Showing 39001 words to 42000 words out of 88313 words

Chapter 14 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt

izna, yanzu zai gane abinda yake aikata wa dai-dai ne ko ba dai-dai ba, duk abinda mutum zai ɓoye wa Mutane Allah ƙyale sa kawai yake yi, domin duk ranan da ya so tona masa asiri lokaci ɗaya zai yi, ba a masa wayau ko dabara". Yana gama faɗar haka ya miƙe zai fice

Mamy ta kira sunan sa tace, "Abban su don Allah kar kayi fushi dashi, don Allah".

Murmushi yayi bayan da ya juyo yana kallon ta, sannan yace, "ba fushi zan yi dashi ba Addan mu, abinda ya faru ma dashi ya ishe shi ishara, zan fita Parlour ne ko ba wanka zaki yi ba?"

"Eh wanka zanyi".

"To ki gama akwai maganar da zamu tattauna ma".





"To". Tace dashi tana me miƙe wa tsaye ta wuce Toilet.




🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

            *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:*✍️
             _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻‍♀️

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A*✍️

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️




*________________________________*

              *PAGE 23*

*________*  *MONDAY*
            *RANAR SHIGA COURT*

            Ƙarfe 02:30pm. A lokacin court ɗin da za'a gabatar da Shari'ar na cikin garin Kano ta cika maƙil, gaba ɗaya ahalin su sun iso wajen, har su Ummu da Aunty Fatima tun safe suke Kano, haka ma Uncle Abbas yau ya iso Kanon, tare da matar sa Safiyya suka zo, su Umma Salamatu, Umma Hassana, Umma Hussaina duk sun zo, haka ma Alh. Sunusi da Hajiya Falmata su ma suna cikin court ɗin, ita dai Hajiya Mama ta gaza zuwa domin hankalin ta a tashe yake matuƙa, baza ta iya ganin shari'ar ba. Zee itama Abba ya hana ta zuwa sabida cikin dake jikin ta, su Maimuna ma suna ciki, kai duk wasu masoyan su sun hallara a court ɗin har Inna Aliya ta zo,  ita da Inna Maria duk sun zo, in ka ɗauke Inna Halisa da su Umma Sulaima da Uncle Sani su ne kawai basu da ninyan zuwa.


         Alƙali na isowa aka tashi aka yi masa gaisuwar ban girma, kana suka zauna bayan ya zauna

A lokacin ƴan sanda suka iso da ABUL KHAIRI dake cikin Hand cuff, aka shigar dashi ɗan zagayen da ake ajiye masu laifi, ko kuma waɗanda ake musu tambayoyi

Maga-takarda ya miƙe ya soma jawabi kamar haka: "A yau June ɗaya ga wata, shekara ta dubu biyu da ashirin da ɗaya. 1 June 2021. Zamu saurari ƙara wanda Alh. Muh'd Iyaal ya shigar, a kan kashe masa ɗiya da Yunusa Hayat Sunusi yayi a gidan sa na gona dake bakin titi G.R.A". Sai ya miƙa wa Alƙali File ɗin

Amsa yayi yana gyara zaman sa, tare da gyara zaman Eyeglasses ɗin sa ya soma duba wa. Ɗago kansa yayi bayan ya gama yana kallon jama'ar wurin sannan yace, "Ina lauyoyin? Su gabatar da kan su".

"Suna na Brr. Sharif Muhammad El-emam, Ni ne lauyan dake kare masu kawo ƙara".

"Ni kuma suna na Brr. Khadeejah Yunusa Ubale, Ni ce me kare wanda ake zargi".

Rubutu Alƙali yayi kafin ya ba su damar su soma

Brr. Sharif ne ya miƙe ya soma magana, "Ya me girma me Shari'a, Yunusa Hayat Sunusi wanda aka fi sani da ABUL KHAIRI, saurayi ne ga Marigayiya Ziyada Alh. Muh'd Iyaal, kuma shi ne wanda ya kashe ta da hannun sa.."

"Of jection my low, Brr. Sharif Yana son ɗaura wa ABUL KHAIRI laifi bayan kuma zargin sa ake yi, har yanzu ba'a gano gaskiya ba".

