Showing 15001 words to 18000 words out of 88313 words
Chapter 6 - ABUL KHAIRI Complete Hausa Novels by Nafisa Ismail lawan.txt
ko ki neme Ni Ko?"
"A'a wlh Aunty, sai da na tambayi Umma Sulaima ina kike?"
Azeeza na kallon ABUL dake tafiya tace, "Yaya don Allah ku jira Ni nima zan bi ku".
Ko bi ta kanta be yi ba ya bar gidan, yayinda su Maimuna suka take masa baya
Riƙo hannun Batool tayi da itama zata bi bayan su kar ABUL yaji ta shiru, amma sai Azeeza ta riƙe mata hannu tana faɗin, "Plz Sister jira ni na ɗauko kayana mu tafi tare, kinga idan kika fita zai tafi ya bar Ni".
Waro ido Batool tayi tace, "a'a Aunty Azeeza bar Ni in tafi, sai dai ki je ki haɗo kayan zan faɗa masa ya jira ki, wlh idan ya ji Ni shiru tafiya zai yi".
Umma Sulaima dake tsaye tana sauraron su tace, "ai kuwa babu inda zaki bi su Azeeza, sakar ta ta tafi, wa billahil lazi kika bi su Ni dake ne, shashashan yarinya kawai, ki rasa ma wanda zaki manne ma wa sai irin tsiyan nan".
Turo baki Azeeza tayi tace, "wlh Umma babu uban da ya isa ya hana Ni bin su, ko Baba ne kuwa bare ke".
Ita dai Batool tunda ta samu ta zame hannun ta daga riƙon da Azeeza tayi mata, bata tsaya sauraron cacan uwa da ƴar ta ba tayi saurin fice wa, time ɗin ma har ABUL yaja motan yana da ninyan tafiya, ai da gudu ta ƙarisa wajen tana kiran sunan sa kamar zata yi kuka
Yana ganin ta yaƙi tsayawa, sai da yayi nisa kafin yaja birki
Time ɗin har Batool ta soma kuka tana bin motan da gudu, tana ganin ya tsaya ta sake sheƙawa a guje ta nufi motan, tana zuwa ta buɗe ta shige ya ja motan da gudu ganin Azeeza itama ta sheƙo wajen su, sai dai ya bar mata ƙurar motan
Ci je baki tayi cike da tsantsan takaici, Allah ya gani tana tsananin ƙaunar ABUL, kuma baza ta taɓa bari ya suɓuce mata ba, ko wane hanya sai tabi don mallakan sa.
Juyawa tayi ta nufi gidan da sauri, tana shiga ta wuce ɗakin su ta hau haɗa kayan ta cikin akwati
Umma da ta biyo bayan ta ta soma sababi, "gidan uban wa zata je?"
Bata saurare ta ba sai da ta haɗo kayan ta kafin ta juyo tana kumbura fuska tace, "Umma ki dena ma wannan haukan taki, zan je gidan su Yaya ABUL ne in Yi kwana biyu, sabida ina kewar sa matuƙa, idan har ban je kusa dashi ba na nuna masa ƙaunar da nake mishi, bazai taɓa gane wa ba, bazai taɓa gane zan iya ba da raina sabida shi ba, Umma ina tsananin ƙaunar Yaya ABUL KHAIRI, kuma wlh duk wanda yace zai shiga tsakani na dashi, na rantse da Allah sai naga bayan shi, ABUL KHAIRI nawa ne Ni kaɗai, kuma dole shi zan aura, tun wuri ma gwara ki bi abinda nake so". Tana gama faɗar haka tayi fuuuu ta wuce jaye da akwatin ta.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga mahaifiya ta Abar Alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma._ ❤️
*________________________________*
*PAGE 8*
*________* Su ABUL sun shigo gidan babu daɗe wa, itama Azeeza ta sauka daga keke napep ta shigo gidan, da sallaman ta ta isa parlour'n fuskarta cike da annashuwa
Mamy, Maimuna da Batool dake zaune a cikin parlour'n suka bi ta da kallo, sai kuma suka amsa mata sallaman a tare, yayinda Mamy ta ƙara da faɗin, "a'ah Azeeza ke ce a gidan na mu?"
