Showing 30001 words to 33000 words out of 88313 words

Chapter 11 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt

yayi masa koran kare

Mamy duk ta rikice ganin yanda ta gansu, cikin hawaye tace, "yanzu Abban su me suka yi da Baba na zai yi musu wannan hukuncin?"

Cikin kuka Batool tace, "babu abinda muka yi masa wlh, kawai ya shigo ɗakin mu ne ya ga muna sa'insa da Sa'ima a kan tashi na da tayi daga barci, shi ne ya hau jibgan mu har Maimuna da bata yi masa komi ba".

Itama Sa'ima na kukan ta amshe zancen da faɗin, "wlh Mamy ba muyi masa komi ba, da fushi ya dawo gidan shi ne ya ƙare a kan mu".

Sosai ran Abba ya sake ɓaci, yace, "wlh muddin wani abu ya sami Maimuna sai na ba shi mamaki, domin Nasan da gayya yayi mata wannan dukan, yau sai nayi mummunan ɓata masa rai wlh, bari mu koma gida". Yana gama faɗar maganan yayi waje don duba ABUL KHAIRIN idan be tafi ba, tun yanzu yaci mutuncin sa, sai dai ina tuni babu shi a haraban asibitin, har motan nasa ma.

        Lokacin da Doctorn dake duba Maimuna ya fito, nan suka je gaba ɗaya suka same sa, yace, "su biyo sa office". Suna zuwa ya sanar musu da abinda ke faruwa

Ba wani abu bane illa mugun dukan da aka yi mata ya haddasa mata firgita, hakan yasa ta sume, sannan sai raunuka da taji a kanta da jikin ta da ya farfashe, an samu yanzu ta farfaɗo, sai dai sun yi mata alluran barci sun saka mata ruwa, sannan kuma baza a sallame ta ba sai zuwa gobe ko jibi saboda yanayin jikin nata akwai zazzaɓi me zafi da ya kama ta.


      Duk da haka dai sun ɗan ji sanyi a ransu tunda lafiyan ta lau, tare suka je gaba ɗaya suka duba ta, inda Abba ya wuce da Sa'ima har gida ya kaita, ya sanar wa Umma Salamatu da komi (Ƙanwar sa ce idan baku manta ba)

Duk da hankalin ta ya tashi, amma bata wani damu da dukan su Sa'iman ba, a ganin ta su ne ba sa ji, sabida son da take yiwa ABUL KHAIRI shiyasa ko kaɗan bata ga laifin sa ba, illa tausayin Maimuna kawai da taji

Tare suka dawo da Abban asibiti ta duba ta, a lokacin ma har ta farka, sai dai gaba ɗaya jikin ta ciwo yake mata, duk yayi tsami, ga zazzaɓin da ya ƙi sauka.


     Mamy bata sanar wa kowa ba, har Ummu duk ta ƙi faɗa musu, ko su Hajiya Mama bata sanar musu ba, ta bar abun daga su sai su, tunda an ce zazzaɓin na sauka za'a sallame su, kuma komi ya zo da sauƙi alhamadulillah. Tayi kiran wayan ABUL KHAIRI amma duk ya ƙi ɗauka

Yana can ya bar ta a ɗaki, shi kuma ya ƙi komawa gidan, gaba ɗaya ya rasa inda zai saka kansa, ko kaɗan bazai so ya koma gida a wannan halin ba, domin yasan muddin ya koma sai ya haɗu da fushin Mahaifin sa, ga Sagir ba ya nan bare ya ba shi shawara, ga baƙin cikin abinda Ziyada tayi masa yau, ya rasa inda zai saka kansa, duk damuwa tayi masa yawa, har kansa ya soma masa ciwo tuni, dole ya nufi gidan gonan sa, don yana jin a nan zai kwana ƙila, ko kuma zuwa dare ya koma gida, amma ya san zai sha faɗa, shiyasa ma ya yanke shawara be koma ba, a can ya kwana.


      Zuwa dare zazzaɓin ya ɗan sauka kaɗan, Mamy ta kwana da ita dole. Washe gari kuma Batool ta kawo musu Breakfast, ita da Abba suka zo, bata jima ba ta koma tunda an bar su Amir.





◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️

       Da safen ABUL KHAIRI ya shirya ya wuce Office daga can, tunda yana da komi nasa a gidan babu abinda zai buƙata sai wayan sa da jakan sa, amma kuma ya ƙi zuwa gida ne don gudun haɗuwan su da Abba da Mamy, don be san me zai ce musu ba

Yana zuwa Office ɗin sa kuwa, aka sanar masa, "Abba ya zo neman sa yanzu," yana jin haka ya fito ya bar Companin, gida ya wuce kai tsaye, ya ci Sa'a babu Mamy tana asibiti, sai yaran. wayan sa ya ɗauka ya bar gidan, ya gummaci ya tafi wani wajen har sai sun huce kafin ya dawo, don shi ya tsorata sosai.


     Kai tsaye gidan Umma Hussaina ya wuce (itama ƙanwar Abba ce) amma gidan ta da nisa sosai, ya san ba lallai taji labari ba, shiyasa ma ya wuce can.


◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️

      Yau ma Azeeza shirya wa tayi ta fito ta nufi gidan ABUL KHAIRI, don tasan a can zata gansa, tunda kullum sai ya zo idan ya tashi aiki, kuma tasan yanzu haka lokacin zuwan sa ne

Jiya da farin ciki ta kwana, Allah-Allah take yi dama yau tayi ta sake koma wa, don yau tayi ninyan nuna masa videon da tayi musu, zata ce masa, "idan har be aure ta ba, to, zata je ta nuna wa Iyayen sa komi, sannan ta faɗa musu duk yanda suke rayuwar soyayyar su". Ta san dole zai amince, dole ne zata ci galaba a kan sa.


    Me nepep na sauke ta ta fito ta biya sa kuɗin sa, sai ta nufi bakin Gate ɗin, buga ƙofan tayi. Sai dai shiru babu me Gadin kusa, sai ta tura ƙaramin ƙofan ta ga ya buɗe, tayi shigewar ta

Abun baƙin cikin tana shiga ta hangi motan Ziyada, "kenan dai har yanzu baza ta rabu da shi ba? To tabbas yau zan yi mata iyaka dashi na har abada". A zuciye ta nufi cikin gidan zuciyar ta na tafarfasa.




◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️

       A dai-dai wannan lokacin ne ABUL KHAIRI ya nufo gida, ya san cewa dole yanzu zuciyoyin iyayen sa sun sauka, duk da ya ga basu kira sa ba, amma dai gwara yau yaje ya ba su haƙuri zai fi

Yana cikin tuƙin ne aka kira sa a waya, a tunanin sa ko Abba ne shiyasa yayi saurin ɗaukar wayan yana duba wa, sai dai ba shi bane, baƙuwar number CE. Shiru kawai yayi yana tunani, domin tuni zuciyar sa ta raya masa numbern da jiya ta hargitsa masa rayuwa ce, duk da wannan ɗin ba'a rufe ta ba. "yanzu to meyasa aka kira sa? Ko wani abun ne Ziyada tayi?" Nan da nan zuciyar sa ta harbu da ɓacin rai, sai faman ajiyan zuciya yake yi ya kasa ɗaukar wayan, domin tsoro ne tsantsa ya shiga zuciyar sa har wani mugun bugawa take yi, saurin tsayar da motan yayi a gefen titi yana dafe ƙirjin sa tare da runtse idanu, ya hau karanta, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" domin ba ƙaramin hautsinewar zuciya yake ji ba, tamkar wani abu mummuna zai same sa

Me kiran be fasa kira ba, har sai da aka yi masa two missed calls, ana ukun ne ya ɗaga yana karawa a kunne hannun sa na faman rawa

Maganar na miji ne ya duke kunnen sa, sai dai babu ko daɗin ji muryan nasa, don daƙyar ma yake iya gane me yake cewa, tamkar dai ya toshe bakin nasa, ko kuma ya cika bakin nasa da wani abu yake magana

Dariya ce ta fara biyo baya, sannan ne ya soma magana, "Yunusa Hayat Sunusi.. shin kana ina tashin hankali ke jiran ka a gidan gonan ka? Tabbas idan har baka ƙarisa da wuri ba, to, zaka yi nadamar rayuwan ka. Hhhhh".

