Showing 18001 words to 21000 words out of 88313 words

Chapter 7 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt

musu hotuna ba tare da sun sani ba, sai da ta gama taja motan tayi gaba, tayi nisa sosai kafin ta tsaya, tana hango motan ta mirror can daga nesa. Sai da taga sun yi gaba kafin taja motan ta karya kwana tabi bayan su.

       A wani hotel suka tsaya, itama sai taja ta tsaya, ta ɗauki wayan ta tayi musu hotuna kafin ta saki shu'umin murmushi tana faɗin, "yanzu aka soma wasan, tabbas Ziyada nayi alwashin ko ta halin ƙaƙa ne sai na raba ki da ABUL KHAIRI, domin ABUL KHAIRI nawa ne Ni  kaɗai, da sannu zan cire soyayyar ki a ransa, in kuma dasa nawa a cikin ransa". Sai ta sake sakin murmushi taja motan ta nufi school ɗin su dake BUK.



▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

              *03:30pm.*

       Lokacin da Azeeza ta fito daga gidan su ƙawarta, sai ta sami keke napep kanta tsaye ya wuce da ita gidan gonan ABUL KHAIRI. Bayan me napep ɗin ya sauke ta tana biyan sa kuɗin sa; ta hangi motan Ziyada tana buga horn a bakin Gate ɗin, da idanu tabi motan da kallo har ta shige, sannan itama ta nufi bakin Gate ɗin. Tana isa ta ƙwanƙwansa ƙofan

Me gadi ya buɗe ya fito yana tambayan ta, "lafiya?"

"Baba don Allah ABUL KHAIRI na ciki?"

"Eh yana ciki, in ce dai lafiya ko?"

Gyara tsayuwar ta tayi tana faɗin, "eh Baba, dama so nake Yi in gansa, don Allah idan babu damuwa ka taimaka min".

"To shikenan, bari inje in sanar masa".

Azeeza tace, "a'a Baba ba sai ka je ba, ka bar Ni in shiga dan Allah".

Ɗan jimm.. yayi yana kallon ta, sai kuma yace, "gaskiya Hajiya baza ki samu ganin sa ba, sai dai ki bari inje in sanar masa kamar yanda yace na riƙa yi".

Jakan ta tabuɗe ta ciro dubu biyar ɗin da suka rage mata, ta miƙa masa tana cewa, "don Allah Baba kayi min wannan alfarman, ka yarda dani kaji babu abinda zai faru bare ya sami aikin ka, yanzu zan shiga in fito, tunda dama shi yace in zo".

Me gadi washe baki yayi ganin farare bugun Abuja a hannun ta, ya saka hannu ya amsa yana cewa, "to Hajiya babu damuwa ai, in ce dai shi ne yace ki zo ɗin ko?"

"Eh shi ne".

"Tom shiga, a fito lafiya". Yafaɗa yana matsa mata a hanya

Shiga tayi ta nufi hanyan Part ɗin sa, ɗan ƙaramin Plet ne da aka yi sa tamkar bukkan Fulani, sai dai da gini aka yi, saman rufin kuma ya kasance irin na Bukka ne.

      Tana isa sai ta zagaya ta bayan ginin, babban windows ta gani guda biyu, waɗanda aka yi su da Glasses, dama a buɗe suke sai ta leƙa kanta ciki. abinda ta gani ne ya ɗaga mata hankali

ABUL KHAIRI da Ziyada ta gani zaune saman kujera, Ziyada na kan cinyan sa yana bata abinci dake cikin take-away, ita kuma sai zuba masa shagwaɓa take yi

Da sauri Azeeza ta runtse idanuwan ta tana jin zuciyarta na tafarfasa, sake ware idon tayi kan su ranta duk a ɓace, tsananin baƙin ciki ne da kishi ya mamaye ta. "Wace ce wannan yarinyan?" Tambayan da yazo mata a zuciya kenan. Sai dai bata da me bata amsa illa ƙura musu idanu da tayi tana kallon kayan takaici, zuciyarta na sake tafarfasa tamkar zata mutu, da sauri taja jiki ta matsa a wajen hawaye na kwaranya a face ɗin ta, ta daɗe a haka tana dafe da ƙirji kafin ta sake kallon windown, kamar ta leƙa sai dai tana tsoron abinda zata sake gani, dole ta nufi hanyan fita daga gidan

Tana hango me gadi ta saka gefen gyalen ta ta share hawayen fuskarta, ta dai-daita kanta sannan ta nufi bakin Gate ɗin, sallama suka yi da me gadin tafice da sauri.


