Showing 69001 words to 72000 words out of 88313 words

Chapter 24 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt

a Kan Umma, na gode Baba".

"Ki dena min godiya kin ji? Wa nake dashi a duniya sama daku da zan kasa muku abinda kuke so? insha Allahu ABUL KHAIRI sai kin aure sa muna nan da ke".

        Umma Sulaima dake waje tana sauraron komi tayi shewa tace, "hehehe yau ake yin ta, wahala ce bata ishe ka ba wlh muddin kace zaka biye mata".

Uncle Sani da ya fito ya shura takalman sa ya saka be ce mata komi ba ya wuceWar sa waje

Ita kuma sai habaici take musu tana faɗin, "ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta".






▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

          Jollof rice and veggies ta girka musu, sai ta haɗa musu kunun aya tunda duk tana da kayan haɗin. Sai da aka kira magriba ta gama komi ta shirya su a kan dainning

Har a lokacin Baby tana kwance tana barci bata tashi ba

Zuwa tayi ta tashe ta suka wuce ɗaki don yin alwala.


        ABUL KHAIRI shima barcin ne ya kwashe sa tun sanda ya gama shan ruwan Lipton ɗin, sai da yanzu da yaji kiran sallah ya tashi ya shiga Toilet yayi alwala ya fito ya wuce masallaci.




        Bayan sun gama sallan Kur'ani ta ɗauko musu suka yi karatun tare, har sanda aka kira sallan isha'i kafin su tayar suka yi, suna idar wa wanka ta shiga ta fara yi kafin ta yiwa Baby, ta shirya ta cikin riga da wando na Barcin ta, sannan ta iza ta Parlour ita kuma taci gaba da shirin ta, bayan ta gama itama ta sanya riga da wandon na barci masu santsi, sun lafe mata sosai a jiki kuma sun yi mata mugun kyau, hula ta sanya ta fita Parlour

A lokacin ABUL KHAIRI ya dawo daga masallaci suna zaune da Baby suna kallo. Fitowan Maimuna da ƙamshin turaren ta da ya bugi hancin sa shi ya jawo da hankalin sa gare ta, da kallo kawai yake bin ta ya kasa ɗauke ido a kanta har sanda ta dangana ga wajen dainning, sai ya lumshe idanu kawai yana saka hannun sa a goshi, tsawon lokaci yana a haka kafin kuma ya buɗe idon sa da suka soma kaɗa wa ya mayar kan Baby yace da ita, "get up and go eat".

Tashi tayi suka wuce kan dainning ɗin

Lokacin dama Maimuna har ta gama zuba musu tana shirin kiran Baby ne, ɗago kan da zata yi suka haɗa idanu tayi saurin janye nata tana zama kanta a ƙasa

Shima zaman yayi Baby ta Zauna a gefen sa da ya raba su

Abincin suke ci kowa yayi tsit

ABUL KHAIRI kansa na ƙasa sai cakuɗa abincin yake yi ya gaza ci, idan ya kai loma ɗaya sai ya jima kafin ya sake kaiwa bakin sa

Sai duk hakan ya saka Maimuna a tunanin, "ko abincin be masa daɗi bane?" Ta rasa yanda zata yi ta tambaye shi, dabara ya faɗo mata sai ta kalle sa tace, "Ko kana buƙatan wani abu ne?"

Ɗago kai yayi ya kalle ta yana me tsayar da cokalin cak, ido cikin ido suka kalli juna

Hakan yasa ta kasa jure wa ta sauke nata idon a ƙasa jiki a matuƙar sanyaye

Shi kuwa kasa janye nashi idon yayi a kanta ya hau bin ta da kallo sai dai a baɗini tunani ya faɗa... Wayan sa da tayi ƙara yasa ya mayar da hankalin sa ga wayan, ajiyan numfashi ya ja kafin ya miƙe yana faɗin, "ki ɗauki wayan nan ku yi magana, ki sanar mata ba na wajen, idan kin gama ki kawo min ɗaki". Daga haka ya wuce abin sa ɗaki

Sakato Maimuna tayi ta kasa motsi illa juya maganar nasa da take yi, "da ita yake yi ko kuma wace?"

