Showing 21001 words to 24000 words out of 88313 words
Chapter 8 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt
kallon Maimuna da ke sake sunkuyar da kanta
"Kai kuma kaji ta amince, saura kai ka amincen ne ko kuwa har yanzu shirun ne maganar ka?" Cewar Abba yana tsare ABUL KHAIRI da idanu
Kansa a ƙasa cike da tsananin takaicin Maimuna gami da tsanar ta yace, "abinda kuka zaɓa min nima shi ne zaɓi na".
Sosai amsar nashi ya faranta ransu, cikin fara'a sukai ta saka musu albarka, kamin suka ba su damar tafiya
ABUL KHAIRI ya soma tashi ya shige ɗakin sa
Su ma su Maimuna miƙe wa suka yi suka bar parlour'n, suka shige ɗakin su.
Da shigar su Maimuna ta nufi kan gadon ta ta zauna, kanta a ƙasa ta hau zub da hawaye a hankali
Batool ƙarisowa kusa da ita tayi ta zauna gefen ta fuskar ta yalwace da murmushi, don sosai wannan haɗin yayi mata daɗi, ta saka hannu ta ɗago kan Maimuna tana shirin magana, sai ganin hawaye saman fuskar ta tayi, take a nan fara'an ta ya gushe, tayi saurin tambayan ta da, "lafiya, mesaya take kuka?"
Shiru Maimuna tayi mata tana ci gaba da kukan ta
Sosai jikin Batool yayi sanyi, ta saka hannu tana share mata hawayen
Amma kuma Maimuna ta kasa dena kukan, sai yi take yi har da shashsheƙa
"Maimuna meyasaka kika amsa musu bayan kin san ba kya son shi? Idan har kin san zaki Cutu me zai saka ki amsa musu?"
Lumshe idanuwan ta Maimuna tayi tana sauke ajiyan zuciya akai-akai, ba tare da hawayen sun tsagaita daga zubar da suke yi ba, sai ta gyara ta aza kanta saman pilow ba tare da ta tanka wa Batool ba
Ita kuma Batool sai ta tsaya kawai tana kallon ta, tsawon mintuna goma suna a haka amma Maimuna bata dena shashsheƙan kukan da take yi ba
"Sister bazan iya ganin ki cikin wannan halin ba, zan je in sanar wa da su Abba ba kya son wannan haɗin". Batool tafaɗa tana miƙe wa zata fice
Da sauri Maimuna ta tashi zaune ta riƙo mata hannu, cikin rawan murya tace, "a'a.. kar ki je don Allah".
Kallon ta tayi na ɗan wani lokaci, kafin ta koma ta zauna, cikin tausayawa tace, "meyasa baza ki bar Ni in je in sanar musu ba tunda ke kin kasa? Shikenan kuma sabida wannan sanyin halin naki sai ki zauna koda yaushe kina cutan kanki? Tabbas wannan haɗin yayi min daɗi matuƙa, amma kuma yanzu da na tuna irin zaman da kuke yi da yaya ABUL kullum cikin tsangwaman ki yake yi, sai naji sam hakan ba me yiwuwa bane, zaman ku a inuwa ɗaya babban illa ne a gare ki".
