maganar cike da barkwanci

Hakan ya saka shi sakin yalwataccen murmushin da ya fito da jerin haƙoran sa

Sanyi taji a ranta ganin ya ɗan saki ransa fiye da ɗazu ɗin, hakan yasa taci gaba da jan sa da hiran tsokana don dai ta dawo mishi da walwalan sa

Shiyasa sau tari yafi ƙaunar kasancewar ta kusa dashi fiye da kowa a duniyar nan, tabbas uwa daban ce, a duk sanda yake cikin matsala, ita ke fara gane damuwar sa fiye da kowa dake gidan, that's why yake tsananin ƙaunar mahaifiyar shi fiye da komi da kowa dake cikin duniya.

                   ▪️▪️▪️

              Koda Maimuna ta dawo kiran Aƙilu drever, zaman ta tayi a Parlour ba tare da tayi yunƙurin komawa cikin ɗakin Mamyn ba.

Tana zaman itama Batool ta fito ta zauna gefen ta tana tambayan ta, "shin ta kira Aƙilun?"

Kafin ma taba ta amsa Aƙilu ya shigo yana baza idanuwa cikin parlour'n, hannun sa ɗaya riƙe da aswakin da ya cire daga bakin sa ya ƙariso cikin parlour'n, ya zube ƙasa yana faman washe baki tare da yiwa Batool kirarin da ya saba

Ita kuwa nan ta biye masa suna kwasan dariyan Aƙilun daga ita har Maimuna, kasancewar sun fi saba wa da Batool ɗin, kullum suna cikin surutu da junan su, ita kuma Maimuna koda yaushe dama nata ido ne idan suna yi, sai kuma ta dara idan abun ya bata dariya, idan kuma sun sako ta sai ta tsulmiya baki, dayake ita ɗin ba me yawan surutu bane, bata da hayaniya ko kaɗan.

Lokacin ne Mamy da ABUL KHAIRI suka fito daga ɗaki

Kai tsaye ABUL KHAIRI hanyan ɗakin sa ya wuce ko kallon inda suke be yi ba

Mamy ne ta ƙariso cikin parlour'n ta zauna tana amsa gaisuwar Aƙilun, sannan ta kalli Maimuna tace, "Maimuna tashi ki haɗa wa yayan ku abincin sa ki kai masa".

Amsa mata tayi da "Toh". tana miƙe wa tsaye, ta kalli Batool tana mata alama da ido ta biyo ta

Maƙe kafaɗa Batool tayi tana mata dariya ƙasa-ƙasa

Sai Maimunan ta marairaice fuska ta soma tafiya, har da haɗe hannayen ta biyu alamun roƙo

Amma ƙiri-ƙiri Batool ta ƙi motsa wa, sai ma gwalo da tabi ta dashi

Babu yanda ta iya haka ta nufi kichen jiki a sanyaye, tasan halin Yayan nasu yanzu abu kaɗan zaka yi masa kuskure yaci uban ka, bare ma shi da ya tsane ta fiye da kowa dake gidan, ko kaɗan bata san meyasa ba ya ƙaunar ganin ta ba, shiyasa ba ta son ma a aike ta wajen sa bare tayi kuskuren abun da zai haɗa su.

Ita Mamy tuni ta maida hankalin ta kan Aƙilu tana ba shi saƙo, sai kuma ta juyo tana kallon Batool ɗin tace, "ke baza ki je ki shirya bane kin zauna? Ai kuwa idan Abban ku ya dawo ya hana ku fita babu ruwana, ki zauna kasa kunne kina ji na kar ki tashi ki wuce".

Da sauri Batool ɗin ta tashi tayi hanyan ɗakin su tana faɗin "wlh Mamy Ni ban ma ji me kuke cewa ba".

Itama Mamy bata tanka ta ba tamayar da hankalin ta ga Aƙilu tana sallaman sa.