Wayan Baby ta miƙo mata tace, "Aunty ga shi zai tsinke".

Kallon ta tayi sai kuma ta amshi wayan, a lokacin har ta tsinke sai ga wani kiran, wayan tabi da kallo ganin Number babu suna, ta kasa ɗaukan wayan daƙyar tayi ƙarfin halin amsa wa zuciyar ta cinkushe da tunani, sai dai koda ta kara a kunnen shiru tayi ta kasa magana

Sai da can ɓangaren ne Rahina tace, "Hello Aslm alaikum".

Jin muryan mace sai ta amsa

Shiru ne ya biyo bayan sallaman nata

A tunanin ta ko bata ji bane sai ta sake amsa mata

"Ina me wayan?"

Maimuna tace, "ba ya kusa".

"Ki kai mishi".

Bata san sanda ta samu kanta da faɗin, "ya shiga wanka". ba

Ƙitt ta kashe wayan

Ita kuma tabi wayan da kallo kamar ta sami t.v

"Aunty kawo in Kai mishi wayan".

Miƙa mata tayi ta koma taci gaba da cin abincin ta, amma zuciyar ta ta matsa mata da son sanin wace ce da har ya iya bata wayan? Shi meyasa be amsa ba sai ita? Sai kuma ta taɓe baki a ranta tace, "ta yiwu yan matan sa ne, dama ai ɗan iska ne". Wani iri taji a zuciyar ta da faɗar kalman, sosai ta ji wani abu ya soke ta amma kuma sai tayi tunanin, "to Meye nata da damuwa rayuwar sa ne". Tashi tayi tsam ta haɗa Plates ɗin, ko iya kaiwa kichen bata samu damar yi ba ta wuce ɗakin ta, kai tsaye kan gadon ta ta faɗa tana me lumshe idanuwan ta tana sakin numfashi.. shigowar Baby yasa ta ɗago kai tana kallon ta

"Aunty Yaya ya CE ki zo". Tayi maganar tana hayo wa kan gadon

"Ya ce in zo?" Ta maimaita maganar a fili ba tare da ta sani ba

"Eh haka yace in CE Miki".

Bata sake cewa komi ba illa miƙe wa da tayi ta fita ta nufi nasa ɗakin, sallama tayi ta shiga

Yana gefen gadon sa zaune da wayan sa a hannu daga shi sai dogon wando da Singlet, be ɗago kai ya kalle ta ba yace, "me nace miki idan kika gama wayan?".

Nan gaban ta ya faɗi, cikin rawan murya tace, "ka ce idan na gama in kawo maka wayan".

"Shi ne kika aiko ta? Kin kai girman da ke baki isa ki kawo min ba wato?"

"A'a wlh, kayi haƙuri ita tace in bata ta kawo maka".

Sai a lokacin ya ɗago kai ya kalle ta fuskar sa murtik, "duk ranan da na sake sanya ki abu kika sako min wani a ciki zaki ga yanda zan yi dake, ke a garin ku haka ake koya miki baza ki iya zuwa ki gyara min ɗaki ba? Common wuce ki wanke min bayi tunda ba a haka zan yi amfani dashi ba". Sai yaja dogon tsaki yana faɗin, "a rasa ma wacce za'a aura min sai wannan tatsitsiyar yarinyan, basu iya komin su ba sai an nuna musu".

Ita dai tuni ta wuce Toilet ɗin da sauri jikin ta na ci gaba da rawa. A ɗan ƙanƙanin lokaci ta gama wanke masa, Allah-Allah take ta fice kar wani tsautsayi yasa ya sauke mata bala'in sa a kanta. Tana gama wa ta fito ta fice ba tare da tace da shi uffan ba, tana jin sanda ya saki dogon tsaki ita dai ko tsayawa bata yi ba sai da ta ganta a ɗakin ta, oho dai tunda ta gama babu abinda yayi mata, ita lafiyan jikin ta ne kawai ba ta ƙaunar ya taɓa, tun sanda yayi mata wancan dukan take tsoron abu ya haɗa su.