Murmushi Maimuna ta saki, tana son mayar da ƙwallan da ya cika mata idanu, sai dai kuma bata yi nasaran hakan ba, sai da suka zubo saman fuskar ta, ta saka hannun ta ta share still tana murmusawa tace, "ke ma kin faɗa da bakin ki haɗin nan ya saka ki farin ciki, to su ma su Mamy hakan yake a wurin su, to me zai saka Ni in ɓata muku wannan farin cikin a kan abinda be fi ƙarfi na ba? Kar ki manta Mamy tace ita da Ummu suke son su haɗa mu, kinga kuwa idan har na nuna ba na so na san Mamy baza ta taɓa bari ayi auren nan ba, wanda kuma hakan dole zai saka su ji babu daɗi a ransu, Ni kuma ba na fatan hakan, zan so in faranta musu rai kamar yanda suka nemi alfarma a waje na, Ni babu wanda nake so a raina tunda har yanzu ban taɓa yin saurayi ba, sannan kuma ba na ƙin Yaya ABUL KHAIRI a cikin raina, kawai dai na kasa jure wa ne, amma ban san dalilin da ya saka nake yin kuka ba.." ta ƙarike maganar nata tana me fashe wa da wani sabon kukan
Batool itama hawaye ta soma yi na tsananin tausayin Maimuna, ta san halin Maimuna tana da sanyin hali da tsananin haƙuri, zata iya jure ko ma mene ne sabida ta faranta wa makusantan ta, Allah yayi ta da haƙuri da jure ko wani hali ne da ya same ta, tamkar dai Mamy ce ta haife ta, halin su ya zo ɗaya matuƙa, domin kuwa Maimuna ita kaɗai ce ta fita Zakka a ɗakin su, gaba ɗaya sauran ƴan uwanta halin Ummu suka biyo, basu da haƙuri ko kaɗan, idan kayi musu za su rama ko kai uban waye, amma ita Maimuna idan ka cuce ta, sai dai ta bi ka da murmushi, halin ta daban ne, har tafi Mamy haƙuri da sanyin hali, ga ta shirun ta yayi yawa matuƙa, akasari tafi son yin murmushi a kan ta buɗe baki ta baka amsa.
Rungume ta Batool tayi suka ci gaba da kukan tare.
▪️▪️▪️
ABUL KHAIRI tunda ya shiga ɗakin sa ya haɗa kai da gwiwa, sosai ya shiga cikin wani hali da abinda ya faru yanzu ɗin, gaba ɗaya ya nemi natsuwar sa da farin cikin sa ya rasa. Ba zai taɓa iya yin ma iyayen sa musu ba, sabida be saba ba, be kuma tashi da hakan ba, tun farko a kan turban da suka raine shi kenan, ba su taɓa neman abu wajen sa ya ƙi musu ba, don haka wannan ma ba ya tunanin zai iya musa musu, sai dai kuma ya ɗau alwashi a ransa sai ya ƙuntata wa Maimuna tunda har ta amince da auren nan, yana ganin kamar amincewar ta shi ne yasa auren su zai yiwu, kuma hakan shi ne babban kuskuren da ta tafka a rayuwan ta, da bakin ta sai ya saka ta dawo ta faɗa musu ba ta son auren, bazai taɓa bari ayi auren nan ba, duk hanyar da zai bi sai yabi ya saka ta ta faɗa musu ba ta son auren nan..
Lumshe idanun sa yayi yana jin wani irin tuƙuƙin baƙin ciki a zuciyar sa, ya jima a haka kafin ya ɗago kansa ya soma neman inda ya ajiye wayan sa, can ya hange sa saman mirror, a hankali ya sauka ya ƙarisa wajen ya ɗauka, komawa yayi ya zauna a bakin gadon ya soma duba wayan, missed calls ɗin Ziyada ya gani har wajen goma, yayi dialling Numban, sai dai a kashe ne, sosai ransa ya sake ɓaci, ya ajiye wayan yana kwanciya cike da baƙin ciki da tsanar Maimuna a ransa, Allah-Allah yake yi gari ya waye ya aiwatar da ƙudirin sa a kan ta. Numfashi yaja yana sake gyara kwanciyar sa, daƙyar barci ya ɗauke shi a wannan daren cike da mafarkai kala-kala, har da mummunan mafarkin da yayi a kan Ziyada ta rabu dashi sabida auren sa da Maimuna, a firgice ya tashi jikin sa duk ya jiƙe da zufa, sosai hankalin sa ya tashi da mafarkin nan duk da kuwa ya san ba gaske ne ba, amma kuma a yanda ya ɗauka hakan zai iya faruwa a gaske ɗin, tunda ya fi kowa sanin baƙin kishin Ziyada. Be iya komawa barcin nan ba a daren, illa zagaye ɗakin da yayi ta yi ya hana kansa sukuni.
.
