Showing 36001 words to 39000 words out of 88313 words

Chapter 13 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt

lauyan sa na zo". Sai ta ciro I.D Card ɗin ta ta nuna masa

Ɗan kallon ta ya yi yana gyaɗa kai, kamar yana shirin magana sai kuma yayi shiru yana duba I.D ɗin, bayan ya gama ya miƙa mata yana murmushi yace, "Good Madam, uwa zata kare ɗan ta a court? Abun gunun burge wa! Allah ya taimaka".

"Amin". Tace dashi still fuska babu fara'a

Daga nan kiran ASP ɗin da Case ɗin ke hannun sa DPO ɗin yayi, inda ya faɗa masa, "a bar ta ta shiga lauyan sa ne." don haka aka yi mata jagora har ɗakin da ABUL KHAIRI yake ciki.


       Yana zaune kamar kullum ya haɗe kai da gwiwa ya maƙure a jikin bango, babu abinda yake yi sai tunanin da ya zame masa jiki.. buɗe cell ɗin da ake yi ya dawo dashi hayyacin sa, sai dai be ɗago kai ba bare yaga me shigo wa, illa sake ɗaura hannayen sa da yayi a kansa yana matse wa

Shigo wa Mamy tayi idanun ta a kansa, ko bata ga fuskar sa ba tabbas ta ga sauyi sosai a tare da shi, nan kawai taji hawaye na son cika mata idanu sabida yanda ta ga ya ƙare sosai, fatar jikin sa yayi baƙi alamun wahala. A hankali ta taka izuwa inda yake zaune, bakin ta na motsi amma bata iya cewa komi ba

Ƙamshin turaren ta da bazai taɓa manta shi ba, wanda ya san wajen mutum ɗaya yake iya jin sa, wato mahaifiyar sa, jin sa yasa ya ɗago kai a wani irin firgice don gasgata abinda hancin sa ya jiyo masa, ilai kuwa itan ce tsaye a gaban sa ta zuba masa idanu, shima haka zalika idanun ya zuba mata ya kasa ko motsi, yayinda idanuwan sa suka cika fal da hawaye har suka soma zubo wa saman kuncin sa

"Baba na". Tafaɗa a hankali hawayen itama na zubar mata a fuska, zuciyar ta cinkushe da tsananin tausayin sa na ganin yanda fuskar sa ya yi matuƙar sauya wa, gaba ɗaya fuskar tayi baƙi da rama, ga kumburan da tayi sabida dukan da yake sha, duk ciwuka ne a jikin sa. "Ba..ba na". Ta sake faɗa da rawan murya tana me ɗaura hannun ta ɗaya kan bakin ta

"Mamy". Shima ya faɗa da sauri yana me miƙe wa tsaye, rungume ta yayi yana me fashe wa da wani irin kukan da tunda ya zo cell ɗin be yi irin sa ba, kuka sosai yake yi yana ƙara ƙanƙame ta

While itama tana taya sa, ta kasa rarrashin sa har tsawon wani lokaci, kana kuma ta ɗago sa tana me bin fuskar sa da kallo. "Baba na haka ka zama?"

Lumshe idanu yayi wasu sabbin hawayen na zubo masa, kana ya buɗe a kanta, cikin rawan murya yace, "Mamy.. kin ga ƙaddaran da ta faɗa min ko?.. wlh.. ban aikata ba, wlh ban kashe ta..."

Hannu tasa ta rufe masa bakin sa, kana ta riƙe sa suka zauna a saman bencin dake cikin cell ɗin, shafa kansa tayi hawaye na ci gaba da zubo mata, sai kuma ta soma bin jikin sa tana shafa wa da hannayen ta

Shi kuwa yana kallon ta ba tare da ya ce komi ba, still shima ya kasa tsayar da hawayen fuskar sa

Numfashi taja kafin tace, "na san baka aikata ba Baba na, ko da kowa be yarda da kai ba, Ni bazan taɓa ƙaryata ka ba; domin na san abinda zaka iya da wanda baza ka iya ba, na san ƙaddaran ka ce haka, kuma Allah shi ne zai fitar da kai, insha Allahu duk me bin ka da sharri Baba na; wlh bazai taɓa yin nasara ba".

