Showing 45001 words to 48000 words out of 88313 words

Chapter 16 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt

❤️




*________________________________*

                *PAGE 25*

*________* ƙarisawa inda take Mamy tayi, sannan ta kalle ta tace, "Azeeza zan so ki yiwa kotu bayanin abinda yake kai ki gidan gonan ABUL KHAIRI ba tare da sanin shi ba?"

Ɗan jim Azeeza tayi kanta a ƙasa, sai kuma ta buɗe baki a hankali tace, "ina zuwa ne domin sa".

"Kamar ya domin sa? Kiyi bayani ne sosai yanda kotu zata fahimce ki".

Cikin muryan kuka Azeeza tace, "wlh Allah ba Ni ce na kashe taba, hasali ma Ni gawarta nazo na tarar a gidan".

Gyara tsayuwar ta Mamy tayi jin abinda ta faɗa, sai tace, "Azeeza ki kwantar da hankalin ki ba wai an ce ke ce kika yi kisan ba, abinda kika sani kawai nake son ki sanar da kotu, sannan me yake kai ki gidan gonan shi?"

Shashsheƙa ta soma yi, daƙyar ta buɗe bakin ta tayi musu bayanin abinda yake kawo ta, da kuma zuwan da take yi tana ganin ABUL KHAIRI tare da Ziyada, wannan dalilin ne yasa itama ta yanke shawaran ta bashi kanta domin ta same shi kamar yanda Ziyada take yi, a ganin ta hakan zai jawo hankalin ABUL KHAIRI ya so ta itama. Shiru tayi a wannan gaɓar sanda  kukan yaci ƙarfin ta

Tsit kotun yayi ana sauraron ta

Sai da taja soconni kafin taci gaba da faɗin, "sai kuma ranan da na dawo na uku sanda ban tarar da Me gadi ba, na shiga gidan kai tsaye nabi ta ƙofa, na je da ninyan in nuna masa videon dana ɗauke su a lokacin da suka yi faɗa, idan be yarda da buƙata ta ba Ni kuma zan kaiwa iyayen sa su ga abinda yake aikata wa, sai kuma ina shiga na ga gawan Ziyada a cikin parlour'n, na ruɗe sosai har ban tsaya ba na fito da gudu na fice a gidan, kuma a lokacin ne na hangi motan ABUL KHAIRI shi kuma ya taho gidan, iyakan abinda na sani kenan".

Kotun yamutse wa da hayaniya suka yi

Sai da alƙali ya dakatar dasu sannan aka natsu, yace da ita, "yanzu ina wayan taki?"

Hannu tasa ta share hawayen fuskar ta da yayi caɓe-caɓe tace, "yana gida".

"Ina buƙatar yanzu aje a taho da wayan nata". Sai kuma ya kalli Mamy yace, "zaki iya ci gaba".

Daga nan Sagir aka kira, wanda shi ne ya bada shedan halayyar ABUL KHAIRI da kuma soyayyar su da Ziyada, ya ƙara da cewa, "duk da na san Ziyada ƙanwa ta ce amma bazan iya ƙala wa aboki na wannan mugun sharri ba, aboki na yana matuƙar ƙaunar ta, ba zai taɓa iya kashe ta ba, tabbas ba shi ne ya kashe taba domin ko ba ita ba bazai iya kashe ƙuda ba bare masoyiyar shi".

"Da haka nake roƙon wannan kotu me adalci ta wanke ABUL KHAIRI daga zargin da ake yi masa a kan shi ne ya kashe Ziyada, wannan ba gaskiya bane, duba da ƙwararan shedu da aka gabatar wanda ko ta wani fanni an tabbatar da cewa ABUL KHAIRI ba shi da laifi, na gode ya me Shari'a". Cewar Mamy tana juya wa ta zauna

Barrister Sharif Alƙali yace, "idan yana da abinda zai ce ya tashi ya gabatar".

Sai cewa yayi "be dashi".