Ƙarisowa Azeeza tayi ta zauna kusa da Batool tana amsa mata, sannan ta gaishe ta tana washe haƙora
Cikin fara'a Mamy ta amsa mata tana tambayar ta mutanen gidan
Tace, "suna lafiya". Tare da faɗin, "sun ce a gaishe ta".
Mamy murmushi tayi tace, "ina amsa wa, Azeeza kwana biyu shiru ko leƙo mu ba kya yi?".
Dariya Azeeza tayi tace, "ai Gwaggo gani na zo, sai kin gaji da gani na tunda da kayana na taho".
Itama Mamyn dariya tayi tana cewa, "ai kuwa kin kyauta wlh, Batool ku je da ita ta ajiye kayan nata a ɗakin ku, sai ki zo ki ci abinci".
Da sauri Azeeza ta tashi tana ɓashe baki, har tayi gaba kuma sai ta dawo tana sosa kai tana kallon Mamy tace, "Gwaggo wai ina Yaya ABUL ne?"
Mamy na murmushi tace, "yana ɗakin sa ai, halan baku haɗu bane da suka je gidan na ku?".
"Mun haɗu Gwaggo, bayan ma sai da nace ya jira Ni zan biyo su yaƙi, ya tafi abun sa".
"Allah Sarki be kyauta ba kuwa, amma zai fito zan yi mishi magana".
Ɓashe baki tayi tabi bayan Batool
Mamy ta raka ta da kallo a ranta tana me faɗa wa tunani.
Ita dai Maimuna kanzil bata ce ba, don ita ba shiri suke yi sosai da Azeeza ba, ko kaɗan jinin su be haɗu ba, ko Maimuna ta gaishe ta ba ta amsa mata, sai dai ta riƙa bin ta da harara, ta rasa mene ne ya jawo hakan
Koda su Azeezan suka dawo, Maimuna taje ta ɗibo mata abinci ta kawo mata, ta zauna gefen Mamy tana ci tana zuba mata surutu, dama ita gwana ce wajen iya surutu, sai dai hiran nata gaba ɗaya ya tafi kan ABUL KHAIRI ne
Ita dai Mamy ba ta cewa komi sai kallon ta da take yi tana murmusawa.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Sai da aka kira sallan la'asar sannan ABUL KHAIRI ya fito daga ɗakin sa
Lokacin har su Mamy sun tashi yin na su sallan, sai Azeeza dake zaune tana kallo tana ɓashe baki da ya zame mata jiki, ganin sa sai tayi saurin tashi tana faɗin, "Yaya.."
Wani kallo ya sakar mata da dole yasa tayi shiru, ta tsaya tana sosa kai, hanyar fita yayi ba tare da yace mata uffan ba, ko kaɗan a rayuwan sa ba ya ƙaunar yarinyan shi dai, jinin su be haɗu ba, tana da matuƙar rawan kai, ga ta ko kaɗan bata da class, duk da idan ka kalle ta tana da waye wa a ido, sannan tana da kyau matuƙa.
Azeeza tana kallon sa har ya fice, sai ta ja tsaki tana komawa ta zauna, a fili tace, "dani kake zancen, wlh sai ka so Ni ABUL KHAIRI, baka da wata mace da zaka aura sai Ni, mu zuba dani da kai yanzu aka so ma wasan".
Sai dai maganar nan duk a kunnen Mamy suka faɗa, tsayawa tayi daga bakin ƙofan ta tayi shiru tana kallon Azeeza da bata san ma tana wajen ba, sai kuma ta juya cike da sanyin jiki ta koma ɗaki, a bakin gado ta zauna tana buga tagumi ta hau tunani, maganganun Azeezan ne kaɗai ke mata yawo a kwanya, kallo ɗaya idan kayi mata zaka san hankalin ta ba ya jikin ta, ta jima a wannan yanayin kafin ta ɗauki wayan ta dake ajiye kan drowern gado ta hau latsawa, Numban ƙanwar ta Ummu ta soma lalubo wa.
▪️▪️▪️
ABUL KHAIRI tare suka shigo gidan da Abba, shima dawowar sa kenan fitan da yayi zuwa dubo kayan da aka sauke masa, shi ne suka wuce masallaci a tare ba tare da ya shigo ba
Babu kowa a parlour'n sai t.v dake faman aiki, shi dai ABUL ɗakin sa ya wuce yana faman latsa wayan sa
Time ɗin ne su Batool suka fito daga ɗaki suna ma Abba, "sannu da zuwa."