Kuka ya ɓarke dashi yana me ɗaura kansa saman kafaɗan ta

Bata ce mishi komi ba illa bubbuga bayan sa da take yi

"Mamy na fi kowa sanin haka, na san cewa zaku goyi baya na duk da baku sani ba Ni ne na aikata ko ba Ni ba, amma wlh bani bane, tabbas na san hakan ƙaddara ta ne, amma kuma ji nake yi a raina abinda nayi muku shi ne sila, da ace tun farko na bi zaɓin ku nayi muku biyayya na rabu da ita, da tuni hakan be faru ba, da ace ba na kawo ta gida na da hakan be faru ba..."

"Haka Allah ya so ka dena faɗar haka, na tabbata ko da baka da alaƙa da ita; idan Allah ya so hakan ya faru da kai sai ya faru".

Shiru kawai yayi be ce komi ba illa hawayen da yake yi

Ɗago kansa tayi tana kallon sa, kafin kuma tace, "ba na zo nan bane domin na duba ka, na zo ne a matsayin lauyan ka".

Shiru yayi yana kallon ta shima

Sai ta gyaɗa masa kai kana taci gaba da cewa, "eh na zo nan ne domin na kare ka, don haka ina son sanin komi, ina son na san mene ne ainihin alaƙar ka da yarinyan?".

Sauke kai yayi ƙasa, be san me zai ce ba, a yau yana nadamar mummunan rayuwan da yake yi, ya gummaci mutuwar sa da ace iyayen sa sun san ainihin alaƙar sa da Ziyada, taya zai iya bayyana musu cewa yana rayuwar banza da ita? Yana aikata abinda Allah ya hana? Wannan abun kunya ne a tare da shi, duk da dai be taɓa aikata zina ba, amma hakan babu bambanci a wajen sa, kuma kunyan da zai ji idan ya aikata zinan; shi ne yake ji a yanzu, ji yake yi kamar ya tsaga ƙasa ya burma yake ji...



          Mamy katse masa tunanin sa tayi da dafa masa baya, zuciyar ta na buga wa saboda ganin yayi shiru, tunanin ta ya tafi, "kar dai ace da gaske shi ne ya kashe ta? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" take maimaita wa a zuciyar ta, kana tace dashi, "ka faɗa min gaskiya ABUL KHAIRI, ba na son ka ɓoye min komi, Ni mahaifiyar ka ce, ba zan taɓa gudun ka ba". Ta ƙare maganar da guntun murmushi ganin ya ɗago kai yana kallon ta.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

            *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:*✍️
             _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻‍♀️

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A*✍️

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️




*________________________________*

              *PAGE 22*

*________* Cikin rawan murya ya soma ba ta labarin duk alaƙar su da Ziyada, tun farkon haɗuwar su har irin rayuwar da suke yi da ita, da kuma abinda ya faru a ranan da ya je gidan gonan sa ya tsinci gawan ta

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Shi kawai Mamy take ambata a bakin ta, idanun ta a kansa tamkar za su faɗo don kallon sa

Cikin kuka yace da ita, "wlh.. wlh Mamy iya gaskiya ta na faɗa miki, wlh ban taɓa sanin ta ɗiya mace ba, ina tsoron abinda Allah zai min idan na aikata zina, wlh ban bi son zuciya ta ba..."

Katse sa tayi da faɗin, "baka bi son zuciyar ka ba Yunusa ko kuwa ka bi son ranka? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. wlh ko da wasa wani ya zo ya sanar min da wannan halin naka; wlh sai dai Allah ya bi mini haƙƙi na a kan ƙazafin da yayi maka, domin bazan taɓa yarda dashi ba, amma sai ga shi da bakin ka kake sanar dani?.. Kake sanar dani wai kana aikata wannan mummunar aika-aikan ABUL KHAIRI? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ina wayon ka yaje ABUL KHAIRI? Ina tarbiyyar da muka ba ka? Ashe kana cin amanar mu haka?"