Alƙali bayan ya gama rubutu ya ɗago kai yace, "zamu ɗaga wannan Shari'an zuwa nan da sati ɗaya tunda har yanzu ba'a gano wanda yayi kisan ba, don haka lauyoyi suna da daman da za su je su sake kawo ƙwararan shedu, sannan kuma a tabbatar a ranan an kawo mana videon da Azeeza ta ɗauka domin ganin abinda suka faɗa da idon mu, a kuma ci gaba da tsare ABUL KHAIRI har zuwa ranan". Sai ya buga guduma ya miƙe tsaye

 

Daga nan kowa tashi yayi aka soma fice wa. Wannan zaman ya yiwa masoyan ABUL KHAIRI daɗi sosai, duk da ba sakin shi aka yi ba, amma hakan ya tabbatar musu da cewan ba shi ne yayi kisan ba.



       Washe gari Mamy shirya wa tayi tabi address ɗin da aka bata na shagon me siyar da Simcard, tana zuwa ta ga shagon har yanzu a rufe yake, sai na maƙocin shi dake buɗe, ƙarisa wa tayi tayi masa sallama

Ya amsa yana kallon ta

Tace, "bawan Allah don Allah me shagon nan nake nema?" Ta nuna shagon kusa dashi

"To gaskiya Hajiya nima ban san inda yake ba, saboda nima jiyan nan na dawo daga tafiya, wata na biyu kenan ba na gari sai yau na buɗe shago".

"To da Allah baka san inda ya tafi ba? Ko kana da labarin wani abu game dashi, ko da inda zan same shi ne don Allah?" Mamy tafaɗa tana kallon sa

Shiru yayi na ɗan soconni, yayi kamar yana tunani sai kuma yace, "wlh Hajiya babu inda zan ce miki zaki same shi tunda shi dama ba ɗan nan anguwan bane, ƙauyen su yana can... Me ma yake da suna?" Ya ɗaga kai yana ɗan buga yatsar sa a kan gefen goshin sa. "na manta Hajiya".

Mamy tace, "don Allah ka tuna ka taimaka min abu ne me muhimmanci shiyasa nake neman sa".

Duk yanda ya so ya tuna ɗin amma ya manta, sai ya kalle ta yace, "wlh Hajiya na manta, garin nasu da wahala, domin sau ɗaya ya taɓa faɗa min".

"To amma in tambaye ka? A nan Kanon ne ko kuma a wani gari yake?"

Yace, "a nan Kano yake, sai dai daga ƙauyaku ya taho".

"To babu damuwa, bari in baka number na idan ka tuna sai ka kira Ni ka sanar min, don Allah kayi min wannan alfarman".

"To shikenan insha Allah zan yi ƙoƙari".

Wayan sa ya ciro ya kwashe Numban ta da ta karanto mishi

Sannan tayi masa godiya tare da yin masa alheri ta wuce.


     Kai tsaye gida ta koma, Abba na Parlour shi da su Batool suna hira.

    Sannu da zuwa suka yi mata

Inda ta zauna tana amsa musu tare da zame gyalen ta

Maimuna ta tashi ta ɗauko mata ruwa

Ta amsa ta sha tana amsa tambayar da Abba yayi mata, "a'a Abban su wlh ba'a dace ba, sai dai muna sa rai insha Allah". Nan ta sanar mishi da komi abinda ya faru

Abba yace, "to Allah yasa a dace, Allah ya bayyana gaskiya, baza mu gaji da roƙon Allah ba".

"Amen amen". Duk kan su suka amsa

Mamy tace, "ya kamata Aƙilu ya je ya dawo da su Amir gida tunda an koma school tun wancan satin, ya kamata ku koma school gaba ɗayan ku". Ta ƙare maganar da kallon su Batool

Batool ɗin ne tace, "a'a Mamy don Allah ki bari har a gama Shari'an nan, wlh ko mun je baza mu mayar da hankalin mu ba".

Kallon ta tayi Mamyn tace, "ƙaniyar ki Batool! Ku koma makarantan ki ce baza ku koma ba? Kin san ranan gama Shari'an ne?"

Zumɓuro baki kawai tayi bata ce komi ba

Abba yace, "ai muna sa ran insha Allah wannan zaman da za'a yi shi ne na ƙarshe, ko da ba'a gano wanda yayi kisan ba dole su sake shi tunda bashi da laifi".