       Tafiya kawai take yi tana tunanin abinda ta gani, sosai ranta ke suya tamkar ta koma ta kashe su duka biyun haka take ji, a ranta ta ɗauki alwashin dole sai ta raba su, koda kuwa hakan na nufin sai ta kashe Ziyada ne, sai yanzu ta gane cewa sabida Ziyada ne ABUL KHAIRI ba ya kula ta, tunda ya samu wacce tafi ta komi da komi, tabbas ta ɗau alwashi sai ta raba su, kuma sai ta saka soyayyar ta a zuciyar ABUL KHAIRI, domin shi ɗin nata ne ita kaɗai, ba'a yi macen da zata riga ta mallakan sa ba. Tana tafiya tana share hawayen ta, a haka har ta kai bakin titi, ta tare me napep tayi gida.

      Koda ta shiga gidan babu kowa a Parlour, kanta tsaye ta shige ɗakin su Batool

Suna zaune a kan gadon Maimuna suna duba Books a tare, suna muhawaran yanda jarabawar zai kasance musu gobe, sai ganin ta suka yi ta shigo ko sallama, da idanu suka bi ta dashi babu wanda ya tanka mata cikin su

Ita ma kuma bata bi ta kansu ba, ta nufi wajen jakanta ta hau haɗa kayan ta, har ta fice babu wanda ya kula ta

Batool ce ma me ƙoƙarin shiga harkan ta, tunda tasu tafi zuwa ɗaya, amma dayake tana jin haushin ta shiyasa bata kula ta ba, sai ma taɓe baki da tayi a fili take faɗin, "a gayas, dama bamu gayyar ki a nan, mtsww! Ƴar wahala".

Ita dai Maimuna bata ce komi ba, illa murmusawa da tayi tana mayar da kanta zuwa ga kallon littafin dake gaban su.



    Azeeza na fita ta shige ɗakin Mamy

Mamy dake zaune da Laptop a gaba, sai ganin Azeeza tayi cikin ɗakin ta babu ko sallama, kallon ta tayi cike da mamaki ganin ta da kayan ta, tace, "ah ah Azeeza lafiya, ina zaki je da jakan?"

Azeeza tace, "tafiya zan yi Gwaggo".

"Tafiya kuma? Me ya faru ne, wani abun aka yi miki?"

"A'a kawai dai..." Shiru tayi don bata san me zata ce ba

Mamy tace, "ko dai kin fasa mana kwana biyun ne? Ko kuma wani yayi miki wani abu ne wanda baki ji daɗin shi ba? Ki faɗa min don Allah".

Murmushi Azeeza tayi tace, "wlh Gwaggo babu komi, na fasa zaman ne sabida na tuna akwai bikin da zan je wannan satin, kuma ina so in je gidan Gwaggo Halisa gobe (Ƙanwar Mahaifin ta)".

Murmushi Mamy tayi sabida jin abinda ta faɗa, sai tace, "ki ce dai zaki tafi Azeeza, amma me ya haɗa tafiyan ki da bikin da zaki je sati me zuwa? Kwana wajen biyar fa, sannan nan da Jigawa gidan Adda Halisa ai ko gobe zaki iya komawa gida kuma ki je a goben. Ki faɗa dai idan su Batool ne suka yi miki wani abun sai in ɗau mataki".

Azeeza cike da borin kunya jin ƙaryan ta be shiga ba, ta saka hannu tana sosa ƙeya tace, "babu komi wlh, zan tafi ne, amma zan dawo ai Gwaggo tunda ina nan".

"To shikenan. bari in baki na mota, idan kin je ki gaishe da iyayen naki, ki gaida min da umma itama, insha Allahu zan saka lokaci in zo duba ta".

Ita dai Azeeza da, "to". Kaɗai ta amsa mata tana tsaye a inda take

Jakar ta ta janyo dake kan gadon, ta ciro kuɗi masu yawa, ta ƙirga ta cire mata duba goma cif, sannan ta miƙa mata tace, "ga shi to sai ki siya kayan kwalliya, babu yawa, Allah ya kiyaye hanya".