_Hmm akwai chakwakiya fa, yanzu ne aka soma wasan._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
𝙽𝚊 𝚜𝚊𝚍𝚊𝚞𝚔𝚊𝚛 𝚐𝚊 𝙼𝚊𝚑𝚊𝚒𝚏𝚒𝚢𝚊 𝚝𝚊 𝙰𝚋𝚊𝚛 𝙰𝚕𝚏𝚊𝚑𝚛𝚒 𝚗𝚊, 𝚞𝚠𝚊𝚝𝚊 𝚖𝚊𝚐𝚊𝚗𝚒𝚗 𝚔𝚞𝚔𝚊 𝚗𝚊, 𝙸 𝚕𝚘𝚟𝚎 𝚢𝚘𝚞 𝚜𝚘 𝚖𝚞𝚌𝚑 𝙼𝚘𝚖𝚖𝚊 ❤️
*________________________________*
*PAGE 11 & 12*
*________* Washe gari da wuri ya bar gidan zuwa wajen aiki. Koda ya je Office be zauna ba, yayi ta zagaye yana faman ƙulla wa da kwance wa a zuciyar sa, sai da ya tabbatar Abban sa ya zo Companin kafin ya lallaɓa ya baro. Gida ya wuce kai tsaye tunda ya san itama Mamy ta tafi wajen aikin ta.
Yana shiga Parlour ya tarar da Baby da Amir suna kallo
Da gudu Baby ta taso ta nufo sa tana murna. "Yaya sannu da zuwa". Tafaɗa da ƙarfi tana dariya
Jan hancin ta yayi shima yana murmushin yace, "Auta na an samu hutu sai zaman kallo ko?"
Still dariya tayi tace, "Yaya ai ba Ni na kunna ba Ya Amir ne".
A lokacin ne Amir yayi masa sannu da zuwa, yana ƙaryata abinda Baby ta faɗa
Yace, "to ya isa haka, ai ban hana ku kallon ba sai dai ku riƙa yi kuna karatu, musamman na islamiyya tunda yanzu kun samu hutu, lokacin da Yakamata ku riƙa yi kenan".
"To Yaya".
"Yauwa good Baby". Ya faɗa yana sake jan hancin ta, sannan ya miƙe daga ranƙofowar da yayi zuwa tsawon ta, yace, "kira min Maimuna ta same Ni a ɗaki".
Da sauri ta amsa mishi ta nufi ɗakin nasu
Shi kuma ya wuce cikin ɗakin sa.
Da shigar sa ya wuce kan gadon sa ya zauna, wayan sa ya zaro cikin aljihu yana latsa wa, sai kuma ya miƙe ya shige Toilet.
Lokacin ne Maimuna tayi Nocking tana jiran a bata iznin shiga, sai dai jin shiru sai ta sake yin Nocking ɗin, nan ma shirun da taji sai ta buɗe ƙofan ta shiga bayan da tayi sallama. Bata ga kowa ba, sai ta ja ƙafafuwan ta a sanyaye kamar yanda ta saba koda yaushe, ta nufi ciki ta duƙa a ƙasa tana jiran sa, kanta a ƙasa yake tana murɗa yatsun hannun ta, amma kuma a baɗini tsoro ne fal a zuciyarta, tana tunanin, "meyasaka Ya ABUL ya dawo gida kuma ya nemi ganin ta?" Tabbas tana ji a ranta ba alkhairi bane kiran nan da yayi mata..
Buɗe ƙofan Toilet ɗin da yayi, shi ne ya katse mata ɗan guntun tunanin nata, ta ɗago kai tana kallon sa, ganin fuskar sa a matuƙar ɗaure sai ya sake ɗaga mata hankali, da sauri ta mayar da kanta tana gaishe shi cikin girmamawa
Be ce mata komi ba sai da ya zauna a gefen gado, ya kuma ɗaukar wayan sa ya soma latse-latse, sai da ya gama can kuma ya kara a kunne yana sakin murmushi me sauti. "wai har yanzu barcin kike yi baki tashi ba?" Yayi maganar cikin wani salo na kashe murya
Daga can Ziyada ta ba shi amsa cikin shagwaɓa, tana faɗa masa, "kasala ne take ji, shi ne ya sa ta kasa ta shi."
Lumshe idanuwan sa yayi, kafin ya buɗe yace, "ko in zo in taimaka miki ne?".
Maimuna na a yanda take tana sauraron sa, sai dai ba ta jin muryan wacce yake waya da ita. maganar da yayi yanzu ɗin ya hautsina mata ciki, har ta ɗago tana kallon sa..