Ƙittt aka kashe wayan

Sosai a wannan karon ya dafe setting ƙirjin sa, sabida wani mahaukacin buga wa da take yi, gaba ɗaya jikin sa rawa yake yi, ya rasa me ke masa daɗi, addu'an ma daƙyar yake iya karanta wa, sabida ba jikin sa kaɗai bane yake mazari har ta zuciyar sa ta gama hautsine wa, kuma ya rasa dalili, be ma fahimci me maganar nasa yake nufi ba, amma haka ya daure yaci gaba da tuƙin nasa ya nufi gidan gonan.





               ◾▫️◾▫️◾▫️

      A rikice Azeeza ta fito daga cikin gidan, wani irin rawa jikin ta yake yi tamkar mazari, har tuntuɓe take yi wajen sauri, Allah yasa me gadin be dawo ba har yanzu, shiyasa ta lallaɓa ta fice da gudun gaske. Tana fita ta hangi Motan ABUL KHAIRI ya shanyo kwana, wani irin sara wa gaban ta yayi, tayi saurin ɓuya a jikin bango har ya wuce ta, ajiyan zuciya ta sauke taci gaba da sauri-sauri tana waigen bayan ta, tana fita bakin titi ta sami napep ta shige sai gida.





          ◾▫️◾▫️◾

    Horn me ƙarfi ABUL KHAIRI yake danna wa jin ba'a buɗe masa ƙofa ba

Da gudu me gadin ya ƙariso, dama ashe yana can baya wajen masu aiki ya shantake suna hira. Da sauri ya buɗe masa ya shigo da motan

Tunda ya hangi motan Ziyada ya ɗaure fuska kamar hadari, zuciyar sa gaba ɗaya ta sake hassala, ya fito a wani yanayin da jikin sa ko kaɗan babu ƙwari, kiran me gadin yayi ya tambaye sa, "tun yaushe Ziyada ta zo gidan nan?"

"Ranka ya daɗe tunda ka fita da safe ta zo".

"Meyasaka ka buɗe mata ƙofa? Ban maka kashedi ba?"

"Ranka ya daɗe ka yi, ayi haƙuri, wlh balbale Ni tayi da tsiya dole na buɗe mata".

ABUL KHAIRI be sake cewa komi ba ya nufi cikin gidan, yana buɗe ƙofan idanun sa suka sauka a kanta tana kwance a tsakar ɗakin, be hangi komi ba sai da ya shigo sosai yaga kamar wuƙa ne a jikin ta, ga jini na kwaranya ta ƙasan jikin ta, da ƙasan ƙafafuwan ta.

Daskare wa ABUL yayi a wajen tamkar an zare masa rai, sai da yaji wani dumm kamar ba ya duniyar kafin ya dawo hayyacin sa, wani irin zaro idanu waje yayi ya nufe ta da sauri yana salati. Duƙawa yayi gaban ta, ya saka hannyen sa da kamar za su tsinke tsaban rawan da suke yi, wuƙan ya ɗauka yana me kiran sunan ta

"Ke.. ke ZIYADA.. ke.. tashi mana meye.. haka?" Yayi maganar kamar zuciyar sa zata faso ƙirjin sa tsaban tsoro. Girgiza ta ya hau yi, amma dai kamar ba ta motsi, kamar dai ranta ya daɗe da fice wa a jikin ta. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Abinda yake ta maimaita wa kenan yana zame wa dirshan ya zauna a ƙasa. "Me ke shirin faruwa ne?" Yayi maganar a cikin zuciyar sa yana kama kansa da hannayen sa biyu ya soma hautsina gashin kansa, sai kuma ya sake saka hannu yana girgiza ta yana faman kiran ta, sai ga hawaye shaaa sun soma zubo masa.