       Koda ta koma ɗaki kwanciya suka yi, babu jima wa barci ya kwashe su. Sai asuba ta farka, tashin Baby tayi suka yi alwala suka gabatar da sallah, ita Babyn ta koma barci yayinda ita kuma ta soma gyara gidan, daga Parlour ta soma gyaran. Tana cikin yi ne ABUL KHAIRI ya dawo daga masallaci, gaishe sa tayi kanta a ƙasa

Be amsa ta ba ya wuce ɗaki don da haushin ta ya kwana, shi idan ba dole ba taya zai zauna da ita kullum tana ƙara masa matsala, dole ne ma ya samo mafita gaskiya bazai yiwu ba.


         Ci gaba da aikin ta tayi bata damu da rashin amsa mata ba. Duk wani ayyukan ta sai da ta gama har Breakfast, ta so ta shiga ta gyara masa ɗakin amma kuma tana jin tsoron kuma wani laifin, gwara zuwa anjima idan sun dawo sai ta gyara masa. Suna gama shirya wa suka yi Breakfast suka zauna zaman jiran sa

Yau ma be yi Breakfast ɗin ba koda ya fito, fita kawai yayi abin sa

Haka suka bi bayan sa suka shiga yaja motan suka tafi, yana kai su ya ajiye su ya wuce Company.. office ɗin Abban sa ya soma zuwa, amma lokacin be ƙariso ba shiyasa ya wuce nasa kai tsaye.


       Kamar awanni 2 da zuwan sa Aka yi masa Nocking. Izni ya bayar

Rahina ce ta buɗe ƙofan ta shigo taci uwar kwalliya gyale a rataye a wuya

Yana ganin ta ya ɗauke kai a kanta yana sake tamke fuska, be ce mata komi ba har sanda ta samu wuri ta zauna

Sai tace, "yallaɓoi Barka da safiya, fatan na same ka lafiya?"

Shiru yayi be ce mata komi ba

Sai tayi dariya tana faɗin, "ba ma wannan ba. I called you yesterday but you gave your wife an answer. Why didn't you answer?"

Tsare ta yayi da ido, amma kuma ya kasa aiwatar da abun da yake shirin mata, sosai yake jin haushin ta a ransa amma kuma be san meyasaka ba gaba ɗaya ya kasa dakatar da ita a rayuwar sa, ya rasa meyasa ba ya iya mata abinda ke ransa

Be san cewa sai da ta shirya kafin ta dawo gare sa ba, ta san ta sauƙi baza ta taɓa samun sa ba, yayi mata nisan da ko a mafarki baza ta iya samun shi ba, shiyasa ta shirya tsab kafin ta sake tunkaran sa da soyayyar ta. Wannan dalilin ne yasa ba ko wani abu dake zuciyar sa yake iya sanar mata ba, ba don haka ba da tuni ya ci uwar ta ya saita mata hanya...

Katse sa tayi da faɗin, "kayi shiru My Love. Wlh Ina matuƙar ƙaunar ka meyasa baza ka bani dama in maye gurbin Ziyada ba?.."

Muryan sa na rawa ya katse ta da faɗin, "kar in sake jin kin kira sunan Ziyada a nan wurin, babu wanda ya isa ya maye min gurbin ta, Please Rahina ki fita a rayuwa ta kina ji ko?"

Dariya ta saki tace, "Fine. Bazan sake ambatan ta ba tunda nima ba daɗin abin nake ji ba, amma ka sani ABUL KHAIRI ina matuƙar ƙaunar ka, kuma bazan taɓa iya rabuwa da kai ba har sai ka aure Ni, don Allah mene ne laifi na idan na nuna maka soyayya? Meyasa baka da tausayi ne ABUL KHAIRI?"

Shiru yayi yana ɗauke kansa a kanta, sai dai ya kasa ci gaba da aikin da yake yi, zuciyar sa ke kawo masa tunanin, "shin me zai saka bazai iya amsar ta a matsayin maganin matsalar sa ba? Tunda wancan bata da amfani a wajen sa, infact ma bazai taɓa zuwa wajen ƙanwar sa da irin wannan matsalar ba, shi fa ganin ta yake yi kamar ƙanwar sa Batool," shiyasa kawai a ransa ya yanke shawarar ya sake aure wataƙil hakan zai fi mishi tunda bazai dauwama a haka ba... Kaɗa masa hannun da Rahina tayi a fuska shi ya dawo dashi hayyacin sa, ya dube ta ba tare da ya sassauta fuskar sa ba

"Kayi shiru Honey? Meyasa baza ka aure Ni ka tsamo Ni daga cikin ƙuncin da nake ba?"..

