Showing 24001 words to 27000 words out of 88313 words
Chapter 9 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt
ta haƙura, Mamy tace, "Ni Ina ga, ba sai lallai sai da Baba na zamu iya haɗa zumunci ba, Allah ya sani na so mu ga wannan al'amarin ya ƙullu, sai dai tunda ya ƙi haka zamu bar sa kamar yanda yake so, ina ga idan Sulaiman da Batool za su iya amince wa sai mu mayar da akalan zumuntan namu ta nan, amma ba ina nufin su ma a matsa musu bane, mu bi abun a sannu mu sanar musu, idan sun amince shikenan sai ayi".
Sosai Ummu tayi farin ciki da maganar, ta ce, "shikenan Adda Allah ya tabbatar mana da alkhairi, insha Allahu duk yanda mu ka yi da Sulaiman ɗin zaki ji".
Daga nan sallama suka yi, ko wannen su ya ji sanyi a ransa, tunda sam sun manta da ko ba da ABUL KHAIRI ba za su iya yin haɗin zumuncin su, tunda ba shi ne kaɗai namiji ba.
Yaran Ummu su Takwas ne, amma biyu sun rasu. Aunty Naana _(Nana Aminatu)_ ita ce ta farko, sai Aunty Rufaida, ita ce sa'ar ABUL KHAIRI, kuma duk sun yi aure ko wacce da yaranta, sannan sai Sulaiman shi ne ɗa na uku wajen Ummu, shekara biyu da rabi ABUL ya ba shi, sannan sai twins da tayi Hassana da Hussaini, sai da suka girma kafin suka rasu gaba ɗayan su, daga su ne tayi Aliyu sannan ita Maimuna, sai kuma autan su Yunusa takwaran ABUL KHAIRI, amma su suna kiran sa da Shureim.
▪️▪️▪️
Koda Abba ya dawo haka Mamy ta zayyane masa abinda ke faruwa, sosai ran Abba ya ɓaci har yake mamakin har yaushe ABUL KHAIRI ya kai da za su yi mishi magana a kan abu, amma ya ce ba ya so bazai bi umarnin su ba?
Yanda Abba ya ɗau zafi, sai Mamy ta koma rarrashin sa, duk da be kai ta jin zafin abun ba a ranta, sai dai kasancewar ta me haƙuri da danne abu a rai shiyasa bata fito da ɓacin ranta a fili ba
Sai da taga ya sauko sosai sannan tayi masa maganar haɗin da suke so su yi na Sulaiman da Batool. Yayi na'am da maganar sai dai sun ajiye maganar ba yanzu za su sake tayar da maganar ba, za'a bari bayan sun gama school ɗin su, tunda shi dama Sulaiman yanzu yana N.Y.C.E ne, in yaso idan ya amince shima sai a turo sa nan ɗin, ya nemi soyayyar Batool ɗin ba tare da su sun faɗa mata za su haɗa su ba, da haka suka bar maganar.
Amma da dare sai da Abba yayi ma ABUL KHAIRI zaga-zaga, sannan ya ce, "ya ba shi dama ya kawo zaɓin nashi, maganar kuma Maimuna an soke".
Farin cikin da ABUL ya shiga har ya kasa ɓoyuwa, domin be damu da faɗan Abban ba, duk da kuwa ya ga rashin jin daɗin iyayen nashi ƙarara a fuskar su, amma be damu ba, sai ya faɗa musu yanda Daddyn Ziyada ya ce mishi a kan "bazai aurar da ita yanzu ba, sai nan da shekara biyu masu zuwa".
Abba cike da ɓacin rai ya ce, "to Ni kuma ban yarda ba, na baka nan da watanni uku ka kawo min matar da zaka aura, idan ba haka ba wlh tallahi sai ka auri Maimuna, kaji na rantse maka".
Sosai ABUL KHAIRI ya sake shiga damuwa da jin abinda Abba ya faɗa ɗin, ba shi kaɗai ba har ta Maimuna da har taji sanyi a ranta, sai ga shi magana ta sake dawowa sabuwa
Mamy ta ce, "Abban su da ka bar zancen ma, tunda ya.."