"Ka gyara kalaman ka Barrister". Alƙali yace dashi

"Na gode ya me Shari'a". Yayi maganar cikin girmamawa, kana ya gyara wuyan rigan sa yaci gaba da faɗin, "ya me Shari'a ABUL KHAIRI shi ne saurayin Ziyada, kuma a gidan gonan sa dake bakin titi G.R.A aka samu gawan ta, sannan ƴan sanda sun same sa a lokacin da suka isa gidan gonan nasa, sun tarar dashi riƙe da wuƙan da ya kashe ta a hannun sa, kana kuma likitoci sun yi bincike a kan sawayen hannayen sa; kuma bincike ya nuna tabbas shi ne ya kashe ta, domin shi yayi amfani da wuƙar, ya me Shari'a muna son kamar yanda kotun nan take da adalci; ta yiwa ABUL KHAIRI hukunci dai-dai da abinda ya aikata, na gode ya me Shari'a". Sai ya koma ya zauna bayan ya miƙa wasu takardu ga Maga-takarda

Itama Mamy miƙe wa tayi kana ta soma magana, "Ya me Shari'a abinda ake zargin ABUL KHAIRI da cewan shi ya kashe budurwan sa wannan ba gaskiya bane, samun gawan ta cikin gidan sa ba shi ne zai tabbar da cewan shi ne ya kashe ta ba, hasali ma ABUL KHAIRI ya isa gidan ne bayan da aka yi masa waya a kan yaje gidan gonan sa akwai abinda ke faruwa, kuma ya isa gidan inda ya tarar da gawan ta, ruɗe wa ya saka shi ɗaukar wuƙar ba tare da ya san me zai je ya dawo ba, kuma ya me Shari'a a lokacin ABUL KHAIRI ba sa tare da Ziyada, domin saɓani ya shiga tsakanin su, shi kansa be san meyasaka ta shigo gidan ba, ya me Shari'a ta ya idan ABUL KHAIRI ne yayi kisan za'a kira sa a sanar masa yayi gaggawar zuwa gidan akwai abinda ke faruwa? Sannan ta ya ƴan sanda suka san abinda ke faruwa bayan ko ma'aikatan gidan basu san da cewan yayi kisan ba amma kuma labari har ya je ga ƴan sanda? Ya me Shari'a kamata yayi kotu tayi duba da idon basira domin gano ainihin wanda yayi kisan amma ba ABUL KHAIRI ba, wasu ne kawai suke ƙoƙarin laƙaba masa kisan domin ganin bayan sa, na gode ya me Shari'a". Koma wa tayi ta zauna

Inda Alƙali yayi rubutu bayan ya duba file ɗin da aka sake miƙo masa, sai kuma ya ɗago kai yace, "Kotu na buƙatar ƴan sanda su yi bayanin ta yanda suka san an yi kisan kai a gidan sa har suka je can?"

ASP wanda binciken yake hannun sa ya fito ya tsaya a gaban court ɗin

Inda Alƙali ya buƙata yayi bayani

Yace, "ya me Shari'a muna zaune a Office aka yi kiran mu da wata baƙuwar number, aka sanar mana akwai wani wanda yayi kisa a bakin titi G.R.A mu yi gaggawar zuwa, wannan yasa na ɗauki abokan aiki na muka isa gidan domin tabbatar da abinda aka sanar mana, kuma mun je mun tarar da shi ABUL KHAIRI a gaban gawan Ziyada riƙe da wuƙa a hannun sa, wannan yasa muka kama shi muka wuce dashi Station".

Rubutu Alƙali yayi kana ya ɗago yace, "shin kun yi bincike a kan wanda ya kira ku?"

"Eh ya me Shari'a, daga baya mun yi bincike ba mu samu komi ba, kuma alama ya nuna mana layin ta dena amfani gaba ɗaya, har dai yanzu muna kan bincike da inda aka siya Simcard ɗin".

"Ok zaka iya zuwa ka zauna". Cewar Alƙali bayan ya rubuta jawabin nasa. "Lauyoyi za su iya ci gaba da kawo shaidun su".

"Ya me Shari'a ina neman izni a bani damar yiwa ABUL KHAIRI tambayoyi". Cewar Brr. Sharif da ya miƙe

"Kotu ta baka dama". Alƙali ya ba shi amsa

Isa yayi gaban kantan da ABUL KHAIRI ke ciki, wanda tun soma shari'ar kansa ke ƙasa be ɗago ba, shiyasa baza ka iya gane a halin da yake ciki ba

Brr. Sharif yace dashi, "ABUL KHAIRI zan so ka yiwa kotu bayanin alaƙar ka da ita Marigayiya, da kuma abinda ya jawo saɓani a tsakanin ku ana gobe zata mutu?"