"Mamy don Allah don girman Allah kiyi haƙuri ki yafe min, wlh nayi nadama matuƙa nayi nadama, Mamy bazan sake ba wlh, ki yafe min kinji ki yafe min, ko haka Allah ya bar Ni wlh nayi nadama". Kuka sosai yake yi yana roƙon ta, gaba ɗaya ya susuce ya durƙushe ƙasa yana ta kuka magashiyan

Sosai ya bata tausayi, abinka da uwa da ɗanta, nan ta ɗago sa tana cewa, "ba komi ya wuce, Ni babu abinda zan iya tunda komi ya rigada ya faru, me zan yi to? Haƙurin shi ne ya fi, sai dai kuma ka roƙi yafiyar Allah domin ganin dai-dai a rayuwar ka Baba na, haƙiƙa kayi kuskure matuƙa, tunda har ka zaɓi wannan ɗabi'ar banzan a matsayin waye wa, su ma waɗanda suke yi Allah ya shirye su domin basu san inda kansu ke musu ciwo bane, sun manta cewa za su tashi gaban Allah kuma duk rayuwar su za a nuna shi tamkar t.v, abinda suke tunanin sun yi a ɓoye suna ganin suna da wayau babu wanda ya gani, to, haƙiƙa akwai ranan jin kunya, akwai ranan nadama, kuma dole na sanar da Abban ku komi dole zai sani".



       Mamy sai da ta rarrashe sa sosai domin ya ƙi yin shiru, sai da ta tabbatar da ta kwantar masa da hankali kafin ta tafi. A waje suka ci karo da Sagir shima ya zo

Gaisawa suka yi kafin yace, "Mamy ya ABUL KHAIRIN yake? Na je gida su Batool suka ce min kina nan shi ne na taho, Allah yasa dai yana lafiya?"

Murmushi tayi masa tace, "yana nan lafiya Sagir".

Fuskar sa da damuwa yace, "wlh sun hana Ni ganin sa, na shiga damuwa matuƙa da halin da yake ciki, na san halin ABUL KHAIRI bazai taɓa aikata ko da kisan kiyashi bane bare mutum, mutum ɗin ma Ziyada wacce yake matuƙar ƙauna, Mamy don Allah ku yarda dashi wlh ba shi ne yayi kisan nan ba, duk da Ziyada ƴar uwata ce amma ina goyan bayan Aboki na, na san halin sa bazai taɓa aikata wa ba".

"Kar ka damu Sagir insha Allahu mun fahimce shi, Allah dai ya shige mana gaba kawai, yanzu ma zan wuce in soma aiki na ne a gidan nasa tunda babu lokaci".

"To Mamy bari in raka ki mu je tare".

Mamy ta amsa mishi da, "to" sannan ta wuce motan ta ta shiga

Shima ya shiga nasa yabi bayan ta.



       Kai tsaye gidan gonan suka wuce, inda suka tarar da me gadin a bakin aikin sa

Gaishe su yayi, domin ya san su duk kan su, kuma ya san matsayin su wajen ABUL KHAIRI

Sagir shi yace masa, "su shiga ciki suna son magana dashi ne."

A waje suka bar motan su suka shiga, suka zauna a bencin me gadin; da shi me gadin da Sagir ɗin. Ita kuma Mamy ta zauna a kujeran Robber tana fuskantar me gadin

Kiran sunan sa tayi tace, "Baba Iro zan so ka sanar min komi a ranan da abun ya faru?"

Baba Iro gyara zaman sa yayi ya soma sanar mata da komi, lokacin da Ziyada ta zo gidan, da kuma sanda ABUL KHAIRI ya zo shima, sannan da maganar da suka yi kafin ya shiga cikin gidan, sai kuma abinda ya biyo baya na zuwan ƴan sanda gidan a matsayin an yi kisan kai

Numfashi Mamy taja bayan ta gama rubutun ta, kana ta kalle sa ta sake jeho masa wani tambayar, "Baba Iro a tunanin ka baya ga su; babu wanda ya shigo gidan?"