Lokacin ne Maimuna ta fito daga kichen riƙe da Faranti a hannun ta, kanta tsaye ta nufi ɗakin ABUL KHAIRI ta soma Nocking a bakin ƙofan, sai dai har ta gaji babu amsa, dole ta haƙura ta tura ƙofan ta shiga da sallama.

Yana zaune a bakin gadon sa idanun sa kafe a kan ƙofan, ashe duk yana jin Nocking ɗin but yaƙi amsa wa

Shiyasa tana shigowa idanun su suka haɗe cikin na juna, saurin sad da kanta ƙasa tayi gaban ta na matsanancin faɗuwa, ko kaɗan ba ta ƙaunar ta haɗa idanu dashi sabida kwarjinin da yake mata, shi kaɗai ne mutumin da idan suka haɗa idanu dashi take jin daban a cikin rayuwan ta, tana shiga wani yanayi da har yanzu ta kasa fassara shi

Jiki a sanyaye ta ƙariso cikin ɗakin, ta nufi gefen sa inda Centre table ke ajiye gaban gadon da yake zaune, akai ta ajiye farantin muryan ta na ɗan rawa ta soma gaishe shi, tare da son isar da saƙon abincin daga Mamy

Amma kuma ko ci kanki be ce mata ba

Don haka ta juya da ninyan fice wa ba tare da ta kalle sa ba, sai jin saukar dakakkiyar muryan sa tayi yana faɗin

"Kee Ina zaki je da wani dogon goshin ki a nan wajen? Wa kika bari ya zuba miki?"

Saurin juyowa tayi kanta a ƙasa ta duƙa ta soma zuba masa abincin a cikin Plate, sai da ta gama sannan ta zuba masa Coke cikin Cup; tunda ta san yana so sosai, kuma ko ta tafi zai iya dawo da ita, shiyasa tayi gwanintan zuba masa kar tayi laifi

Mi ƙe wa tayi da zumman tafiya, sai ji tayi an riƙe ta.








😲 _Hmmm wannan salon labarin na daban ne, shin wace ce ma wannan Maimunan? Me ya kawo ta gidan nan har take zaune da ahalin ABUL KHAIRI?_

_shin wace ce Ziya?_

_Ni dai taku JIKAR LAWALI Ni ce nake da amsoshin tambayoyin ku, ku kasance dani don jin ya za'a kaya?_

_kar ku manta comments ɗin ku kaɗai nake buƙata, idan har yayi muku to ina son nima ku faranta min ta hanyar comments, sannan kar ku manta ku yi following ɗina a Wattpad da kuma bakandamiya, sannan ku danna min Vote. Nagode_
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

             *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:* ✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                   𝗣.𝗪.𝗔✍️

*JIKAR LAWALI CE* ✍️

*Wattpad: UmmuDahirah* 👈

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga mahaifiya ta Abar Alfahari na, uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma._ ❤️






*________________________________*

                   *PAGE 2*

*________* Da sauri ta juyo domin a tunanin ta shi ne, saɓanin tunanin ta ashe ƙasan rigan ta ne ya maƙale a jikin Centre table ɗin

Shi ko kallon inda take ma be yi ba, duk da kuwa yana ganin abinda ke faruwa

Jiki na rawa taja rigan ta da sauri, wanda hakan ya ja Centre table ɗin; Cup ɗin dake kai yayi tambal-tambal ya zubo saman cerfet ɗin gaba ɗaya, kasancewar dama a baki-bakin table ɗin ta ajiye. "Innalillahi.." tafaɗa a matuƙar firgice tana kai hannayen ta duka kan bakin ta ta rufe, tare da zaro idanuwan ta kan shi jikin ta na rawa

Zuba mata idanu kawai yayi fuskar sa a murtuke tamkar be taɓa sanin wani fara'a ba

Hakan ne ya sake tsorata ta; ta duƙe ƙasa da sauri, bakin ta na rawa ta soma ba shi haƙuri

Sai dai kamar tana yi da dutse, duk da kuwa be cire idanun sa a kanta ba

Cup ɗin ta ɗauke daga ƙasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login