Katse ta Abba yayi yace, "dole ne ya bi abunda na ce masa, na gama magana". Ya miƙe ya bar wajen
Itama Mamy tashi tayi tabi bayan sa. Koda ta shiga ɗakin a bakin gado ta same shi har ya janyo computer ya fara latsa wa, zama tayi gefen sa tana cewa, "Abban su Ni a gani na da an bar maganar tunda ba ya so, don Allah kar ka ɗau zafi a kan maganar tunda mun rigada mun ajiye ta gefe".
Ɗago kai yayi yana kallon ta, ya san halin ta akwai sanyin hali, haƙurin matar shi yayi yawa duk da sosai yake hango damuwa a fuskar ta. Ɗan numfashi ya sauke kafin ya riƙo hannayen ta ya ce, "kar ki damu matata abar alfahari na! nima ba wai na zafafa maganar bane, ki ƙyale ni Ni dashi ne".
Zata sake magana ya katse ta da faɗin, "Please Dear ya wuce ba na son damuwar ki kinji?"
Gyaɗa masa kai tayi tana sauke ajiyan zuciya
Shi kuma yaci gaba da aikin sa yana sauya maganar da zancen bikin Uncle Abbas da ya rage kwanaki.
Nan kuwa ta saki jikin ta suna ta zanta wa.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🇵 𝐄𝐑𝐅𝐄𝐂𝐓 🇼 𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 🇦 𝐒𝐒𝐎𝐂𝐈𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍🌞
( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
𝗣.𝗪.𝗔✍️
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝙽𝚊 𝚜𝚊𝚍𝚊𝚞𝚔𝚊𝚛 𝚐𝚊 𝙼𝚊𝚑𝚊𝚒𝚏𝚒𝚢𝚊 𝚝𝚊 𝙰𝚋𝚊𝚛 𝙰𝚕𝚏𝚊𝚑𝚛𝚒 𝚗𝚊, 𝚞𝚠𝚊𝚝𝚊 𝚖𝚊𝚐𝚊𝚗𝚒𝚗 𝚔𝚞𝚔𝚊 𝚗𝚊, 𝙸 𝚕𝚘𝚟𝚎 𝚢𝚘𝚞 𝚜𝚘 𝚖𝚞𝚌𝚑 𝙼𝚘𝚖𝚖𝚊 ❤️
*________________________________*
*PAGE 13 & 14*
*________* Tun daga ranan kuma, sai ABUL KHAIRI ya ta da wa Ziyada ɓalli a kan maganar auren su, sai ya zauna ya haɗa mata ƙarya da gaskiya don ta ɗauki maganar da muhimmanci, a kan, "Iyayen sa za su yi masa aure da ƴar uwan sa, kuma sun ce dole sai ya aure ta idan be kawo wacce yake so ba." har da ƙarin gishiri da maggi
Ai hankalin Ziyada yayi matuƙar tashi fiye da zaton ABUL KHAIRI, nan kuwa ta je ta samu Daddyn ta da zancen
Shi kuma yace, "be yarda ba, ba yanzu zai mata aure ba".
Haka Ziyada ta tada rikici, dole ba don ya so ba ya amince, sai dai ya ce, "ba yanzu za'a yi auren ba, za'a saka ranan auren ne nan da shekara biyu masu zuwa". Time ɗin ta gama school
Haka Ziyada ta sanar wa ABUL KHAIRI, shi kuma ya zo ya sanar wa Abba, amma Abba ko bi ta kansa be yi ba, daga ƙarshe ma be sake tayar da maganar ba
Shi kuma dama Daddyn Ziyada be wani ɗauki maganar shima da muhimmanci ba, ya amince mata ne kawai don ta kwantar da hankalin ta, dama tafiya zai yi, haka ya tsallake maganar ya bar garin ba tare da ya ce ABUL KHAIRI ya turo magabatan sa ba.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Su Mamy suna ta shirye-shiryen bikin Uncle Abbas tunda har ya matso, tun ana kwana huɗu Ummu ta taho tare da Shuriem da Aliyu da ya biyo ta, sai Aunty Rufaida itama tare suka taho da yaran ta duk ta kwaso. Aunty Naana sai ana gobe bikin zata zo, dama shi Sulaiman yana kudu yin service, ba ma zai halarta bikin ba.