Katse ta yayi da faɗin, "Please don Allah ki bar Ni haka in huta, ki je zan neme ki".

Jin hakan yasa ta saki fara'a cike da farin ciki tace, "da gaske kake yi don Allah? Yau kai ne da faɗa min hakan?"

Gyaɗa mata kai kawai yayi yana ɗan sakin guntun murmushi

Wani farin cikin ne ya sake kama ta, "Ok zan jira ko yaushe ne Please ABUL KHAIRI, Kar kace zaka shanya Ni don Allah?" Ta ƙare maganar da shagwaɓa

Bata san cewa abinda ke matuƙar ɗaga masa hankali ba kenan, ya ga mace tana masa shagwaɓa, shiyasa be ja zancen ba daƙyar ya furta mata, "nayi miki alƙawari zan neme ki please ki je". Da haka dai ya samu ta bar masa Office. Kifa kansa yayi a saman table ɗin, "shin ta ina ma zai fara?" Dole shawaran zuciyar sa zai ɗauka gwanda ya aure ta hakan shi ne kaɗai maslaha, domin ko ba ita ba dole ne ya auro wata, tunda ga shi ya sami me son shi why not bazai aure ta ba? Ya san dai ya rasa wacce yake ƙauna har abada, duk wata mace da zata shigo gidan sa a babun lalura ne, yana ji a ransa har ya koma ga mahalicci bazai taɓa samun wacce zata maye mishi gurbin Ziyada ba. Duk da ta wani ɓangaren ko kaɗan Rahina bata mishi ba, amma kuma yana ji kamar akwai abinda ke ingiza shi gare ta, har idan ya ganta sai ya gaza sukuni kuma ya kasa taɓuka mata komi.. ajiyan zuciya ya sauke yana ɗagowa tare da dafe kansa, a fili ya furta, "to ya zan yi in je ma su Mamy da zancen ƙara aure na? Me za su ɗauke ni bayan two weeks kenan da auren?"










*Sunday 12 September 2021.*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

            *ABUL KHAIRI*

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧

*MALLAKAR:*✍️
             _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻‍♀️


*بسم الله الرحمن الرحيم*


*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A*✍️


*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️






*________________________________*

              *PAGE 36*

*________* Wajen ƙarfe biyu da rabi Uncle Sani ya isa gidan Mamy, a lokacin Abba ba ya nan sai Mamy ɗin ya tarar, itama dawowar ta kenan daga aiki

Sulaiman na zaune a Parlour yaji Nocking, shi ne yaje ya buɗe masa. Gaishe sa yayi cikin fara'a

Amma sai be amsa ba illa sake kicin-kicin da fuska da yayi, sai da ya shigo ciki sosai sannan ne ya kalle sa yace, "lafiya. Ina ita Deebizan? kira wo min ita".

"Ok". Kawai Sulaiman yace yana nufan ɗakin Batool, Nocking yayi mata, da ta fito yace mata, "kira Mamy Uncle Sani ne yazo".

"To". Tace dashi tana fitowa, a nan ta hangi Uncle Sanin har ya hakimce a saman kujera, tace, "Uncle Ina wuni".

"Lafiya lau".

Wuce wa tayi kawai ɗakin Mamyn ta je ta sanar mata ta dawo ta shige ɗaki tana taɓe baki, "ɗan rainin hankali mutane sai baƙin hali kamar dangin fir'auna". Taja tsaki tana rufe ƙofan ta

Shi dama Sulaiman tuni ya fice haraban gidan abin sa.



      Mamy na fito wa ta soma gaishe sa cikin faram-faram kamar yanda ɗabi'an ta ne hakan, sai ta wuce ta kawo masa ruwa kafin tace, "bari in sawo maka abinci Yaya".