"Amen amen Gwaggo". Azeeza ta faɗa hakan tana washe baki bayan ta saka hannu ta amsa

"Koda yake nasan Aƙilu na nan, ki duba idan yana nan sai ya kai ki gida kawai, Allah ya tsare hanya, ina nan dai ina jiran ki". Mamy tace hakan tana murmushi

"To Gwaggo". Ta'amsa tana fice wa

Ta daɗe Mamy tana tunani a ranta, kafin ta ja numfashi taci gaba da latsa Laptop ɗin ta.




           ▪️▪️▪️

      Azeeza na fita ta samu Aƙilu a bakin famfo yana wanke mota, ƙarisawa wajen sa tayi, tana shan ƙamshi tace, "Kai Drever kazo ka kai Ni gida in ji Gwaggo Deebizah".

Ɗagowa yayi yana kallon ta, sai ya taɓe baki a ransa yace, "ji da Allah yanda take yi sai kace ita ɗin ƴar wasu shegu ne a garin, mtsww". Ya ja tsaki yana mayar da kansa yaci gaba da wanke tayan motan ba tare da ya tanka ta ba

"Kai dan uwar ka ba da kai nake yi ba? Dama ai matsalan ƴan ƙauye kenan a kawo ku birni, Ku zo kuna nuna kun fi ƴan birnin, matsiyacin banza matsiyacin hofi".

Still ɗago da kansa Aƙilu yayi, ya kalle ta da murmushi a face ɗin sa yace, "daɗin abun ma, su uwayen ki duk daga ƙauye su ke, in ji dai duk asalin ku kenan?"

Ta banka masa harara tace, "mun fi ƙarfin ƴan ƙauye wlh, sai dai iyayen ka ne ƴan asalin can, banza kawai ajawo. Kuma wlh idan baka shiga mota ka kai Ni ba na rantse da Allah sai na je nayi maka sharrin da baza ka taɓa cire kanka ba a gidan nan, ɗan iska ɗan tasha".

Ran Aƙilu sosai ya ɓaci, sai dai kasancewar shi me yawan dariya da barkwanci, dole ya danne ɓacin ransa, sai ma murmushi da ya sake yi yana kallon ta yace, "to ranki ya daɗe! Ki jira Ni mana saura taya ne kaɗai in wanke, idan na gama sai mu tafi ko?"

Ƙwafa tayi tana mishi kallon wulaƙanci, bata ce komi ba ta juya ta ɗaya side ɗin motan ta shige

Shi kuma Aƙilu be sake bi ta kanta ba ya ci gaba da wankin sa, har sanda ya gama amma ya ƙi shiga motan, sai faman ƙalƙale motan yake yi, ya wanke nan ya wanke can

Azeeza fa ta shaƙa da yawa sabida jiran nan da take yi, sai ta zuge Glasses Motan ta leƙo tana faɗin, "wai uwar me ka tsaya yi ne har yanzu baka gama ba?"

"Uwar ki na tsaya yi". Ya faɗa ƙasa-ƙasa yana hararan gefen ta

"Ka ce mene?"

"Cewa nayi gani nan zuwa na kammala". Ya faɗa da sauri yana nufan ƙofan motan ya buɗe ya shiga

Dogon tsaki taja tace, "ƙaryan iskanci kake yi wlh, matsiyaci wanda be gaji arziƙi ba".

Aran Aƙilu yace, "ban gaji arziƙi ba ko baki gaji arziƙi ba, shegiya birgi-birgi! Yau da Ni kike zancen sai na koya miki hankali". Jan motan yayi da gudu yayi bakin Gate, horn yayi me gadi ya buɗe masa ya fice

    Yana fita shima motan ABUL ya ƙariso wajen, hakan yasa me gadin be mayar da Gate ɗin ba, ya bar masa ya shigo. Shi ABUL KHAIRI be kalli motan ba bare ya san waye a ciki

Ita kuma Azeeza kallon motan ABUL KHAIRI take tayi, a ranta tana ayyana abubuwa da dama, ta so tana gidan ne ya dawo tayi masa magana, sai kuma ta saki murmushi a fili tace, "na san duk tsula tsiyan nan da kake yi babu wanda ya sani a gidan ku, amma mu je zuwa da sannu zan fasa ƙwan, tabbas wannan hanyar kaɗai ya isa na raba ka da tsinannaniyar can dana ganku tare".