"Kin san idan har na zo ba iya nan zan tsaya ba, Ni zan miki wankan da kaina, sannan in shirya ki, kin san ba na son wahalar ki fa, amma fa bazan tsaya a iya nan ba, zan...."
Da sauri Maimuna ta sake duƙar da kanta tana ƙudundune jikin ta, sabida yanda maganar nasa suka bata matuƙar kunya, ai nan da nan ta rufe kunnuwan ta jin sauran maganar sun fi ƙarfin tunanin ta bare ƙwaƙwalwan ta, tuni jikin ta ya soma rawa, a ranta kawai raya wa take yi, "dama haka Ya ABUL yake ba ya da kunya?"
Shi kuwa ko a jikin sa wai don a kwai ta a wajen, yana kuma lura da ita, don idanuwan sa a kanta suke, sai dai yayi tamkar ba ita yake kallo ba, kuma yana hakan ne da gayya don taji ɗin. ya ɗau lokaci yana wayan kafin ya gama, ya ajiye wayan a gefen sa yana ɗago kai sosai ya kalle ta, cikin yatsina da dakakken muryan sa ya ce, "kee! Zo nan".
Jikin ta na rawa ta janyo jikin ta ta iso gaban sa, cikin rawan murya tace masa, "ga ta".
"Ɗago kanki ki kalle Ni".
Kasa ɗago kan nata tayi sabida kunya irin nata, ga kuma maganar da ya gama yi yanzu a waya, ya saka ta sake jin kunya matuƙa
"Wlh idan baki ɗago kai kin kalle Ni ba sai na miki..."
Kafin ma ya ƙarisa maganar har ta ɗago kan nata ta zuba masa idanuwan ta, sai dai yanda idanun suka shige cikin na sa sai ta kasa jure wa, ta sauke ƙwayar idanun nata ƙasa
Ƙare ma fuskar ta kallo yayi, sai kuma ya yatsina fuska yana sake ɗaure fuskar sa yace, "kina ji na? Ina son ki je ki samu su Abba ki sanar musu ba kya son auren nan tun wuri, idan ba haka ba, kika kuskura kika shigo gida na, wlh tallahi sai na ƙabari ya fi ki jin daɗi, sai na wulaƙanta rayuwar ki, sai na sa kin gudu da ƙafar ki, babu ke babu samun rahama duk sanda kika zama mata a waje na, domin baki kai matsayin da zan haɗa shimfiɗa da ke ba. Ki sani zaɓi na baki, ko ki je ki san yanda zaki yi ki faɗa musu ba kya son auren nan, ko kuma ki dauwama cikin uƙuba da baƙin ciki har ƙarshen rayuwan ki".
Tun sanda ya soma maganar na sa, Maimuna ta duƙar da kanta tana hawaye
Sai ya daka mata tsawa a kan, "ta tashi ta bar masa ɗaki".
Har ta miƙe sai taji muryan sa ya kuma cewa, "I hate you! I hate you more than anything's in this world! sabida kina son ki shiga cikin rayuwa ta, kina son ki shiga tsakani na da wacce nafi ƙauna".
Bata iya cewa komi ba ta nufi ƙofa ta bar masa daƙin.
Tana fita, Batool dake zaune a Parlour ita da su Amir, sai dai su suna kallo ne, yayinda ita kuma tana tsimayen fitowar Maimuna. ganin ta da tayi sai tayi zumbur ɗin mike wa ta nufo ta da sauri ganin hawaye a fuskar ta. Riƙo ta tayi ta hau tambayan ta, "me yayi mata?"
A lokacin ne ABUL KHAIRI ya fito daga ɗaki, harara ya wulla mata, sabida tambayan da tayi wa Maimuna a kunnen sa ya sauka
Da sauri ta sad da kanta ƙasa cike da tsoro
Be ce komi ba ya taka ya bar parlour'n ya fita waje.
Ita kuma Batool jan hannun Maimuna tayi suka nufi ɗakin su. Suna shiga ta zaunar da ita saman gadon ta, itama ta zauna ta hau tambayan ta, "wani abun yayi mata?".