Gidan Mamy suka sauka gaba ɗayan su, ai a ranan su Batool tamkar baki zai tsage sabida murna, musamman ma Maimuna da tayi missing ɗin su ainun, nan taje ta ɗare jikin Ummu tana murna har da ƙwallar ta
Aliyu yana tsokanar ta da faɗin, "ke dai an yi sokuwa wlh, meye kuma na kuka? Wlh da ke Auta ce an bani da sangarta".
Turo baki tayi gaba tana share hawayen fuskar ta
Dariya gaba ɗaya suke mata
Ita kuwa sai kwaɓe fuska take yi tana ƙara shige wa jikin Ummu
Ummu tace, "to Ni sake Ni da Allah ban son sakarci".
Ɗaga ta tayi tana komawa kusa da Aunty Rufaida, Nan itama ta maƙure mata tana zuba mata surutu
Batool ta matso kusa da ita a hankali tace, "ashe haka kike kina surutu? Tunda mu kin mayar damu dodannin ki ai ba kya mana".
Hararan ta Maimuna tayi tana kau da fuska
"Uhmmm yi da kyau yanzu zan je in sanar da Yaya ABUL in ce kin murguɗa mishi baki". Batool ta sake faɗa a hankali
Juyowa wajen ta tayi ta saka hannu ta ranƙwashe ta, sai kuma ta kalli Mamy da suke hira da Ummu tace, "Mamy kin ganta ko?"
"Ah ah lafiyan ki ƙalau kuwa Batool? Me kike mata?" Cewar Mamy dake kallon su
Ita dai dariya Batool take yi
yayinda Maimuna take kumbura fuska tana faɗin, "tono na take yi Mamy".
"To ki mayar da hankali kinji?". Mamy ta sake faɗar hakan tana mayar da hankalin ta kan Ummu dake magana.
A haka ranan suka wuni suna hira, daga ƙarshe ma barin gidan suka yi su Maimuna, suka bi Aliyu da ya fita a motar gidan yawon ganin gari, duk suka bi shi har yaran Aunty Rufaida su uku maza da ta taho da su.
Sanda ABUL KHAIRI ya dawo gidan, ai kuwa ya ga faɗa wajen Ummu, sai da ta zauna ta sille sa da bala'i ta inda take shiga ba tanan take fita ba, wai a cewar ta, "har su za su zaɓa mishi abinda suke ganin ya dace da shi, amma ya shafe wa idanuwan sa toka ya ƙi bin umarnin su".
Shi dai be ce komi ba sai haƙuri da yayi ta ba ta, tunda dama ya san halin ta da shegen faɗa, bata da haƙuri ko kaɗan. Daga ƙarshe barin mata gidan yayi ya fito haraban waje ya zauna, tunda ta ƙi dena wa domin ta shaƙa ba kaɗan ba. Mamy da Aunty Rufaida suna ba ta haƙuri amma ina, sai da tayi ta gaji don kanta kafin a koma hira kuma ita da Mamy, ita kuma Aunty Rufaida ta wuce kichen yin musu girki.
▪️▪️▪️
ABUL KHAIRI na zaune a farar kujeran da ya turke ta a farandan gidan, ya hangi motar da Aliyu ya fita da ita ta shigo, dayake jip ce motan; su wajen rai Tara a cikin ta. yana kallon su duk suka fito a cikin motan suna ta hayaniya. Sai da suka taho ne ma suka lura da shi, ai gaba ɗayan su suka nufe sa ban da Batool da Maimuna da suka yi cikin gida
Haka yaran sukai ta gaishe shi, yana amsa musu yana musu wasa tare da tambayar su school da mutanen gida. Aliyu shima gaishe sa yayi kafin ya aiki Amir ya ɗauko masa kujeran shima, yana kawo masa ya turke ta kusa da na ABUL ya zauna, sannan yaran kuma duk suka yi cikin gidan suka bar su nan suna hira.