Ɗago kai ABUL KHAIRI yayi idanun nan nasa sun kaɗa sun yi jazur, duk me imani idan ya gansa sai ya tausaya masa, tamkar dai ba shi ba, ya sauya ya gama fita hayyacin sa gaba ɗaya, kai da gani ka san yana a cikin tashin hankali tsantsa

Su Batool da su Umma Salamatu har sharan hawaye suke yi a yanzu ɗin, domin tunda abun ya faru ba su ganshi ba sai yanzu

Be iya magana ba sai da Brr. Sharif ya sake maimaita masa tambayar kana yace, "kotu tana sauraron ka kana ɓata mana lokaci ABUL KHAIRI."

Murya a dishe ya buɗe baki a hankali ya soma magana, wanda ba kowa yake ji ba

Dole Alƙali yace dashi, "ka ɗaga murya ba ma jin ka".

Hakan yasa ya sake ɗan ɗaga murya kaɗan, duk da haka muryan ba ta fita sabida ta rigada ta disashe, kukan da yake sha da kuma kwana a inda be saba ba; shi ya haifar masa da wannan yanayin

Tiryan-tiryan ya soma bayar da labarin soyayyar su, sai dai be faɗa alaƙar dake tsakanin su ba, har zuwa ranan da suka yi faɗa ya kore ta, kana kuma washe garin ranan ya zo ya tarar da gawan ta

Murmushi Brr. Sharif yayi yace, "kenan kana so ka ce mana ba kai ne kayi kisan ba? Amma to ya aka yi gawan ta yazo gidan ka? Infact ma ya aka yi wani ya zo har gidan ka ya kashe ta bayan kai ne me gidan, kuma kai ne ke da damar shiga ciki?"

Shiru ABUL KHAIRI yayi ba tare da ya amsa ba, illa runtse idanu da yayi yana tunano ranan da abun ya faru, masoyiyar sa a kwance babu rai, yayinda shi ne ake zargi da kisan nata

"Muna sauraron ka fa ABUL KHAIRI? Nan fa kotu ne ba wajen wasa ba, ka buɗe baki ka yiwa kotu bayanin yanda aka yi ka kashe Ziyada, idan kuma kana son ɓata wa kotu lokaci ne sai ka faɗa mana, bamu da time ɗin wasa a nan. Shin mene ne ainihin abinda ya haɗa ku wanda yaja faɗa a tsakanin ku a ranan? Wanda kowa ya san ku masoya ne meyasa kuma a ranan kuka yi baram-baram? Hakan na nufin kai ne ka kashe ta kenan?"

"Ya me Shari'a Barrister ya dena kausasa kalaman sa ga ABUL KHAIRI, hakan zai zamo barazana a gare sa har ya faɗa abinda ba shi ne ba". Mamy tafaɗa lokacin da ta tashi a fusace, domin sosai zuciyar ta ke ƙuna tana jin baƙin ciki da abinda ke gudana ga ɗan nata, ko kaɗan ta kasa control ɗin kanta, wanda hakan ba halin ta bane, amma bata san meyasa yau take matuƙar jin haushi ba, ƙiri-ƙiri tana gani ana son laƙaba wa ɗanta kisan kai, wanda hakan yasa ta kasa jurewa

"Ka kiyaye Barrister, sannan kaima ABUL KHAIRI ka amsa wa kotu tamboyin da yake maka, domin shirun ka na nufin raini ne ga kotu". Cewar Alƙali yana kallon ABUL KHAIRIN

Shiru dai ABUL KHAIRI yayi be ce komi ba

Hakan yasa Brr. Sharif yace masa, "muna sauraron ka, wani saɓani kuka samu?"

Daƙyar ya buɗe baki ya soma sanar musu da abinda ya faru sanda yake Office, text ɗin da aka yi masa da kuma hotunan da aka tura masa, wannan yasa ya isa gidan gonan sa har suka samu saɓani da Ziyada, kuma ya yanke alaƙar su tare

Alƙali yace, "ina buƙatar wayan sa yanzu domin bincika gaskiyar zancen sa".