Amma Maimuna tayi shiru illa kukan da take yi
"Don Allah ki faɗa min abinda yayi miki, be kamata ki zauna kina zurfin ciki a kan abinda kika san tabbas akwai matsala ba. shin mene ne yace miki? Ko wani abun yayi miki ne?" Batool ta sake jero mata waɗannan tambayoyin
Ɗago idanun ta da suka kaɗa suka yi ja tayi ta sauke a kan Batool ɗin, cikin sanyin murya da rauni irin nata tace, "cewa yayi in sanar da su Mamy ba na son auren, domin ya ce idan na aure shi babu Ni babu farin ciki har abada". Sai ta sake fashe wa da kuka tana ɗaura kanta saman cinyoyin ta
Hannun ta Batool ta saka ta ɗaura saman bayan ta, nan ta soma rarrashin ta cike da tsananin tausayin ta, ita kanta ta rasa tunanin da zata yi domin ta sama mata mafita. "Me zai hana ki bi abun da ya ce miki, ina ga shi ne kawai mafita kamar yanda ya faɗa miki, wlh bazan iya juran ganin ki kina shan wahala wajen ya ABUL ba, tunda ba ya ƙaunar ki ki sanar da su Mamy kema ba kya son auren.."
"Taya kike tunanin Ni zan iya zuwa in sanar musu ba na son auren?" Maimuna tafaɗa hakan bayan da ta ɗago kanta tana kallon ta, sai taci gaba da faɗin, "wlh bazan iya ba, meyasaka shi bazai je ya faɗa musu ba? tunda shi yana da wacce yake so".
Batool tace, "yana da wacce yake so, haka ya faɗa miki?"
"Eh mana haka ya faɗa min, kuma a gaba na yayi waya da ita, sannan ya ce min ba ya ƙauna ta, ita yake so". Ta sake faɗar haka tana me fashe wa da sabon kuka
"To Ni zan samu Mamy in sanar mata tunda ke baza ki iya ba, kiyi shiru don Allah ki bar kukan nan".
Daƙyar Batool ta rarrashe ta tayi shiru, sai dai ta kasa taɓuka komi a ranan, dole ita Batool ɗin ne taje ta ɗaura musu girkin rana, ta bar ta nan a kwance tana faman tunani, gaba ɗaya ta hana kanta sukuni illa maganganun ABUL KHAIRI da take faman tuna wa, da kuma yanda makomar ta zai koma
Ta sani a ranta bata taɓa tsanar sa ba, duk halin da yake nuna mata bata taɓa jin haushin sa ba, kuma zata iya yin biyayya ta aure sa ta zauna dashi da zuciya ɗaya ko wanne irin wahala zai ba ta. sai dai itama zata so a raba auren nan tunda ba ya son auren nan, "amma ta ya?" Ita baza ta iya zuwa ta faɗa ba.
▪️▪️▪️
Koda Mamy ta dawo, Batool da kanta ta sanar wa Mamy abinda ke faruwa, dawowar da ABUL KHAIRI yayi da abinda ya faɗa wa Maimuna
Mamy bata iya cewa komi ba sanda Batool ta gama zayyano mata, sai da ta jima tana tunani kafin ta kalli Batool ɗin, tayi mata umarnin, "ta je ta kira mata Maimuna."
Bayan ta kira ta ne, Mamy ta sake tambayan ta, nan Maimuna ta sake faɗa kamar yanda Batool ta faɗa ɗin
Ajiyan zuciya Mamy ta saki, kana ta ce, "babu damuwa, insha Allahu bazan bari ayi auren nan ba, da yardan Allah maganar nan ta mutu daga yau, kema kuma ki cire komi a ranki kinji?"
Gyaɗa kanta Maimuna tayi, cike da sanyin jiki ta miƙe ta fice kamar yanda Mamy ta bata umarnin tafiya, sai dai sosai taji tausayin Mamy ganin yanda fuskarta ya kasa ɓoye damuwar dake zuciyarta, amma babu yanda ta iya.
Da fitar ta, Mamy ɗaukar waya tayi ta kira wo Ummu ta sanar mata da komi
Amma sai Ummu ta hau masifa a kan, "ABUL KHAIRI be isa ya hana su ƙulla zumuncin da suka daɗe suna buri ba".
Sai da Mamy tayi ta ba ta baki kafin