Sai dare duk suka tarkata suka tafi gidan Hajiya Mama, ban da Ummu da ba yau zata je ba, sai jibi za su wuce da su Mamy
Batool dai ta bi su, amma ita Maimuna taƙi bin su, kasancewar ta me ƙulafucin uwa, don ta ga Ummu ne ta ƙi tafiya, ita kaɗai ce a yaran aka bari.
A gidan su Mamy suke ta shirye-shiryen bikin, duk sun yi toye-toyen su a nan ne, itama Zee nan ta taho aka yi aikin da ita, har Aunty Rufaida da ta tafi can sai da ta dawo aka yi da ita, tunda can gidan Hajiya Mama babu wani aiki. A ranan itama Aunty Fatima ta zo, da yaran ta ƙannin Humaira. a daren suka tarkata suka koma can suka ci gaba da hidiman bikin, sai aka bar ABUL KHAIRI da Abba kaɗai.
Washe gari Aunty Naana ta taho da nata iyalan, gida dai ya cika Masha Allah sai zuwa ake yi, har su Inna Aliya da su Inna Maria duk a ranan suka zo bikin, Inna Halisa ce kaɗai bata zo ba, itama ta bar wa gobe ne tunda yanzu duk ana mutunci da ita, duniya ta koya mata darasi.
Washe gari aka ɗaura auren Abbas Yunusa Ubale, tare da Amaryan sa Safiyya Usman, da yake itama ƴar cikin garin ne. Gaskiya an samu mutane ba kaɗan ba a bikin nan, Allah yayi ruwan mutane, ta inda ba ka zato mutane sun taho, gidan Hajiya Mama ya cika maƙil duk girman sa, ta ko wani ɓangare su Mamy, Ummu, Aunty Fatima da suka yi gayya duk an zo musu. An sha biki an ragargaje, dayake su ba su yi wani Event na bidi'a ba, gaba ɗaya har aka gama taron babu wani bidi'a a ciki, sai Walima da suka yi da yamma, zuwa dare kuma aka kawo mishi matar sa tunda a gidan Part ɗin ta yake.
Tun a ranan mutane suka soma watse wa, washe gari da yamma su ma su Maimuna suka wuto gida suka bar Mamy a can, itama Aunty Fatima a ranan ta wuce Zaria, haka ma yaran Ummu su Aunty Naana da Aunty Rufaida duk a ranan suka nufi Kaduna garin gwamna kasancewar duk a can suke aure, Ummu ce dai sai washe garin ranan Litinin suka wuce da yamma, itama Mamy da dare ABUL KHAIRI ya zo ya mayar da ita gida
Aka bar Uncle Abbas da matar sa Safiyya ana cin amarci, sai mu ce Allah ya sanya alkhairi ya ba da zaman lafiya.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 15 & 16*
*________* *TWO WEEKS AGO*
Zaune yake a cikin Office ɗin sa, ya tasa takardu sai faman rubutu yake yi, gaba ɗaya yau ba shi da lokacin kansa, duba da yanda aiki suka yi masa yawa birjik, kuma be samu ya zo ba sai yanzu ɗin, sabida kiran gaggawa da Uncle Abbas yayi masa, kuma yana son ya tashi a kan lokaci saboda yaje gidan gonan sa su haɗu da Ziyada su huta, shiyasa komi nasa cikin sauri yake yi
Wayan sa da tayi ƙaran shigowar saƙo, shi ne yasa ya ɗago kai yana kallon wayan, a tunanin sa ko Ziyada ce, saɓanin haka private number ya gani aka turo masa text, ɗaukan wayan yayi ya buɗe ya soma karanta wa:
_"Yunusa Hayat Sunusi, Na san zaka yi mamakin ko waye yake bibiyan rayuwan masoyiyar ka, amma ba abun mamaki bane, domin Ni ɗin me ƙaunar kace, saboda ina son kasan wani sirri a tare da ita, idan har kana son sanin wace ce Ziyada, to ka shiga WhatsApp yanzu na tura maka saƙo ka duba.."_