"Wai da Ni kike yi ne?" Cewar Aƙilu yana kallon ta ta mirror

Harara ta sakar masa tace, "a'a da uwar ka nake yi".

Dama yayi ne don ya tsokane ta, shiyasa yayi murmushi ya soma jan motan da wani irin Speed, sosai yake gudu kamar zai zubar da su a kan kwalta, ga shi titin a cike take maƙil, haka yake yin over taking, sai yayi kamar zai buga wata motan sai ya ja birki ya rage gudun a lokaci ɗaya

Hakan yasa Azeeza dake baya take ta bige wa da kujerun gaba, sosai ta jigata a ɗan lokaci ƙanƙani. Cikin fusata tace, "wai kai haka ake tuƙi a garin ku ne? Ba ka da hankali ne zaka ji min ciwo?".

Cikin murmushin ƙeta yace, "yi haƙuri, wlh kinga sauri nake yi Alhaji na jira na zai aike Ni, kuma ke kin ce sai na kai ki, yanzu idan ya dawo be gan ni ba akwai matsala, shiyasa nake wannan gudun in je in dawo".

Zagin shi ta hau yi, tana gaya masa maganganu

Shi kuma be fasa tsula gudu ba, yana tuƙin ganganci ta yanda zata sha wahala, har suka kai ƙofar gidan su Azeeza sai ƙunduma masa ashar take yi

Tana fita ya ja motan ya baɗe ta da ƙura ya bar wajen yana sheƙa dariyan mugunta

Ai kamar ya kunna Azeeza, nan ta tsaya tayi ta auna masa zagi tana cewa, "za su haɗu ne, sai ta shuka masa rashin mutunci duk sanda ta dawo gidan nan". Sai da ta gama tijaran ta a waje har yara sun soma taruwa kafin ta ɗau jakar ta ta shige gidan na su.

       Umman ta na bakin ƙofa a zaune tana lissafin kuɗin awara, sai ganin Azeeza tayi ta shigo, da idanu tabi ta, kafin tace, "a'a ke kuma da waye ne kike ta wannan kumburin? Koro ki suka yi ne kika dawo yau?"

Sai da taja tsaki kafin tace, "ba koro Ni suka yi ba, Ni ce na dawo don ganin dama na". Taƙarishe maganar tana shigewa ɗaki

Taɓe baki Umma Sulaima tayi tace, "ina nan zaune ai zaki zo ki sanar dani duk abinda ke faruwa". Taci gaba da abinda take yi.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

             *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN*💧💧

*MALLAKAR:*✍️
             _NAFISA ISMA'IL LAWAL*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT *🧝🏻‍

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A*✍️

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

   .....   *SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga mahaifiya ta Abar Alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love you so much Momma._  ❤️

*HIKIMAR FARILTA SALLAH*
      '''An farilta sallah domin a cikin ta akwai godiya ga Mani'imcin sarki jalla Ta'ala, wanda yake shi ne macancancin godiya da yabo, kuma shi ne kaɗai muka keɓe shi da ruku'u da sujada. Ba wani mahaluki da ya dace da wannan. Idan wata masifa ta sami mutum yakan yi maza ya fake da Allah ta yin Sallah, kamar dai yadda Allah yayi umurni a cikin suratul Baƙara, aya ta 45 da cewa:
       "Kuma ku nemi taimako da yin haƙuri, da Sallah".
    Ganawar da bawa yake yi da Ubangijin sa a cikin Sallah ita ce bauta wadda take ƙarfafa zumunta tsakanin bawan da Ubangijin nasa. Ubangiji kuma yana yi wa bawan baiwar darajar samun kusanta da shi. Hikima ce kammalalliya da aka farilta sallah, don kuwa ta yin Sallah ne ake kankare wa bawa zunubai, muddin dai ya yi sallah yadda ake so.
     An ruwaito cewa annabawan da suka wuce, ko wannen su yana da Sallah da yake ibada da ita. Sallolin suna da lokatai biyar; asuba, azahar, la'asar, lokacin faɗuwar rana da na isha'i. Ashe za mu lura cewa Allah ya tara wa Annabi da al'umma tasa sallolin dukan annabawan da suka gabata.
    Allah ya sa mu dace.'''