"Eh gaskiya babu".

"Kuma babu inda kaje?"

"Eh to, na fita gaskiya, domin na zaga bayi sosai a ranan sakamakon gudawa da nake yi, sannan na fita bakin titi saboda rashin kati da babu a waya na, ina son Kiran Matata domin inji lafiyar ɗana da be da lafiya, to a lokacin zan kira ta sai na fuskanci kamar babu kati, shi ne na fita domin na siyo".

Kallon sa kawai Mamy take yi har ya dire maganar sa, kana tace, "to, amma kana da masaniyar wani saɓani da ya shiga tsakanin su a ranan? Ko kuma kafin dai ranan haka? Wanda zai iya jawo wani zargi?"

Baba Iro yace, "eh to, Hajiya Ni dai bazan iya cewa a'a ba ko eh, domin dai na saba ganin saɓani makamanciyar haka, duk da hayaniyar su nake ji a cikin gida, amma kuma a ranan da mummunan abun nan zai faru, ana gobe sun yi wani saɓani da shi, wanda har nan waje suka fito suna faɗa, inda ita Ziyadan take kuka tana ba shi haƙuri amma shi kuma yana sanar mata, "idan ta sake taɓa masa jiki to zai bata mamaki." sannan ya hau motar sa ya bar gidan, ita kuma a lokacin zama tayi tasha kukan ta, har naje ina bata haƙuri amma taƙi kula Ni, inda daga baya kuma ta bar gidan, to, bata sake dawowa ba sai washe gari a ranan da abin zai faru, bayan shi Alhaji ya fita gidan, tunda shi a gidan ya kwana a lokacin".

Bayan Mamy ta gama rubutun ta sai ta sake kallon sa tace, "Bayan haka babu wani abun kuma?"

"Gaskiya babu, domin sun ɗan kwana biyu babu abinda ya shiga tsakanin su, tun wani faɗa dai da suka yi, to kwana ɗaya ne ina ga suka shirya".

Mamy ta sake cewa, "to babu wanda ya shigo gidan a ranan ko kafin ranan? Ko da yaushe su ne kaɗai masu shigo wa?"

Shiru ya ɗan yi yana faman tunani yana zare ido

Sai Sagir da ya nutsu duk yana sauraron su yace dashi, "ana magana, ka faɗa mana komi don Allah domin samun kuɓutar Aboki na, ko meye ma idan ka sani ka daure ka sanar mana".

Baba Iro yace, "eh to akwai wata wacce ta taɓa zuwa kwanakin baya.."

"Wace ce? Shin ka santa?" Cewar Mamy cikin ƙosawa tana me katse masa zancen sa

"A'a ban san taba gaskiya, sai dai ta ce min ita ƙanwar Alhaji ne, kuma na bar ta ta shiga, to, ban dai sake ganin ta ba sai ana gobe abin nan ya faru, ta zo ta ce min saƙo zata amsa a wurin sa".

"Shin baka san sunan ta?" Mamy ta sake tambayar sa

"A'a ban sani ba wlh, sau biyu na taɓa ganin ta, kuma wlh na ga suna yanayi da Alhaji shiyasa na yarda na barta".

"Taya zaka bar ta bayan baka santa ba? Sannan kuma baka damu da sanin me take yi a ciki ba?" Sagir ya faɗa hakan a ɓacin rai

Me gadin na shirin magana, sai Mamy ta katse sa da faɗin, "zaka iya fasalta min kamannin ta?"

"Eh zan iya Hajiya, tana da tsawo dai yarinyan, sannan fara ce, kuma bata da jiki sosai; ƴar matsakaiciya dai".

Shiru Mamy tayi tana tunani, sai kuma ta sake jeho masa tambaya, "a lokacin da take zuwa gidan Tana daɗe wa? Kuma tana tarar da shi ABUL KHAIRIN?"

"Eh duk a lokacin tana tarar dashi, domin har ita Ziyadan a lokacin tana gidan, amma dai ba ta daɗe wa sosai gaskiya, sai dai zuwan ta na biyu ta fi daɗe wa".