    A dai-dai lokacin ne jiniyan ƴan sanda suka cika anguwan, kan kace me har sun ƙariso gidan sun shigo

Ruɗewar da ABUL KHAIRI yayi har ya kasa motsa wa a inda yake zaune, kawai kafe ƙofa yayi da manyan idanun sa da suka sauya kala lokaci ɗaya tsaban rikici.












_Ya za'a kaya? Shin wani irin tsaka me wuya ABUL KHAIRI yake ciki? Wa ya saka shi a wannan mawuyacin halin?_

_Anya ma Ziyada ta mutu? Ko tana raye?_

_Shin waye ma ya kira ƴan sandan nan?_

_Me Azeeza ta aikata?_

_amsar ku na waje na. Ta Comments ɗin ku kaɗai zan gane kuna son ci gaba. More Comments more typing_





*HAPPY JUMA'AT MUBARAKH FAN'S 🤩*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

            *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:*✍️
             _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻‍♀️

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A*✍️

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

          *SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️

*TARIHIN FARILTA SALLAH*
      '''An farilta sallolin nan biyar ne gabanin ƙaura, watau hijira, da shekara ɗaya da rabi. Sallah ce kaɗai ibadar da aka farilta ta a sama a daren Isra'e, kamar dai yadda aka ruwaito a hadisin nan na Anas. Da farko an umurce shi da Sallah guda hamsin ne; da sannu aka dinga rage su har suka zama biyar a bisa roƙon da shi Manzon ya yi wa Ubangijin sa. Da suka zama biyar, sai Allah ya ce masa su biyar ɗin nan, dai-dai suke da hamsin.
   Malamai da yawa sun yi bayanin yadda sallar ma'aikin Allah, mai tsira da aminci, take gabanin Isra'en.
Wasu malaman sun ce, "Gabanin Isra'e, babu wata sallah wadda aka farilta sai sallar dare (Ƙiyamul lail) wadda aka umurci ma'aiki da yin ta ba da iyakataccen lokaci ko adadi ba, kamar yadda yake a suratul Muzzammil, ayoyi huɗu na farko:
    "Ya wanda ya lulluɓe! Ka tsayu domin yin Sallah a cikin dare (duka) face kaɗan, rabin sa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi, ko ka ƙara kansa...
         Ma'aikin Allah ya kasance yana yin sallar a kashi biyu cikin uku na dare ko a rabin sa ko kuma sulusin sa. Musulmi suka dinga yi tare da shi kamar shekara guda har suka gaji; daga nan sai Allah ya shafe ta don jin ƙan su.
      An ruwaito cewa sallar da Musulmi suke yi gabanin tafiyar dare suna yin ta ne kafin faɗuwar rana da kafin ketowarta kamar yadda yake a sallah littafin Almanhalil Azb. Gabanin ƙaurar Annabi zuwa Madina raka'o'in sallah bibbiyu ne, bayan ƙaura ne suka zama hurhuɗu, illa magriba da ta kasance raka'a uku, ita kuma sallar subahi ta tsaya a kan biyu saboda dogon karatun da ake yi cikin ta. Buhari da Ahmad sun ruwaito daga Nana A'ishah cewa, "an farilta sallah raka'a bibbiyu, bayan ƙaura ne aka mai da ita raka'a hurhuɗu, amma an bar sallar tafiya a kan raka'a ne bibbiyu, sai sallar magriba ita ko da ma raka'a uku-uku ce."
        Allah ya sa mu dace.'''





*________________________________*

              *PAGE 19 & 20*

*________* Gaba ɗaya wajen sa suka yo suna me ƙale sa da bindiga, yayinda Shugaban cikin su yace, "You are under arrest".

ABUL KHAIRI be ma San suna yi ba, domin kuwa tuni tunanin sa ya tsaya cakk ya dena motsi

Ɗaya daga cikin ƴan sandan ne ya cafke hannayen sa ya zagayo dasu ta baya ya saka mishi hand cuff

Har ya gama ABUL KHAIRI be motsa ba, domin shi gani yake yi tamkar mafarki yake yi, kuma zai farka nan ba da jima wa ba, sai da ya ji sun daka matsa tsawa a kan, "ya tashi". Sannan ne ya dawo hayyacin sa, ya bi su da kallo da manyan idanun sa da suka ƙanƙance tsaban firgita suka yi jazur, wasu sabbin hawayen ne suka wanke masa fuska, nan da nan jikin sa ya soma rawa, muryan sa na fita daƙyar yace, "Wlh ban san komi ba a kai.., ba.. Ni ne.. na aika ta.."