Cike da fara'a ya amsa musu yana ɗaga Baby ya ɗauke ta
Ita kuma sai washe baki take yi tana masa nata, "sannu da zuwan."
Nan ya biye mata suna ta surutu yana tambayan ta su Kaka da yanda suka baro su
Labarin komi ta hau ba shi suna dariya.
Azeeza ce ta fito daga ɗaki itama, gaishe da Abba ta hau yi
"A'a Azeeza ce a gidan na mu? Ku ce muna da babban baƙuwa?"
Murmushi tayi tana amsa mishi
Sai da ya gama tambayar ta mutanen gida, kafin ya wuce ɗakin Mamy riƙe da hannun Baby da ya sauke ta.
Abba sallama yayi suka shiga cikin ɗakin
Dai-dai time ɗin da Mamy ta gama wayan ta, sauke wayan daga kunnen ta tayi ta'ajiye gefen gado tana amsa sallaman na sa, sannan tayi masa sannu da zuwa
A kan sofa ya zauna yana amsa mata, sannan ya kalli Baby dake zuba masa surutu tana ba sa labarin Exams ɗin su, yana mata murmushi
Mamy tace, "Abban su idan ka biye ta yarinyan nan baza ta barka ka huta ba, ba ta gajiya ko kaɗan da labarin school ɗin su".
Still Abba na murmushi yace, "ban da abinki ADDAN MU kin taɓa ganin sabon shiga ya gundura? Ki bar ta tayi abun ta, nan gaba ai baza ta yi ba idan ta saba".
Dariya Mamy tayi sabida jin sunan da ya kira ta da shi, ta san tunda ya kira ta da wannan sunan, to, tsokana yake jin yi, ita kuma tana son su tattauna magana me muhimmanci shiyasa baza ta biye masa ba, sai ta kalli Baby tace, "Auta na je ki Parlour wajen ƴan uwanki, zamu yi magana da Abban ki".
"To Mamy". Baby tafaɗa tana miƙe wa tayi waje da gudu.
Itama Mamy tashi tayi ta dawo kan kujeran kusa da Abba, sannan ta kalle shi tace, "Abban su magana zamu yi a kan Babana".
"To, ina jin ki ADDAN Mu, Allah yasa dai lafiya?".
Murmushi kawai tayi tana girgiza kanta, sai ta ɗan ja numfashi tace, "Abban su maganar shi da Maimuna ne nake son a tado shi yanzu".
Ɗan gyara zaman sa yayi yana sake kallon ta yace, "kamar ya fa? Ban fahimce ki ba?"
"Ya kamata ayi auren su a huta, ina ga zai fi, nima hankali na zai fi kwanciya, duk da har yanzu be sake nuna alamun ciwo ba, amma kuma ka san halin Baba na, ta yiwu jure wa yake yi, amma wlh yana son aure". Taƙarishe maganar da marairaice wa tamkar zata yi kuka
Murmusawa Abba yayi yace, "ban da abun ki Adda dama wa yace miki ba ya son aure tunda har ya isa? ba kya ganin hakan zamu shiga haƙƙin Maimuna ne? Ki duba fa ki gani yarinya ce ita, duka-duka nawa take? yanzu ne za su shiga ajin ƙarshe na Scondary".
"Na sani Abban su, nima ba wai na ce yanzu za'a yi auren ba, amma ina so a tsayar da ranan auren zuwa nan da shekara ɗayan, idan ta gama karatu sai a ɗaura auren, inyaso taci gaba a gidan ta, kuma wannan ba Shawara ta bane shawaran Ameera ce (tana nufin mahaifiyar Maimuna) kuma nima naga hakan ya fi, ka ga za su fi saka wa a ransu dole za su auri junan su, Ni dai ba na ƙaunar maganar nan ta tashi a banza Abban su, sabida take-taken Baba na ya nuna hakan ƙarara ba ya son Maimuna matsayin mata".