ASP ya miƙe ya sanar da cewan, "ya me Shari'a wayan sa ta samu matsala sakamakon faɗin da tayi a ranan da muka je kama sa ya saki wayan, yanzu haka tana office".

"To ya kamata a kai gyara domin tabbatar da abinda yake faɗa a zama na gama". Cewar Alƙalin

Brr. Sharif yace, "ya me girma me Shari'a ABUL KHAIRI zai iya shirya wannan ƙaryan ne domin ganin babu idon Marigayiya, kuma babu ta yanda za'a yi a tambaye ta, shiyasa ya shirya wannan ƙaryan da son laƙaba mata sharrin fasiƙanci, wanda kuma shi ne mutumin da yake tare da ita a ko da yaushe, Ziyada bata da wani saurayi da take kula wa sai shi, kuma iyayen ta sun tabbatar da hakan, abun mamaki koda aka kai ta asibiti a sanda abun nan ya faru, likitoci sai da suka yi binciken gawan ta, inda suka gano tana ɗauke da ciki, ta mutu tare da cikin ABUL KHAIRI, shi ne kaɗai take mu'amala dashi kuma cikin nasa ne, yana son kawai ya zame kansa ne tare da ƙulla mata sharri".

Nan kotu ta hautsine da surutu, inda Alƙali kuma ke ta faman rubutu, sai da ya ɗago ya tsawatar musu kana yace da Brr. Sharif, "shin kana da shaidan hakan?"

"Eh ya me Shari'a, a bani damar gabatar da doctor ɗin da ya duba ta domin jin cikakken bayani daga bakin sa".

"Kotu ta baka dama".

"Na gode ya me Shari'a". Yafaɗa cikin girmamawa

Inda Maga-takarda ya miƙe yayi kiran doctor ɗin

"Kotu zata so jin cikakken sunan ka, da kuma bayani gamsashshe game da binciken da kuka yi a kan gawan Ziyada?". Brr. Sharif ya faɗa hakan sanda yake gaban Doctor

"Suna na Dr. Aliyu Mu'awiyah, Ni ne likitan da nayi bincike a kan gawan Marigayiya Ziyada Alh. Muh'd Iyaal, mun gano tana ɗauke da ciki a jikin ta har na tsawon watanni uku, ga kuma bayanan". Doctor ɗin yayi wannan furucin yana miƙa takardun hannun sa ga Barrister

Amsar takardun Brr. Sharif yayi, yaje ya miƙa aka ba wa Alƙali, shi kuma sai da ya gama duba wa kana yace, "idan Brr. Khadeejah tana da tambayar da zata yiwa Doctor zata iya gabatar wa".

Brr. Sharif koma wa yayi ya zauna

Ita kuma ta tashi ta nufi inda doctor yake, fuskar ta babu walwala ko kaɗan jin ƙazafin da ake son ƙara liƙa wa ɗanta, "kana da tabbacin cikin jikin ta na ABUL KHAIRI ne? Wani shaida kake dashi da zai tabbatar da hakan?"

Shiru Doctor Yayi don be da tace wa

Sai Brr. Sharif ya miƙe yace, "ya me Shari'a be kamata Barrister tayi wannan tambayoyin ba, domin kuwa an tabbatar da cewar ABUL KHAIRI kaɗai shi ne saurayin Ziyada, kuma iyayen ta sun tabbatar min da haka, babu wanda ya taɓa zuwa wajen ta illa shi, don haka wannan cikin nashi.."

Katse shi tayi cikin fusata da faɗin, "ya me Shari'a babu ta yanda za'a yi a tabbatar da cikin nan nashi ne don kawai shi kaɗai ne saurayin ta, kamar yanda ABUL KHAIRI ya faɗa an turo mishi hotunan ta da na wani, dole hakan zai tabbatar mana da cewan tana tarayya da wasu ba tare da sanin iyayen ta ba.."

Shima Brr. Sharif ɗin amshe maganar yayi da zafin rai yace, "ya me Shari'a Barrister Khadeejah tana ƙoƙarin dole sai ta laƙa wa Ziyada sharri ne, tunda har iyayen ta suka tabbatar da cewan ba ta mu'amala da kowa, dole cikin nan nashi ne, Ziyada ba ta fita ko ina sai da yardan iyayen ta, kuma daga makaranta sai makaranta, taya za'a ce tana mu'amala da wasu mazan ba tare da sanin iyayen ta ba?".