"Yi mana shiru. Idan ka je can zaka amsa ne". Cewar Ogan cikin su, sannan ya ba su umarnin su tafi dashi

Da ƙarfi suka ja sa dole ya miƙe, suka tasa ƙeyan sa suka yi waje

Inda shugaban da wasu biyu cikin Yan sandan suka yi saura a wajen

Ogan ya kalle su yace, "ku duba min wancan jakan ko za'a sami address ɗin ta".

"Ok Sir". Suka amsa a tare suka nufi jakan Ziyada dake kan kujera

Shi kuma ogan sai ya ciro wayan sa ya nemi agajin gaggawa wajen masu jinya.

     Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci motar asibiti ta iso gidan, inda aka ɗauko Ziyada aka saka ta cikin motan aka yi asibiti da ita

Gidan kuma ABUL KHAIRI nan aka zuba police ko ta Ina aka hau bincike, gaba ɗaya an tarkata daga me gadi da masu kula da gidan, duk an wuce da su station.


      Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya je wa iyayen Ziyada, inda suka ji mummunan labarin ɗiyar su na nan rai a hannun Allah a asibiti, babu ɓata lokaci suka garzaya can. A lokacin har an tabbatar da mutuwar ta ma. Daga Dady har Mom Kuka suka saka, gaba ɗaya sun hargitsa asibitin da koke-koke, nan da nan labari ya soma bin dangin su, har wasu sun rigada sun iso, haka ma iyayen Sagir duk sun zo, har shi Sagir ɗin ma da ba ya garin ya ji mummunan labarin. musamman inda aka ce masa wai ABUL KHAIRI ne yayi kisan, take a nan ya kusa yanke jiki ya faɗi, sai da aka riƙe sa, nan da nan ya biyo hanya ya nufo Kano cikin tashin hankali.

       Iyayen ABUL KHAIRI ma tuni labari ya je musu, domin tuni sun matsa shi ya faɗa musu address ɗin sa, kai tsaye gidan suka wuce, inda suka sami Abba dawowar sa kenan, suka faɗa masa mummunan labarin nan, salati kawai ya dinga rafka wa yana shirin faɗi, shima daƙyar ya samu ya tsayar da ƙafafun sa, nan da nan hankalin sa yayi mugun tashi, kai tsaye ya wuce Hospital tunda har yanzu ba'a sallami Maimuna ba, sai dai yau ake saka ran sallaman nata dama, Batool ma na can. Sai dai sanda yaje ya kasa sanar wa Mamy

Ita kuma ganin hankalin sa a matuƙar tashe, sai ta hau tambayar sa

Sai da yace, "su fita waje su yi maganar". Kafin ya sanar mata

Take a nan ta yanke jiki ta faɗi. Tashin hankalin da ba a saka mishi rana

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, a cikin awanni biyu labari ya zaga ko ina a dangin su, domin tuni kowa ya sani, dangi na kusa duk sun taho gidan Mamy, sai dai Mamy har yanzu tana asibiti bata farfaɗo ba, domin sosai take a mawuyacin hali

Su Batool kuka sosai suke yi, daga ita har su Maimuna da su Amir, duk suna asibitin

Sai da Abba ya je ya amsar mata sallama, sannan ya saka Aƙilu ya mayar da su gida, haka mutanen anguwa da dangi duk sun cika gidan, kowa ya zo jaje. Gaba ɗaya ahalin sun ruɗe da wannan babban al'amarin.






            ◾◽◾◽◾

     Fannin Ƴan sanda suna ta binciken su, inda suka saka ABUL KHAIRI a gaba da tambayoyi tare da gana masa azaba, amsa ɗaya yake ba su, "ba shi ne ya kashe ta ba". Gaba ɗaya ya rasa tunanin sa, domin ba kaɗan ba mutuwar ta shige sa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login