Still dai Abba murmushi ya sake yi, kafin ya riƙo hannayen ta duka biyun yace, "ki kwantar da hankalin ki matata, insha Allahu burin ku ke da ƴar uwan ki na son haɗa zumunci sai ya cika, ABUL KHAIRI yana jin maganar mu bazai taɓa watsa mana ƙasa a idanu ba, sannan ma ai Maimuna jinin sa ne, bazai taɓa ƙin ta ba, ki dena ma maganar nan kin ji? zan neme sa zuwa nan da kamar sati ɗaya tunda a time ɗin Maimuna sun gama Exams ɗin su, inyaso sai a sanar musu har ita domin tasan da maganar itama".
Yalwataccen murmushi Mamy ta saki, cike da farin ciki tace, "to hakan ma yayi, Allah dai ya dafa mana baki ɗaya".
"Ameen Matata, yanzu tashi mu koma Parlour mun bar yara su kaɗai kar suyi zaton wani abun muke yi".
Dariya ta sheƙe dashi tana bugun kafaɗan sa na hagu, tace, "kai Abban su kaji ka da wata iriyan magana, to me kake nufin za su zarga? Ko yau suka saba ganin mun ƙule a ɗaki?".
Ɗage giran sa ɗaya yayi yana dariya yace, "to ke ce fa don Allah da wani korar Autana don zamu yi magana, kuma ai su sun san mu ba tsofaffi bane, da sauran mu dai".
Mamy ta harare sa tace, "kana da kamar Baba na kace baka tsufa ba? Ga shi har ka kai ɗiya cikin ɗaki".
"To mutane nawa ne suka kai ɗiyoyi cikin ɗakin, amma ganin kansu suke yi tamkar yara ƴan shekara ashirin?"
"Haka ne, amma dai ban da kai, don su ma basu san inda kansu ke musu ciwo bane, sun ci zamanin su, sannan suna son su ci zamanin ƴaƴan su, nan gaba ma zamanin jikokin su za su ce zasu ci, Allah dai ya kyauta, yasa mufi ƙarfin zukatan mu".
"Ameen ameen ADDAN MU Deebizah".
Murmushi kaɗai tayi masa, ta miƙe tana nufan ƙofa
Shima tashi yayi yabi bayan ta suna sauya wani hira.
🌐🌐🌐
Da dare da suka zo kwanciya, Azeeza kan gadon Maimuna ta kwanta, (asali gadon Zee ne kafin tayi aure) don a cewar ta a kan gadon take son kwanciya yafi girma, shiyasa suna gama cin abinci, da ta tabbatar yaya ABUL ya shige ɗakin sa, itama sai ta miƙe ta shige tayi kwanciyar ta.
Su Batool basu taso ba sai da suka gama kallon su, Maimuna ta soma shigo wa ɗakin, nan tayi turus tana kallon Azeeza dake saman gadon ta tana faman kashe murya tana waya, tsayawa tayi tana kallon ta, sai kuma taja ƙafafuwan ta cike da sanyin jiki ta nufi gefen gadon, har ta ɗaga ƙafa zata haye, Azeeza ta tsayar da ita da hannu
Sai da ta kashe wayan kafin ta tashi zaune tana buga mata harara tace, "a gidan uban wa zaki kwanta ke kuma?"
Murya a sanyaye Maimuna tace,"zan kwanta a nan ne Aunty".
Dogon tsaki Azeeza taja tana sake banka mata harara tace, "dalla ware a nan, babu ƙatuwar da zan kwana da ita, gwara ma ki nemi wajen kwanan ki, don nima nan yayi min kaɗan idan zan samu ƙari ina so".
Kasa motsi Maimuna tayi a wajen
Azeeza koma wa tayi ta kwanta tana ɗaukan wayan ta, ta soma latse-latsen ta.
Lokacin ne Batool ta turo ƙofan ta shigo, sannan ta mayar ta rufe ta juyo tana kallon Maimuna dake tsaye, ta kasa motsa wa a inda take ɗin
"Lafiyan ki ke kuma kika tsaya a tsaye?"
Ɗago ido tayi ta kalli Batool ɗin, sai dai ta kasa cewa uffan
"Nima dai wlh duk ta ishe Ni a nan, tana ta tsotse min ruwan kai, ki tashi min a kai da Allah". Cewar Azeeza cike da taƙama
"A'a a kan me zata matsa miki a kai, ba gadon zata hau ba?" Batool tafaɗa tana ƙarisowa wajen
"Sai dai ta hau gadon ki amma ba nan ba, Ni kaɗai zan kwana ba na son a takura min".