*________________________________*

              *PAGE 10*

*________* *AFTER TEN DAYS*

    Gaba ɗayan su suna zaune a Parlour da misalin ƙarfe 09:00pm na dare, bayan sun gama cin abinci Abba ya tsayar da su a cewar, "Zai yi magana da su," in ka ɗauke Baby da take barci a saman kujera kowa ya zauna ya nutsu yana sauraron Abban

Sunan ABUL KHAIRI Abba ya kira

Sai ya ɗago kansa yana kallon sa tare da amsa mishi cikin girmamawa

"Na san baka mance maganar da muka taɓa maka shekaru biyu baya da suka wuce zuwan Maimuna gidan nan ba, da kuma maƙasudin zaman nata a gidan?"

A tare gaban Maimuna da na ABUL KHAIRI suka yi mummunan buga wa, wanda har sai da Maimuna ta saka hannun ta ta dafe ƙirjin ta tana sake sad da kanta ƙasa tare da runtse idanu

Shi kuwa ABUL ya kasa cewa Abban komi, illa kafe sa da idanu da yayi yana sauraron yanda gaba ɗaya jikin sa ya sauya da wani irin yanayi me wuyan fassara wa, tare da bugawan zuci da fargaban abinda ke shirin faruwa da shi ɗin da har Abba yake son tayar da maganar

"Kayi shiru Babana ana maka magana?" Cewar Mamy da ta tsare sa da idanu tana karantan yanayin nasa

"Ina ji ai Mamy". Yafaɗa a hankali yana mayar da kansa ƙasa

Abba yace, "to maganar ce yanzu zamu yi ta, don mun rigada mun tsayar da magana nan da shekara ɗaya me zuwa idan ta gama karatun ta". Sai ya mayar da idanun sa kan Maimuna, ya kira sunan ta

A hankali Maimuna ta amsa mishi cike da tsananin fargaban da bata san dalili ba

"Maimuna muna fatan zaki yi mana wani alfarma a matsayin mu na iyayen ki, wanda baza mu taɓa zaɓa miki abinda zai cuce ki ba, sai dai ma idan mun ga abun dake shirin cuta miki mu yi gaggawar tare wa. Mun yanke shawaran haɗa ku aure dake da yayan ki ABUL KHAIRI. Da fatan zaki yi mana biyayya kamar yanda muka nemi alfarma wajen ki?"

Lumshe idanuwan ta tayi hawaye na zubo wa a saman kuncin ta suna ɗiga a ƙasa, take jikin ta ya soma rawa wanda ya saka ta kasa ma buɗe baki bare tayi magana

Batool dake kusa da ita, cike da sanyin jiki ta saka hannun ta ta riƙo nata tana matse wa a cikin nata

"Maimuna.." Mamy ta kira sunan ta cikin sanyin murya

Sai dai har a time ɗin ta kasa amsa wa Mamy, kuma ta kasa ɗago kanta

Mamy tace, "idan har ba kya son wannan haɗin kiyi magana kin ji? don babu wanda zai miki auren dole ɗiya ta, Ni da Mahaifiyar ki ne muke son mu haɗa ku, kuma kinga zaɓin mu be zama dole ya zama zaɓin ku ba, idan har ba kya so, to, babu wanda zai miki tilas".

ABUL KHAIRI dake sauraron duk abinda ke faruwa, zuciyar sa na wani irin tuƙuƙi tamkar ya tashi ya maƙure Maimuna, ita kawai yake jin haushin ta a halin yanzu, jira kawai yake yi yaji amsar da zata ba su. Runtse idanuwan sa yayi jin muryan ta me tsananin sanyi ya bugi kunnen sa

"Na amince".

Gaba ɗaya da Abba da Mamy murmushi suka saki

Abba yace, "yauwa ƴar albarka, dama mun san baki da matsala baza ki taɓa watsa mana ƙasa a idanu ba, Allah ya miki albarka".

Batool ce kawai ta amsa, fuskar ta cike da murmushi tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login