"Tom na gode Baba, kayi min magana da masu aikin ciki sai mu tattauna dasu su ma".

"To babu damuwa Hajiya, bari in Kira su". Me gadin ya faɗa yana tashi da sauri ya nufi cikin gidan.




            Babu daɗe wa sai ga su sun dawo tare da masu aikin gidan su uku, domin su kaɗai ne masu aiki yanzu a gidan, da su huɗu ne amma ɗayan ya daɗe da yin tafiya, saboda rasuwan da aka yi musu shi ne ya tafi gida.


    Duka Mamy sai da tayi musu tambayoyi, sannan suka yi sallama suka fito

A nan Sagir yayi mata sallama shima ya wuce gida

Itama kai tsaye gidan ta wuce. Tana shiga Parlour da su Batool taci karo

Ita Batool tana zaune saman Three sitter, ta kwantar da kanta a jikin kujeran tare da lumshe idanu

While Maimuna tana kwance kan One sitter, ta ɗaura kanta a hannun kujera tare da ƙudundune ƙafafuwan ta a saman kujeran, ta tsira wa waje ɗaya ido tana faman tunani, gaba ɗayan su sosai abinda ke faruwa da Yayan nasu ya shige su, barin ma Maimuna, domin ita akwai ta da tausayi, duk abinda zaka yi mata idan har wani abu ya faru da kai, tana nuna tausayawan ta matuƙa, bata da riƙo ko kaɗan, bata damu da ABUL KHAIRI na musguna mata a gidan ba, tausayin sa gaba ɗaya take ji, idan ta zauna tana tunanin, "yanzu haka yana can yana shan duka a wajen ƴan sanda." sai hakan ya riƙa saka ta kuka, ta san shi ba me son wahala bane a rayuwa, ta dinga tunanin, "ko me yake yi yanzu? Ya yake yanzu?"..



         Har sau biyu Mamy tayi sallama amma basu amsa mata ba, gaba ɗaya hankalin su ba ya jikin su, sai da ta shigo ta sake yi kafin suka ɗago kai a tare suna amsa wa

Da kallo ta bi su dashi, kana kuma tace, "tunanin me kuke yi haka har ya ɗauke muku hankali?"

"Babu komi Mamy, sannu da zuwa". Cewar Batool kenan tana kallon Mamyn

Itama Maimuna sannu tayi mata

Ta amsa su tana zama a gefen Batool, sannan kuma tace, "Abban ku be dawo ba?"

"Ya dawo ya sake fita yanzu". Batool ta sake bata amsa

"Ok kawo min ruwa Maimuna".

Tashi tayi da sauri taje ta kawo mata

Amsa tayi tasha da yawa, sannan ta tashi ta wuce ɗaki.



              Dayake tun jiya Ummu ta koma Kaduna, sai ranan da za'a shiga Court za su sake zuwa.



      Babu jima wa Abba shima ya shigo gidan, inda su Batool suka yi masa sannu da dawowa, ya amsa su yana wuce wa ɗakin Mamy

Sallama yayi ya shiga

Mamy dake zaune kan gado ta tuɓe riga tana ɗaura zani a ƙirji, ta amsa mishi sallaman tana kallon sa, kana kuma tayi masa, "sannu"

Ya amsa ta yana zama shima a gefen gadon, sannan yace, "har kin dawo?"

"Eh wlh".

"Ya yake?"

Numfashi taja kana kuma tace dashi, "lafiya..." Sai tayi shiru

Kallon ta yayi yace, "ki dena saka damuwa a ranki kinji? Insha Allahu Allah zai taimake mu".

Amsa mishi tayi da, "Amin" kafin kuma tace, "mun tattauna da Baba na, sannan na je gidan gonan nasa mun tattauna da masu aikin gidan". Nan ta sanar mishi da duk abinda ABUL KHAIRIN ya sanar mata

Shiru Abba yayi be ce komi ba

Hakan yasa Mamy ta kalle sa tace, "baka ce komi ba?"

"To me kike so in ce? Duk abinda ya faru yanzu sai ya ɗau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login