"Haka ne Abban su. Amma Ni dai na faɗa muku ku san da sani gobe zaku je school".

Maimuna ce kawai ta amsa

Ban da Batool da take ta zumɓura baki gaba, sai kuma ta kalli Abba tace, "Abba ka saka baki mana Mamy ta bar mu zuwa Monday".

"Allah Batool zan zane ki ba na son rashin hankali, kin san dai yanzu ina ji da kaina ne kar ki saka in ci ƙaniyar ki".

"A'a baza ayi haka ba ke kuma kar ki huce min a kan yara, ban san ki da wannan ɗabi'an ba, Batool Maimuna gobe ku shirya ku je school kuna ji na?"

"Eh Abba". Suka amsa shi su duk ka biyun

"Yauwa ƴaƴan albarka, yanzu ke Maimuna je ki sanar wa Aƙilu ya je ya ɗauko su Baby".

"To Abba". Ta amsa shi tana tashi tsaye ta wuce

While Batool tuni tabi bayan ta itama ta ficeWar ta

Girgiza kai kawai Mamy tayi tana tashi ta wuce ɗaki

Yayinda Abba ya ɗauki remote yana sanja channels.





           Washe gari da yamma sai ga kiran me shagon nan da Mamy ta bashi number, ya sanar mata da sunan ƙauyen da ya tuna

Sosai tayi masa godiya cike da murna, da Abba ya dawo ta sanar masa an dace.


      The next day bayan su Batool sun dawo school ta shirya ta wuce ƙauyen

Koda ta isa da tambaya ta gane gidan sa, ta shiga da sallama

Matar dake tsakar gidan ta amsa mata tana mata lale marhabun

Fuskar Mamy da murmushi ta ƙariso ciki

Tabarma ta shimfiɗa mata tana cewa, "zauna Hajiya zauna".

Zama Mamy tayi sannan matar itama ta zauna, sai suka sake gaisuwa sosai

Mamy tace, "dama wajen Mijin ki Sadau nazo".

"To Allah yasa dai lafiya?" Matar ta tambaya tana kallon Mamy da mamaki

"Lafiya lau wlh, don Allah idan yana nan ki faɗa mishi yayi baƙuwa".

shiru matar tayi har yanzu idanun ta a kan Mamy, sai kuma ta kaɗa kai kamar ƙadangaruwa tace, "bari in Kira miki shi yana ɗaki ne yana barci".

"To na gode".

Koda matar ta dawo sai ta dawo da ruwan sha, ta ajiye mata a gaban ta tana faɗin, "ga shi nan zuwa, ga ruwa Ki sha".

Mamy godiya tayi mata, kafin ta ɗauki ruwan ta ɗan sha kaɗan gudin kar tace ƙyamar su take yi, duk da hankalin ta be kwanta da ruwan ba

Sosai kuwa matar taji daɗi, ganin yanda Mamy bata nuna ƙyamar su ba ta sha ruwan gidan su a matsayin ta na ƴar gayu

Lokacin ne Sadau ya fito yana hamma, ganin Mamy sai ya bi ta da kallo kafin yace, "ke ce baƙuwar tawa Hajiya?"

"Eh Ni ce".

"To sannu da zuwa amma ban waye ki ba?". Yayi maganar cikin fara'a

"Haka ne, amma idan babu damuwa zan so in yi maka bayanin kai na". Mamy tafaɗa tana kallon sa

Jinjina kansa yayi kafin ya kalli Matar tashi yace, "bamu wuri Kande". Sannan ya ƙarisa ya zauna a saman turmin dake kusa da inda Mamy ke zaune

Ita kuma tuni Kanden ta wuce madafa kasancewar dama girki take yi.



       Gyara zaman ta Mamy tayi tace, "suna na Barrister Khadeejah Yunusa Ubale, idan babu damuwa don Allah ina so kayi min bayani a kan wani layi da aka zo aka siya wurin ka, kuma kai ne kayi registern Numban a ranan".

"Amma Hajiya Ni ya zan yi in san waɗanda suka siya layi a wuri na har nayi musu register? Ni wajen wata ɗaya kenan rabo na da zuwa birni buɗe shago".