Turo baki Batool tayi, sai kuma ta mayar da idanun ta kan Maimuna da har ta soma shimfiɗa zani a ƙasa zata kwanta, wafce zanin tayi tana jan tsaki tace, "kee dalla wuce can! wlh kina da kayan takaici, a ƙasan ne zaki kwana?"
Murmushi Maimuna kaɗai tayi mata bata ce komi ba
Cike da takaicin ta tace, "ki hayo gado na mu kwanta don wlh baza ki kwana a ƙasa ba". Daga haka Batool ɗin haye wa gado tayi ta bar ta a nan
Sai itama daga baya ta hayo gadon, tunda ta san ko tayi ninyan kwana a ƙasa Batool baza ta barta ba
Ita kuwa Batool sosai take takaicin halin Maimuna, wani zubin ji take yi tamkar ta maƙure ta sabida haƙurin ta yayi yawa, ko kaɗan in an cuce ta baza ta taɓa rama wa ba, "in ba iskanci ba ita Azeezan ina taga irin gadon a gidan su da zata ce za'a takura mata?". Dogon tsaki taja tana juya wa Maimuna baya.
Duk da Maimunan taji ta, kuma ta san ɗayan biyu ko da ita take yi, ko kuma da Azeeza, amma bata yi magana ba bare ta motsa, illa sake lafe wa da tayi tana lumshe idanu.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT *🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
𝙽𝚊 𝚜𝚊𝚍𝚊𝚞𝚔𝚊𝚛 𝚐𝚊 𝙼𝚊𝚑𝚊𝚒𝚏𝚒𝚢𝚊 𝚝𝚊 𝙰𝚋𝚊𝚛 𝙰𝚕𝚏𝚊𝚑𝚛𝚒 𝚗𝚊, 𝚞𝚠𝚊𝚝𝚊 𝚖𝚊𝚐𝚊𝚗𝚒𝚗 𝚔𝚞𝚔𝚊 𝚗𝚊, 𝙸 𝚕𝚘𝚟𝚎 𝚢𝚘𝚞 𝚜𝚘 𝚖𝚞𝚌𝚑 𝙼𝚘𝚖𝚖𝚊 ❤️
*________________________________*
*PAGE 9*
*________* Washe gari gaba ɗaya gidan watse wa suka yi suka bar Azeeza, tunda ita dama ba ta zuwa makaranta, tunda ta gama Secondary School ɗin ta ta'ajiye karatu a gefe.
Yau ma kamar kullum su Batool suka soma dawowa, Azeeza na ganin hakan ta shiga tayi wanka ta fito tayi musu sallama a kan, "zata je ta dawo". Ba ko ina ta zarce ba sai gidan su ƙawarta dake ƙasan layin, dama ta rabu da zuwa shiyasa ta shirya zuwa mata wuni tunda ta zo anguwan.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
Ƙarfe 09:00am. Ziyada suke da Lectures yau, sai dai koda ta shirya gidan su Rahina ta wuce ta ɗauko ta a motan ta, suna zuwa bakin titi tayi peacking suka zauna zaman jiran Saleem kamar yanda yace mata.
Suna nan a zaune suna hiran su Saleem ya ƙariso a motar sa, sai suka fito daga motan. gaisawa suka yi da Rahina cikin barkwanci suna tsokanar juna, sannan ya kalli Ziyada dake ta faman yauƙi yace, "Baby taho muje ko?"
Murmushi tayi masa tana masa fari da ido, kafin ta kalli Rahina tace,"Besty mun tafi, insha Allahu zuwa kafin a tashi zan dawo, sai ki wuce school ɗin da motan".
"Babu damuwa ƙawa ta". Rahina tafaɗa tana murmushi, kafin ta sanya hannu ta amshi keey ɗin motan, shiga motan tayi ta zauna tana kallon su ta mirror
Suna tsaye ne suna magana basu rigada sun ƙarisa inda Saleem ɗin yayi peacking ba
Wani irin murmushi Rahina tayi tana ɗaukan wayan ta ta hau ƙesta