Kallon sa Mamy tayi cike da baƙin ciki, zata yi magana sai Alƙali ya buga musu gudumar sa

"Ya isa haka, Barrister Sharif zaka iya zama, ka bar ta tayi tambayoyin ta suna bisa kan tsari".

Zama yayi cike da takaici

Wanda hakan kuma ya sanyaya wa Mamy rai, sai ta mayar da hankalin ta kan Doctor tace, "Ina jinka Doctor, ya aka yi ka san cewa cikin jikin ta nashi ne?"

Doctor yace, "gaskiya Ni ban sani ba, amma dai bincike ya nuna mana tana da ciki a jikin ta".

"Good, to babu ta yanda za'a yi ku bincika cikin na wane ne? Ai ana yin gwajin NDA ko?"

"Eh akwai halin yin hakan, sai dai matsalan tun farko ba muyi hakan ba, kuma ga shi babu yanda za'a yi a dawo da gawan ta. Kuma dai an fi yin hakan bayan haihuwa ne".

Murmushi Mamy tayi, kana ta juya ga Alƙali tace dashi, "ya me Shari'a wannan ƙazafin cikin da ake son liƙa wa ABUL KHAIRI, basu da wani shaidan da zai tabbatar cikin sa ne, duk da an san cewa shi kaɗan ne saurayin ta, amma babu wanda ya san ko tana mu'amala da wasu mazan a ɓoye ko kuma ba ta yi? Don haka ya me Shari'a ayi duba da rashin hujja da basu dashi, a wanke ABUL KHAIRI daga zargin shi ne wanda yayi mata ciki, na gode ya me Shari'a". Ta koma wajen zaman ta ta zauna

Alƙali yayi rubutu kana ya ɗago yace, "kotu tana buƙatar Brr. Sharif ya kawo ƙwararan shaidu da suka ga lokacin da ABUL KHAIRI yake mu'amala da Ziyada, wanda hakan ne kawai zai tabbatar wa da kotu shi ne yayi mata ciki, idan babu, to, kotu tayi watsi da zancen". Sai kuma yaja fasali yaci gaba da cewa, "zamu ɗaga sauraron wannan Shari'an zuwa nan da sati biyu masu zuwa". Sai ya buga gudumar sa

Mutanen kotun suka tashi suna me giramama sa

Yana fita ƴan sanda suka tasa ƙeyan ABUL KHAIRI suka yi waje dashi

Mamy na tsaye tana kallon sa idanun ta sun cika taf da hawaye

Abba ne ya zo wajen da take, ya dafa kafaɗan ta

Hakan yasa ta juyo tana kallon sa, wanda hawayen ta suka sami damar zubo wa

Shima ƙarfin hali yake yi, ya sakar mata murmushi don ƙara mata ƙwarin gwiwa yace, "kin yi ƙoƙari Addan mu, Allah ne zai fito dashi insha Allahu, baza mu sare ba kinji? Ki dena zubar da hawayen ki yanzu lokacin juriya ce". Daga nan hannun ta yaja suka yi wajen su Ummu

Babu wanda ya samu halin magana har suka fito, haka haraban kotun ya cika da jama'a, har da ƴan jarida suna ɗiban labarai

Kai tsaye Abba wajen motan su ya nufa da Mamy, ko kaɗan be bari ƴan jarida sun yi mata tambayoyi ba. Suka shige motocin su suka yi gida, kai tsaye gidan su Abba suka wuce gaba ɗaya har su Alh. Sunusi.

      Bayan sun isa, a nan ne Alh. Sunusi ya sake ƙarfafa wa Mamy gwiwa, ya kuma musu nasiha tare da fatan alheri, kana suka wuce shi da Hajiya Falmata

Su ma su Umma Salamatu basu daɗe ba suka tafi gida, sai kuma ranan da za'a sake zaman kotu

Haka ma su Ummu bayan sun huta sosai, sai suka wuce gidan mahaifiyar su Hajiya Mama, inda a nan za su kwana washe gari su koma garin su, su ma sai ranan da za'a sake zaman kotu na biyu za su sake zuwa.


       Su Batool bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login