"Eh haka ne naji labarin hakan wajen me shagon kusa da kai, amma ai na san da dalilin rashin zuwan ka, kuma ina maka maganar tun wancan watan ne aka siyi layin, ka ga kuwa a wurin ka aka siya".

Zazzare idanu yayi yana share zufa yace, "amma Hajiya mene ne alaƙa ta da ke da har zaki zo min gida nema na? Ni ban ga abun da nayi ba".

Murmushi Mamy tayi tace, "ba wani abu bane ya kawo Ni wajen ka ba Malam Sadau, idan har zaka bani haɗin kai zan yi maka tambayoyi ne kaɗai in tafi, in kuma ka fi son ƴan sanda su yi maka tambayoyin fine babu matsala, saboda yanzu haka neman ka suke yi shiyasa ka gudu".

Shiru yayi har yanzu zufa na keto masa, sosai cikin sa ya ɗuru ruwa

Mamy jakar ta ta buɗe ta ciro Numban da aka rubuta a cikin takarda, "na san kana da bayani a kai da kuma ranan da aka siya, don haka kayi min bincike".

"Ai Hajiya ba sai ma nayi bincike ba tunda na san wanda ya siya layin, kuma sanadin hakan na baro aiki na tsawon wata ɗaya da satikai yanzu". Sai da ya ɗan goge fuskar sa kafin yace, "Alal haƙiƙa wani ne yazo ya siya Simcard a wuri na har nayi masa register, bayan kwana biyu sai ya dawo ya bani kuɗi har dubu ɗari yace min in bar buɗe shago har na wani lokaci, sabida idan har naci gaba da buɗe wa tabbas da yiwuwar ƴan sanda za su zo su kama Ni, kuma ko da sun tambaye Ni bayani a kanshi bazan san shi ba, don haka yake bani shawara in Yi abinda yace min. To, Ni kuma gaskiya na tsorata a tunani na shi ɗin ɗan kidnapping ne za'a bi diddigin inda ya yi registration azo a kama Ni, wataƙil ma ace har dani tunda na san yanzu abubuwa sun ci gaba, abu kaɗan ne zai saka a san inda ya siya layin, sai na amshi kuɗin da yayi min tayi a ranan na kulle shago na na dawo ƙauyen mu, daɗin da naji ma ba'a cikin gari nake ba kuma babu wanda ya san inda nake sai me shagon kusa dani, shima sau ɗaya muka taɓa hira dashi har na faɗa masa inda nake, a tunani na bazai iya tunawa ba ma tunda abun ya daɗe, wlh iya abinda na sani kenan kar ki daɗa kar ki raga". Ya ƙare maganar kamar zai yi kuka duk ya gama haɗa gumi yana faman fifita da hannayen sa

"Idan muka je can da kai zaka iya gane shi?"

"Taya zan gane shi Hajiya bayan sau biyu na taɓa ganin shi? Kuma ban san ma inda zan ganshi ba a halin yanzu, mutum daga zuwa siyayya wuri na sai azo ana titsiye Ni?"

"Ba maganar titsiye ka bane bawan Allah, idan har ka taimaka kamar kayi jihadi ne domin ta sanadin ka za'a kama wanda yayi kisan, kuma na tabbata shi wanda ya siya Simcard ɗin a hannun ka shi ne wanda yayi kisan". Cewar Mamy cikin kwantar da murya

"Innalillahi... Kisa kuma? Hajiya don girman Allah ki fitar dani a wannan maganar wlh ban san inda yake ba, ki yiwa Allah ki yiwa Annabi".

Ganin ya ruɗe sosai sai Mamy ta sake kwantar da murya tana cewa, "don Allah Mlm Sadau ka kwantar da hankalin ka, ba wani abu bane nace zaka bi Ni can saboda ka ba da shaida ne, Ni ko baka je kotu ba na san zaka iya cin karo da mutumin, ka ga idan ka nuna min shi shikenan aikin ka ya ƙare, nayi maka alƙwari zan ruɓa maka abinda ya baka har sau biyu".

"To Hajiya amma ke taya kike ganin zan ganshi? Garin Kano fa ba ƙaramin gari bane?"