"A'a dama kin bar shi don ba shi ya kawo Ni ba". Yayi maganar yana ciccin magani

Murmushi kawai Mamy tayi tana zama

Sai da ya sake ɗaure fuskar sa kafin yace, "maganar ɗiya ta Azeeza nazo miki dashi, yarinyan nan gaba ɗaya na kasa gane kanta ban san me ta gani a wurin ɗan ki ba da har ta nace sai ta aure shi, don haka nake son Idan da yiwuwa a haɗa su aure".

"Aure kuma Yaya Sani?"

"Eh Aure, shi nake nufi aure".

Mamy tace, "to yaya duka-duka yaushe ABUL KHAIRIN yayi aure da har za'a sake mishi wani maganar? Sannan ma ai shi ba ya son ta bare Ace zamu haɗa su".

Miƙe wa yayi yana ɗaga murya da cewa, "eh dole ki ce haka tunda ɗiyar ƴar uwan ki ta fi ta, kin fi son ta tunda ita ga shi kin haɗa su aure, sai ga shi nawa ɗiyar ne kike son ta shiga duniya a kan banzan ɗan ki, wlh Deebiza idan kina son zaman ki da arziƙi dole ne sai ABUL KHAIRI ya auri Azeeza".

Kawai sakato Mamy tayi tana bin sa da kallo kamar t.v, ganin faɗan nasa yayi yawa sai tace, "to shikenan Yaya ka bari zamu yi shawara da Abban su da shi ABUL KHAIRIN idan da yiwuwar hakan sai ayi, amma gaskiya sai dai ka bari ko nan gaba tunda bazai yiwu yanzu ayi musu aure ba saboda be daɗe da yi ba".

"Oho can dai ta matse miki, Ni dai na gaya miki bazai yiwu ace a sanadin ɗan ku ɗiya ta ta rasa farin cikin ta ba, duk yanda ma za'a yi sai dai ayi ku haɗa su aure kawai". Yana gama faɗar haka ya kaɗa bujen rigan sa ya fice yana ci gaba da tsiyan

Sulaiman dake haraban gidan a tsaye da kallo kawai ya bi shi, sai kuma ya juya ya shiga cikin gidan, ganin Mamy har yanzu a zaune sai ya isa wurin ta yana tambayar ta, "ko lafiya?"

Time ɗin itama Batool tuni ta fito jin hayaniyar Uncle Sanin da abinda yake cewa

Haka shima Amir da aka tashe sa daga barci wurjan-jan ya fito yana faman mitstsike idanu.

          Mamy sai da ta sauke  numfashi me ƙarfi kafin tace, "to ba lafiya ba dai za'a ce Sulaiman, wai maganar Azeeza ya kawo a haɗa su aure da ABUL KHAIRI".

"Wani ABUL KHAIRIN kuma?" Sulaiman ɗin yayi tambayar da mamaki

"ABUL KHAIRI dai na nan gidan".

Sai kawai ya fashe da dariya yana cewa, "amma dai Uncle Sani ya soma shan ƙwaya ne dai ko? Idan ba haka ba taya zai zo miki da wannan shirmen nashi?".

"Ka ga naka Sulaiman, yanzu Uncle ɗin naku ne yake shan ƙwaya?"

"Wlh kuwa Mamy idan dai ba ƙwaya yake sha ba Ni dai ban ga wani me hankalin da zai zo da wannan maganar ba, yaushe ma yayi auren da za'a sake kawo mishi wata?"

Batool na dariya tace, "nima abinda na gani kenan Yaya, ta yiwu wlh Uncle ya soma afa wani abun".

Hararan ta Mamy tayi kafin tace, "kai ba na son iya shege wlh ku shiga hankalin ku".

Su kuma sai dariya suke yi

A lokacin ne Abba ya shigo ya cidda su a haka, zama yayi yana tambayar ba'asi bayan da ya amsa gaisuwar nasu

Daga Sulaiman ɗin har Batool suka haɗa baki wajen sanar da Abban abinda ke faruwa

Kallon Mamy yayi yace, "Wai haka ne me ke faruwa?"

"Hmm Abban su da gaske ne, yanzun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login