Abin da aka tura masa kenan, ya karanta har sau biyu ba tare da ya ajiye wayan ba, tsayawa kawai yayi yana son fahimtar inda saƙon ya nufa, sai kuma ya buɗe data ya shiga WhatsApp kamar yanda aka ce masa. Sai da ya bari komi ya gama daidaita na shigowar messages, kafin ya ga ɓoyayyiyar Numban da aka tura masa saƙo, shiga yayi don ganin mene ne. Wani irin zabura yayi tamkar zai yar da wayan, har sai da takusa faɗi yayi saurin taro wa, jikin sa na rawa yaci gaba da kallon hotunan da aka tura masa
Hotunan Ziyada ce ita da Saleem, wasu hotunan suna tsaye a tare suna magana, wasu kuma suna riƙe da hannun juna a wajen shaƙatawa, babu abinda yafi ɗaga masa hankali sama da hoton da yaga an ɗauke su suna shirin shiga hotel, har wanda suka kai bakin ƙofan ɗakin da za su shiga an ɗauke su suna dariya, tamkar dai masoya idan an gan su
Sosai a lokacin jikin ABUL KHAIRI yake rawa, nan da nan zufa ya soma keto masa, zuciyar sa na wani irin bugawar tashin hankali, a lokaci ɗaya jijiyoyin kansa dana wuyan sa suka fito raɗo-raɗo, motsin kirki ya kasa yi illa hango Ziyadan da yake yi tare da Saleem ɗin a kan gado ɗaya suna... Wani irin kishi ne ya rufe sa, take ya jefar da wayan, ya buga saman table ɗin sa da ƙarfi yana me faɗin, "no impossible! Ziya..." Sai kuma ya kasa ƙarisawa saboda rawan da bakin sa yake yi. zube wa yayi saman kujeran sa yana huci tamkar zaki, gaba ɗaya zuciyar sa zugi take masa kamar zata fito
Ƙaran wayan sa, yasa ya ɗago jajayen idanun sa ya zuba a kan wayan dake yashe a ƙasa, kallon ta kawai yake yi ba ya motsi, tamkar dai yana son a tabbatar masa da cewa ƙarya ce abun da ya gani, sai kuma ya saka hannu a hankali ya ɗauko wayan hannun sa na rawa kamar an jona sa a shock. Text ɗin dai Numban ne da aka turo masa saƙo, buɗe wa yayi ya soma karanta wa:
_"hhhh abun mamaki ko? Na san dama zaka ruɗe duba da yanda kake matuƙar son masoyiyar ka, but taci amanar ka, wannan ma kaɗan ne daga abubuwan da take aikata wa, amma da sannu zan ci gaba da bayyana maka wace ce ita, zaka san cewa kana tare ne da baƙar macijiya.. hhhhh amma fa ina ga laifin ka ne, tunda ka kasa yin mata abinda take so.. HHH don ta nema a wani waje ba laifi bane.."_
Lumshe ido ABUL yayi, sai ga hawaye sharrr sun soma zubo masa, kifa kansa yayi a saman table ɗin ya hau zirarar da hawaye tamkar mace, sosai zuciyar sa take suya kamar ya ciro ta ya jefar, gaba ɗaya fuskar sa tayi jawur sai haɗiyar zuciya yake yi. Ya jima a haka a wani mawuyacin hali kafin ya ɗago kansa da yayi sharkaf da zufa, fuskar sa kuma ta jiƙe da hawaye, numfashi kawai yake sauke wa tamkar ransa zai fita tsaban kishi, ji yake yi kamar ya kashe kansa saboda baƙin ciki, macen da yafi ƙauna a duniya ita ce take tare da wani, har ta iya ba shi kanta. kama kansa kawai yayi yana jin hajijiya na son kada shi daga zaunen, da sauri