Shiru Mamy tayi tana tunani, sai kuma tace, "to shikenan na gode, amma don Allah idan da hali zan dawo zan iya neman ka".

"To.. to babu damuwa, nima na gode". Ya faɗa yana me yaƙe haƙora

Sallama suka sake yi har da matar shi, sannan ta fice tahau motan ta ta wuce gida, a ranta duk tunani ya cika ta, "waye to wannan mutumin da yayi kisan? Taya zata iya gane shi? Ya zata yi ta fitar da ABUL KHAIRI a wannan zargin da ake mishi? Ta tabbata duk wanda yayi kiran shi ya sanar masa da kisan, sannan kuma ya kira ƴan sanda tabbas shi ne wanda yayi kisan. Kuma da ikon Allah sai tayi iyakan bakin ƙoƙarin ta."
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

*ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻‍♀️

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️




*________________________________*

*PAGE 26*

*________* Mamy har ta kusa isa gida sai kuma ta juya kan motan ta ta koma ƙauyen nan, tana yin parcking shi kuma Sadau ya fito

Ganin ta sai ya tsaya nan bakin ƙofar gidan har ta fito ta same shi

"Malam Sadau nayi mantuwa ne, idan babu damuwa ina son kayi min kwatancen yanayin mutumin don Allah, hakan zai sake taimaka min ƙwarai".

"To shikenan bari in kwatanta miki shi, Mutumin dogo ne kuma yana da kauri, don zan iya ce miki kamar fasalin jiki na, kuma baƙi ne shi yana da yawan gashi a fuskar sa, amma ba ya barin gashi sosai a kanshi, sannan gashin giran sa sun haɗe waje ɗaya, iyakan abinda zan iya faɗa miki kenan gaskiya, amma dai gaskiya ɗan gayu ne sosai".

"To amma a mota yazo wurin ka?"

"Eh a mota yazo wuri na, sai dai motan da yazo dashi sanda ya siya Simcard a wuri na daban ne da wanda ya dawo yace dani na gudu nabar buɗe shago na ɗan wani lokaci".

"Yi min bayani don Allah wani irin mota ce? Ya kuma sunan su?"

"Hajiya wlh ban san sunan motocin ba, Ni dai na san motan farko baƙa ce, sai kuma ta biyun kalan ruwan goro ce me ɗan fatsi-fatsi".

Numfashi Mamy taja kafin tace, "Nagode sosai da bayanan ka Sadau Allah ya saka. Ga wannan ka ƙara na gode".

Washe baki yayi ya amshi kuɗin jikin sa na rawa shima yana bin ta da godiyar

A haka Mamy ta wuce tahau motan ta taja ta koma gida, tana shiga cikin parlour'n da sallama

Baby ta soma ganin ta ta ruga aguje ta rungume ta tana mata sannu da zuwa

"Yauwa Auta na".

Shima Amir yayi mata sannu da zuwan

Ta amsa tana shirin tambayar sa su Batool sai ga su sun fito daga kichen a tare

"Mamy sannu da zuwa". Cewar Maimuna tana amsar Jakar ta

Itama Batool tace, "Oyoyo Mamy sannu da dawowa".

Duk amsa musu tayi kafin ta tambaye su Abban su?

Baby tayi saurin cewa, "Mamy yanzun nan suka fita shi da Yaya Sagir".

"Ok to sake Ni inje ɗaki".

Sakin ta tayi sai dai tabi bayan ta tana faman tsalle tana cewa, "Mamy tsaraba na".

"Auta ba anguwa naje ba, aiki naje yi kin ji".

Shagwaɓa ta soma mata tana bin ta duk inda tayi a ɗakin

Bata kula ta ba har sai da ta zauna tana janyo computern ta, ganin zata takura mata sai tace, "je ki wajen Maimuna ta baki sweet a cikin na school ɗin ki, yi maza ki je".

Ai kuwa da gudu ta fice, ganin basu a Parlour sai ta nufi kichen

Suna ciki kuwa suna girkin dare, ita Maimuna ne take girkin, while Batool ta zauna a kujeran Robber tana latsa waya tana bata labarin abin dariyan da ta gani cikin group ɗin *MATA ADON

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login